Showing 330001 words to 333000 words out of 356830 words

Chapter 111 - RAINA KAMA Document

fito..
Iya falon saman na tsaya ina masa adawo lafina.
Harya fara taka steps d'in ya tsaya, juyowa yay yana kallona, “Wai kina nufin iya nan zaki tsaya?”..
“Nidai wlhy kunyar su Momma nakeji”.
Dariya tabashi, amma sai baiyiba, yay murmushi yana cigaba da sauka abinsa.

Shi kansa dai daya sakko k'asan sai kunya ta kamashi, ganin Momma da Aunty Mimi duk suna falon, saiya samu kansa dak'in yarda su had'a ido.
Aunty Mimi Ce kawai tayi k'aramar dariya, amma Momma yitai tamkarma batasan inda ya dosaba, saima ta shiga yaba kwalliyarsa da tambayarsa sai ina kuma?.
Ganin Momma ta share shima saiya fuske yay mata tamkar yanda ya saba, yasamu ya fice abinsa.



*****

Ni dai kam nakasa sauka kasa, ganin kad'aici da kewar Galadima zata fara addabata saina d'auki waya na kira innarmu, hayaniyar danaji a gidan yasani tambayar mike faruwa?.
Innarmu tace, “To sarkin son gulma basai kinjiba, ya kuke?”.
Dariya nayi, nace, “Kai innarmu Dan ALLAH kid'an gumtsamin”.
“O ni Ai'sha ALLAH ya shiryeki Munaya, wato dai bazaki canjaba kekam?”.
Nanma dariyar nayi harda k'yalk'yatawa, “Kai Innarmu na canja mana, kinsan gidan namune sai a slow, nasan dai yanzu duk kin wuce da iskancinsu d'innan?”.
Itama dariya tayi daga can. Tace, “Ai tsakanina da kowa yanzu sai girmamawa, ni dariyama suke bani, Safara'u ce wai mijinta zai k'ara aure, shinefa inaga ta tada hankalinta taita zuba masa rashin kunya ya shashshek'a mata mari, to jiya dai a gida ta kwana, kinsansu da gutsiri tsomar tsiya, wai Jamila tashiga gaida Hadiza ta iske suna gulma itada Mero, shine taje tasanarma uwar tasu, wannan yakawo wanan fad'an da kikeji, Maman safara'u babu hak'uri tafito tanata zaginsu da fad'in ai ko auren Safara'u mutuwa yayi ba kanta farauba, tunda ga Siyama da Zarah nan a gida tun kafin ita. Shinefa suka kaure fad'a da cin zarafin juna”.
“Tofa, ALLAH ya k'yauta to, tosu su mom indai banda take laifinka ka hango na wani ai baikamata su zauna yida waniba ganasu y'ay'an zaune, anriga an koyama yaran gidanan d'aukar gulma wlhy, yanzu kamar jamila tasan ta d'auki zance takaima mamansu, to su Abba duk basa nan innarmu?”.
“Wlhy suna nan, kuma duk sunajinsu, shiyyasama danaje nabad'a hak'uri sau d'aya naga sunk'i saurarena nai dawowata d'aki, Aryaan na kwance yana fama da zazza6i gara Nazo natattali yarona yafimin”.
“hhh innarmu kinaji da autaras d'innan nakifa, ALLAH yabashi lafiya, sukuma ALLAH ya dai-daita komai. Hajiya Innaro fa?”.
“Tana gidanta mana, bama tajin dad'i kwana biyunnan wlhy, tana fama da ciwon k'afa, ki kirata ki gaisheta, dan jiya gwaggonku Safiyya ma tazo itama”.
“To su Innaro kodai gangarawa za'ayine? ALLAH yabata lafiya”.
“Ja'ira saidai tsohonki ya gangara, amindai to, ai dama sauk'i”.
Dariya nayi kawai.
Daganan muka cigaba da hirarmu wadda ta shafemu, nan ma innarmu ke sanarmin Aunty Salamah tazo gidan ansaka aurenta.
Cikin tsantsar farin ciki nace, “Innarmu dan ALLAH da gaske?”.
“To Munaya ana wasa da maganar aurene? Nasanma zata kiraki ai”.
Farin cikine sosai ya mamaye zuciyata, nace, “ALLAH sarki Aunty Salamah komai nada lokaci, anata surutun ta tsufa agida batayi aureba, gashi ALLAH yakawo iyakar, lallai aure da Haihuwa duk lokacine dasu, duk saurin mutum saiya jira ALLAH, ALLAH yabama sauran y'an matanmu mazajen aure nagari masu addini da nagarta, suma mazan haka”.
“Amin dai Munaya”. Inna ta amsa itama cikin farin ciki..
Nace, “Innarmu zancen Ayusher fa itama?”.
“Itama kwanannan sukace min zasuzo akan maganar, dan kawu Mani ma munyi waya dashi d'azunnan, tsohuwar nan ce tarasu mai ciwon hannun nan, shinema ya dakatar dasu”.
“ALLAH sarki Innarmu, badai wadda tabama yara maganin ciwon kai ba?”.
“Aiko dai ita, ashe kin ganeta, ALLAH ya d'auke kayansa shekaran jiya wlhy, Abbanku ma zasuje gaisuwa su dukansu harda Baba mai kanwa ”.
“Wayyo, to ALLAH ya gafarta mata, amma shi baba mai kanwa ina yaga k'arfin wannan doguwar tafiyar innarmu?”.
“Ai ba'anan takeba Munaya, dayake ALLAH yabashi lafiya, yace insha ALLAH saiyaje yaga tushena”.
“ALLAH Sarki baba mai kanwa, ALLAH yak'ara lafiya da tsawon kwana”.
Inna ta amsa da amin.
Munsha hira sannan mukai sallama.

Itama Innaro na kirata namata ya jiki, daganan muka gaisa da gwaggo Safiyya da aunty Habiba.
Na kuma kira Munubiya, sosai mukasha hira, take kuma bani labarin auren Aunty Salamah dayazo kamar ha6o. Tace, “Alhajinan dai dayayta naci wanda muke cema Cingom Alhaji dai shine mijin”.
“Oni rayuwa, Sweetheart kinga hikimar Ubangiji ko, idan yazo muyita masa iskanci har ita aunty salamah d'in Ashe dai shine mijin, gaskiya ya cancanci ta auresa, wajen shekaru biyarfa bawan ALLAH nan baita6a gajiyawaba”.
“Wlhy kuwa Sweetheart, son gaskiya kenan ai, ga Ayusher nan anata soyewa itada Hamma Youseeff, duk wannan shan k'amshin nasa ya mace mata, Yaa Fadeel ma in fad'a miki shida Badeerah Ashe sun k'ulle”.
“Dan ALLAH da gaske ko wasa?”.
Cikin Dariya Munu tace, “Wlhy kuwa, waike bak'ya waya da kowama kenan?”.
“Wlhy ba haka bane kemakinsan d'an tsakaninan damuwar data hanani sukuni, amma yau dolene na kirasu nasha kanu, shegiya Ayusher bara itama na kirata, dukda kud'ina sun kusa k'arewa, a gaidamin da Sweetness babies d'ina da Yaa Marwan inya dawo”.
“Zasuji insh ALLAH, asha amarci lafiya, aidai kulamin da yara kar soyayya tasa abarminsu su rame”.
Kafim nayi magana ta yanke kiran.
Dariya kawai nayi ina girgiza kai, alokacinne Samha ta shigo.
“Ah lallai aunty gimbiya yau Uncle Sam ya 6oye mana ke, Momma Ce tace yau bazaki sakko bane?”.
“Dan ALLAH da gaske?”. Nai maganar cikin waro idanu.
Dariya ta sanya, “Wlhy kuwa da gaske nake”.
“Ni munaya naga idi, ALLAH kunya nakeji”.
“Kam kunyafa aunty gimbiya, to miye najin kunyar? Wlhy ALLAH yabani miji irin Uncle Sam a gabanki zan mak'alk'ale abina”.
Duka nakai mata ta kauce tana dariya.

******


Cikeda jin kunyar su Momma na sakko k'asan, amma saisukayi tamkar basusan minike mawaba, tun ina sunne-sunnen kai hardai na warware nasaki jikina kamar yanda nasaba.
Momma da Aunty Mimi sunji dad'in haka, a zukatansu suna mana addu'ar d'orewar zaman lafiya nahar Abadan.................✍🏻




Inaga sai Monday zakujini, kuyi fatan nama kammala gaba d'aya😅🤝🏻👌







ALLAH ya gafartama iyayenmu😭👏🏻




♦RAINA KAMA...!!♦
(Kaga gayya)


Bilyn Abdull ce🤙🏻


BOOK 3 👉🏻2⃣8⃣


.................Har yamma Galadima bai dawo gidanba, abincin ranama da aka ajiye masa sai d'aukeshi akayi, sainaji inajin tausayinsa, dan nasan yanacan ba zaune waje d'ayaba, yawan harkoki dayakeyi kansa kullum yake yawo tamkar wata motar haya, shidai kullum burinsa ya iya d'aukar nauyin ahalinsa, bai yarda zama rago ko jira daga waniba koda ace papi ne, ya yarda yasha wahalar nema amma ta gumin halak, sa6anin matasanmu da kullum burinsu nakan gwamnati ko alhajin anguwarsu ko d'an siyasa, ko alhajin da yafi kowa arzik'i a danginsu. Akwai wata kalma da Galadima yata6a fad'ama sauban Wanda akulum Na tunata tana k'ayatar dani. Lokacin inada tsohon cikinsu Amaturrahman, da yawan cin abincinnan Na masifa, aranar jikin Abie yad'an motsa, sai yakasance nikad'ai aka bari a gida sai hadiman gidan, cikin barci yunwa ta addabeni, hakan yasani farkawar dole Na sakko k'asa da k'yar, kitchen Na shiga nasami madara Na d'umama kafin kuku yad'an girkamin wani Abu, fitowata daga kitchen d'in keda wuya sai Galadima da Sauban suka shigo, da alama ya tuk'osane, dan idan yana cikin damuwar tashin ciwon Abie Momma hanashi driving takeyi. Da mamaki Sauban ya kalleni da cup a hannu yana fad'in “Yanzu nan Aunty duk hadiman gidannan saikin shiga kitchen da kanki a wannan halin? Aiko yau saisun gane kuransu”.
Ya tafi fuuuu cikin fushi saina dakatar dashi ina murmushi. Nace, “A'a Yaa Sauban, kabarsu please, nice ban sasunba nayi da kaina, amma aiga shican nasaka kuku wani aikin”.
Galadima dake zaune saman kujera ya d'aura k'afa d'aya kan d'aya idonsa a lumshe tamkar baisan mi mukeyibama ya bud'e baki cikeda k'asaitar nan tasa yana fad'in, “Ai duk Wanda ya dogara da k'arfin wani to lallai nasa na cikin jerin k'arewa a sahun marasa amfani, dan zai dawwama cikin bibiyar samu daga waninsa shikuma bai amfanu datasa fik'irarba, kazama mai k'arfin zuciyar gina kai ba zaman jingina da bangon waniba”.
Yana gama fad'ar haka ya tashi ya haye sama, dagani har Sauban da kallo kawai muka bishi, kowa na fassara zancensa dalla-dalla, ni abinda na fahimta kai tsaye bada Sauban d'in yakeba, akwai abinda yafaru daga can inda suka fito, amma saiya za6i mu yamana sharhi bisa dalilin dashi yabarma kansa Sani. (ALLAH dai ya ganar da matasanmu domin tashi su nemi na Kansu ta hanya mai k'yau basu cigaba da dogaro a bangon wasuba.👏🏻😢).

Tun d'azun yake tsaye akanta amma bata saniba, ta Lula duniyar tunani mai zurfi, ga Abdurrahman dake gefenta yanata mutsu-mutsu da k'ananun kuka amma batama jishiba.
Agabanta yay wani durk'uso mai birgewa, yakai fuskarsa daf da tata yana hura mata iska a saman ido zuwa hanci.
Wata sassanyar ajiyar zuciya na sauke tareda dawowa hayyacina cikin zabura, yay azamar damk'e hannuna da fad'in “My Mata!?”.
Ajiyar zuciya na sauke tareda dai-daita dan fahimtar shine, na zuba masa idanu cikin mamaki nace, “Yaushe ka shigo?”.
Murmusawa yayi sannan yamik'e daga durk'uson dayay agabana, batareda ya bani amsaba ya fara k'ok'arin cire farar rigar suit d'insa. Mik'ewa nayi na taimaka masa, sannan nadawo gabansa na warware tia.. 'Din da bottoms d'in pink d'in rigarsa ta ciki. Sai wani faman lumshe idanu yake da bud'esu akaina, bansan miyake tunaniba.
Ina cire bottom d'in k'arshe na rigar ya rik'e hannuna, idanu na d'ago na kallesa, ya sakarmin wani k'asaitaccen murmushi yana matsoni jikinsa sosai, a saman la66a ya furta “Kinyi k'yau sosai, amma mikike tunani haka?”.
Da mamaki na kalli kaina, sanye nake doguwar rigar shadda milk color, anmata simple aiki da brown d'in zare, an k'awatashi da stones, Wanda sune suka fidda ainahin k'yawun d'inkin, sai siririyar sark'a data kwanta a wuyana d'as, nayi d'aurin Maryam babangida daya kuma fidda ainahin suffata ta bahaushiyar asali mai rik'o da al'ada. Yanda nake bin jikina da kallo haka Galadima kebi shima da idanunsa, na maida kallona ga face d'inshi dake kadaran kadahan, bai d'aureba kuma babu walwala sosai tare dashi.
Gira d'aya ya d'agemin sai kuma yad'an ta6e baki yanajan hancina da had'e yatsunsa biyu na k'arshe👌🏻alamar komai yaji.
Nad'an murmusa ina k'ok'arin barin wajen dan naga alamar miskilawan suna kusa.
Ruwa naje na had'a masa, na fito ina goge hannuna da towel.
Durk'ushe na iskeshi gaban Abdurraheem da cup d'in ruwan dana ajiye danshi a hannunsa. Ya d'ago yana kallona dad'an murmushi a face d'insa, “kinsan minake gani a jikin Abdurraheem kuwa?”.
Kaina na girgiza masa alamar a'a.
Kallonsa ya maida ga yaran yana cigaba da murmushinsa. Yace, “Kamannin Abie”.
Takowa nayi Inda suke Nima Ina murmushi mai sauti da fad'in, “Nadad'e da wannan tunanin a raina, saidai nabarma zuciyatane har sai randa zan gansu a waje d'aya, Ashe kaima kana lura?”.
Wata y'ar dariya yayi, wadda tafi kud'i tsada awajensa. Yace, “My Heartbeat ALLAH kin iya haihuwa”.
Ba k'aramar dariya maganarsa tabaniba, aiko nashiga k'yalk'yalawa. Shiko ya shagala da kallonta saboda birgeshi da dariyar tata tayi, burinsa dama yaganta cikin farinciki.
Bayan na tsagaita da dariyar na kallesa Ina d'aga kai da kashe masa ido alamar kallonfa?.
Mik'ewa yay tsaye ya dawo inda nake tareda rank'wafowa kaina yana dafa hannayensa biyu asaman gadon gefe da gefena. Kusancin namu yasakani d'anyin baya kad'an ina kallon cikin idonsa, yakuma matsowa, na matsa, yakuma again, Nina still na matsa, saida na haye gadon sosai shima yay balance yanda yake buk'ata sannan ya kwanto gefena kusan Rabin jikinsa a nawa, har lokacin idonsa na sark'e da nawa. Galadima yay bala'in Sanin sirrin kallo, inhar ya sark'e idanunsa da nawa duk wani hope d'ina nemansa nakeyi na rasa, yatsansa kawai naji saman la66ana yana zagayawa ahankali, santsin hannunsa Dana lips gloss d'in Dana sanya sunayin kamar susa, kasa jurewa nayi na lumshe idanuna a hankali.
Galadima ya murmusa da bud'e baki da k'yar yana fad'in, “Kin cancanta, kin cancanta zama matar Muhammad Sameer Munaya, ked'inki da dukkan halayyarki irinta Muhammad Sameer ke buk'ata ga matarsa, ko ayarda ko kar ayarda nasan nama sauran maza zarra, dan matata tafi ta kowa, kinzama fitila mai hake gabana da bayana, kinzamarmin bango abin jingina lokacin danawa yanemi rushewa, shigowarki rayuwata na dai-dai da farkawata daga nannauyan barci mai cikeda rud'ani, nabaki dukkan zuciyata ki jani a sannu danna cigaba da ribantuwa da ni'imomin da ALLAH ya azurtaki dasu, I love you so much Munaya, I love you har a aljanna matsayin uwargidan matana”.
Bansan lokacinda hawayen farinciki suka fara zirarominba, na bud'e idanuna dakai hannu saman kwantaccen sajensa ina shafawa a hankali, cikin wani yanayi nace, “Ka cancanci fiye da haka mijina, dan kanada zinariyar zuciya, kaimai tarin tsoron ALLAH ne dabin dokokinsa, a wannan zamanin samin matashin saurayi mai kud'ad'e da mulki a hannunsa dabaya wata masha'a abune mai wahala, baka kasance mazinaci ba, baka kasance mai shaye-shaye ba, ko sigari wannan bakasha, kulum cikin Neman halalinka kake Dason k'yautatama iyayenka dana k'asa da kai, kaimai ibadane, salla bata wuceka, mai yawan tsayuwar dare, mai yawan bitar littafi mai girma dake d'auke da zancen ALLAH ne, mai yawan sadaka da taimakon mutanen da bakuma had'a addiniba, bakada wata majalissa ta abokai daza'ace gaka cikin jerin masu cin naman wani ko zind'en wani, abinda ke gabanka da Wanda ALLAH ya halatta maka kawai kakeyi, mijina tayaya bazaka samu nasaroriba a rayuwarka? Ubangiji mai ni'imane ga dukkan Wanda ya ra6u samun ni'imar, babu wani Bawa dazai tsinci kansa a ta6ewa inhar yabi dokokin Ubangiji da koyi da manzon tsira, babu cuta mafi rad'ad'i da ciwo kamar bijirema Umarnin ALLAH Wanda ayanzu shike wahal da matasan duniya irinka, burunsu kawai su hole su mori k'uruciyarsu, sun manta babu tagomashi mafi k'yak'yk'yawan farashi irin morar k'uruciya bisa ga Umarnin ALLAH, yadda da k'addara, samu ko rashi, tsayawa matsayin da ALLAH ya ajiyeka, kaucema dukkan wata bad'ala, matasa sune k'ashin bayan al'umma, lalacewarmu ta saka al'ummar tafiya a karkace a halin yanzu, da'ace zamu gyara da kowa ya mik'e, dolene Momma da Abie suyi alfaharin samun d'a irinka, dolene Aunty Mimi da Yaa Sauban suyi alfaharin samun d'an uwa irinka, dolene su Samha dasu Amaturrahman suyi alfaharin samun Uba irinka, dolene k'asarka da addininka yayi alfaharin samunka, saidai duk nice nafisu sa'a da alfaharin samunka a matsayin miji uban y'ay'ana, inaji inama y'ay'yana su gaji k'yawawan hallaya da d'abi'u irinna mahaifinsu, saidai kash ina cike da fargabar tsoron kalmarnan ta bahaushe dakance Bakowanne tauntsu bane ke raira kukan gidansu wani tun a koyan tashi yake canja salo. Mijina ka more, ka matuk'ar morewa da k'yawawan hallaya, irinku kunada tsadar samu a cikin al'umma, da mutane zasu gane dasun fuskanci ba k'yawun fuska dana jiki bane abin alfahari, zinariyar zuciya da hallaya shine abin alfahari da d'agawa, saidai kash, burin samarin yanzu da y'ammata k'yawun fuska dana halitta, nauyin aljihun wayewa, basa tunanin mika tara mizaka taras, sannan mika barma bayanka da ahalinka Wanda ko bayan shekaru aru-aru tarihi bai Isa mantawa da kai ba, da inada dama sainabi matasan mata da maza dukna musu allura sunzama kamarka mijina, inasonka, ina sonka, zan fad'a a hankali, nafad'a da k'arfi, na fad'a da kuwwa, na fad'a da ihu agaban kowa kuma, Kaine duniyar Munaya, Kaine farincikin Munaya, zanta k'aunarka har randa nufashina zaibar gangar jikina, nakumayi fatan ganina a cikin matanka dake aljanna Muhammad Sameer”.
Kasa magana Galadima yayi, sai bakinsa ke motsi alamar buk'ar firta wani Abu amma yakasa, idonsa yacika taf da kwalla, lallai hikimar zancema baiwace ga mace tagari, dashi kawai zata iya mallakar mijita babu boka babu Malam, dan gashi Munaya tasamu dukkan nasarori, ya rungumeni tsam a jikinsa tareda d'ora bakinsa saman la66ana, hawayen dayake rik'ewa suka gangaro


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login