Showing 27001 words to 30000 words out of 32509 words

Chapter 10 - DUTSEN CIKIN RUWA

yafaru yanadaka gurin k'ofar shiga _Complex_ in yana hangosu,"dukda baiga
fuskartaba, hakan datai musu yanuna tanasan sukasance cikin tarbiya, ba kwad'ayi dasan abin
duniya ba.

Kayan dayasimusu suka bari, yazo yad'ibesu amotarshi yasa, yabar gurin shima ko siyayyar
dayazoyi baiyiba. Direct gida yawuce.
Mahaifiyarsu dasuke kira da Umma, tana zaune littafin *Garkuwar Musulmi* ne a
hannunta tana dubawa, da Sallama yashiga falon. Ganinshi tai d'auke da kaya. "Sannu da gida
Umma" yace tareda zama. Ummantasa tadubeshi da kulawa tace "Harka dawo ashema ba
jimawa zakaiba, afitarba?" Ajiyar zuciya yasauke yace "Ah Umma d'an akasi akasamu a inda naje.
Anan yakwashe komai yagayamata, dan itace abokiyar shawararsa tun yana k'arami, shi ko
yawan abokanai bashida su. Ummansa itace kominsa, har _recording_in surutun di Hassan da
Husna yakunna mata taji, na dariya tayi na tausayi ta jimanta, yad'ora dacewa "Shifa gaskiya
seya bisu yakai musu kayan" yashige d'akinsa. Umman tasu tabishi da kallo aranta tana
Addu'ar Allah yabashi mata tagari dazata kuladashi. Shima yai Auren koya dad'a samun
nutsuwa arayuwarsa.


Arc Sulaiman Tajuddin Kazaure shine sunansa. Mahaifinsa Alh Tajuddin Hafiz Kaxaure da
mahaifiyarsu Hajiya Maryama. Asalinsu 'yan jihar Jigawane, Aurensu tunna Saurayi da
Budurwa, Allah ya albarkacesu da 'ya'ya Hudu duk Maza, Muhammad Kabir shine Babba
Barister ne mai zaman kansa, suna zaune a Abuja tareda Matarsa Farha da 'yayansu uku. K'aninsa Tasi'u shima da iyalansa su suna zaune a Kazauren inda yake aiki. Mebimsa
Yusuf dabai dad'e da Aureba yatafi da Amaryarsa can Bony a Phorthacoat inda yasamu Aiki.

K'araminsu shine Sulaiman matashi dabai haura shekara 30 ba, Archtecturing yakaranta a
Jami'ar ```Kano University of Science and Technology dake Wudil ```A Kano . Zane zane da
Allah yabashi baiwa da fasaha akan haka, Taswirar Gidaje da Ma'aikatu har mutane ma,

yamaida kai sosai akan harkar tasa. Allah kuwa yasamai Nasibi acikinta. Hayarsa ake d'auka
gari-gari wani sa'in har wasu K'asashe . K'ark'ashin kamfaninsu mai suna _"The Shariff
Construction"_.

Suna zaune a D'an Agundi G.R.A, dake Zoo road, sakamakon Aiki dayada da Mahaifinsu
Ma'aikatar Ruwa ta Hadeja-Jam'are, reshen jihar Kano.

Hajiya Maryama mace ce mai tsafta, kawaici dasanin yakamata, uwa uba rik'o da Addini. Ga
zumincin 'yan uwa nakusa dana nesa, duk ta d'ora 'ya'yanta akan
turbar hakan.
Allah baibata haihuwa dayawaba, shiyasa takeso Sulaimanu in yai Aure yazauma kusa da
ita. Kota rik'a ganin 'yan kufi-kufi akusada ita. Duk sauran 'ya'yannata da iyalansu sunmata nisa.

Wannan kenan.

Naja'atu dasuka koma gida ko kayan data siyo bata idasa ajewaba, takamo 'yan biyun nata
Hassan da Husna "Kneel down & close your eyes" tace tana zare idanu. Bashiri sukayi atsorace
bawanda yace uffan.
Harta gama jera kayayyakin, ta adana komai inda yadace. Abinci tazubo dantaci, kasa cin
abincin tai, dan tasaba yanzu tare dasu takecin Abincin. Abunka da Uwa da d'a tausayinsu
yatasomata, janyosu tai duka tarungumesu tsam ajikinta kamar za'a k'wace matasu.

Hak'uri suka bawa Mamyn tasu, taja musu warning sosai, suka fara cin Abincinsu cikeda ladabi
dan duk takoyar dasu Ladubban ci dasha:-
*Kaci da hannun dama*
*kaci da Bismillah*
*kaci Abinda ke gabanka*
*kada kai Numfashi acikin kofi/k'waryar ruwan*
*kada kashafi band'aki da hannunka*
Ire irensu da neman yafiya yayinda kaima mutum badedaiba. Duk takoyardasu.
Bayan sungama cin Abincin, aka hau labarai anan taji labarin Uncle mai zane daduk yadda
sukai dashi. Taita dariya kuwa, toilet tanufa dan haramar Sallar Magriba.


Sulaiman tunaninsu duk ya addabi kwanya da zuciyarsa, ranar da wuri yashige d'aki bayan yaci
Abinci. _Recording_ na surutunsu dayayi yazame masa abokin hira alokacin, tunani yai tayi
koyaje yakaimusu kayan gida? To maizaice, gurinwa yazo? Tambayoyin dasuka dami zuciyarsa
kenan. Cikin lokaci k'ank'ani yabi yatakura kansa, zaman hira dasuke da Umman tasu yarage,
bashida aiki se saurara _Recording_ insu kusan ya haddaceshi har zanasu yai yadda yagansu.
Yakumayi wani haddashi. Yaita kallan zanen hoton.

Ummantasu ganin haka tafara mai zancen yai Aure koya samu nasa Iyalin. Secemata yai

"Lokaci nayi zaiyi tacigaba damasa Addu'a.



© *Aneesa_didi*🍼🍉�
[2/18, 10:50 AM] +234 703 962 5239: *♡DUTSEN CIKIN RUWA.....♡*
*Na*
*Haleema G Khaleel*

*91*

~~~K'arshe shawarar da Umman tabashi, yaje yakai musu kayan, koya samu ganinsu yaji
sassauci da rangwame.
Number wayar daya rik'eta akansa kamar karatu, wadda baisan tak'amaimai tawaye cikin
wanda suka lissafo maiba, ya rubutata cikin tasa wayar. Yai jimm, yakira koya je harcan gidan?
To inyaje, yace gurinwa yazo? Cin biyun dole yai d'aya. Kiran wayar yashiga yi.

Naja'atu zaune akan k'aramin cushing, Hafsa k'awarta data kamata ziyara tana mata Oiling
agashinta,mai tsayi da santsi, Husna nagefanta tana bacci. Hassan kuwa wasansa yaketayi,
dan intana gida duk inda tasa k'afa suna gurin. Intatafi School kuma suna gurin Inna, harta
dawo. Wayarta tashiga ruri, ganin bak'uwar Lamba harta katse bata d'agaba, yakuma kira har sau
uku, akaro nahud'u ne Hafsa tadubeta tace "Haba my K'awa ki amsa mana, inkuma kink'i ni
mik'on wayar nad'aga, wayasan ko sabon Miji muka samu".
Naja'atu dai batace komai ba tad'aga wayar.
"Peac be upon you, danAllah ahad'ani da friends ina, Hassan da Husna. Inason jin lafiyarsu,
nakasa sukuni, since the time i was meet them, am feeling like they are my Kids". Yashiru yaji
maizata ce.
Itakuwa _Husky Voice_ insa taji amonta har tsakar kanta, kalamansa nak'arshe sun ta6a
zuciyarta, basan sanda tace "Kaine Uncle mai Zane da ake tamun surutunta?"
Murmusawa yai kamar yana gabanta yace.
"Nine Arc Sulaiman T Kazaure, Uncle mai Zane,i hope bazaki hanani jin muryar Yaranaba?"
"Gasu"
Tace tamik'awa Hassan wayar. "Hassan ga Uncle mai Zane".
Da murnarsa yakar6i wayar suka hau surutu kuwa hartaji yafad'a masa "Husna tayi Bacci".
Labari Naja'atu suka shiga itada Hafsat, dukda tunaninta yatafi gurin wayar da Hassan suke.
Hassan yamik'o mata wayar tasa akunnanta.
"Please Mamynmu abani Permision nazo naga yarana?"
Dariya tai tace
"Anbaka"
Batasan miyasaba tun kafin suhad'u taji yakwwanta mata, kodan yanasan 'ya'yantane.
Sallama sukai duk sun murmushi, suka aje wayar.

Yammacin ranar kuwa, segashi yazo dukda bata fito ba, yaji dad'in ganin yaran dayazo
sabidasu.
Sukai tasurutu yana biye musu harda hotuna. Kayayyakin daya siya musu suka bari yabasu,
hadda k'arin zanensu dayai Manya, sukad'ai dawanda yahad'a harshi. Seda yaga shigewarsu
gidan shima yatafi.

Kayan suke ta duddubawa, idanuwanta sukai tozali da kyakyawan bahaushe d'an mutan
Kazaure, kan Zanen dayai musu, Hoton taji yashi Zuciyarta, taita shafar fuskarsu.

Duk abinda take da yanayin datashiga, a idan Inna, Murmushi tai irin nasu na manya, zataga
iya gudun ruwansu duka.

Yawan wayar dasukeyi da sulaiman, yafakaice dayiwa Hassan da Husan waya. Abin
yashigesu sosai, har takai ga in ba ai wayar ba basa jin dad'i, banda sak'onni dasuke turawa
junansu. dukda basu had'u ba. *Soyayya da Shak'uwa*(littafin my xoxo) tashiga Zuk'atansu.
Naja'atu gani take sabida yanasan 'Ya'yanta, shima yasamu gurbi aZuciyarta.

Sungama waya da Yaran dadaddare, yace
"Subawa Mamynsu"
Mik'a mata wayar sukai, sukatafi kallan Cartoon da Deedat yakunna.
Cikin wata iriyar murya dabata sabajin yayi irintaba a shagwa6ance yace.
"Mamyta!"
Har cikin jikinta da kanta taji amon furucin, kamar shikad'ai yafi kowa iya Ambatar sunan.
Akasalance ta amsa da "Na'am Uncle yaukuma nima nazama taka?"
Kamar yana ganinta yai murmushi tareda fad'in "Zanso hakan Mamyta"
Rintse idanu tai, besam yadda kalamun ambaton sunanta da yake lugwigwita Tanderun
zuciyartaba, daya tausaya yak'i ambaton sunan.
Yakuma cewa
"Please kibani dama nanuna miki hakan, bakida matsala dani, in short kiji labarina. Yad'an
gaya mata ```Biographynsa```," yakashe wayar yabatta da tunani.

Nannauyar ajiyar zuciya tayi tasan za'ai haka dama.



© *Aneesa_Didi*🍼🍉�
[2/18, 10:50 AM] +234 703 962 5239: *♡DUTSEN CIKIN RUWA.....♡*
*Na*
*Haleema G Khaleel*


*92-93*

~~~Bata 6oyewa Inna komai akan saba, yadda yagayamata, Innartamusu fatan alkairy da za6in
Ubangiji.

To 6angaren Sulaiman yagayawa Ummansa yasamu Mata, amma Bazawarace hadda 'Ya'ya
biyu, Umman tai shiru kamar bazatai maganaba.
"To amma ita yarinyar tana sanka?"
Murmushi yai yace
"Batada matsala Ummana ki amince tazama Surukarki, Matar d'anki, dazata bawa Autanki
cikakkiyar kulawa."
Umman tadubeshi tareda cewa "to Allah yatabbatar da Alkairi."
Rungumeta yai yace "ina sanki Ummana, Nagode Nagode yabata peack agoshi."

Dariya Umman tahauyi, tana hango yadda Matar dazata Auri Sulaimanunta zatai d'awainiya
dashi, da shagwa6a dukda ya girma befasaba.
Sukaita hirarrakinsu kafin akirashi awaya yafice daga Gidan.

Fad'uwar da gabanta yake ya tsananta aranar, tunda Sulaiman(Uncle mai Zane) yace mata
zaizo.
Simple makeup tayi, ita kanta kwalliyarma takwan biyu bataiba. Less _Mint Blue_ tasa riga da
skirt tai d'aurinta daidai da zamani, spray tasa kad'an da turarenta _Urban Woman_ ta d'ora
babban gyale akan kayan. Jelolinta Hassan da Husna suna gefanta suma sunsha ado. Sun
nutsu kamar basuba kar ace kartace bazata fita dasuba. Ta dubesu tai murmushi.
Wayarta tashiga Sauti, Hassan dasaurinsa ya mik'a mata, ganin sunan "Uncle Sman" a Screen
d'in wayarta, dan haka tai _saving_. Samun kanta tai da rikicewa kaman bata ta6a tsayawa da
namijiba. Seda takai zuciyarta nesa tad'aga wayar. Cikin sassanyar muryatta, ya amsa tareda
langa6ar dakai "Ran Gimbiya yadad'e, fatan nasameku lafiya?"yafad'a kamar yana gabanta. Murmushi takumayi, suka gaisa yasanarmata dagashi ya iso, tasa aimasa iso. Seda tai jim
sannan takashe wayan.

Innarsu tasanarwa take tasa Fawad yashigo dashi falon bak'i na Babansu, Ruwa tabayar aka
kaimasa da leman d'anyar citta, daya d'au sanyi dai-dai sha had'eda Meat-pie.
Akunyace tacewa Inna bari taje, tabita da Murmushi tanaimata Addu'ar samun Alkairy.

Zaune yake d'aya daka cikin Kujerun falon, wadda take fuskantar k'ofar shigowa, yanata
danna wayarsa. Sassanya kuma Zazzak'ar Muryatta datai masa Sallama tasashi d'agowa, ya
amsa idanunsa akanta, sanda ta d'ago itama idanunsu suka had'u, dukkansu saida wani bak'on
al'amari ya tsirga musu, itatai saurin d'auke idanunta ta sunkuyar dakanta.
Tana guri guda daka can gefe tazauna, su Hassan da Husna suka gaidashi kowa ya mak'ale
agefan kafafun "Uncle mai Zane" injisu da fad'a.
Naja'atuma ta d'ago kai tareda rusunawa tagaidashi "Barka da Yamma" muryatta kaman ana
busa sarewa.

Ya maidamata da "Barka kadai Mai kyau, nasameku lpy?"
Murmushi tai daya k'ara fito da tsantsar kyanta. Tace "Lafiya lau ya mutan gida?"

Hira yaitamata, dukda rabin hira ta Yarantace, Hassan da Husna, sedai tad'an saki jiki dashi
kad'an.
Jaka yad'auko agefansa guda biyu, yabasu kowa d'aya ahannunsa yace "Sukaiwa Inna"
danduk yaji labarinsu gurin 'yan biyu, yahad'asu da Sweat suka fita sunata Farinciki. Dukkansu
suka bisuda kallo suna murmushi.

Haske tagani Walll! Tajuya tana kallansa, yasakar mata k'ayataccen Murmushinsa daba kowa
yakewa shiba. Waya tagani a hannunsa alamun Hoto yamata. Sulaiman Ganindayai takafeshi
da _Bold Eyes_ d'inta yasashi cewa "Am sory Ummana zan kaiwa taga Surukarta mai kyau
that why nai Snapinng naki dukda Original Pic inki yananan Album guda a Bottom of my heart"
sunkuyar dakai takumayi ganin irin kallon dayake binta dashi yace "Lallai yau kinaso nakwana
gidannan indai zaki cigaba damun wannam Smile innaki dake tafiya da Ruhin mai kallo, Uwa
Uba Kunyar ki datake k'aramin shauk'in san kasancewa tare dake."

Anan yarik'a bayyana mata *Babban Sirri (My Yaya Hajja Novel)* dake ransa. Ita kuwa
Naja'atu mamakinsa take daga *Had'uwar Farko* mutum ya zak'e, lallai saitayi dagaske zata
gano irin San dayake mata bata k'ara mamakantuwaba seda taji Sulaiman yace "Naja'atu ga
k'ask'antaccen bawa yazo gareki da k'ok'on barar soyayya har tazama ta Aure *Ni dake
(Phertylicious ta)* muzama k'ark'ashin inuwa d'aya, ga miji yazo gareki akaro nabiyu. Amma
zanbaki lokaci ki shawara saidai da had'uwarmu da Auren bazai wuce wata biyuba banma son
hakan."
Baijira maizata ceba yaimata sallama yatafi.
Ita kuwa Naja'atu bin bayansa tai da idanu harya fice. Dak'yar tatattaro dukkanin nutsuwarta
tashige cikin gida.


© *Aneesa_Didi*🍼🍉�
[2/18, 10:50 AM] +234 703 962 5239: *♡DUTSEN CIKIN RUWA.....♡*
*Na*
*Haleema G Khaleel*


*94-95*

~~~Lokutan dasuka biyo baya, duk batada sukuni. Gani tai Tunanin bazeje mataba sai tashiga
adduoi da neman za6in Allah.
Har d'an fad'awa tayi yasa Inna takuma mata nasiha.

Kullum cikin dare zatai Nafila Raka'a biyu ta *Salatul Istikara* tai addu'a danneman za6in
Ubangiji.

_Garemu 'yan uwa Musulmi yayinda wani abu yashige mana duhu komike shiga dabaibayi
gameda neman abu ko samun abu na Rayuwa, Neman Aiki, Neman Aure, Karatu. Wani Abu dai
makamancin haka. Inmukai hak'uri komi mai sauk'i ne_.

Cikin Hisnul Muslim(Garkuwar Musulmi) dasauran Litattafai na Addini da Addu'ar tazo.

*Jabir bin Abdullah Allah yak'ara musu yarda: Manzan Allah S.A.W yakoyar damu ISTIKHARA
acikin kowane al'amari kamar yadda yakoyar damu sura daga Al-Qur'ani yana cewa:- "Idan
d'ayanku yana dawani Al-amari seya Sallaci Sallah raka'a biyu, badaga cikin Farilla ba,
seyace:-* ```ALLAHUMMA INNI ASTAKIRUKA BI ILMIKA, WA'ASTAQ DIRUKA BIQUDRATIKA,
WA'ASALUKA MIN FADHLIKAL AZEEM. FA'INNAKA TAQDIRU WALA AQDIRU, WATA'ALAM
WALA A'ALAM, WA ANTA ALLAMUL GUYUB.
ALLAHUMMA INKUNTA TA'ALAMU ANNA HAZAL AMRA(ka/ki fad'o Matsalan taki ko wani
abu daki/ka ke nema) KAIRULLI FI DINIY WA MA'ASHI WA'AQIBATA AMRI, FAQADIRHULI
WAYASSARHULI SUMMA BARIKLIY FIHI, WA INKUNTA TA'ALAMU ANNA HAZAL AMRA
(ki/ka fad'o matsalan kowani abu daki/ka nema) SHARRILY FI DINIY WAMA ASHI, WA
AQIBATU AMRI FASRIFHU ANNIY WASRIFNIY ANHU, WAQADURHULI KAIRA HAISU KANA
SUMMA ARDINIY BIHI.```
Yaitayi in sha Allahu zaisamu daidaito da za6in ubangiji.

**********

Sulaiman kuwa, Mahaifinsa yasanarwa yasamu mata danhaka Addu'ar dasuke masa akullum
lokacinta yayi, sai aje anemomasa Auren.
Ba jimawa Manya suka shiga maganar, aka tsaida za'a d'aura musu Aure tareda 'yan uwanta
inyaso tatare daga baya.

Shirye-Shiryen biki ake tayi. Amaren Gidan se kintsasu ake da gyata according to Sunna.
Wayar da Sulaiman kemata, sema abinda yak'aru, har fad'a sukeyi yadda tak'i sakin jiki
suzuba Soyayya dashi. 'Yan biyunta su Hassan da Husna sun zama 'yan Gidansu "Uncle mai
zane" bawanda besan dazamansuba se yayunsa dabasanan kokuma insunzo lokacin
bekasuba. Yazama wani sashe narayuwar yaran dayalashe gurbi dadama a zuk'atan yaran da
'yan uwan Naja'atunma tukafin ya Auri Mahaifiyarsu. Hakan yasa duk yasamu Shaidun k'warai
dakykkyawan zato.

Agajiye liss! Tadawo gida daka Sch karatun yad'auko k'arewa basuda wani hutu inba
_Exams_ dake gabansu sukai suka gamaba. Ga abubuwa duk sun had'e mata, wayanma ba
kasafai take barinta akunneba.
Ruwa tawatsa tazauna tana hutawa, dan fashin Sallah take alokacin. Riga ce Bubu me fad'i
ajikinta me launin ruwan Madara tasaka hula ruwan k'asa se k'amshin turarenta na _Urban
Woman_ take. Wayarta takuna bata jimaba kiran "Uncle Sman" yashigo kamar bazata d'agaba.
Jin sassanyar muryatta yasashi sakin wata wahalalliyar ajiyar zuciya yace "Haba
Mamynmu(inyaso raha haka yake kiranta dashi) kina wahal da daddyn yarafa, ko laifi nayi

bansaniba?"
"Ah ah fa Uncle"
"To miyafaru?"
"Allah Uncle ina busy ne dayawa kasan munkusa fara _Final Exams_ dole wasu abun semun
hak'ura dashi mi _Concentrate_ akaratunmu kodan muwuce gurin kawai."
Tafad"a dawata irin Murya a shagwa6e.
Numfashi Sulaiman yakuma saki yace
"Allah sarki kice inzo miyi karatun tare, bakomi ma ai nasan Mamynmu _Gifted_ ce ko _Guru_
zance?".
Dariya tasaki tana "kaikam kacika tsokana. Nidai katayani Addu'a kawai."
Irin muryatta yakwaikwaya yabata amsa. Dariya takuma saki sukai ta hira kamar karsu rabu.

Abinda yai shirin fad'a mata ma yabarshi ganin abubuwane agabanta ba kad'an ba.
"Ina sanki Naja'atu"
"Hmmmmmm! Alamun ajiyar zuciya yaji. "Nibazakice kina sonaba?"

"Ina sanka mana Uncle, kaine sanyin idaniyata dazaka maye gurbin abubuwa dayawa... harda
zuciya...." bata k'arasa fad'in maizatace ba da _Hanging_ wayar ganin shigowar Inna dasu
Ibrahim da Isma'il Yayunta, wanda alokacin sunzama matasa sosai dako Auren kowace mace
sukaje nema za abasu yadda Allah yaimusu kwarjini da Baiwar kyau tsantsa. Sunkuyar dakai
tayi tana juya Cup in hannunta. Ganin basuce mata komaiba, taware sukaita hira wadda
yawancinta ta bikin dazasine da yadda suke shirya Al-amuran sukasance cikin lafiya da
kwanciyar hankali har agama bikin.



© *Aneesa_Didi*🍼🍉�
[2/18, 10:50 AM] +234 703 962 5239: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login