Showing 12001 words to 15000 words out of 47250 words
dan haka baki bud’e ta tsaya ta na kallan wayar har ya d’aga ya kara bisa kunan sa, ji take da zai bata ta d’an kara kunan ta da ba haka ba.
Bintu ba ta dad’a shagala ba sai da ta ji ya ambac
i sunan Barde, nan da nan ta manta da wani nauyin Aisar da ta ke ji, ta fara Allah Allah ya gama wayar.
Ta gani ya kashe ta ce "Malam dama kasan Yaremi Barde na Fabarusa?’’
‘’ Na san Barde, amma yanzu ba da shi na yi magana ba’’ sai da ya ba ta ams
a sannan kuma mamakin yanda aka yi ta san Barde ya kama shi, be san sanda ya ce ‘’Yerima Barde ke? Ina ki ka san Barde ke kuma ki na yar masarautar Sa’ayrasa?’’ ya tambaya cike da mamaki.
Nan fa Bintu ta fara jero bayani cike da nuna gwanintar yan ajin
su ma ba a barsu baya ba ta ce "ai rannan a aji aka yi hirar shi, ance shi ne mai kyawun duniya kuma k'asar nan kaf babu wanda zai gwada masa k'asaita, rabin yan ajin sun ta6a ganin shi, ni ma ina so na gan shi ko da sau d’aya ne a rayuwa ta’’
Jin kala
man Bintu tuni Aisar ya had’e rai, yayi k’icin k’icin ya fara fad’a "wato a shekarun ku har kun san ku zauna ku yi hirar samari ko? Ba ku san komai ba sai kula samari da karanta littafin soyayya ko?’’
"wallahi malam ba na kula samari ni ba yar iska ba
ce’’ furucin Bintu kenan yayinda idanun Bintu su ka fara kawo ruwa, sai a sannan ta ankare da 6aran6aramar da ta yi na tambayar Barde, duk da dai ita ba da wata manufa ta yi. Ganin Bintu na shirin masa kuka har da batun ita ba yar iska bace ya sa hankalin
sa kwanciya, wato kenan ba ta kula samarin tun da har ta masa wata fassara na da ban, hakan ya masa daidai har ya na mai murmusawa. Ita ko Bintu ta shi ta yi da sauri ganin wasu d’alibai sun fito daga d’akin karatu, ta ce malam dama karatu na ke Iya Dije t
a ce za ka bani sak’o’’
Sai a sannan ya tuna fa ashe ba ranar makaran ta ba ne, gashi shi babu wani sak’o da ya kawo mata dama ganin ta kawai ya ke san yi. Amma gudun kar ta d’auke shi sakarai fakewa yayi da dama ya zo wucewa ne ta makarantar ya ce bara y
a tsaya ya ji ta na karatu kuwa, maza ta koma ta cigaba da karatun. Da wannan ta masa sallama, har ta na fad’awa cikin ca6i dan saurin kar wannan d’aliban da ta hango su gan ta tare da Aisar. Shi kuwa gogan na ta ko ganin su be yi da ke su ma d’in lab’ewa
su ka yi domin su tabbatar da abun da su ke gani.
***
Sai da Bintu ta k'urewa ganin sa sannan ya tashi ya nufi motar sa, ya gifta ta gaban wannan d’alibai da ke leb’e bayan wata yar katanga sam be lura da su ba har ya kai ga
motar shi ya shige ya fice daga makarantar.
"kut yau kuwa za yi bantan uwa a makarantar’’ fad’in d’aya daga cikin d’aliban kenan wacce su ke Marry yayinda su ke fitowa daga wajan 6uyan su ganin Aisar ya fice. Su uku ne, kuma dukan su yan aji shida ne
ma su mik’amin. Marry ita ce mai ruk’e da muk’amin horo, sai shedigyal da kuma mai kula da tsafta da lafiyar d’alibai, wacce su ke kira da Sikanti.
Marry ba ta gushe ba jiki na rawa tsabagen masifa ta k’ara da "wai ido na ne ke zagi ko kuwa Malam Aisar na
gani da wata kwaila a makarantar nan?’’ Cikin Jimami Shedigyal ta ce ‘’ni ma dai abun nan ya ban mamaki, ki ga yanda mu ke bin sa ya na mana wulakanci amma ya rasa wacce zai bi sai Bintu d’iyar bayi’’ sikanta dan mamaki ta ma kasa magana. Marry ta d’aga k
’afa ta doka k’asa cikin ca6ali, nan da nan zanin ta ya 6aci amma ko aji kin ta, idanun ta ya rufe, kana ta ce ‘’ba d’iyar bayi, ko d’iyar saraki ce yau sai ta ci Uban ta, za ta min bayanin dalilin da ya sa ta kyebewa d Malami, kut Malamin ma wanda na ke s
o dan uban ta? Yau sai ta lashi kashin b’and’akin k’asa dan uban ta Bintu ta ke kowa? Ta yanki tsiya!" ta wuce fuu, dama ga ta jibgegiya tabarakallah. Su shedigyal su ka rufa mata baya, kai tsaye sashin kwanan d’alibai su ka nufa.
***
Bintu kuwa komawar ta d’aki ta tadda Gimbiya ta dawo tare da k'awayen ta, ko da ta tambaye ta daga in da ta ke sai ta mata k’aryar Iya Dije ce ta aike ta. Ta ci sa’a yan masifar Gimbiya ba sa kusa, hankalin ta na kan labarin da Zahira ta ke ba su.
Can gefe Bintu ta zauna ta na mai mamakin dalilin da Aisar ya fad’a mata na zuwa ganin ta. Zaman ta ke da wuya ta ji ana kwala mata kira "Bintu Bala Mahuta dan uban ki sauko!’’
Ba Bintu ba hatta su Gimbiya sai da su ka kasa kunne su na jiran tsammani.
ita kuwa Bintu jikin ta ne ya hau b’ari jin muryar Marry da gaba d’aya ya 6angaran d'akin kwanan d'alibai. Gimbiya ce ta kai kallan ta ga Bintu ta na mai tambayar ‘’yar nema me kuma ki ka yiwa wannan mai fasalin mazan?’’ Bintu ta kasa magana tsabar tsoro,
nan fa su ka k’ara jiyo har gowar Marry ta na mai fad’an ‘’dan uban ki na ce ki sauko kimin bayanin wani malami ki ka kyebe a bayan aji!’’
Nan fa Bunti ta kware saboda firgici da tsoran maganar da Marry ta furta, inda Gimbiya, Zahira da Ruqayya su ka
tashi tsaye a a tare, Gimbiya na fad’in ‘’ki tabbatar wannan malamin da ake magana akai ba Malam Aisar ba ne!’’
Can waje kuwa tuni d’alibai kowa ya fito jin shela da tonan siririn Marry, wasu ma babu cikakken sitiran arziki jikin su haka su ka fito baw
a idanun su abinci dan kuwa sun san koma wacece wannan ta shiga hannun Marry ta kad’e har ganyen ta, musammam jin ance "ta kyebe da Malami."
"BINTU BALA MAHUTA! Ko ki sauko ko na zo na sauko da ke ta!’’ fad’in Marry ta na mai kumfar baki.
®
✏
📖
FIK
RA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫
BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
©Khadija Sidi.....
✍
🏼
0
⃣
7
⃣
Babu shiri Bintu ta tashi da sauri, jin Mary na maganar sauko da ita ta ka ta san muguntar Mary za ta aika. Hanyar fita ta nuf
a ta na jera adduoi iri-iri, ta kama wannan ta saki, wani ma ko k’arshen shi ma ba ta iya kai wa. Su Gimbiya ma ba su yi k’asa a gwiwa ba, biye su ke da ita, ita dai burin Gimbiya ta ji shin da wa Bintu ta ke6e, idan kuwa Aisar ne sai na lahira ya fita ji
n dad’i, dan kuwa a daren ranar kwanan Sa’ayrasa ne ya kama ta.
Ganin Bintu ba ta jira ta k’arasa gabanta ba, ta na haki kamar zakanya ta fizgo ta, ta hard’e kafar ta sai ga Bintu zube gabanta cikin ca6al6alin ruwan sama "Rage tsinannan tsayin naki dan
ubanki, shiyasa ki ke tunanin kin balaga kin isa ke6ewa da malamai." Fad’in Mary ta na mai shararawa Bintu mari. Bintu durkushe bisa gwiwowinta, hannunta bisa kuncinta inda
hawaye ke gangarowa daga idanunta, fad’i ta ke ‘’Ina tuba Anty Marry, ki gafarce
ni, kimin rai’’
Fili ya cika maki’il da d’alibai, kowa na fad’in albarkacin bakinsa, da masu tausayawa Bintu musammam da su ka san ita ba ‘yar kowa ba ce ta shiga hannun Marry, da ma dai ita d’iyar masu mulki ko sarauta ce da duk jarabar Marry sai ta s
aurara mata gudun abun da zai je ya dawo. Sai kuma masu mata Allah shi k’ara. Wani wawan mari da Marry ta dad’a kaiwa Bintu, sai ga Bintu a k’asa, sunkuyawa Marry ta yi, hannu bisa kan Bintu ta kama gashinta, ta fisgo ta cikin zafin nama, sai da Bintu ta
runtse ido tsabagen azaba. Cikin rad'a ta ce "Ke da wani Malami ki ka ke6e a sashen karatu?’’
Idanun Bintu runtse, da kyar ta iya furta ‘’Ina tuba Anty Marry’’ Cike da mugunta Marry ta fizgi gashin Bintu kamar mai shirin raba gashin da fatar kan Bintu, wa
ni kuka Bintu ta saki, sai ga kallabin ta hannun Marry, inda gashin da dama nad’e shi ta yi cikin kallabi ya warware, sai gashi ya sauka har gadon bayan ta. Ba Marry da su shedigyal ba, hatta sauran d'alibai sai da su ka yi mamakin kyawun gashin Bintu, da
ke kullum kanta d’aure ya ke da kallabi, idan ba tsautsayi ba, babu wanda ta ke bari ya gani.
Sikanti ba ta san sanda ta ce ‘’Car uban nan, gide akwai mai irin wannan gashin cikin makarantar nanniya?” Shedigyal da wani bakin kishi ya rufe ta ganin gashi
n Bintu cewa ta yi ‘’Wannan har wani gashin azo a gani ne?’’
Marry kuwa da tuni ta yi mutuwar tsaye, hannun ta rik’e da kallabin Bintu, murmushin mugunta ta saki, ta na mai jinjina kai ta ce ‘’Sikanti ba ni aran almakashina ki.’’ Gaban Bintu ne yayi mu
mmunar fad’uwa, ta d’ago idanunta da su ka yi jajur ta na mai duban Marry. Marry na murmushi ta gyad’a mata kai ta ce "Gashinki zan yanke muddin ba ki fad'a min da wanda mu ka ganki ba, bayan kuma kin fad’amin na kai bayin k’asa ki lashe kashin yan aji d
'aya da su ka yi da harshen ki.’’
Wani sabon kuka Bintu ta saki, musamman jin Sikanta ta tura wata yar aji d’aya ta d’auko mu su almakashi. ‘Dalibai ta bi da kallo cikin neman d’auki, amma sam ba ta ga mai niyar taimakon ta ba, kowa na tsoran sa baki ka
da gobe idan an je wajan matemakiyar shugaban makaranta wacce ta ke mace ce, a ce har da su, suna ji suna gani a had’a da su. Idanunta ya sauka kan Gimbiya, ta watsa mata harara dan ita ko a jikin ta, Ita so ta ke ma a zo a yanke gashin Bintu ko ta samu ta
ji wani Malami ne aka gan shi da Bintu, dan kuwa ta san tun da Bintu ba ta musa ba ko shakka babu da gaske an gan ta d’in ne.
Hankalin Bintu be dad’a tashi ba sai da ta ga an mik’awa Marry almakashi, yayinda ta tsugunna, ta sa hannu ta tattare gashin B
intu cikin hannun ta, wanda rabi kad’ai ta iya kamawa tsabar cikar gashin Bintu, tsakiyar gashin ta sai ta almakashin na ta, ta na mai fad’in ‘’Gide da wani Malami mu ka gan ki?’’
Bintu da ta za6i masifar da hukuncin Marry akan na Gimbiya, ta kasa bud'
ar baki ta furta sunan Aisar, sai ta tsinci kan ta ta na mai fad’in ‘’Ki yi hakuri, ina tuba, ba zan k’ara ba.....’’
Jin sautin almakashi ya na ratsawa cikin gashin ta, da kuma sautin mamaki da ya fito daga bakin d’alibai ne ya katse amsar da ta ke bata
, idanu runtse yayinda zafafan hawaye su ka zubo daga idanun ta, jin saukar jelar rabin gashin ta k’asa.
‘’Lah'ilaha'illallahu’’ Fad’in Iya Dije wacce dawowar ta kenan ta shigo dan ganin ko Bintu ta koma d’akin ta, ta tadda d’alibai sun yu da'ira, ta na
kutsawa ciki Marry na yanke jelar rabin gashin Bintu. Da saurin ta k'arasa in da Bintu ke tsugunne gaban Marry, Shedigyal da Sikanti, ta yi saurin d’ago Bintu ta na mai fad’in ‘’Yo menene zan gani ni Dije?!! Gide wannan wani irin rashin hankali da zalinci
ku ke yiwa yarinyar nan?!!! Gide akan wani dalili?!!! Gide wa ya ba ku wannan lasisin?!!’’ Ta shiga jera mu su tambayoyi kamar mai shirin taya Bintu kuka ta na mai duban gashin Bintu da su ka yanke.
Ba tare da nuna nadamar abun da ta yi ba Marry ta
amsa mata da ‘’Kama ta mu ka yi ta ke6e da Malam Aisar....’’ Waje ya kaure da hayaniyar d'alibai, Gimbiya kuwa kukan kura ne kad’ai ba ta yi ba ta je ta shak’o wuyar Bintu.
Ran Iya Dije idan yayi dubu ya 6aci, kallabin Bintu ta fizge daga hannun Marry y
ayinda ta mik’awa Bintu ta na mai fad’in ‘’Gide daura ki koma d’aki, kar ki damu ni Dije sai na bi mi ki hakkin ki, aradu ma kuwa" A sanyaye Bintu ta karbi kallabin, har lokacin kuka ta ke, gaba d’aya kayan ta ya b’aci da ta6on ruwan sama da ta kwaso, kan
ta sun kuye ta shige ciki. Bayan tafiyar ta Iya Dije ta mayar da kallan ta ga su Marry kana ta ce ‘’Ni Dije ni na ce Malam Aisar ya bar min sak’o wajan Bintu kasancewar ba zai same ni ba, kuma sak’on ba na kowa ba ne face sak’on Malam Hashim.’’
Wato dag
a Marry, har shedigyal da Sikanti babu wanda bai tsorata ba cikinsu, dan tabbas sun san matsayin Iya Dije gun Malam Hashim, da sun san da sa hannunta da ba su yiwa Bintu abun da su ka yi mata ba. Tuni idanunsu ya raina fata, cikin kame-kame Shedigyal ta ce
‘’Yetto Allah shi an sheda na hallau daliban nanniya su assheda na, yatsa ban kai ga jikin yarinyar ga ba, idan k’arya na kai aratta kashe ni."
Ko da jin haka Sikanti ma ta yi saurin d’age hannu sama ta na mai fa’d’in ‘’Balanta ni hallau Marry na rako
’’ Marry kuwa da ta san k’iri-k’iri Iya Dije ta ganta tana yanke sumar Bintu, jikin ta ne ya hau b’ari, kana ta yi k’ok’arin jan Iya Dije gefe domin bata wani abu dan kuwa kowa ya san Iya Dije da san abun duniya. Amma Iya Dije ta yi kyememe ta k’i sauraron
ta, sai ma barin ta ta yi awajan ta yi tafiyar ta. Tuni makaranta ta d’auka gobe Marry za ta sha horo, har da masu shagali dan murna. Gimbiya kuwa duk da jin Iya Dije ce ta tura Bintu gun Aisar ba ta fasa mata bambamin wai akan me ya sa ba ta fad’a mata ba
ita je a madadin ta tun da ta san ta na san shi, ko damuwa da abun da Marry ta yiwa Bintu ba ta yi ba bare ta saurara mata.
Da daddare Iya Dije ta kira Bintu ta na mai jaddada mata kar ta damu, ita za ta tsaya har sai an bi mata hakkin ta, ita dai duk
abun da Iya Dije ta ce gaban Malam Hashim ta amsa mata da eh. Da ke Bintu mace ce mai yafiya sai cewa ta yi ‘’Dan Allah Iya Dije ki bar ta kawai ba sai kin wani bi min hakkina ba, Inna ta tace kowa yayi na gari dan kan sa’’
Iya Dije na mai girgiza kai t
a ce ‘’Wagga gaskiya d’aita, amma wannan maganar ban barin ta ko dan rufin asirin kai na, aradu ma kuwa! Yo ki na tunanin idan shi Malam Aisar d’in ya ji bari zai yi? Abun da dai ya fi sauki ki yi yanda na ce kin ji ya?'’
Da wannan su ka yi sallama. Da
ren ranar Marry kuwa kasa bacci ta yi tsabagen fargaba, gashi ta cire wa d'iyar mutane suna, gashi duk abun nan da ta yi a banza tun da da sanin Iya Dije, babban tashin hankalin ta shi ne matakin da Malam Aisar zai d'auka idan ya ji abin da ta aikata. "Kar
dai fa ace ita d’in sai an yanki rabin gashin kan ta!'’ Abin da zuciyar ta ke raya mata kenan, yayinda ta ke kwance bisa gadan ta, kowa yayi bacci ya bar ta. Sai shafa d’an gajeran gashin da be ma kai kamu d'aya ba ta ke, ta san lalle idan da za a cire sh
i duka ko kwatan wanda ta cirewa Bintu ba zai kai ba. Girman kai ya hana ta iya zuwa ta bawa Bintu hakuri ko ta sami rangwame, "Ni Marry gide tawa ta same ni kishiya tara rana d’aya’’ Ta fad’a a fili yayinda ta tashi zaune ta na mai d'aura han[truncated by
WhatsApp]
®
✏
📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫
BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
©Khadija Sidi.....
✍
🏼
0
⃣
8
⃣
Tin da Iya Dije ta fara jawabi idanun Aisar da ya k’ada yayi jajur ke bisa fuskar Bintu
, wacce ke zaune kusa da Iya Dije kan ta sunkuye. Zaune su ke offishin Malam Hashim, dan kuwa gari na wayewa ko taron d’alibai(Asembly) ba a yi ba Iya Dije ta ja Buntu zuwa ofishin, ta na cikin masa jawabi ne Aisar ya shigo sanye da wannan shigar na sa da
ya saba, wato (suite) amma wannan karan ruwan k’asa ya saka.
Shigowar Aisar babu alamar da Malam Hashim be yiwa Iya Dije na ta yi shiru ba,
amma ina ta kasa d’aukan haske. Hankalin sa ba k’aramin tashi yayi ba ganin Asar ya tashi tsaye a fusace ya n
a mai maimata ‘’ta saka Ciseaux (Almakashi) ta yanke sumar Bintu!’’ shima Malam Hashim d’in tashi yayi, ya na yiwa Iya Dije alama da ido