Showing 111001 words to 111391 words out of 111391 words

Chapter 38 - TRIPLETS BOOK 4 COMPLETE

12 Jul 2025

4443

muka sanya William ɗin ya daki JAMES da sanda a kai, hakan ne ya bamu damar ɗaukar babban yayanku, muka dawo maku da ɗan autanku da muka ɗauka da farko wato Michael, so mu ba wani canza ku da muka yi, ita ma Josephine da wannan taɓa ƙwaƙwalwar Michael ɗin da muka fara yi ne ya bata damar samun hanyar baku kariya ai, so a takaice Michael shi ne wanda muka fara ɗauka, daga baya muka dawo da shi muka ɗauki yayanku, wannan dalilin yasa kaga Michael ƙwaƙwalwarsa ba'a dai'dai take ba, mun rigada mun birkita kwakwalwar mun fara yin tsafi da shi ne, kai baka yi mamakin idan kun tambayi William menene ainahin musabbabin ciwon Michael sai ya ce maku haka aka haife shi ba? Ai shi yasan komai, a gabansa aka yi komai, kawai yaki gaya maku ne, dan ma kada ku gane ba shi ne ainahin mahaifinku ba, William na ainahi yana kungiyarmu! Shiyasa ko wani asibiti da kuka je suka kasa gane me matsalar kwakwalwar ta Michael ɗin...........".

Shiru Lion ɗin ya yi yana mamakin yanda waɗan nan tsofaffi suka zauna suka shirya abu tiryan tiryan babu mistake a ciki, lallai sun cika shahararrun ƴan duniya, musamman shi Jacob Uban William ɗin da ya mutu, ya fi kowa iya tantiranci da haɗama, har da bada yaransa guda biyu, Allah mai iko, yanzu wani irin hukunci ne ma ya dace da waɗan nan azzaluman? A kan neman duniya kawai?.........Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, shi Lion yana nan, su gwaggo kuma suna gida Nigeria, kada kuma ku manta suna a tare da Uncle Herry da William na karya wanda kuma dukka sun kasance mambobine na kungiyar su His excellence ɗin, kuma ga Lion ya tirke kakansa a nan ya tonawa kungiyar tasu asiri, kuna ganin ƴan kungiyar za su barsu kuwa? Kuna ganin ba za su yi amfani da William da Uncle Herry su cutar da su gwaggo ɗin da suke gida ba kuwa? Kun dai ji Anderson ya yi umarnin a kashe Rimsha! Ga kuma garkuwanta Lion a nan ya taho ya barta, ga shi sun juya mata kwakwalwa ko sallah ma bata sani ba bare ace zata yo askar Allah ya kareta. My peoples PRINCESS TEEMA naku ta amana yau bana jin daɗi, saboda cakwakiyar TRIPLETS har wani zazzaɓi zazzaɓi nake ji! Na barku lafiya❤️


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login