When she got up in the kitchen she came out with a bag she is saying, "Ummi, Aisha let us go and lock the house door." At the same time she had baki wajen maimaita, "Kofar gida kuma?" She thought how hawaye suna zuba akan idanunta tace, "Ina so in gani daga nesa sallah da za'ayi Umma, inyi mata bankwana inyi mata kallon karshe a yayinda za'a wuce da ita gidanta na gaskiya. Amma idan ba zaku iya rakani ba, babu damuwa sai inje ni daya."
Before su yunkura har ta saka takalma ta fice suka bi bayanta tareda sauran kewayenta dake a dakin.
Hajiya Hakima dake zaune a parlour tana sanye da hijabinta na sallah wanda shine kadai take dashi, daga sallah sai zuwa gaisuwa take sakashi, tafi gane harkar yafa gyale akan kafada.
"Labiba Ina zakije kuma?" Ta tambaya.
Saidai Labiba bata tsaya ba ballantana ta samu zarafin bata amsa sai kawarta Aisha ce ta tsaya tana mata bayani.
Hajiya Hakima da neman hanyar batawa Labiba tace, "Sahun sallar gawar zataje?" Aisha ta cika da mamaki ganin tayi bayani tes amma matar tana neman juwa zancen, da alamar gajiya tace, "A'a gajiya daga nesa zata tsaya tana hangowa, tace tana sone taya barkwana da mamarta." Hajiya Hakima tace, "Yanzu so take sai ta saka an bude gawa a waje, kamar a kanta ne aka fara rasa uwa." Aisha ta cika da al'ajabi lallai makircin wannan matar ya cika makirci tabi bayansu tana fadin, "Ba haka nace ba, ba haka take nufi, maganar bude gawa a waje hankali kansa bazai dauka ba."
A bakin get Labiba ta tsaya tana hango komai yayinda hawaye suka wanke fuskarta tana ji tana gani suka wuce da Ummarta domin sadata da gidan na gaskiya, ta durkushe tareda fashewa da kuka, Aisha tana bata baki.
Saida tayi kuka mai isarta sannan ta mike suka koma ciki, ta takure a dakinta hawaye suna fita daga idanunta. Saida Aunty Salima kanwar Mama Saude da suka zo daga maiduguri ta malsa mata sannan ta amshi abinci taci, rabonta da abinci tun daren jiya kafin wannan bakar kaddara ta afka mata.
Tura abincin kawai takeyi tana jin dandanonsa kamar na magani.
At the gate, Alhaji Sadi is sitting answering greetings, wayarsa tayi tsuwwa ya zarota ya duba sunan H.D SOJA BOY ya bayyana baro-baro a farkon sakon tes message din, ya waro idanu waje yayinda zufa ta fara karyo mashi, ya mike da sauri ya bada uzuri ya zura takalma ya shiga cikin gidan yana tafiya kamar zai kifa, yabi ta kofar baya ya shiga dakinsa ya danna sakata sannan ya fiddo wayar ya bude sakon.
_H.D SOJA BOY ne yake magana, dama na fada mata akwai ramakon gayya wacce tafi ta gayya zafi, kayi wa budurwata da nike matukar so fyade har bakin ciki ya saka ta hadiyi zuciya ta mutu, yarinyar da na shirya shiryuwa inyi rayuwar sunna da ita, amma ka katse mata rayuwa ta mafi munin zalunci ka barmin tabo a zuciya wanda har in koma ga mahaliccina bazan manta dashi ba, torh da diyarka nan kwaya tal mafi soyuwa a gareka na aikata mata kwatankwacin abun da ka aikatawa Fatimatu, duk da dai ban ji bakin ciki da damuwata ya ragu ba amma a hakan ma babu faduwa tunda nayi nasar sakaka a irin halin