Showing 33001 words to 36000 words out of 80926 words
Sanam
manya kenan , Alhaji Abba na lura da yadda Huneed d'in ke kallon 'yar tasa wani murmushi
yayi irin nasu na manya......
Nan Alhaji Abba ya shiga yiwa Huneed tambayoyi game da asalin sa , Huneed ya gyara
zama yafad'awa Alhaji Abba asalin sa da kuma aikin da yakeyi , Alhaji Abba yanajin Huneed
yace shi d'an gidan Canal Abdallah marigayi ne yasan Huneed , dan bawani Mahaluk'in da
baisan Canal Abdallah ba , yayi aiki tuk'uru a k'asar nan kafin Allah ya amshi ransa , kuma har
gobe ana labarin yadda yayi gumurzu da mugayen mutane , Nan take Alhaji Abba ya jinjinawa
Huneed da yadda yake k'ok'ari shima , dan da alama shine zai maye gurbin Mahaifin sa , sosai
Alhaji Abba yaji ya yarda da Huneed kuma ya amince masa a matsayin wanda zai zama miji ga
shalelen 'Yar tasa , gyaran murya yayi sannan yace " naji duk bayaninka kuma na gamsu , dan
haka nabaka izinin kaci gaba da zuwa wajen Sanam har Allah ya dai daita hankulan ku , Allah
yayi muku Albarka yasa Alkairi a cikin tarayyar ku , Huneed ya amsa da Ameen tare da
rissinawa yana fad'in " nagode sosai Daddy Allah yaja da rai , da Ameen Alhaji Abba ya amsa
tare da mik'ewa ya haye sama ....
Sanam ce ta fito ta wata kusurwa rik'e da tire a hannun ta , tana k'arasowa ta ajiye a gaban
Hubeed tana fad'in " bisimillah ga abin tab'awa , Huneed ya kalleta yana murmushi tare da
kashe mata ido yace " ai bazan iya tab'a komai anan ba sai naji daga bakin gimbiya ta in ta
amince dani , Sanam tayi wani wal da ido sannan tace " ni bazan iya soyayya da me mata ba ,
da ace baka da mata to tabbas zan iya ansar tayinka kodan na rama abinda kamin a baya , da
sauri Huneed ya dubeta yace " waye yace miki ina da aure kuma ? Sanam ta kallesa tana
hararar sa tare da turo baki tace " waye kuwa ya gayamin in ba kai ba , ko kamanta randa
muka fara waya kace na tasoka kan tare da iyalinka , sannan sauran wayoyin ma da muke
kullum sai kamin zancen matar ka , wata irin dariya Huneed ya fashe da ita yana duban Sanam
, sai dayayi me isar sa sannan yace " ni fa bani da wata mata tsokanar ki nakeyi for sale ne
inkin shirya , duban sa tayi ya kashe mata ido ta kauda kai sannan tace " sainayi shawara naga
a wajen da yakama ta insaka , Huneed ya taso ya dawo kuda da ita numfashin su na dukan
juna yace " abar maganar wasa Babyna wallahi da gaske nake k'aunar ki kuma aure nakeso
muyi , yanzu maganar da nake miki Daddy ya amince min akan inzo neman auren ki ya bani ke
, da sauri Sanam ta dube sa ya d'aga mata kai alamar da gaske , k'asa tayi da kanta dan
tabbas ba wasa a cikin idon sa , ci gaba yayi da magana yace " ina fatan zaki iya zama da Soja
? Sanam bata d'ago ta dube sa ba kuma batace komai ba , Huneed jikin sa yayi sanyi kodai
Bata son sa ? wata zuciyar tace " inbata sonka yazatayi kishinka , jin shurun da yayi yasa
Sanam d'agowa tana duban sa kafin tace " dama kai Soja ne ? Huneed cike da Comfidence
yace " Soja ne ni Sanam ina fatan jin hakan bazai sa ki canza ra'ayi akaina ba , yadda ya
marairaice yayi kalar tausayi yasa tace " inaso kabani lokaci zanyi tunani , sannan ta mik'e
tafara tsiyaya masa lemo a cup , kallon ta yashiga yi yana zancen zuci " Allah yasa ki amince
min dan in har kika k'i to tabbas nasan zan shiga wani halin Sanam , mik'o masa lemon tayi tare
da janyo filet d'in su donut da samosa tane fad'in " maza kaci kar muyi fad'a , murmushi yayi
yana curb'ar lemon yana fad'in " ai bazan so yin fad'a da Gimbiya taba , sai dai lallashi da
tausasawa wanda kayi ada ma angode , Sanam tace " nikuma kasan ban gode ba , dan saina
rama duk abinda kamin d'aya bayan d'aya , dariya yasa yana gutsirar Donut d'in yace " haba
gimbiya ta kiyi hak'uri dan karkimin horon da zan kasa rik'e kaina , hira sukeyi sosai me dad'i
har yayi mata sallama yatafi.......
Bayan fitar sa da kamar minty biyar saiga megadin su ya shigo , har lokacin Sanam na
zaune tana murmushi ita kad'ai tare da jin wani nishad'i , zuwa yayi ya rissina a gabanta yana
mik'a mata wata leda yace " ranki ya dad'e gashi inji bak'on ki daya fita yanzu , hannu tasa ta
ansa sannan ta sallamesa yafita , tashi tayi da ledar a hannu ta nufi sama cikin d'akin ta ....
Alhaji Abba yana hawa sama d'akin Hajiya Nafeesa ya shiga , nan ya zauna yana fad'a
mata yadda sukayi da Huneed , yace " nifa yaron sosai ya burgeni dan har na aminta dashi ,
yanzu kawai sonke Inji ta bakin Shalele in ta amince dashi shikenan , Hajiya Nafeesa ta tab'e
baki sannan tace " nikuma Alhaji sai nake ganin kamar kayi saurin yadda dashi , yana da kyau
dai kayi bincike akansa sosai dan tabbatar da waye shi , sannan kana ganin Sanam ta dace da
ta auri Soja ? gaskiya ni ba irin mijin da nakeso Sanam ta aura bane wannan , Murmushi Alhaji
Abba yayi sannan yace " kufa mata akwai ku da san burga , amman fisabilillah ina aibun Soja ?
kuma abin burgewa yaron yana kasuwanci sosai to meye laifinsa ? inaso ki sameta kuyi
magana mutuk'ar yayi mata shikenan dan nima ya yimin , kuma gashi d'an gidan manyan
mutane ko iya nan nasan Sanam tayi mijin da yadace , in kuma itama ra'ayin naki gareta to
babu takura Allah yabata wanda zaiyi dai dai da ita , yana gama magana ya shiga toilet d'in
dake cikin d'akin.....
Hajiya Nafeesa ta bi bayansa da harara tana fad'in " zaka canza ne dan wannan komawar
da zanyi gun boka har da zancen shegen saurayin nata zanje , dan kwata kwata ni baiyimin ba
ko kad'an kuma bazai tab'a yimin ba , take ta fice daga d'akin tana kiran number Hajiya
Harira......
Sanam tana shiga d'aki tafad'a kan gado tana murmushi , ledar da aka kawo mata ta shiga
bud'ewa , wasu manyan turaruka tagani masu tsadar gaske kala kala , sai wani Hankici me
kyan gaske da hoton heart a jikin sa sai k'amshi yake , tana duba wata leda daban kuma taga
su chocolate kala kala masu tsadar gaske , murmushi tayi tana fad'in tamkar kasan inason
chocolate , sai wata Ambulance k'arama data gani ajikinta wata tak'arda an rubuta " _ina sonki
da dukkan zuciyata Sanam_ tana bud'ewa taga bandir d'in dubu dari sannan ankuma rubuta "
_Gashinan babu yawa ko sweet kinsha_ wani murmushi ta kuma yi tana jin dad'i , tunda take
babu wani mahaluk'in daya tab'a bata kyautar kud'i , saboda yadda matsayin ta yake amman
yau gashi Huneed yabata , duk da yasan matsayin ta da kuma irin dukiyar mahaifin ta amman
baisa ya karaya ba yayi mata kyauta , tabbas wannan Huneed d'in nata nadaban ne , kuma taji
dad'in yadda yayi mata hakan ko ba komai ya nuna mata irin k'aunar daya kemata , kwanciya
tayi tana duba wannan takardar me rubutu tana ta maimaita kalmar " inasonki da dukkan
Zuciyata Sanam.....
Huneed yana k'ara sawa gida ana sallar magariba , arwala yayi sannan ya wuce masallaci ,
tunda yashiga cikin masallaci bai fito ba sai bayan sallar isha'i , mutuk'ar Huneed yana gari to
indai yashiga masallaci baya fitowa saiyayi tilawar k'ur'ani tare da azkar yake fitowa , gida
yashiga kai tsaye ya nufi falor Hajiyar su , yana zuwa yasameta ita da Hisham suna hirar su
gwanin sha'awa , dan Hajiyar su mace ce ita me janyo 'Ya'yan ta jikin ta , shiyasa sukuma suka
maida ta abokiyar shawar su tare da fad'a mata duk wata damuwar su , yana shigowa ya
k'araso gunta ya zauna yana fad'in " sannu da gida Hajiyata , murmushi tayi tana fad'in " sannu
da dawowa Huneedullah dafatan kabaro sirikar tawa lafiya ? Murmushi yayi sannan yace "
nabarota lafiya Hajiya har tace ingaidake kafin tazo , Hisham yafara murmushi yana fad'in " au
kace zance kaje shiyasa naganka kayi guyu sosai tamkar sabon ango , dukan su suka sa
dariya Huneed yana fad'in " Naje neman aure ne wacce zata zo ka runga ce mata Aunty ,
Hisham yasa dariya yace " zance mata Aunty indai zata dunga bani lafiyayyan Abinci , Hajiya
tayi dariya tana fad'in " yauwa kaji acici ko baisan komai ba sai ci , nikam naga randa zaka rage
wannnan cin Abincin naka Hisham, Hisham yace " aikuwa sai sai in k'ara Hajiya tunda gashi
zamu samu kuku , kinsan 'Yan matan zamanin nan akwai iya girki kala kala , dariya suka kuma
sakawa baki d'aya Hajiya na fad'in " kai tafican matan zamanin da duk basu iya girkin gargajiya
ba sai nasu na iyayi , Huneed yace " ko bata iya ba Hajiya ai sai ki nuna mata kinga kema kin
huta shiga kitchen , murmushi tayi sannan tace " baza ayi haka dani ba kuwa , yarinya daga
zuwan ta ace tana aikin girki ai sai ta gaji baruwana , yanzu dai gayamin yadda kukayi da ita ,
nan Huneed yashiga bawa Hajiya da Hisham labarin yadda sukayi da Alhaji Abba da kuma ita
kanta Sanam d'in .........
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 24.
Sosai Hajiya taji dad'in yadda Huneed ya sheda mata Baban Yarinyar ya amince
masa , nan tayi masa addu'ar samun nassara tare da daidai tawa da Sanam d'in .......
Sanam na zaune a kan gadon ta rik'e da wannan takadda , sai murmushi take tare da
d'aukar chocolate tana sakawa abakin ta , wayar tace tashiga ruri da sauri ta d'auka tana duba
screen d'in wayar , number Diyana tagani da sauri ta d'aga tana fad'in " kina ina k'awata yau
anzo har gida wajena zance , wai dama zanga wannan ranar ace ga wani yayi zarrar zuwa
wajena da sunan yana sona ? Diyana tayi murmushi sannan tace " Besty ai kece kike tsare
gida dayawa , amman kinsan ko a sch kina da tarin masoya 'Ya'yan Manya wanda suka amsa
sunan su a Nageria , amman kallo ma basu isheki ba saboda halinki , lallai ko waye wannan ya
cika me sa'a dakuma zarrah kuma lallai shid'in Sadaukine a cikin maza , Sanam tayi murmushin
jin dad'in yadda Diyana ke kuranta Huneed , duk da itama ta yadda da lallai Huneed jarumine
ko acikin mazan , a hankali ta furta " tabbas Jarumine sosai Diyana , kuma yayi Nasara a cikin
zuciyata , dan tuni zuciya ta takamu da san shi tuntuni , Diyana ta k'yalk'yale da dariya tana
fad'in " gaskiya da zangan sa a daren nan dana sheda masa cewa ya k'arawa malamin sa kud'i
, dan wannan tsayuwar da yayi masa ta dare yayi amfani , dariya sosai Sanam take tana fad'in "
wato dan kinji cikina shine zaki tsokaneni ko ? to ai ban sheda masa ina son nashi ba dan haka
har yanzu zuciyar sa acikin zulumi take , Diyana tace " ai aikin gama ya ruga da yagama tunda
har yayi nasarar shiga zuciyarki ai ya wuce gun , sosai suka sha hirar su wacce rabi duk labarin
Huneed Sanam ke bawa Diyana , a k'arshe sukayi sallama akan zasu had'u gobe a garden
wajen hutawa dan sake tattauna wa .........
Jaydeen sosai yasawa Mumyn sa rigimar sai an nemo masa gidan su Sanam , Hajiya
Halima tace " to yanzu My son a wanne estete take da zan tafi nemo maka ? shuru yayi na
wasu lokacin kafin yace " tana Estate d'in Area 11 kamar haka naji Direban daya zo d'aukar ta
ya fad'a , Hajiya Halima tayi murmushi sannan tace " to ka kwantar da hankalin ka zuwa safiya
sai mu shirya muje Area 11 d'in muduba cikin Estate d'in nasu , Jaydeen ba haka yaso ba so
yayi ace a daren nan Mumyn nasa taje ta dubo masa gidan su Sanam , dan ko sunan ta ma bai
rik'e ba sai dai zanen surar ta dayafi komai tafiya da hankalin sa har yatsaya masa aransa
,.......
Washe gari sai wajen Sha d'aya Sanam ta tashi daga bacci , dama batayi baccin gajiya ba
shiyasa bata tashi da wuri ba , abinka da wacce ibada bata dama ba , tana mik'ewa tashiga
toilet tayo wanka abinta tare dayin brush , tana fitowa ta zauna gaban Mirror tana shafa
mayukan ta masu tsadar gaske , sannan ta d'auko Humra masu k'amshi tabi jikin nata dasu ,
take tafara wani lafiyayen k'amshi tamkar amarya , Kwata kwata kwalliya ba damun Sanam tayi
ba , kwalli kawai tasa a idon ta sannan ta shafa lips stick a abakin ta , take tayi wani kyau na
daban tamkar kasace ta , tabbas duk Namijin da yayi tozali da Sanam dole zuciyar sa ta harba ,
wani kyau gareta me d'aukar hankali , ribom ta d'auko tashiga tattaro gashin kanta me uban
yawa wanda baya kitsuwa , tana saka ribom d'in ya zubo gadon bayan ta tamkar a indian film ,
bud'e wajen kayan ta tayi ta d'auko wasu riga da wando sababbi masu kyan gaske , rufewa tayi
sannan ta d'auko turarukan da Huneed ya kawo mata tashiga fesawa a cikin kayan , tana saka
kayan tasake yin wani kyau tamkar kasace ta , rigar ta tsaya mata iya cinya me k'aramin hannu
, shikuma wandon tamkar fela haka k'asan sa ya bud'e tare da wasu duwatsuna masu kyan
gaske , mayafin kayan ta yafa d'an k'arami ta rufe kanta sannan tasa filet d'in takalmi tafito daga
d'akin tayo k'asa.......
Jaydeen tuni ya shirya yasa Mumyn sa a gaba sun nufo Area 11 , dayake unguwa ce ta
masu dashi kuma bawani yawa gidajen ciki suke dashi ba tuni me gadin cikin Estate d'in
yagane wacce yake nufi , take ya sheda musu number gidan , wasu mahaukatan kud'i
Jaydeen ya d'iba yabawa me gadin tare da yi masa godiya , har k'asa ya durkusa ya ansa yana
musu godiya suka wuce ciki .....
Sanam na saukowa ta nufi dinning don karyawa , tana zuwa me aikin su tayi saurin had'a
mata tea tana rissinawa tana fad'in " ranki ya dad'e barka da fitowa tafatan antashi lafiya ,
Sanam batare da ta dube ta ba tace " lafiya taci gaba da danna wayar ta , sak'on Huneed ne ya
shigo wayar ai take tafara murmushi , Uwani ta rissina tana fad'in " ranki ya dad'e me zan had'a
miki a cikin kayan karin ? Sanam tace " jeki kawai zan had'a da kaina ta fara duba sak'on ,
kowanne sak'o na soyayya ne masu dad'in karantawa , nan Sanam ta shagalce wajen karan ta
sak'on Huneed tare da maimai tasu , .......
Tunda ga k'ofar gate Hajiya Halima tasan lallai ba k'aramin me kud'i bane me gidan , hon
sukayi me gadi ya lek'o dan ganin waye , ganin bai dan motar ba yasa ya fito ya k'arasa wajen
su , gaisawa sukayi sannan suka sheda masa su bak'ine sunzo gun matar gidan , megadi
yace " to Hajiyar tasan da zuwanku ? Hajiya Halima ta yi murmusjo sannan tace " batasan da
zuwan mu ba amman kaje ka sheda mata matar Ambasador ce tazo gunta , da sauri Mehadin
yace to bari naje nadawo , komawa tayi ciki dan shedawa Hajiya Nafeesa zuwan su , koda
yashiga yasamu Sanam sai wayar ta take sha abinta hankali kwance , sallamar ma batasan
yanayi ba , har Hajiya Nafeesa ta sauko daga sama ta amsa masa ya sheda mata bak'in datayi