Showing 9001 words to 12000 words out of 25334 words

Chapter 4 - GUDUNA AKE

10 Sep 2025

2703

hankali ta ke yawo da idonta dukkanin wasu sassan jikinsa kafin idonta ya sauke kan kyakkyawar fuskar dake d'auke da wani irin full lips pink masu matuƙar shek'i. Hancin nan kaman biro tsaban tsayi ya tafi da manyan idanuwan da ko ita Albarka. Tsananin bak'in kwayar idan nasa da girman idon nasa idan yana kallon ka sai kaji kaman mai kallon ruhin ka.

"Min ant?"

Taji kakkausar murya sa kaman saukar aradu. D'an firgita tayi saboda yanda tayi nisa wajen bege. Saida ta lashe leb'en ta daya bushe kamas ta buɗe baki zatayi magana , kaifin idonsa da yanda ya kafeta da manyan idanuwan sa, fuskar nan babu wani emotion yasa taji fitsari na neman kwace mata. Had'iya ta k'arayi ta k'ara buɗe baki amma ko kalma d'aya ta kasa fitowa. Gaba d'aya a firgice take da tsananin kyawun sa da kuma kwarjinin sa . Dif,dif ya nufota kaman wani bijimi. Aafiya batasan sanda ta juya da wani bala'in gudu ba tayi waje. Turus ya tsaya inda ta bari ya kafe k'ofar da ido. Wacece ne kuma wannan harta samu ikon shigo masa d'aki haka kai tsaye. Duk cikin masarautar nan ansan yanda baya son mata suna masa aiki. Why Malika zata turo masa ita don yasan bazata wuce wata Baiwar ba. To amma anya Baiwa ce? Yanda ta chaba ado haka. In har bai manta ba harda gwala-gwalai ya gani a wuyanta da hannun ta. Wacece ne wannan?. Kafin ya sake wani yunƙuri an sake buɗe had'addiyar k'ofar tasa an shigo kai tsaye. Wacce ta shigo yasa ya d'an saki ajiyar zuciya yana binta da kallo. Sanye take da alkyabba da aka Chab'awa ado da zinare. Alkyabba mai hula ce data rufe fuskatar ta ruf kaman rariya. Sannu a hankali ta maida k'ofar ta rufe saboda bayinta dake bakin k'ofar. A hankali ta juyo ta tako har inda Lk ke tsaye. Hannu ta kai ta yaye hular alkyabba data rufe mata fuska.

"RAINHA" (ma'ana Sarauniya da harshen PORTUGAL). Kyakkyawan murmushi tayi masa ta d'ago hannun ta daya sha ado da gwalgwalai ta shafa fuskar sa. Tsananin kyawun ta saiya firgita duk wanda ya ganta. Saboda haka ne take rufa fuska. MATILDA baturiyar k'asar Portugal ce. Sanadin had'uwar ta da Sarki KHALELULLAH ta musulunta har sukayi aure shekara takwas da suka wuce. Matilda ta girmi MALIKA nesa ba kusa ba don tayi shekara 50, amma zakayi mamaki idan ka ganta baza kace tayi shekara 25 da biyar ba. Kullum yarinya take k'ara zama ga wani irin shirtaccen kyau da take dashi mai firgita maza da sasu zama bayinta. Tunda ta shigo masarautar ABU DHABI ta shiga jikin LK sosai ta zame masa tamkar uwa. Kusan a yanzu yafi amfani da maganan ta akan ta Malika. Sosai sun samu sabani Saboda hakan, amma duk yacce Malika tayi LK baya tab'a daina bin umarnin Matilda.
Da yaranta na Uwa wato Portugal tayi masa magana don sosai ta koya masa yaren.

"Quem é aquela garota que acabou de sair do seu quarto?"

"Wacece naga ta fito daga d'akin ka yanzu?"

Kafin ya bata amsa suka tsinkayi muryar Malika data shigo ita da Aafiya basu kula ba.

"Matar sace"

Da azama suka juya suna kallon Malika dake takowa cikin izza da Mulki Aafiya b'oyenta. A tare suka maimaita.

"Mata?"

"Wife?"

Ran Matilda sosai ya b'aci. Wato Malika saboda taga bata nan taje garin su can Portugal wajen iyayen ta shine tayi masa aure bata sani ba?. Wato Malika bata tsoron abubuwan da suke faruwa duk lokacin da LAMEEN ya yi aure. Ido cikin ido suke kallon juna ita da Malika kafin ta maida idonta kan Aafiya. Wani irin kallo ta watsawa Aafiya da Allah kaɗai yasan abunda ke cikin ranta. Rai a b'ace ta rab'a ta gefensu ta fice daga d'akin. Lameen ji ya yi kaman ya rushe da kuka yana kallon mahaifiyar tashi dake kallonsa babu alamun wasa tattare da ita.

"Samu guri ki zauna Aafiya "

Babu musu ta zauna kan wata had'addiyar kujera . Hannun sa Malika ta kama ta zaunar dashi kusa da Aafiyan. Baki ya taune ya k'ara matse rigarsa da bai gama cirewa ba. Zama tayi kujerar dake fuskantar su tace

"Ga Aafiya matar ka dana aura maka ita yau da safe. Dukkanin wani tunani dake ranka ka ajiye sa gefe don bata amince da auren ba saida tasan kome ke faruwa. Du da haka tace tana son ka a haka zata zauna dakai. InshaAllahu zamu cigaba da Addu'a har Allah ya kawo mana sauki. Yanzu lokaci ya yi daya kamata ace ka ajiye iyali. Girma ka ke Lameen ba yaro ka ke komawa ba. Lokaci ya yi daya kamata ka hau kan kujerar mahaifin ka duk rashin sonta da ka ke"

Miƙewa tayi tsaye tana kallonsa ya sunkuyar da kai ya kasa cewa komai tsabar bak'in ciki. Wai sai yaushe Malika zata gane shifa mata ya tsanesu ne in general, saboda wata yarinya data tab'a shiga rayuwar sa wani lokuta da suka shud'e.Numfasawa tayi ta k'ara cewa

"InshaAllahu auren ka da Aafiya babu komai sai alkhairi. Zansa yanzu a kawo muku abinci. Ina mai umarta ku, ku fara yin sallah don neman tsari daga dukkanin wani sharri na b'oye dana fili. Naga kaman wanka zakayi Aafiya ki had'a masa ruwa ya yi wanka. Allahumma barikum"

Kai Aafiya ta d'aga cikin girmawawa duk irin matuƙar tsoron dake cinta. Kallonsa Malika ta k'arayi ganin har zusa lokacin kansa na k'asa ya kafe kafet da ido. Girgiza kai tayi ta juya ta fice rai a dagule.
Shiru ne ya ratsa d'akin bayan ficewar Malika. Aafiya ta cigaba da kallon sa a kaikaice ta k'asan ido tana k'ara kistima matsanancin kyau da yake dashi. Gefe tana shak'ar daddadan kamshi da jikinsa yake na vanilla and flowers. Tsaban yanda kamshin ya game jikinsa ,ya yi wanka ko baiyi ba, yasa turare ko aa. Koda yaushe kamshi yake mai sassanyan dad'i. Sama da minti d'aya suka d'auka haka babu wanda ya yi motsi sai bugun k'irjin ta dake k'ara tsannanta. Can ya miƙe bai kalli inda Aafiya take ba ya nufi wata arniyar glass door. Ko ba'a fad'a mata ba tasan hanyar banɗaki ne. A hanzarce ta miƙe ta bishi cikin banɗakin daya shige. Sarkewa numfashin ta ya yi ganin tamgamemen banɗakin data shiga dake d'auke da wani irin jacuzzi kaman swimming pool. Bata tsaya tunanin Lameen ba daya juyo yana kallonta da b'acin rai ya taune leben sa na k'asa. A hanzarce ta had'a masa ruwan wanka ta fice da sauri don ji take kaifin idonsa na neman shek'ata barzahu. Da ido ya bita harta fice kafin yaja wani dogon tsaki kaman mace ya hau cire ragowar kayan dake jikinsa.

B'angaren Aafiya d'akin ta dawo tana binsa da kallo. Tabbas duk kuɗin iyayenta. Duk fice fice da take kasashen duniya buɗe ido, wani abun ma b'ata taba ganinsa ba sai a nan. D'akin Lameen yaci sunan sa Aljanna duniya. K'ofa aka kwankwasa ta matsa da sauri ta buɗe. Wata baiwa ce ta shigo da wasu a bayanta riƙe da kayan abinci. Da girmawawa suka jera kayan suka fice. Guri ta samu ta zauna tana jiran fitowar sa. Sama da minti ashirin ya d'auka cikin banɗakin duk ta kotsa. Finally taji motsin tab'a k'ofar sa. A hanzarce ta daga kai ta kafe k'ofar da ido. Sai gashi ya sanyo kai in all his glory sanye da tawol dake d'aure k'ugunsa. Sai d'an k'arami dake rataye a wuyansa yana goge jik'akk'en gashinsa dashi. Wani irin had'iyar yawu tayi tana binsa da kallo tun daga k'afafuwansa harzuwa k'irjin sa. Tsabar yanda ta shagala da kallonsa bata lura da yanda ya ke mata wani irin kallo ba. Saida ta d'aga idonta zuwa fuskar sa. Lokaci guda ta saki wani irin mummunan ihu da saida gaba d'aya masarautar ta d'auka. Kafin Lameen ya yi wani yunƙuri ta zube k'asa a sume. Numfashi ya fesar mai zafi cikin ransa yace.
'Here we go'

A hanzarce ya yi k'ok'arin numfar inda take yashe a k'asa, amma kaman wanda aka kafe ya kasa motsi. Lokaci guda kuma ya kai hannu ya rik'e wuyansa da yake ji kaman an shake shi. Kakari ya fara yana wani irin tari daidai yaji muryar Malika na magana da bada umarni a b'alla k'ofar. Dazun ma daya sa suka shigo saboda yabar muk'ullin a jiki ne. Bayan an kawo abincin Aafiya ta ciresa ta dawo dashi ciki. Luu shima nashi idon suka fara rufewa numfashi ya masa wahalar fita. A take fuskar nan tayi jazur da ita na tsaban wahala . Har zuwa lokacin kokawa yake da koma menene yake tunanin ya shakeshi ta baya. To amma baiji komai a wuyan nasa ba sai hannun sa kawai. Gaba d'aya ya yi k'asa shima daidai Malika ta dannu kai d'akin. Ihu tasa da kiran sunansa tayo kansa a guje kafin ta k'araso tuni ya zube gurin a sume. A tare Malika da Matilda suka k'araso inda ya zube a sume. Da k'araji Matilda ta bada umarni a kira family doctor nasu. Aizak da Aryan suka fad'o d'akin suma a guje don tuni labari ya riske so. Saidai Matilda ta k'anannade shi kan cinyarta ta hana kowa ya tab'a shi sai Dr ya shigo. Tsaban taikaci Malika ta zuba mata ido ta kasa cewa komai. Rai a b'ace tasa aka d'auko Aafiya akayi waje da ita. Sosai gabanta yake mugun fad'uwa duk yanda take k'ok'arin danne wasu zafafan hawaye da suka cika mata ido saida suka zubo. Kan gadonta tasa aka kwantar da Aafiya da bata ko motsi. Duk a tunanin su itama ta mutu kaman sauran matan. Amma na Aafiya yafi ko wanne sauri don su alamu sun suna sai ya fara kusantar su hakan ke faruwa dasu. Yanda taga Aafiya da kayanta batayi tunanin wani abu ya shiga tsakaninsu ba tukun. Tanajin Aryan ya rungume ta ta baya. Hawaye ne kebin fuskarsa shima. Aizak yana can tare da Lameen da Matilda ta kafa ta tsare a kansa. Likitane ya shigo a guje ya yi kan Aafiya. Kallo d'aya ya yi mata ya yaga yanda take numfashi kad'an sai ka zuba ido sosai zaka kula. Numfashi ya sauke a hankali yace da Malika tana da rai. A gaggauce ya bata taimakon gaggawa. Malika ta sauke numfashi mai k'arfi tana kiran sunanyen Allah. Wai wannan wane irin abu ne?.











𝗚𝗨𝗗𝗨 𝗡𝗔
𝒜𝓀ℯ.





𝓐𝓼𝓱𝓪𝓷𝓽𝔂 𝓵♡︎𝓿𝓮






26/30.




Saida Lameen ya kwana biyu a sume sannan ya farfaɗo. Matilda ta kafa ta tsare ko nan da can bata matsawa. Malika ta kasa jurewa tayi mata tas ganin yanda k'arfi da yaji take neman rabata da d'an ta. Sosai sukayi fad'a Matilda tayi fushi wunin ranan ko hanyar Lameen batayi ba. A daren ranan ya farfaɗo twins dake d'akin a guje suka rungume shi. Da ido yake binsu yana son tambayar su ko Aafiya ta mutu. Aizak daya fuskanci abunda ke cikin ransa yace.

"Ya akhie. Ka kwantar da hankalin ka wannan karon koma menene ke bibiyar rayuwar mu bai samu nasarar kashe matar ka ba"

Numfashi ya sauke a hankali ya koma ya kwanta. Aryan dake waya ya mik'o masa da sauri yana cewa 'gashi' da ido yabi wayar kafin ga k'arata a kunne. Wani irin numfashi ya ratso wayar mai k'arfi murya Zain ta ratsa dodon kunnensa cike da damuwa yace

"Alhamdulillahi ka farfaɗo?"

Lameen bai bashi amsa ba yace "I'm coming "

"Dude ina Nigeria. "

"I know gani nan zuwa"

Baijira Lameen d'in ya k'ara cewa komai ya kashe wayar. Yana buk'atar guri da zaiyi breathing air. Away from all this. Malika ta fad'a d'akin cikin sauri. Kai tsaye ta rungume shi tana masa ya jiki. Rabonda ya kebe da mahaifiyar sa haka shi kanshi ya manta. Don haka ya yi luff a k'irjin ta. Ita ta sahi a gaba yaci abinci ya yi sallah. Da kanta ta had'a masa ruwa ya yi wanka ya fito. Saida ya gama shiryawa a taushe yace mata zai tafi Nigeria don ya samu salama a zuci. Bata musa ba ta amince masa tana son ta kwato d'anta daga hannun Matilda dake nemanyi mata k'ak'anakayi. Aafiya dai har zuwa lokacin bata farfaɗo ba saidai numfashinta ya daidaita. Idan ka ganta kaman wacce ke bacci. To sanda ya diro Nigeria baiyi tunanin Fate zai k'ara had'ashi da macen da yake nema ba ruwa a jallo saboda wani unfinished business dake tsakanin su.


Present .


Numfashi Zain ya sauke yana cigaba da kallo Lameen da harzuwa lokacin idonsa ke a lumshe. Tabbas Lameen na tare da sirri mai ban aljabi. Ga dai kyau iya kyau Allah ya bashi, amma yana neman tashi a banza. Duk sanda ya yi arba da wata mace sai wani mummunan abu ya faru. A yanzu ma yasan babu tantama Jaleela taga wani abu tattare dashi da ya yi sanadin firgitar ta harta fice haka a guje. Wayarta k'irar iphone x ya juya a hannun sa da tunanin hanyar da zaiyi ya buɗe ta.

"Let me help you with that "

D'agowa ya yi ya kalli Lameen daya mik'o masa hannu. Kai ya d'an jinjina ya mik'a masa wayar. Wato Lameen ba despite duk wannan abun da yake faruwa dashi, he's a damn genius and hacker. Ya iya hacking na ko wane abu sai dai in baiga dama ba. Wayar ya juya a hannun sa ya yi d'an murmushi. Dan danne danne ya yi saiga wayar ta buɗe. First abunda ya fara cin karo dashi jikin screen d'in wayar shine hoton ta da Anees. Suna sanye da k'ananan kaya kansu babu d'an kwali daga ita har Anees gashin su a sake ya bazo ta ko ina ga iska da take kad'ashi. Hoton da sukayi ne wani amusement Park data kai Anees. Ta d'agata suna dariya akayi hoton. Sunyi bala'in kyau kaman wacce suka zo daga wata duniyar. Ido ya zubawa hoton yana jin wani irin abu na ratsa shi yana kallon Anees.

'She has a daughter?' (Tana da y'a?)

Ya furta a fili ya d'ago yana kallon Zain daya zuba masa ido. Cikin rashin fahimta yace

"What. Wacece take da y'a?"

Fuskar wayar Lameen ya nuna masa yana tunanin . Idan har tana da y'a? Ta tab'a aure kenan? Ko kuma a hanyar prostitution(karuwancin) ta sameta?. Haka nan kawai yaji wani abu ya chake shi a zuciya ya yi saurin kawar dashi yana d'an girgiza kai. Why do i care?. Tunda Allah ya sake had'amu, zanyi making sure life nata is a nightmare har sai ta durkusa ta bani hak'uri. Smirk ya saki daya sa Zain shan jinin jikinsa yace

"Me ka ke tunanine?"

"Nothing "

Bai bari Zain ya k'ara cewa komai ba ya miƙe ya fice daga d'akin rike da wayar a hannun sa. Yana fitowa kuwa guards nashi suka kawaye shi. Duk inda ya wuce ya zama abun kallo. Mata duk sun mutu a kansa maza kuma suna burin ina ma dai sune. Suna kallo ya shige shegun motocin sa dake fake a gurin. K'aramar motar Pecanto dake kusa da tashi ya zubawa tsumammun idanuwan sa. Motar waye wannan har ta iya fakin kusa da motocin sa?. Hmm.

"Find who's car is this" (ka nemo motar waye wannan)

Yace da right hand Bodyguards nashi. Da girmawawa yace " yes, Boss)

Har suka fice daga club d'in yana juya wayar Jaleela tafin hannun sa. Despite all the burika dayaci yanda zaiyi making life nata he'll, bazai ignore na kyau da sukayi ba ita da Anees. Yana son ya yi finding out y'ar waye wannan. Yarinya is so beautiful to be true. Tsintar kansa ya yi da shiga gallery nata ya cigaba da kallon hototun nan su ko Allah zaisa yaga wani clue da zai nuna uban Anees. But baiga komai sai hoton Jaleela kawai da Anees. Baya son zarginsa ya zama gaskiya. In dai kuwa har Anees bata da uba, oh life na Jaleela is about to get much worse. Wani irin zafi zuciyar sa yaji tanayi hakanan kawai. Abubuwa da suka shude shekarun baya suna masa yawo cikin ido. A fili yace

"She's a liar. Duk son Allah nata da Manzon sa. Har take iya kiran wasu da sunan y'an iska. At the end ita ce y'ar iskar ashe?. What a snake"

" you will pay for what you did. Just wait am coming for you miss Aleeyna "

Smirk daya saki sai ya matuk'ar bawa mutum tsoro. Bodyguards nashi mai suna James dake zaune gefen zaman mutum banza ya had'iye yawu kutt yana shivering.
Haka ya yi ta bincike a wayar . Duk wasu mutune da take hulda dasu ya d'auke su cikin d'an k'ank'anin lokaci.

To Jaleela da rawar jiki ta shige gida bayan Lami ta buɗe k'ofar. Mamaki ya cika Lami ganin yanda ta shigo a firgice babu takalmi bare d'an kwali. Hankali a tashe ta fara karanta Auzubillahi da dukkanin wasu ayoyi da suka zo bakinta. A tunanin ta ko Jaleelan tayi gamo ne. Yaraf Jaleela ta zube k'ofar d'akin ta. Had'a kai tayi da gwiwa tana wane irin kuka mai ban tausayi. Sai a lokacin Lami ta sauke ajiyar zuciya saboda wani irin tsoro daya rufeta. D'an nesa da ita kad'an ta tsaya a tsorace tace

"Hajiya lfy? Wani abu ya faru ne?"

Jaleela ta kasa cewa komai sai kuka kawai da take. Jikin Lami ya yi sanyi sosai a hankali ta matso ta durkusa kusa da ita. Rungume ta tayi tana d'an buga bayanta. Da ace tabbas Jaleela na tare da uwarta tasan cewa tabbas abunda take buƙata kenan. Aikuwa ta shige jikinta ta cigaba da kuka sosai tana kiran Ammi kaman wata k'aramar yarinya. Jikin Lami ya k'ara sanyi sosai. Menene ya yi sanadin daya sa Jaleela ta bar gida?. Sun d'auki sama da minti goma a haka kafin Jaleela ta janye ta yunƙura ta miƙe tsaye ta shige d'aki. Kai tsaye gadon da Anees ke kwance tayi ta jata ta matse a k'irjinta kaman wani zai kwace ta. Sosai take fad'a da zuciyar ta.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login