Showing 18001 words to 21000 words out of 33602 words
zai juye ruwan ya ji muryarta can ƙasa tana cewa.
"To yanzu me ya rage? Ai ƙarshen tuka-tuka tik, mun yi waya da shi ya sayar da gonar. A tsammaninsa sayar da wannan gonar shi ne rufin asirinsa, bai san ɗaya daga cikin manyan ƙofofin tashin hankalinsa ne suka buɗe ba." Amsa mata aka yi daga can ɓangaren sai ta cigaba, "Wai ka san waye Alhaji Dikko a kan kuɗi kuwa? Kai dai ka zuba ido ka sha kallo."
Fauwaz ji ya yi zuciyarsa ba za ta iya ɗauka ba, don haka ya sauke bokitin kansa ya ƙarasa cikin ɗakin ya ce.
"Ke wacce irin mace ce da ba ta tsoron Allah?"
"Irin wacce mahaifinka yake muradin rayuwa da ita."
Tani ta ba shi amsa tana tsare shi da ido, wata irin tsanarta ta sake mamaye shi. Ya dube ta ido cikin ido ya ce. "In Shaa Allahu yau zan sanar da Abba wace ce ke, da irin cutarwar da kike yi masa." Wata irin dariyar izgilanci ta saki ta ce.
"Ai babban kuskuren da ka tafka a rayuwarka shi ne gangancin sauraron kalaman da nake yi yanzu. Waɗanda suka ingiza ƙeyarka har ka tsoma mini baki, kana tsammanin furucinka zai yi tasiri a wurin mahaifinka?"
Ta wurga masa tambaya tana tsare shi da ido, shi ma ita yake kallo babu ƙiftawa. Yana jin kamar ya yi tsalle ya maƙure wuyanta, yana nan tsaye ya ji ta cigaba.
"Da ace kalamanka suna da tasiri, da a daren da ƙanwarka za ta yi mushe sun ratsa jikin mahaifinka."
Dum! Ya ji a tsakiyar kansa tamkar an buga masa guduma, ya runtse idonsa da sauri yana hasko fuskar Abida cikin mawuyacin hali. Tani ta nuna shi da yatsa cikin wata irin murya mai cike da zallar rashin imani ta ce.
"Ka jira mummunan saƙon da zai iso gare ka..."
Ba ta kai ga dire kalamanta ba, ta ji sallamar Abba ya shigo gidan. Haka ya sa ta saki murmushin ƙeta sannan ta rushe da kuka.
ƊANBATTA
Duk abin da yake faruwa Zuwaira tana daga ɗaki laɓe a jikin labule tana kallo. Farincii ne ya mamaye ta, don ita kanta ba ta san ya shigo ba sai hayaniyar Inna ce ta tashe ta. Sai da ta ga Malam Hasan ya shige banɗaki sannan ya fito tana yamutsa fuska, kan tabarmar da Inna ta shimfiɗa ta hau ta zauna. Cike da kissa da makirci ta ce.
"Inna lafiya kike ta faɗa? Ni ma bacci ne ya kwashe ni da yake ba ni da lafiya, na kira Yaya kuma ya ce mini ya yi nesa da mu ya gangara sabon titi."
Sakin baki Inna ta yi sannan ta ce, "Wato bayan cin amana har ƙarya Hasan ya koya kenan? Dole ya ce miki haka mana tun da yana liƙe a ɗakin baƙar munafukar nan." Zuwaira ta sake narke fuska ta ce, "Ai shi kenan, amma magani fa na ce ya kawo mini ɗazun."
"To idan kika mutu ai ba asara ya yi ba, tun da ba 'yar gaban goshinsa ce babu lafiya ba. Bari ya fito zai zo ya same ni..."
"A'a ki rabu da shi Inna, ni zan yi masa maganar. Idan kika masa zancan muna shiga ɗaki a kaina zai huce." Zuwaira ta tari numfashi Inna, Takaici ya sake rufe Inna ta ce.
"Oh ni Kulu na haɗu da ƙaddara, wallahi da na san kalar asirin da uban yarinyar nan ya yi wa Hasan da tuni na ba wa almajiran soro sadaka sun ba yara zikiri an karya shi."
Suna nan zaune Malam Hasan ya fito ya wuce ɗaki, a lokacin da ya shiga Rakiya tana duƙunƙune a cikin zanen gado tana kuka. Sosai ta ba shi tausayi, don har a ransa yana ji su suke cutar da ita a zamantakewar da suke yi. Sannan abin da Inna ta yi masa ba don mahaifiyarsa ba ce, da babu abin da zai hana shi ɗaukar mataki a kanta. Wanne irin abin ne yake damun Inna da za ta shigar masa ɗaki a lokacin da yake keɓewa da iyalinsa? Me ya sa duk cikin 'yan'uwansa babu wanda Inna take yi wa cin kashin da ake yi masa? Me ya sa ba zai samu farinciki ba? Waɗannan tambayoyin ya shiga jefa wa kansa. Shasshekar kukan Rakiya ne ta dawo da shi daga duniyar tunani, ya zauna a kusa da ita ya riƙo hannunta. Da sauri ta fisge ta sake cusa kanta a tsakanin cinyoyinta.
A yadda yake jin tausayin Rakiya, da ace zai iya rabuwa da ita da a take zai ba ta takardarta domin ta samu salamar rayuwa. 'Idan na sake ta ina za ta je? Da su wa za ta fara rayuwa? Shin na yi mata adalci idan na rabu da ita? Ko kuwa na riƙe amanar da mahaifinta ya damƙa mini?' Tambayoyin da ya dinga ƙissimawa a zuciyarsa kenan.
'Koda babu alaƙar aure a tsakaninku, kuma koda mahaifinta bai damƙa maka amanarta ba. Kai mai zame mata uwa da uba ne, domin mahaifinta ya yi maka gatan da iyaye suke yi wa 'ya'yansu.
"Ba zai yiwu ba."
Ya furta a fili cikin suɓutar baki ba tare da ya yi tsammanin zancan zai fito ba. Sake riƙo hannunta ya yi, tana niyyar ƙwacewa ya riƙe ta tsam a jikinsa. Ya kai bakinsa saitin kunnenta cikin tattausan lafazi ya ce.
"Ba zan hana ki kuka ba, ki yi kukan idan har shi zai sanyaya abin da yake cikin zuciyarki."
Kamar Rakiya tana jira, ta sake sakin sabon kukan da kana ji ka san daga ƙasan zuciyarta yake fitowa. Bubbuga bayanta ya shiga yi, har sai da ta ci kukanta mai isarta ya ce.
"Ki yi haƙuri Rakiya, komai ya yi tsanani maganinsa Allah. In Shaa Allahu da jarina ya ƙara ƙwari za mu koma cikin gari, na sani ba a kyauta miki. Ana zalintarki kuma ana, shiga haƙƙinki, amma In Shaa Allahu zan yi bakin ƙoƙarin gyara wasu abubuwan koda ba a daina yi miki duka ba."
Muryarta a dashe ta dube shi ta ce, "Ba na son ka yi abin da zai sa ka saɓa wa mahaifiyarka, ina son ka cigaba da yi mata biyayya. Kamar yadda ka faɗa ne watarana sai labari..."
"Wai ba za ka yi ka fito daga ɗakin ba ne Hasan? Ka saka mace a gaba idan ba ka fita nema ba me za a ci?"
Kalaman Inna suka katse maganarta, murya babu walwala Malam Hasan ya ce.
"Yanzu zan fito."
Daga haka ya shiga kintsa kansa sannan ya ɗauki kwandon turarensa ya fita. Bayan fitarsa sai da Rakiya ta sake shan sabon kukanta, ta ɗauki hijabi ta saka sannan ta fita banɗaki domin ta gyara jikinta. Tana fita kuwa Inna ta dasa zaginta Zuwaira ta shiga zuga ta, bayan ta fito har ta kusa shiga ɗaki Inna ta ce.
"Ki sako kaya ki fito ga surfen gerona nan kwano uku yana jiranki." Cikin biyayya Rakiya ta amsa sannan ta shiga ɗaki. Kamar yadda ta amsa tana gamawa ta fita ta karɓi geron, tana surfawa Inna tana wanke ta da baƙaƙen maganganu.
A wannan ranar Malam Hasan tun da ya shiga ɗakin Zuwaira ta sha jinin jikinta, amma sai ta nuna kamar ba ta fahimci yanayin da yake ciki ba. Don ko abincinta bai ci ba, dama kuma tun da ta tsiri rashin lafiyar ƙarya ta saka Inna ta sa shi kwana kullum a ɗakinta ya daina cin abincin kirki. Bai fi ya ci cokali ɗaya ya ce ya koshi, a wannan ranar da ta tambaye shi ko kula ta bai yi ba. Yana nan kwance ya ji ta ɗora hannu a jikinsa, cikin zafin zuciya ya fuske ta gefe. Da yake ya san halinta sarai, Zuwaira irin jarababbun matan nan ne da ba su da haƙuri.
"Wai me ya sa kake yi mini haka ne, ko don ka ga na damu da kai? Kusan kullum kafin ka ba ni haƙƙina sai ka wulaƙanta ni."
Zuwaira ta furta a narke cikin damuwa, tashi zaune Malam Hasan ya yi. Ya ji tsanarta ta sake mamaye shi. Da sauri ta ɗan ja baya, don ta yi tsammanin mari zai kai mata. Cikin tsana ya nuna ta ya ce.
"Ke wacce irin mai son kanta ce? Ashe kin san halin da kike shiga amma kika sa nake danne haƙƙin Rakiya? Shin kina lissafin yau kwana nawa rabon da na kwana a ɗakinta? Kullum da kalar ciwon da kike tashi da shi, saboda kin san Inna ta tsaya miki ko? To bari ki ji, tun da abin na ki haka ne ni ma daga yau babu wani abu da zai sake shiga tsakanina da ke."
Da sauri ta ɗago ta dube shi, ganin babu alamar wasa a fuskarsa ya ta miƙe ta ce.
"Ai kuwa dole Inna ta ji, don wallahi ba zan yarda ba."
Tana gama faɗa ta ɗaga labulen ɗakin, cikin ɓacin rai ya nuna ta da yatsa ya ce.
"Wallahi tallahi kin ji na rantse miki, idan har kika sake kika fita daga ɗakin nan sai na sauke igiyar aurena uku da suke kanki. Sakarai wacce ba ta san sirrinta ba, ballantana na mijinta. Wai ganin ina yi wa Inna biyayya gani kike ba zan iya rabuwa da ke ba? Bari ki ji, daga yau za ku cigaba da raba kwana bibbiyun da kuke yi a baya. Idan kuma hakan bai yi miki ba sai na sauwaƙe miki, ƙarƙari na ɗauki matata na bar garin ba tare da kowa ya sake gani na ba."
Yadda ta ga ransa ya ɓaci jikinsa har yana rawa ya sa ta shiga hankalinta, don ta san shi sarai yana da matuƙar haƙuri amma idan ransa ya ɓaci ba ya ji ba ya gani. Jiki a mace ta koma gefen gado ta kwanta, Malam Hasan ya miƙe ya zira doguwar rigarsa ya fice daga ɗakin kai tsaye ya wuce ɗakin Rakiya. Tana gani ta gefen labule ya shiga ɗakin Rakiya, amma yadda take ƙaunar Malam Hasan ya sa ta ji ba ta shirya rabuwa da shi ba. Don haka ta koma ta kwanta tana hawaye, saboda wani irin zafin kishinsa da take ji.
Tun daga wannan ranar Malam Hasan ya raba musu kwana, kuma koda Inna ta ga haka da ta fara faɗa Zuwaira da kanta ta shiga kare Malam Hasan da cewar ita ce su cigaba da kwanansu kamar yadda suke yi saboda ta samu lafiya. Hakan ya sa Rakiya ta samu 'yancin kwana da miji, sai dai wasu ƙalaubalen da ba a rasa ba waɗanda ta yi sabo da su har suka zamwemata jiki.
An yi haka da wata biyu Zuwaira ta samu ciki, tun bayan da ta yi ɓatan wata ta fara tsiro da rashin lafiya duk da cikin mai sauƙi ta same shi. Inna tana ganin haka ta tasa ta a gaba suka tafi asibiti, sai ga shi gwaji na farko aka tabbatar da tana ɗauke da cikin wata ɗaya da sati ɗaya. Tun a asibitin Inna ta kira Malam Hasan ta sanar da shi, bayan da suka je gida a ranar wuni ta yi tana habaici da yarda wa Rakiya maganganu. Malam Hasan abu biyu ne ya haɗe masa, na farko yana farinciki da Allah ya sake azurta shi da rabo. Sai dai ya so a ce a jikin Rakiya ne, na biyu kuma yana fargabar sabon ƙalubalen da Rakiya za ta fara fuskanta daga wurin Inna. Don tun a ranar da aka tabbatar da cikin Inna ta kira Rakiya, ta kafa mata dokaki dangane da aikin cikin gidan.
"Ke Rakiya ina ce dai kin lura arziki ya ƙwanƙwanso mana ƙofa, wacce ta kasance irin albarka ta buɗe masa." Shiru Rakiya ta yi, don ba ta fahimci kalaman Inna ba.
"To ina nufin ciki Zuwaira gare ta, don haka ba kowanne aiki za ta dinga yi ba. Na faɗa miki ne domin idan kina da wani shiri ki ɗaura ɗamara, domin wannan cikin sai an haife shi lafiya kuma ya taka ƙafa shi ma ko ita ma sun hayayyafa. Domin mu gadon haihuwa ne ba juya ba."
Rakiya ta ji wani abu ya soki zuciyarta, amma sai ta danne ta saki murmushi ta ce. "Ma Shaa Allah, wannan abin farinciki ne. Allah Ya buɗi ido lafiya."
Inna ta yamutsa fuska tana taɓe baki ta ce, "Amin, idan ma bai kai zuci ba kanki. To ina son ki sani yanzu aikin gidan nan gabaɗaya ke za ki dinga yi, har zuwa lokacin da cikinta zai yi ƙwari."
Zuwaira da ke gefen Inna tana cin ɗata tana yatsina ta yi zaraf ta ce, "Inna hatta girkin ma ta dinga haɗawa ranar kwanana." Rakiya ta ɗago suka haɗa ido, Zuwaira ta murguɗa baki ta cigaba da cin ɗatarta. Inna ta dubi Rakiya ta ce.
"Kin ji dai abin da ta ce? Za ki dinga komai na gidan nan, idan cikin ya girma sai mu san abin yi."
Muryar Rakiya a raunane ta amsa wa Inna, bayan Inna ta sallame ta ta wuce ɗakinta. Tana shiga ta zauna ta fara zubar da hawayen tausayin kanta.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[16/05, 18:10] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
https://chat.whatsapp.com/LyQRbgQCzbL9iUHgPoeyO2?mode=gi_t
SHAFI NA BAKWAI
Sai da Rakiya ta ci kukanta mai isarta sannan ta ɗebi ruwan randarta ta ɗaura alwala a ɗakinta. Don tana gudun kada ta fita, su Inna su ga fuskarta su ɗauka maganar cikin ce ta saka ta kuka su yi mata mummunar fassara. Uwar ɗakinta ta shiga ta gabatar da sallah raka'a biyu. Ta roƙi Ubangiji da ya yaye mata damuwar da ke ƙunshe a zuciyarta, bayan ta gama addu'ar ta ji sanyi a ranta don ta ji kaso mafi yawa daga cikin damuwarta ta yaye.
Rakiya ita ta cigaba da duk ayyukan cikin gidan, tun daga kan shara, wanke-wanke, wankin banɗaki da sharar turken awaki zuwa girki duk babu mai tallafa mata. Hatta abinci wani lokacin Inna cewa take ta zubo wa Zuwaira, ita dai Zuwaira sai dai idan girki ya zagayo kanta ta karɓi miji. Don ta lura a yanzu yana ba ta kulawa, kuma duk abin da ta ce tana so bakin gwargwado yana yi mata. Sai dai abu ɗaya ne ba ta jin daɗi yadda ta ga har lokacin bai fifita darajarta a kan ta Rakiya ba. Amma abin da yake damunsa bai wuce yadda ake yake cakuɗewa Rakiya ba, tun da ya lura a ɗan tsakanin nan har duhu ta yi duk da hasken fatar da take da shi. Da ya yi yunƙurin yi wa Inna magana sai Rakiya ta hana shi, saboda ta san ko ya yi maganar ba za ta sauya zane ba sai ma wani ƙalubalen da za ta sake fuskanta.
Watarana Rakiya ta gama aikin gidan tas, har ta ɗora abincin rana da yake rana ta yi. Inna ta ɗebo mata kayan wankinta, ta ce ta wanke mata nan take. Ta gaji sosai, domin bayanta har ciwo yake mata.
"Na ce Inna idan babu damuwa ko na bari zuwa gobe da sassafe sai na tashi da wankin?"
Rakiya ta furta a ɗarare, Inna da har ta nufi ɗaki ta waigo ta ce. "Ai da uwarki ce ta ba ki wankin ba za ki faɗa mata haka ba ko?" Shiru Rakiya ta yi, Inna ta gama zazzage mata rashin mutumci ta yi gaba. Babu yadda ta iya, haka ta ja kujera ta zauna, ta haɗa ruwan wankin don ba za ta iya wankin a sunkuye ba. Tana cikin wankin Zuwaira ta fito da nata kayan, tana zuwa kan Rakiya ta watsa mata cike da izgilanci ta ce.
"Ga nawa wankin nan, ciki ne ya hana ni iya taɓa ko rigar mama na wanke ballantawa kayan sawa."
Da ido Rakiya ta bi kayan, saboda tsabar wulaƙanci har da wandunan pant da rigar mama waɗanda suka yi duƙun-duƙun saboda datti. Rakiya ta dube ta ta ce, "Ba zan yi miki wanki ba."
Zuwaira baki ta buɗe cike da mamaki ta ce, "Au ni kike faɗa wa haka?"
"Na faɗa miki Zuwaira, ko kin ɗauka tsoronki nake ji? Ko kuma kin yi zaton ni baiwarki ce?"
Rakiya ta furta a hassale, Zuwaira ta saki dariyar izgilanci ta ce.
"Mene ne marabarki da baiwar to? Ko kin ɗauka kina da sauran amfani wanda ya wuce ki ci ki yi kashi da aikin gida?" Rakiya ba ta kula ta ba ta cigaba da wanke kayan Inna, Zuwaira ta koma ta gabanta ta sake cewa.
"Ki yi ki mayar da hankali ki wanke mini su tas, idan ba haka ba wallahi sai ranki ya ɓaci. Banza juya marar mamora ballantana amfani."
Furucin Zuwaira na ƙarshe ne suka daki zuciyar Rakiya, kamar ba za ta kula ta ba sai ta ɗago ta ce. "Da Ubangiji kike, domin Shi ne ya ba ki cikin, kuma na tabbata ni ma bai manta da ni ba."
Cikin shewa irin ta izgilanci Zuwaira ta ce, "Ahayyee! Lallai fa sumumu-kasau an samu bakin magana, ai ke da haihuwa sai dai ki ga ana yi. Ko mugun halin bokan ubanki ya isa ya hana ki haihuwa...'
"Kada ki sake zagin mahaifina!"
Rakiya ta furta mata da wata irin murya gargaɗi, cikin raini Zuwaira ta ce.
"Uban naki wata tsiyar ce da kike kumfar baki a kansa..."
Tas! Rakiya ta sauke wa Zuwaira mari a fuska, zaro ido waje Zuwaira ta yi tana mamakin wacce ta mare ta. Don haka ta wage murya cikin kururuwa ta ce, "Ni kika mara?"
"Na mare ki, ko yanzu kika yi gangancin sake zagin mahaifina sai na ninka miki wanda ya fi shi."Rakiya ta furta tana tsare ta da ido, Zuwaira ta tsorota da yadda ta ga ran Rakiya ya ɓaci. Amma don kada ta nuna mata ta ji tsoro ya sa ta dake ta sake cewa, "An