Showing 9001 words to 12000 words out of 124388 words
duba amma bata ga number da aka kirata ba, taji babu dadi dan
bata so yaga kamar tana sane ta bayar aka daga wayar tasa. Ko da tafiyar su ba zatayi daya
ba, ba zata so yaji a ransa dan yana lacking wani abu bane shiyasa hakan ta faru. Kwantar da
kanta tayi a saman hannun kujerar ta rufe idon ta tana tariyo zuwan da yayi wajenta, akwai wani
abu me girma a muryar sa sai kuma abu daya da ya tsaya mata shine kamshin turaren da taji
yana yi, wanda yayi kama da me tsada ne irin ajin farko, domin Allah ya hore mata kaunar
kamshi, shiyasa ta kan yi saurin ganewa. Sai dai akwai irin tuurare yan durin nan da suke da
kamshi me dadi har ka kasa tantance su, kila irin su ne, abunda ya kara burgeta dashi kenan,
duk da yana cikin yanayin da zaka ce kai tsaye babu, amma be bar kansa a wulakance ba.
Juya kanta tayi daya gefen ta dora wayar a saman cinyarta ta cigaba da tunani.
***Kiran sallar magriba ya sashi fita daga sashen nasa zuwa masallaci, achan yayi alwala ya
shiga sahun farko sukayi sallar. Bubu na ganin shi yaji dadi sosai. Bayan an idar ya wuce
bangaren nasa domin ya jira shi, yana zaune sai gashi ko ya shigo, ya tashi tsaye har sai da ya
zauna sannan ya zauna shima a k'asa cikin girmamawa ya sake gaishe shi, ya amsa masa
sake yana nazarin sa.
"Muhammadu!" Ya kira sunan sa, gyara zaman sa yayi ya tattara hankalin sa waje daya cikin
son ganin be yi wani abu a gaban Bubun ba
"Kana ji na Muhammad?"
"Inaji Bubu."
"Madallah, Muhammad ka san dai a tsarin gidan nan kana cikin lokacin da ya kamata ace ka
ajiye iyalin ka kaima, ka nutsu waje daya a kalla hakan zai taimaka maka wajen cikar
kamalarka."
Kansa a kasa yana jin Bubun yayi ta bayani yana gida kansa cike da gamsuwa,
**A kofar ta tsaya tana kallon takalmin Muhammad din dake zube a wajen, ta samu labarin
zuwan sa a wajen Kamal amma bata tsammaci irin wannan ganawar da Maimartaba ba,
shiyasa ta kasa hakuri tazo ta nemi iso wajen Maimartaba din wajen sarkin kofa amma sai ya
nuna mata ba zai yiwu ba, domin an gargade shi akan barin kowa ya shiga shashen
maimartaba din har sai ya kammala ganawar sa da Muhammad din, ranta a matukar bace ta
koma sashen ta tana jin wani irin tashin hankali, tana tsoron kar Muhammad din ya amsa tayin
mahaifin nasa a wannan zaman da zasuyi.
Safa da Marwa tayi tayi, har wajen sallar isha basu fito ba, tana hangen bangaren ta cikin
nata shashen, ta kasa zama tana da yakinin ko menene suke tattaunawa haka me muhimmanci
ne sosai.
Tana tsaye jikin window taga fitowar su, fuskar Muhammad din a sake yana takewa mahaifin
nasa baya. Tsaki taja ta saki labulen tana juyawa zuwa gefen gadon ta, ta zauna tana sake jan
wani tsakin, tsakin haushin Muhammad din da ya zame mata ciwon ido shi da mahaifiyar sa.
"Ranki ya dade, Maimartaba ya aiko yana da bukatar ganin ki bayan ya dawo sallar isha'i."
Bata amsa ba, sai ma juya fuskar ta da tayi wani sashen tana sake sakin siririn tsaki.
***Bangaren sa ya koma, ya tattaro abunda ya san zai bukata ya fito, sai kuma ya tuna da
maganar Maimartaba ta karshe da suka tattauna, yana son ganin sa da safe kafin ya fito fad'a,
komawa yayi ba dan yaso ba, ya ajiye komai ya zauna yana kirga lokacin zuwa wayewar gari.
Nisan yayi yawan da yake jin kamar yayi loosing idan har ya kyale shi tsawon wannan lokacin. Wayar sa dake ajiye a gefen sa ta dauki sowwa, ya daga ganin kiran da yake ta jira ne tun
dazu,
"Oga na duba maka number din, akwai bayanan sa da komai har da wajen aikin sa, hoton sa da
kuma location dinsa a yanxu, na tura maka ta mail sai ka duba."
"Ok! Thank you, zan neme ka. "
Ya katse kiran ya shiga mail dinsa, ya hau kan message din ya bud'e. Hoton sa ya bud'e yayi
zooming sosai, sai kuma ya fita ya karanta information din. Karamin tsaki yaja ya ajiye wayar
yana jin a ransa wannan din karamin kwaro ne be kamata ya hana shi walwalar sa ba, abu daya
zai masa ya kama shi a hannun sa, sai dai ba zai hakan ba har sai ya je ya tabbatar da zargin
sa.
***Anan sashen Gajin ta shirya, ta wuce islamiyya tana tafe tana satar kallon hanyar ko zata
ganshi tunda yace mata yana zama ne domin yaga wucewar ta, har ta isa makarantar bata ga
ko me kama dashi ba, sai kawai ta share tayi abinda ya kaita. A dawowa ma haka ta sake yi
shima bata ga kowa ba, ta dawo gida ta chanja kayan ta kenan aka shigo aka ce tazo inji
Muhammad, Hijab ta dora a saman kayan jikinta ta fito. A tsaye yau ma ta hange shi wajen
kujerar, ya rataye hannayen sa a bayan sa yana tsaye kyam akan kafafun sa.
"Assalamu alaikum." Tayi masa sallama tana jan kujerar.
"Sannu da zuwa, nan akwai rana bari na saka maka a chan." Taja kujerar zuwa k'asan wata yar
bishiya ta ajiye,
" Bismillah." Tace masa tana nuna masa kujerar, be zauna ba, ya zaro hannun sa daga bayan
sa, ya dawo dasu gaba ya rungume su a kirjin sa,
" Bismillah." Ya nuna mata kujerar da baki
" Zauna babu matsala." Yace mata
" A ah dan Allah ka zauna, be kamata na zauna kana tsaye ba, ance bakon ka..."
" Kyale fadar hausawan nan, zauna dan Allah."
Allah da taji ya ambata yasa ta zauna a kunyace, ya zura mata ido har sai da ta dan ji wani iri.
" Na cika kallo ko? Kiyi hakuri." Yace mata yana murmushi,kallon ta kadai yayi jin sa yake
kamar yafi kowa sa'a a duniya
" Ba komai." Tace tana gyara wayar hannun ta
" Ina wuni?" Ta gaishe shi yana dan zamowa
" Lafiya lou, sai kika jini shiru, tafiya nayi zuwa kauye Baba ya kira ni, naso ma na zo kafin na
wuce toh tafiyar ce tazo a gaggauce, sauka ta kenan ma."
" Allah sarki... Allah yasa lafiya."
" Lafiya lou, sai godiya. "
" Ka baro su lafiya?"
" Alhamdulillah. Nagode da kulawa."
" Ba komai." Tace tana wasa da hannun ta.
Turo gate din akayi, Habeeb na gaba yana bin sa a baya, wani irin daukewa yaji ganin sa na
neman yi. Iman zaune tare da wani suna hira, a cikin gidan kuma? Be san sanda ya isa wajen
ba, sai ganin mutum sukayi a gaban su.
Wani kallo Moh yayi masa, yayi murmushi yana taune gefen lips dinsa na kasa
"Yaya sannu da zuwa." Yace yana mika masa hannu, kin bashi hannu Khalil yayi, sai Habeeb
ne suka gaisa, ya daki kafadar Khalil din
" Muje ko?"
" Yi gaba ina zuwa." Yace masa,
"Ok." Ya wuce ya bar Khalil din a tsaye
" Iman shiga gida." Yace a gadarance, ta dago ta kalle shi da sauri, ya hade girar sama data
k'asa tamau irin ba wasa din nan.
"My heart, ki shiga gida ki huta dama naji ba zan iya zuwa gida ban zo na ganki ba, shiyasa na
taho nan kai tsaye, zan kira ki anjima ki ajiye waya a kusa dake kinji?"
Kunya ce ta kamata ta noke, ta mike da k'yar tace
"Ka gaida gida." Sannan ta wuce ciki, tana barin wajen ya hade fuskar sa sosai.
" Da tsakar ranar nan ka taso yarinya, kazo zaka ishe ta da uban surutu, ku dama talakawa
haka kuke, da kunga yar hanya sai kuzo kuce kuna so, kai kanka kasan ba sa'ar ka bace, ba
sa'ar auren ka bace shishigi dai, toh ita din matata ce, ni zan aureta an gama magana, sai kaja
tsumman kafafunka a koma in da aka fito, ka samu daidai da kai."
" Zaka ga tasirin talaka da talauci kuwa, baka da ikon tsarawa kowa rayuwa, haka arziki ba wani
abu bane face fitina, wadatar zuciya itace mutum..." Ya dan matso gaban sa
" Mark my word, a gaban idon ka, right under your noses, talaka zai baka mamaki, mamakiin da
har ka kare rayuwar ka zaka fita daga cikin sa ba, count down dinka ya fara daga yanzu."
" 1,2,3!" Sai na jika.
Ya juya ya fice daga gidan cikin takun da ya tsayawa Khalil a rai, cikin wani irin yanayi yayi cikin
gidan yana jin yanzu ba sai anjima ba, zai yi abinda ya dace, gida be koshi ba, babu yadda za'a
yi a bawa dawa.
**A tsaye ya tarar da Habib yana ganin shi yace
"Kaiko me ka tsaya yi ina ta jiran ka."
"Abinda ka kasa yi, kana ganin kanwar ka da mutum a tsaye, kana ganin sa kaga mara gaskiya,
wa ya sani ma ko dan boko haram ne da wannan uban kasumbar, amma baka damu ba kayi
tafiyar ka, hakan ba daidai bane."
Kallon sa Habib yayi, mamaki na kamashi,
" Yaushe hakan ya zama ba daidai ba khalil?"
" Habib, maganar gaskiya ina son Iman, son da ni kaina bansan adadin sa ba, zan iya komai
akan na sameta, dan haka ba zan iya jure ganin ta da kowa ba, musamman mutum irin wannan
da ya nuna alamun rashin gaskiya, gashi fakiri jibi shigar jikin sa, no ba zan iya ba, rakani wajen
Gaji ayita ta kare."
" Idan har kai din jinina ne, idan har na isa da kai babu kai babu Iman Khalil, na rasa kafiya irin
taka, na rasa dagiya irin taka, bayan maganar nan mun dade da gama ta, na gaya maka ba zai
taba yiwuwa ba."
" Akan me? Dan Allah Anty ki gaya min hujja me karfi a musulunci da ya haramta min auren ta,
na daya ni ba muharraminta bane tunda ita din ba ke kika haife ta ba, toh sai menene? Akan
dalili mara tushe?"
" Akan duk abinda zaka kira shi Khalil ka kirashi, amma idan har ina numfashi ba zamu hada jini
ba wallahi, ga mata nan bila adadin, me yasa sai ita, wannan da yazo shi ya dace da ita, shine
daidai da matsayin ta, inaso auren da zatayi ya zama sakayyar aure min miji da uwarta tayi, ta
saka yayana samun yan Uba!."
" Ohh shit! Kin kasa fuskanta ta Anty, kiyi hakuri wannan karon zabin raina zan bi, zanje na
samu Gaji na sanar da ita, gwara kowa ya sani a san me yakamata ayi."
" Khalil!"
Ta k'wala masa kira, ya juya da sauri yayi hanyar fita, wayar sa tayi kara, ya tsaya chak jin layin
da yake ajiye numbers din manyan mutanen sa ne, ciro wayar yayi sunan Sir ya bayyana a
wayar, ya daga da sauri yana daidaita numfashin sa
" Kana ji Ibrahim? Sako ne daga sama ba daga ni bane, an dakatar da kai aiki zuwa wani lokaci,
za'a neme ka idan bukatar hakan ta taso." Be jira yace komai ba , ya katse kiran. Da sauri ya
dafe bangon da yake kusa dan ji yayi jiri na neman kadashi, gaba daya rayuwar sa akan aikin ta
dogara, yana da passion sosai a Kai sannan yana iyakar kokarin sa wajen aikin sa, maganar
promotion dinsa ma ake idan har ya kammala wannan assignment din da ya kawo shi Kano,
shikenan sai dakatarwa haka nan ba wani dalili?
" Ya akayi?! Habib ya matso ya taba shi ganin kamar ya shiga coma
🔥🔥🔥🔥🔥
*_LAST BONANZA_*
*_farincinku shine namu,ZAFAFAN DAI,sun sake amsa kokenku,sun sake rage muku kaso 20
cikin 100_*
*_Daga yau 29 ga wata,har zuwa 31 ga watan nan,xaku iya biyan 800 a amadadin 1000 na
kudin litattafai biyar_*
*_za'a fara posting in sha Allah 1st January da yardar Allah_*
*HANZARTA KI BIYA NAKI KAFIN RANAKUN SU QARE*
*XAKI BIYA TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
SAIKU TURA SHAIDAR BIYA
08184017082
GA MASU TURA KATIN WAYA KO KUMA VTU,SAIKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR
BIYANKU
09134848107
1/2/22, 22:47 - Buhainat: *HALIN GIRMA*
 6
*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*Â
_ASSALAMU ALAIKUM BEAUTIFUL PEOPLE!! ZAFAFA BIYAR
FAMILY💯💯🙌���_
_MUNGODE DA ZABIN LITTAFAN ZAFAFA BIYAR. ALLAH YA KARA BUDI YA KUMA BAR
ZUMUNCI_
_KAMAR KO DA YAUSHE, WANNAN KARON MA MUNZO DA KOKON BARAR YOUTUBE
CHANNEL DIN YARON MU, SUDEIS MASOYI KUMA MAKARANCI, MAHADDACIN
ALKUR’ANI MA GIRMA_
_WANNAN KARON MA DAN ALLAH A TEMAKA ADANNA WA CHANNEL DINSA KARARRWA
DOMIN KASANCEWA DA MU A DUK SANDA MUKA DORA FEFAN BIDIYON SA, A TALLAFA
A KALLA A KUMA DANNA MASA SUBSCRIPTION. HAKAN NA KARAWA SUDEIS KWARIN
GWIWAR SAKE DAGEWA YA KUMA KARA KAIMI WAJEN YIN KARATUN SOSAI. MUNGODE
KWARAI💯🙌���_
_GA CHANNEL DIN DAKE YOUTUBE NAN👇�_
https://youtube.com/c/sudaiskura
_Sudais is a young boy who has passion in recitation of the Holy Qur'an at a very young age._
_Please help him grow his YouTube channel by subscribing and liking his videos to encourage
the little boy. Jazakumullahu khairan��_
***
Girgiza kai ya hau yi da sauri da sauri.
"Habib aiki na, innalillah wa inna ilaihi rajiun."
"Me ya samu aikin naka?" Mama ta matso da sauri tana rik'e shi
"Wai sun dakatar dani, babu wani kwakkwaran bayani kawai wai daga sama ne."
"Innalillah wa inna ilaihi rajiun, zo ka zauna, rik'e shi Habib ya zauna."
Zaunar dashi Habib yayi, yayi saurin dauko masa ruwa ya mik'a masa
"Sha ko zaka ji sauki a zuciyar ka, ba wani abu bane babba in sha Allah, wata yar matsala ce
zasu gyara da yardar Allah."
Jujjuya kansa yake ya kasa magana, shi kadai yasan hakan me yake nufi, shi kadai yasan
yadda yake ji a halin yanzu, tabbas idan suka hana mishi aikin nan sun yi masifar cutar sa, akan
me? Me yayi haka da ya chanchanci wannan hukuncin? Bayan irin kokarin da yake ganin ya
rik'e aikin sa, tsawon lokacin da ya dauka kafin ya samu aikin, da irin wahalar da yasha kafin ya
kawo matsayin da yake, sai yanzu? Daga sama ta ka kawai ace an dakatar dashi? Innalillah wa
inna ilaihi rajiun. Ya sake maimaitawa.
"Kalle ni nan Khalil, karka ce zaka daga hankalin ka akan abinda kasan baka da iko dashi, kayi
hakuri ka kwantar da hankalin ka, in sha Allah ba wata matsala bace, kaji?"
Gid'a mata kai yayi kamar karamin yaro, ya kwantar da kansa yana jin kamar ya zubar da
hawaye saboda bacin rai. Shiru sukayi kowa yana jimamin abinda ya faru, ya ma manta da
abinda yake shirin aikatawa. Shigowa Zeenat tayi dauke da wasu manyan ledoji,uwar ta bita da
kallo bata ce komai ba.
"Daga ina kike?" Habib yace yana bin hannun ta da kallo
"Bashir ne yazo."
Kallon Mama yayi, yaga ta dauke kanta
"Mama fa Bashir din nan naji wasu maganganu akan sa marasa dadi, ya kamata a duba sosai
kafin a barta tana fita wajen sa."
"Bana son maganar nan yanzu, dame zamu ji? Da abinda ya faru da Khalil din ko da naka
zancen?"
Tsuke bakin sa yayi be sake cewa komai ba, ya tashi ya bar falon ma,
"Me ya samu Uncle Khaly din Mama?"
"Babu komai, ki wuce ki bani waje uwar yan magana."
Da sauri tayi gaba da ledojin ta, ta shige dakin uwar ta rakata da kallo kafin ta sauke ajiyar
zuciya tana tuna abinda ya faru daren jiya ita da Abban su.
***
"Ya ake ciki da yaran nan?"
"Name fa?"
"Akan maganar yaran da suke zuwa wajen su, Yaya yayi min magana akai yace ya kamata
asan abinda ake ciki, kindai san tsarin gidan nan ba'a wani daukar dogon lokaci ana zance."
"Eh toh, ita Iman akwai wani wanda yazo."
"Zuwan sa biyu kamar ko?"
"Ashe ka sani?"
"Eh ina sane da komai ai, kinga alamun zasu dai-dai ta ne? Naga zuwan nasa biyu dududu."
"Toh idan bashi ba waye? Babu kowa ai."
"Khalil din fa?" Yace yana mata kallon mamaki
"Wai Dr bar maganar Khalil din nan, ba da gaske yake ba wallahi."
"Ana wasa a maganar aure ne Hajara?"
"Shi dai yayi, gwara a tsayar da magana akan wanda yazo din dan da alama ba da wasa yazo
ba."
"Toh shikenan, Zeenatu fa?"
"Eh ita ai Bashir ne dama."
Tashi yayi tsaye yana girgiza kansa
"Ban yarda ba sam, ban amince da yaron ba, binciken da nayi akansa be min dadi ba, kamar
ance min ma kuma yana da mata duk da hakan ba zai hana a bashi aure ba, sai dai na samu
labarin bashi da hali me kyau gaskiya, a wani labarin ma ance min har zaman prison yayi, sai ki
fad'a mata nace banda Bashir ta kawo wani."
Hankalin ta a tashe tace
" Amma baka ganin sharri akayi masa? Don a hana a bashi?"
" Akan me za'a masa sharri? Akan wanne dalili kenan?"
Ya tsare ta da idanun sa, sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, tsoron yadda za'a kwashe
da Zeenat din take domin ta san yadda ta saka Bashir din a ranta, gashi babu laifi yana mata
hidima sosai, hakan ya saka Maman sake yarda dashi