Showing 18001 words to 21000 words out of 26640 words

Chapter 7 - MURADIN ZUCIYA COMPLETE

28 Sep 2026

727

ita ta kula da yarinyar da taimakon babbar hadimarta Laraba.

Har aka gama hidima

n aka watse Momma bata nemi sanin inda aka kai Fadwan ba haka zalika ko da yan uwanta sun tambayeta inda Yarinyar take bata dogon zance akai.

Sai washegarin ranan su Aina'u suka fara shirin tafiya, sai da suka gama kintsawa tace da Madina "Muje muyi sall

ama da Uwah yanzu" da haka suka fito Babban falon sashen sai suka hadu da Papa da shima shigowarsa kenan tareda Abdulrahman a biye dashi, gaisawa sukayi dan rabonsu dashi tun daren da suka iso sai dai Momma taje sashensa sannan ta koma wajensu, sai gamuwar

tasu tayi wuya. Da fara'arsa yace "Mun gode da hidima fa Maman Kasim" ya kalli Madina "Mungode Khadija" fuska a sake Aina'u tace "Ba komai mune da godiya, Allah ya raya zuri'a" yace "Amin, an kawo muku yar'uwartata kun ganta kuwa?" cike da waskewa tace "E

h mun ganta, Allah ya taya riqo ya bada lada", sai Papa ya amsa da "Amin summa Amin, ba dai ayau zaku koma ba" nan ma tace "Yau ne, zuwa anjima in Allah ya kaimu" sai yace "Okay Kamal zai kaiku" ya juya ga Abdulrahman dake bayansa yace "See to it please, y

azo da wuri kar su jirashi" ya amsa da In sha Allah sannan su Aina'un sukayi godiya, Papan ya sake cewa "Agaishe da Honorable da Allah, mungode sosai" ta amsa sannan suka fice shikuma ya nufi nasa sashen. A falon Uwah suka sameta tareda wasu matan dattawa

guda biyu, bayan sun gaisa aka kawo musu kayan ciye ciye sannan tace da Laraba ta dauko musu Fadwan. Da ta fito da yarinyar sai ya zamto Madina ce ta kusa da ita amma sai ta kafse taqi karbanta wanda yasa Aina'un miqa nata hannun da sauri ta karbi Fadwan d

ake nannade a towel tana bacci, da fara'a tace "Ma sha Allah, Uwah kinga yarinya tas da ita" fuska a sake Uwah tace "Sai Ma sha Allah" tace "Allah ya taya riqo yasa ta zamo cikon addinin muslinci" Matan ne suka riga Uwah amsawa sannan itama tace Amin tana

lura da Madina da tace "Allah ya raya".

Bayan kwana biyu Uwah ta kira Papa zuwa sashenta da dare, ita kadai ya samu zaune riqe da Fadwan a hannunta tana jiran isowarsa, sai da suka gaisa sannan ta fara magana cikin nutsuwa "Ban kasance mai kai idanuna a

cikin gidanka ba sai wannan karon da yazama dole, da farko banyi niyyan saka hannuna a lamuran da suke tafiya da iyalinka ba amma gudun sai ta baci azo ana dana sani yasa zan yi magana" sai Papa yayi shiru yana sauraronta har ta sake gyara zama ta yi masa

tambayan dake ranta tun dawowarsu qasar "Shin da amincewar matarka ka dauko marainiyar Allah'n nan kamar yanda ka fada mana?" da fari shiru Papa yayi sai kuma ya d'an sauqe numfashi sannan yace "Har yanzu muna fahimtan juna akai tukunna" sai itama tayi shi

ru tana kallonsa. Tasan za'ayi haka dan tun ranar zuwansu taga hakan shimfide a fuskar matarsa amma sai ta kawar da komai. Jin shirun nata yasa Papa yace "Babu matsala in Allah ya yarda, nasan zata kula da ita" sai ta dan hade fuska tace "Shine har aka gam

a waliman aka kwana biyu bata nemi yarinyar ba?, Yau kwana uku kenan jinjirar nan tana hannuna, ai ko ba komai sai ta biyo bayan 'yarta indai har ta karbeta a matsayin hakan" nan kuma Papa yayi shiru yanajin bacin rai na taso masa, ta sake cewa "Amma ba da

muwa, yarinya dai in har riqonta zai zamo da mishkila sai ku bani ita in riqe ai" sai lokacin ya dago yana kallon mahaifiyar tasa, a nutse yace "Da yardar Allah za'a gyara hakan" sai tayi murmushi sanin cewa a kaikace yake fada mata bazai iya bata yarinyar

ba, ganin haka sai shima ya sake cewa "Inason ta taso cikin 'yan'uwanta ne su shaqu, a ganina ta hakan ne zasu samu hadin kai da junansu batareda sun wareta ba" kadan ya rage Uwah bata tabe bakinta ba saboda a yanda tasan matar d'an nata zuwa yanzu ma ta

ware yarinyar daga cikin 'ya'yanta, sai kawai ta danne komai tace "Allah ya rayasu gaba daya" ya amsa da Amin. A daren ranan tasa aka maida Fadwan sashen nasu gurin Habiba ta cigaba da kula da ita.

Bayan sati biyu Papa ya shirya tafiya Abuja, a inda bab

ban companynsu yake aiki. Tafiyarsa America yasa Abdulrazaq daya kasance daya daga cikin executive directors yake running a gurbinsa while Abdulrahman kuma yake running branch dinsu na Kano. Sai yanzu da dawowar shi Papan tasa zai cigaba daga inda ya bari

dan shine President a Empire din nasu sannan Mai martaba kuma chairman gaba daya. A ranar da zai tafi sai da ya sake maganan kulawan Fadwan da Momma, suna zaune tana tsiyaya masa tea dinda hadimarsu ta kawo masa while shi kuma yana duba wasu takardun da za

i tafi dasu gurin aikin. Sai da ta gama zuba masa sannan ya ajiye takardun ya karbi Khadijah dake riqe a hannunta daya, sai tace "Da ka fara da tea din tukunna" bai amsa ba ya cigaba da wasa da Khadijan, sai can ya dago yana kallonta yace "Fatima, fadamin

ya zakiji in ace yau ba kya raye kuma aka rasa mai kula mana da Khadijah" sai ta hade girar ta cikin rashin fahimta, ya sake cewa "Ina miki kwatancen hakan ne da yanda har yau kika kasa karban Fadwa a qarqashin kulawarki" sai ta dinke fuska tace "Koda 'yan

'uwanka basu kula dasu ba nasan nawa 'yan'uwan bazasu taba barin 'ya'yana a wulqance ba" ya sake danne komai sannan yace "Kika sani ko ita tafi namu 'ya'yan gata amma Allah ya rabota da kowa nata" sai ta dan juya kanta rai a bace ba tace komai ba, anutse y

a sake cewa "All I'm saying is that, sai ka taimaki wani sannan Allah zai dubi naka a rayuwa Fatima, Think about it. Banason yarinyar nan ta taso ta fahimci tun tana da qarancin kwanaki a duniya kika gujeta da duk abunda ya shafeta, bamuda tabbacin me Alla

h ya ajiye mata a gaba, me zata zamo agaba, ko kuma wani irin kaddarar ce a harde tsakaninki da ita. Akwai mutanen da ko baka son kusancinsu a gareka sai Allah ya barsu a kusa dakai na har abada babu rabuwa, wanda babu yanda zakayi in baka so su ba. Ki far

a taming zuciyarki tun yanzu a kanta in ba so kike Allah ya gwada ikonsa a tsakanin ki da yarinyar nan ba" da haka ya dauki shayinsa ya fara kurba amma har sannan bata juyo da kanta ba tana kallon Tv dake aiki a falon.

Paid book 500

Fatima Musa Maina O

pay

Shaidar biya : 08134692758

MURADIN ZUCI

📖



Bintu Musa

Chapter 10

Free page

A wannan tafiyar da Papa yayi sai ta zamo daidai da tafiyar su Mai martaba da Uwah zuwa saudiya yin Umrah. Sai da yayi wata guda kafin nan ya fara shiri

n komawa gida. Bayan ya sallama sauran ayyukansa ga qaninsa Abdulrazaq da yake zama da iyalinsa anan Abujan sannan ya tafi. Amma daren ranar da ya dawo sai da zuciyarsa ta tsinke da aka miqo masa Fadwa a hannunsa yana kallonta. Cikin sati hudu-sati hudu ka

wai yarinyar ta fita daga hayyacinta kamar ba jinjira ba, tayi wani irin bala'in rama har wasu quraje ne suka fito mata kamar

na qyanda gashi babu alamun kula a jikin yarinyar kwata kwata. Danne ransa yayi ya riqe yarinyar baice komai ba, bayan an kawo mas

a Khadijah ne kuma yaga son kai irinna matarsa qarara a fasalin yaran nasa wanda a bayyane yake basai an fada ba. Duk wasu alamomin lafiyayyen jinjiri mai samun kulawa sun bayyana akan Khadijah amma akasarin hakan akan Fadwa, baiwar Allah sai idanun nata s

uka sake fitowa rauu dasu kamar wadda take zaresu da saninta. Dogon kallon da Papa ya yi mata ne abubuwa dayawa suka darsu a zuciyarsa a wannan lokacin, Amma sai ya danne komai a ransa. Cikin kwanakin da suka biyo baya ya tsananta saka ido akan lamarin yar

inyar, anan ya lura da yanda matar tasa ta maida schedule din kula da Fadwan abun walagigi, bata tashi barin Habiban ta kula da Fadwan sai dare, kuma duk yawan hadimanta bata saki Habiban ba sai ya zamto aduk wunin ranar jefi jefi Habiban zata yanke wasu a

yyukan nata taje ga dakin Fadwan ta bata madaranta. Gashi a wannan lokacin su Imam sun koma makaranta suma basa zama sosai, balle yanzu da ba a sashe daya suke zama dasu akai akai ba. Abunda yafi qona ran Papan ma shine yanda duk da dawowarsa Mai dakin tas

a bata chanja yanayin kulawan yarinyar ba kodan ganin idonsa, It's so extreme that sai da ya fara tunanin anya akwai zuciya a qirjin Fatimansa da yake gani a yanzu kuwa.

A wannan tsukun su Mai martaba suka dawo daga Umrah. A ranar da suka iso da Momman

taje gaishe da Uwah bayan ta baro sashen Mai martaba sai ta sameta riqe da Fadwan tasa an kawo mata ita, ganin yanayin kallon da Uwahn ke jifanta dashi itama sai da ta dan sha jinin jikinta amma da yake zuciyarta ta riga ta bushe akan alamarin sai ta maze

tana gaisheta, nan take babu boye boye rai a bace Uwah tace "Fatima! Allah ya qara gyara miki zuciyarki dan ki samu rabauta da lahirarki, in ba haka ba rayuwarki da kallo, kuma halinki bai zamo abun koyi ga 'ya'yan da suka fito daga tsatsonki ba" nan take

kuwa Momma ta fara kuka saboda yanda maganar ta dake ta kuma ta mata daci arai, ita me tayi toh?. Uwah ta girgiza kai sanin hawayen kada take gani a fuskarta dan ta sani ba gyarawan zatayi ba.

A zuciye Momma ta baro sashen Uwah ranan cikin qunan rai t

a tafi direct zuwa falon mijinta ta samesa zaune da yaransa har Jidda na kwance a jikinsa, ganin haka sai yace da su Imam dake zaunen su dan bashi guri, sai da suka fice sannan ya kalleta amma baice komai ba har saida ta gaji da shirun sannan tace "Ka fada

min shin fina da yarinyar nan tayi a wajenku har yakai a fara zagina a bayyane saboda ita?" anutse ya girgiza kansa batareda ya nuna alamun bacin rai ko akasinsa a fuskarsa ba sannan yace "Ko daya Fatima, Fadwa kaman Khadijah take a gurina dan haka babu ta

yanda zata fiki a gurina har abada, kin fi min ita. Sai dai abubuwan da kike mata yasa zan rabakin da ita kamar yanda kikeso din" kallonsa ta tsaya yi, sai ya kamo hannunta yace "Zan rabaki da itan, kulawanta bazai sake zama abun damuwarki ba har abada in

sha Allah, sai dai zan AURO wadda nakeson ta kulamin da ita tunda itama 'yatace Fatima, hakkin kulawanta ya rataya a wuyana kamar na sauran 'ya'yana, banason mu shiga hakkinta muyi laifi a gurin ubangiji" a sannu ta zare hannunta daga nasa cikin wani irin

sanyin jiki, wani irin daskarewa jikinta yayi kamar batada jini, ganin haka sai ya sake nutsar da murya ya sake cewa "This is for the best Fatima, banason yarinyar nan ta zamo priority a sabanin dake shiga tsakaninmu, Ina sonki matuqa. Kisani wadda zata s

higo bazata taba finki a zuciyata ba har abada" cikin diri tace "Just shut up Abdulaziz" ta miqe jikinta na wani irin rawa tace "Niiii !!..Ni zakayiwa

kishiya akan 'yar tsintuwaaa! Ka rasa akan me ma zakamin kishiya sai akan 'yar da ka tsinto a yashe cikin

sanyin Texas" kallonta yake quri baice komai ba, ta buga wani uban tafi tace "Qaryar me qarya ma, wallahi qarya kake Abdulaziz" sai lokacin yace "I've made my mind Fatima, kuma hakan shine zai zamo maslaha a tsakaninmu" muryarta na rawa tace "Wallahi kary

ane, maslahan banza da wofi! In maslahan kake nema ka dauketa ka bada ita a 'yan'uwanka su riqeta mana, ka kaita gidan Abdulrazaq mana, sai kace zakamin kishiya akanta" tayi wani qwafa mai qarfi tace "Gaskiya ne, lallai Abdulaziz" kawai ta juya a zafafe ta

fice daga falon yana bin ta da kallo.

A daren ranar ya fadawa Uwah decision dinda yayi making. Kawai sai ta tsaya kallonsa taqi cewa komai, ganin haka sai ya dan nusar da murya "Ina ganin hakan ne kawai zai kawo mana maslaha, Inason Fadwa ta taso cikin

gatan da duk sauran yaran namu zasu samu, kuma Fatima is not making any effort regarding that" sai sannan Uwah ta gyada kai cikin gamsuwa dan kowa ya kwana da sanin haka a gidan, sai kuma tayi murmushi tace "Ita wannan da kake son aurowa Yar Ina ce haka?"

Yace "Bamu dade da fara magana ba.Y'ar gidan Muhammad Shettima ce" sai tace "Sarki Muhammad Shettima na Borno?" Papa ya gyada kai a hankali yana kallon mahaifiyar tasa. Sauqe numfashi tayi sannan tace "Hakan duk ba laifi bane, kuma dan ka qaro aure shima

ba laifi bane. Allah ya tabbatar da abunda yafi alkhairi, in har hakan kana ganin shi zai dinke barakar gidanka, na baka goyon baya dari bisa dari. Allah yayi jagora" ya amsa tareda miqewa zai fice ta bisa da kallo abubuwa dayawa na mata yawo arai. Abunda

ta dade tana jirane Allah ya nuna mata, dan ba shakka wannan matar tasa abokiyar zama ce kawai zata dusasar da kaifinta, tayi wa Abdulaziz kaifi dayawa. Kuma wannan decision da yayi making ba qaramin sanyi ya mata a rai ba, hakan na nuni da cewar d'an nata

ya fara tsayawa tsayin daka a sama da matar tasa. Hakan jarumta ce a gurinta.

Saida suka idar da sallahn isha, Papa ya tabbatar Mai martaba ya samu zama a sashen sa kamar ko wane dare sannan ya samesa da maganar. A nutse Dattijon ya sauraresa yana kuma f

ahimtarsa. Sai da Papa ya gama maganarsa sannan Mai martaba ya nusar da murya "Banqi taka ba, amma banason ka gina yaqin da bazai taba qarewa a tsakanin yarka da mai dakinka ba. Zaifi dacewa ka qaro aurenka a domin kana da niyyan hakan amma karka kafa wann

an yarinyar da hujja alhalin bata san komai ba. Zaka rufe ta da wani shinge ne mai hatsari da batasan ta Ina mafarinsa yake ba in ta mallaki hankalin kanta a gaba. Hakan kuma bazai taba haifar muku da d'a mai ido ba acikin ahalinka" Papa ya gyada kai cike

da alhinin furucin mahaifin nasa. Yasani shima hakan ba qaramin tsana zai jawowa Fadwan ba, amma babu yanda ya iya ne, bazai iya zuba ido ana cutar da yarinyar batareda ya dauki mataki ba. Ya daukota dan ya bata duk wani kulawan data rasa sannan ya samu la

da, amma abubuwan da suke faruwa a yanzu, bashi da tabbacin in ya bari aka tafi a hakan zai cimma burin daya daga cikin abunda ya lissafo.

Cikin nutsuwa ya qara yin bayani ga mahaifin nasa. Sannan yasan a yanda Uwah ta karbi lamarin, ita zata sake tausasa

masa Dattijon akan alamarin, dan bai manta ba alaqace mai kyau tsakanin mahaifin Binta da shi Mai martaban, kallon 'ya yake mata a koda yaushe. Amma sai Allah ya juya alamarin, dan bai bar sashen ba sai da suka fara maganan tsarinsa akan auren, nan ya fad

a masa bai son a dau lokaci.

Yaji sauqin nauyin zuciyarsa ganin yanda mahaifansa suka karbi alamarin, daya koma sashensa bai samu Momma anan ba kamar yanda ta sabar masa duk dare, kuma yasan za'ayi haka dan ya shiryawa duk wata fitinarta a wannan karon.

Sai ya qara fita yaje sashen Twins dan wunin ranar tun safe ranbonsa dasu. A bakin part din nasu ya tsaya tareda gaisawa da dogarai biyun dake kula da gurin kamar ba basarake haka ya amsa gaisuwarsu, suka rinqa zubo masa kirari har ya shige. A Babban falon

ya samesu bayan Laure ta zuba musu abinci da ta dafa musu ire ire daban sai wanda suka zaba. Imam na kwance a kujera yana zane a white sheet while Imran yana kallon Tv. Shigarsa Imran ya juyo yace "Papa barka da dare" yana murmushi ya qarasa tareda zama a

kujera, Imam ya miqe zaune suka gaishesa ya amsa, again sai ya qara kai hannu ya dauki sheet dinda Imam din ke zane a cikinsa yana kallo a tsanake, yaso ya gane building din amma sai kansa ya kulle, sai ya kalli Imam din yace "What's this?" Imam ya dan ma

tso suna kallo a tare sai ya kai yatsa yana nuna gurbin da bai gama sketching ba, yace "This has to go from here to the top" ya sake nuna wani gurbin "And from there, it goes straight to the outer layers of..." bai qarasa ba Papan ya sake kallonsa yace "In

a nufin building din Imam, Ina zan san outer or inner layers" ya qarasa maganan yana murmushi, sai Imam yayi murmushin shima sannan yace "It's JPMorgan Chase Tower" Papa ya dan hade girarsa in confusion da fari, sai can yace "Houston??" Imam ya gyada kai t

areda kai hannunsa ya juya zaman sheet din a hannun Papa dan a kaikaice ya riqe ta shiyasa bai gane ba, aikuwa nan Papa yadan ware ido bayan ya fahimci zanen, sai ya sake juyawa ya kalli Imam din da mamaki, yace "Taya kas..." "How do you know it?" sai loka

cin Imran yace "Papa you took us there, remember?" ya gyada kai yana sake kallon zanen. Har gobe baya jin zai daina mamakin abubuwan da Imam ke zanawa, it's just raw talent da Allah ya bawa yaron tun baije ko Ina a rayuwa ba. Sai ya sake cewa "But who taug

ht you this?" Imam ya girgiza kai sannan yace "I

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login