Showing 1 words to 3000 words out of 47250 words

Chapter 1 - BINTU DIYAR BAYI CE COMPLETE

20 Oct 2026

224

Copied By

HAYATU BABA ZUBAIRU

(admin

Hayat hausa novels

Hausa novels and fashion

Cool novel, makeup and kitchen1

⃣

AND

Cool novel, makeup and kitchen2

⃣

)

WHATSAPP NO:

+2347039625239

®

✏

📖

*FIKRA WRITER'

S ASSOCIATION*

🐪🐫

BINTU 'DIYAR BAYI CE!

🐪🐪🐫🐪

🐪🐫🐪🐫🐪🐫

🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

©Khadija Sidi.....

✍

🏼

0

⃣

1

⃣

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI

✍

🏼

SHIMFID'A

🌍



NIAMEY

Niamey shi ne babban birnin Jamhuriyar Nijar, wanda shi ne bi

rni mafi girma a kasar, dake da girman murabba'in kilo mita (239.30) Tun a karni na 18 ne aka kirkiro Niamey, sai dai a wancan lokacin ba'a dauke shi da wani muhimmanci ba har sai bayan da Faransa ta kafa cibiyarta a wajen a shekarun (1890). A shekarar (19

26) ya zamo babbar birnin kasar ta Nijar. Sannu a hankali yawan jama'ar yankin ya yi ta karuwa daga (3,000) a shekarar (1930) zuwa kimanin (30,000) a shekarar (1960). Yawan jama'ar Niamey ya kai (250,000) a (1980), a shekara ta (2000) kuma (800,000). Babba

n musabbabin karuwar jama'a a Niamey shi ne na yawan kaurar jama'a a lokutan fari.

A matsayinsa na babban birnin Jamhuriyar Nijar, akwai wuraren tarihi da suka hada da gidan tarihi na kasa da gidan zoo, akwai kuma cibiyoyin nuna al'adun gargajiya na Amu

rka da Faransa da Nijar. Hakanan kuma akwai manyan kasuwanni bakwai a birnin. Kashi (90)cikin dari na jama'ar Niamey Musulmai ne, anan ne kuma ake da hedkwatar mabiya darikar kirista ta Roman Katolika.

SA'AYRASA

MASARAUTAR SA'AYRASA yana bangar

en kudu maso gabashin Nijar, kuma yana da girman murabba'in kilo mita (156,906). Masarautar Sa'ayrasa na iyaka da Masarautar Fabarusa, ta Arewaci da Zindar ta Yammaci da Najeriya ta kudanci sai kuma Chadi ta Gabashi. Masarautar Sa'ayrasa ta kasance d'aya d

aga cikin masarautar da ba su da yawan jama'a, wanda kidayar shekara ta (2001), ta nuna yawan mutanen masarautar ya kusa dubu dari hudu. Jama'ar Masarautar Sa'ayrasa sun hada da Kanuri da Tubawa Hausawa da Fulani da Larabawa. Tattalin arzikin masarautar ya

ta'allaka ne kan kiwo da noman rani da kuma na damina. Abubuwan da aka fi nomawa a yankin sun hada da gero da masara da shinkafa da kayan lambu irin timatir da barkono. Sai dai kuma duk da noman da ake yi a masarautar, masarautar ta kasance mafi koma baya

ta fuskar noma a Nijar saboda fari.

FABARUSA



MASARAUTAR FABARUSA shi ne ya fi kowanne yanki girma a masarautar Nijar, wanda girmansa ya kai murabba'in kilo mita (634,209), watau kwatankwacin kashi hamsin da biyu cikin dari na girman Nijar baki day

a. Masarautar Fabarusa ta had'a da Hamadar Tenere da Bilma da kuma yankin Air mai cike da tsaunuka. Mafi yawancin jama'ar Masarautar buzaye ne; akwai kuma Tubawa da Fulani da kuma Hausawa. Babbar sana'ar jamaar masarautar ta asali itace cinikin gishiri da

dabino, sai dai a shekarun (1990), harkar bude ido ta zama wata babbar sana'ar yankin, hakanan karfen Uranium da ake samu a garin Arlit na samawa Nijar kashi (20)cikin dari na kudin shigar da take samu.

NIAMEY 1/01/2000

Tafe su ke cikin mota,tin

da suka baro masarautar su wato Sa'ayara ta tsunduma cikin kogin tunani, ba ta gushe ba har su ka shigo Niamey, in da makarantar su wato SOVEREING GIRLS SECONDRY SCHOOL ta ke. Wato ‘ya’yan manya da sarakuna na sassa,masarauta da yankunan jamhuriyyar Nija

r waannan makarantar su ke. Ajiyar zuci ta saki ganin sun doshi kofar makarantar, yayin da motoci biyu da ke gaban ta su su faka, ta su wacce ta ke ta uku ita ma ta faka. Waigawa ta yi dan ganin ko d'ayar da ke tafe bayan ta su ta sami isowa,ile kuwa sai g

asu sun karaso a hankali su ka faka bayan ta su. Hankalin ta ta mayar kan kofar makarantar ta su. Motoci hu

ɗ

u ne jere reres su ka taho kawo Gimbya Binta yar sarkin Sa'ayrasa makaranta. Ta fari

ɗ

auke da dogarawa guda biyu da direba, ta biyu bayi ne mata su

hu

ɗ

u, sai kuma wacce Gimbiyar 'yar sarki mai dole ke zaune gidan baya, ta yi

ɗ

ai-

ɗ

ai ta na shan kamshi, tare da ita baiwar ta ce Bintu zaune gaban mota da kuma direba,sai cikon na hud’un dogarawa ne su hu

ɗ

u zaune, biyu gaba biyu baya.

Tsawar da ta ji

an daka mata ya sa ta yi firgit ta dawo cikin hayyacin ta, jin an furta,

‘’idan kin gama rubuta wasikar jakin da ki ka saba sai ki fita’’.

Fa

ɗ

in _(driver)_ matu'kin mota ya na mai muzurai. Hakan ya sa ta saurin fitowa daga motar dan kuwa har sun shigo

farfajiyar makarantar ba ta sani

ba. Tini sauran bayi yan uwanta sun yi sahu suna jiran fitowar Gimbiya Binta. Cikin su Bintu ta shige ta tsaya kan na ta sahun, yayin da dogarai su ka karaso cikin azama, su ka yi na su sahun ta

ɗ

ayan

ɓ

angaran. Daga bayin h

ar dogarawa kalar yadin da ke sanye jikin su

ɗ

aya, ruwan toka ne da shu

ɗ

i. Rigar ruwan toka sai zanin shu

ɗ

i.

Kan su sunkuye babu mai motsi kai kace gumaka aka aje, matu'kin ya bu

ɗ

ewa Gimbiya Binta kofa. K’afafun ta fara fiddowa waje, sanye cikin takalmi

fata mai dankaran tsada, sai bayan wasu yan dik’ik’a sannan ta k’arasa fitowa. Tuni suka fara ma ta kirari da fa

ɗ

in,

‘’taka a hankali Gimbiya yar sarki mai dole, takawan ki lafiya sarauniyar mata’’.

Sanye ta ke cikin kayan makaranta, riga da _skert_

buje sai kuma hijabi wanda ke tsayawa iyaka kafa

ɗ

a. Alkyabba ce ta alfarma

ɗ

aure bisa kayan makarantar. Cikin sarauta da tak’ama ta ke takawa

ɗ

aya bayan

ɗ

aya ta wuce, su ka rufa mata baya. Haka su ka wuce ciki zuciyar Bintu cike da tunanin halin da akwatin

karfen ta zai shiga matukar ba ta dawo da wuri ba dan Ado matu'ki ba mutunci gare shi ba, dan ya koma da kayan Kuka Sheka ba k’aramin aikin sa ba ne. Hantar cikin ta tuni ta ka

ɗ

a

Motoci sai shiga da fice su ke kasancewar yau rana ce ta dawowar

ɗ

alib

ai daga hutun zango na uku. Kai tsaye sashen

ɗ

akin kwanan

ɗ

alibai su ka nufa, wanda a k’a'ida kowanne

ɗ

aki dan d’alibai biyu aka yi. A dai-dai katangar da ta raba harabar makaranta da sashen

ɗ

akin kwanan

ɗ

alibai su ka tsaya, dan kuwa babu damar dogarai su

shiga

ɗ

akin kwanan kasacencewar dokar makaranta ta hana maza shiga. Nan su ke jiran dogarawa masu

ɗ

auke da akwatina su k’araso su karb’i akwatunan dan karasawa da su ciki. Ita kuwa Gimbiya Binta kai tsaye ta shige,biyu daga cikin bayim biye da ita, ya rag

e daga Bintu sai bayi guda biyu. Dan sauri jikin ta har

ɓ

ari yake, Allah-Allah ta ke su samu su shigar da kayan Gimbiya Binta dan ta samu damar kwaso na ta. Sai da su ka

ɗ

auki kusan minti goma kafin su k’araso

ɗ

auke da kaya niki-niki, wanda kuwa fa

ɗ

ar adad

adin su aiki ne ja, wai kuma a hakan ma akwai saura cikin mota. Haka suka shiga jidar kayan su na hawa da su sama,bhar bene na uku tukanna ka isa

ɗ

akin Gimbiya. Ta nan kishingi

ɗ

e kan gado,

ɗ

akin yayi fes-fes dama tin ana sauran kwana uku a dawo makaranta a

ke gyarawa.

Su na hawa su na sauka har sai da su ka yi sahu uku. Bintu na Murna da sun sake komawa za su kwashe sauran kayan. Budan bakin Gimbiya Binta sai cewa ta yi,

'’akwati nawa ne su ka rage?’’.

’Daya daga cikin bayin ta amsa mata da,

"hu

ɗ

u n

e su ka yi saura ranki shi da

ɗ

e'’.

Gimbiya ta ce,

"to! Za ku iya tafiya kubarwa

ɗ

iyar bayi sauran ta k’arasa hawa da kayan’’.

Tuni idanun Bintu ya raina fata, ba wai wuyar hawa da kayan ba ne damuwan ta ba, a'a ita ta dan akwaitin k’arfe ta ta ke.

Cikin girmamawa su ka durkusa su na mai fa

ɗ

in,

"an gama ran ki shi da

ɗ

e'’,

hannu kawai ta

ɗ

an

ɗ

aga musu alamar sa iya tafiya. Cikin hanzari su ka da

ɗ

a rusunawa kafin su tashi su ka fice. Ai fa Bintu ba ta san san da ta arta a na kare ba, ta na ji sauran

bayin suna dariya suna cewa:-

‘’Ba ke mai yiwa Gimbiya hidima a boko ba, Allah shi k’ara’’,

ɗ

aya ta k’ara da "ai tin da aka zab’e ta wani girman kai ya game jikin ta,

ɗ

iyar bayi a makarantar girma’’.

Yi ta yi kamar ba ta ji su ba, ta k’arasa ta

ɗ

auro a

kwati

ɗ

aya a ka d’aya kuma ta jawo shi a hannu. Ba ta kai ga hawa bene ba ta yi kaci

ɓ

us da su, haka su ka wuce ta suna mata dariyar kyeta. Cikin himma ta haye abun ta sama, sai da ta kai ga kofar

ɗ

akin ta tsaya dan ta

ɗ

an sami nutsuwa dan kuwa idan Gimbiy

a ta gano ta lalle kashin ta ya bushe. A hankali ta tura kofar tare da sallama. Gimbiya ko ta nuna ta san ta shigo bare ma ta amsa sallamar. Cike da nutsuwa ta aje akwatinan sannan ta fito, nan ta sake zurawa a guje, ta kwaso sauran akwatinan kamar dai yan

da ta yiwa biyun farko. Aje akwatinan ke da wuya ta juya da niyyar sake fita, Gimbiya ta daka mata tsawa,

"ina zaki? Nufin ki ni zan jera mi ki kayan yau kuma

ɗ

iyar bayi?’’.

Jiki na rawa Bintu ta zube k’asa ta na mai fa

ɗ

in,

"tuba na ke ranki ya da

ɗ

e

ni ce zan jera dama sauri na ke dan kwaso nawa kayan kar Ado ya manta ya juya da su’’.

Shiru idan Gimbiya Binta ta tanka ko shakka babu dutse ma ya tanka. Da shirun yayi yawa Bintu ta

ɗ

aga kai ta kai kallon ta gare ta, sai gani ma ta yi ta runtse ido ka

mar mai bacci. Dole jiki ba laka Bintu ta tashi ta shiga jera akwatunan, sai da ta gama tsaf sannan ta durk’usa ta ce,

‘’ran Gimbiya ya da

ɗ

e na idda’’.

Sai da wasu dak’ikai su ka shu

ɗ

e, har Bintu ta na tunanin ko dai bacci ta ke sannan ta ji ta ce,

‘

’kya iya kwaso tsummokaran na ki’’.

A wulakance ta yi furucin cike da 'kas'kanci. Russunawa ta yi cike da girmamawa ta ce,

‘’godiya na ke ran ki shi da

ɗ

e", ta tashi ta fice. Nan fa duk nutsuwar ta ya gushe, ta ranta a na kare, ba ta ji ba ta ba ta gani.

Dalibai ma su shiga da fice cikin farfajiyar wajan fa

ɗ

i su ke,

"ta fara, in dai wannan ce dama duk dawowa hutu haka ta ke".

A guje ta fito daga harabar

ɗ

akin kwana ta shigo sashen ajijjuwa. Ba ta ga tahowar shi ba sai ji ta yi karo da shi. Ta yi saurin

yin baya saura k’iris ta fa

ɗ

i ya yi saurin sa hannu biyu ya rik’o ta. Sakin baki ta yi ta na kallan sa,ta ma manta da gudun da ta ke.

Sanye ya ke cikin bakar _suite_, wankan tarwa

ɗ

a be mai dan faffa

ɗ

ar kafa

ɗ

a. Ya na da dogon hanci, yayin da gashin bakin

sa da ya zagaye bakin na sa ya k’ara masa kyau da k’warjini. Idanun sa rufe cikin bakin gilashi hakan ya sa ba ta sami damar ganin kwayen idanun na sa ba. Kamar daga sama muryar sa ya dakin dodon kunnan ta,jin ya ce

‘’hankali mana gudun me ki ke haka ke

kuwa?’’.

Ta yi saurin ja da baya,hakan ya sa shi sakin ta.

’’Yi hakuri dan Allah Ado direba zai tafi da kaya na’’.

Bintu ta furta idanun ta na shirin kawo ruwa. Sai a sannan ya dubi kayan jikin ta ya na mai fa

ɗ

in,

‘’Tabbas wannan shigar ta ki ta bayi

n Masarautar Sa'ayrasa ne, ina shigowa na ga motocin na su na fita, sun manta da ke ne...?’’,

ba ta bari ya karasa maganar ba bare ta bashi amsa ta sa gudu ta na mai fa

ɗ

in,

"shikenan ni Bintu sun tafi da akwati na,shikenan na banu na shiga uku na lalace’

’

Cikin rashin fahimta ya bita da kallo har sai da ta kure masa sannan ya d’aga kafad’a ya sauke sannan ya yi ciki abun sa.Isar ta wajan yawan motoci masu kai kawo ya k’aru,sai dai babu motocin Sa'ayrasa babu alamar su. Kwallar da ke idanun ta tuni su k

a fara gangarowa bisa kuncin ta.

®

✏

📖

​

FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

​

🐪🐫

BINTU 'DIYAR BAYI CE!

🐪🐪🐫🐪

🐪🐫🐪🐫🐪🐫

🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

©Khadija Sidi.....

✍

🏼

Wannan labari sadaukarwa ne kuma tukwici ne ga FIRDAUSI SODANGI,wacce ta amince da w

annan batu na "garin masoya ba ya nisa" har ta kawo ziyarar ta gare ni. Allah ya bar zumunci ya bar kauna Amen.

0

⃣

2

⃣

Bintu na shirin juyawa ta hangi akwatin ta jefe tsakiyar filin, da gudun ta ta k’arasa ta rungumo abin ta ta na maida numfashi. Wani

mai mota ne ya ba a mata k’ura sa’annan ya lek’o ya na fa in

"shashasha sai kin jawo wani ya taka ki’’

ko aga kai bata yi ba bare ma ta san ya na yi. Ita dai burin ta ya cika ta sami akwatin ta.

Offishin shugaban makarantar katan ofishine wand

e aka kawata shi kai ka ce ofishin shugaban wani yankin ne. Ganin wanda ke zaune gaban sa da kuma abun da ke tafe da shi ya sa shi zufa na ba gaira ba dalili rufe shugaban makarantar. Kana ya nisa tare da fa in

"(your excenllency) Ya mai girma....’’

"A

isar,ko ka kira ni Aisar Gaddafi Nur,(his excenllely) ya na gida yallabai’’

ya katse shi hankali kwance. Zufa shugaban makarantar wanda dalibai ke kira Malam Hamisu ya goge,ya na mai gyara murya ya ce

"toh Yallbai,yanzu dai nufin za ka yi bad da kama

kamar malami cikin wannan makaranta ta mu har tsawan zango aya.....’’

Yana mai murmushi ya ce

‘’ba bad da kama ba Yallabai,gyaran lafazin shi ne ina neman alfarmar koyarwa a makaranta na tsawan zango aya’’

cikin nazari Mallam Hamisu ya ke duban

sa "me zai sa dan Shugaban kasa so ya koyar a makarantar nan?na zango aya? Ko shakka babu ya na daga cikin motanen oye wanda ke yiwa kasa bincike da aiki cikin surru, dama ba tun

yau ya ke jin maganar ba,kaddai wani sharrin aka kullawa makarantar sa.....’

’

Zancen zucin da ya ke yi cikin ran sa kenan dan kuwa ruwa ba ya tsami banza. Can dai ya gyara murya sannan ya ce

‘’Yallabai....’’

‘’Aisar’’

Saurayin ne ya k’ara katse shi ya k’ara da

"tunda zan zauna k’ark’ashin ka ya kamata ka saba da

kira na da sunana.’’

Cikin jinjina kai Malam Hamisu ya amsa da

"Haka ne Aisar,muna maraba da kai,kuma ina mai tabbatar ma ka mu yan kasa ne masu kishin kasan mu,na gari ma su san ci gaban kasar mu.’’

Ya na mai murmushin nuna gamsuwa Aisar ya ta

shi tsaye gami da mik’a ma Malam Hamisu hannu ya ce

"madallah da kai,kuma na gode kwarai,gobe InshaAllahu zan fara koyarwa sai a bani aji a kuma zaga da ni makarantar sauran Malamai su sanni ko koyar da ni sharad’an makaranta idan akwai, duk abun da ka

ke buk’ata in koyar shi zan koyar’’

Mallam Hamisu shi ma in tashi yayi,ya na murmushin yake ya amshi hannun Aisar,fa i ya ke

"Madallah Allah ya nuna mana’’

amma a zahirin gaskiya a tsorace ya ke da Aisar.

Sai da ya raka shi har kofa ya tabbat

ar ya tafi sannan ya dawo ofishin sa da sauri dan ha a taron zaman Malamai na gaggawa dan kuwa shi gani ya ke akwai matsala shi ya sa aka mu su shunan Aisar. Shi kuwa Aisar ya na fita shugaban su ya kira ya na mai sheda ma sa yanda su ka yi da Malam Hamis

u,Shugaban na su yayi murna kwarai dan kuwa kamfanin da su ke bincike akai kusa da makarantar ne. Ko da ya aje wayar sai ya tsinci kan sa ya na mai waige waige ko zai sake ganin wannan baiwar,amma yawan daliban da ke kai kawo,da wanda su ka sa masa ido ya

sa shi kasa gane wacece wace

"ba mamaki ma ta sami motar garin na su"

abun da ya fa a kenan kafin ya shige motar shi da ya saba basaja da ita ya bar harabar makarantar.

Wacece Bintu

Bintu Bala Mahuta sunan ta,amma Bintu iyar bayi ake kiranta a

masarautar su kasancewa suna aya ta ci da da Gimbiya Binta, wato sunan maihaifiyar ta wacce Allah yayiwa rasuwa wajan haihuwar Gimbiya Binta. Mahaifiyar Bintu wacce ta ke babbar baiwar matar sarki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login