Showing 6001 words to 9000 words out of 87659 words

Chapter 3 - HADARIN GABAS COMPLETE

11 Jul 2025

4518

da Moddibo Ya gina shi har su kansu asibitin
suke zuwa.

Tana parking Umma T ta fito da sauri Har tana yin kamar zata kifa. Hakan yasa Haulat D’in furta “Be
careful Umma T.” Sannan ta fito ta saka Umman tata a gefen jikinta suka k’arasa cikin asibitin.


Har a lokacin ba Wanda yake magana a cikin d’akin. Kowa da tunanin da yake ransa. Amani idanunta a
lumshe, tana tuno wancan bak’in daren da Dada ya rusa mata rayuwarta saboda son zuciya…. Duk da
sound D’in bu’de k’ofa da ta ji bai saka ta bu’de lumsassun idanunta ba har sai da ta ji maganar Umma
Tee. Tana tambayar Dada me yake faruwa da Didi? “Kiddo ka gaya min mana…” Ta bu’de lumsassun
idanunta tana kallon Dadan tana son ta ga reactions D’in fuskarsa. Iska taga ya fesar bai yi magana ba ya
jingina da kujerar idanunsa a lumshe. Wani irin fa’duwar gaba yake ji ya rasa da wani irin ido zai kalli
Umma T D’in. Fateemah ita ce tasa, ko a cikin siblings d’insu tasu tafi zuwa d’aya. Ita yake tara da dukkan
damuwarsa me zai ce mata a yau da komai Ya Riga ya kwab’e, bayan sai da ta dinga masa warning sau tari
idan yaje wajenta sai ta garga’de shi…. Umma T. Ta isa wajen gadon Didin ta dafa idanunta a kanta. Tana
jin yarda sautin zuciyarta ke k’ara bugu… kafin ta ce komai Didi ta bu’de lumsassun idanunta da suke
zubar da hawaye tana kallonta. Cikin rawar murya ta ce “Fad’imatu…maza fita da ni daga asibitin nan na
daina ganin Moddibo da ahalinsa…. A yau na yi nadamar d’aukar cikin Moddibo na yi nadamar
zamo…..” da sauri Umma T. Ta rufe mata bakinta da tafin hannun ta tana girgiza mata kai gabanta yana
tsananta bugu. Ta ce “Yi barci Didi, kada ki masa baki.” Sai kuma ta juya wajen Moddibo da yake tsaye ya
yi folding hand d’insa a k’irji jirkitattu kuma birkitattun idanunsa da suka sauya color ya zubawa Didin.
Hannunta tasa ta finciki nasa da sauri suka yi hanyar waje, duk jikinta rawa yake tana addu’ar Allah yasa
Moddin ba wani abu mai girma ya aikata ba da Ya tashi hankalin Didin. Bata tsayar da shi a ko ina ba sai a
cikin motarsa tana kallonsa ta furta “Bu’de min mu shiga ciki ka gaya min menene? Koma me ka aikata
lamarin sa na tabbatar ya yi muni Kiddo, tunda har ya zubar da Didi duk jarumar zuciyarta…” Hannu ya
saka ya danna remote D’in motar suka shiga… da suka shiga ma kasa mata magana ya yi ya lumshe
idonsa yana jin yarda idanunta suka bi suka dabaibayeshi. “Ina jiranka” Umma T ta furta…. Idanunsa a
lumshe Ya furta “She is pregnant….” Umma T. Da wani irin tashin hankali ta furta “Who? Kada ka ce min

Amani?” Ya ha’diye wani abu da Ya tsaya masa a wuya da k’yar sannan ya d’aga mata kai…. Ko bai yi
magana ba ya san ta san me yake nufi. Da k’arfin gaske ta jijjiga shi ta ce “Sai da ka aikata Moddibo? Sai
da ka rusawa yarinyar nan rayuwarta? Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna, dole Didi ta firgice dole ta rasa
kanta wannan abin k’azantarsa ya munana…” Ta fa’da idanunta suna zubar da wasu irin hawaye. Jikin
Moddi Ya yi sanyi don abu ne da bai tab’a ganinsa ba hawayen Tee d’insa, tun yarintarsu har yanzu da
suka girma… Ya kama hannunta ya matse da kyau. Kafin ya d’ora fuskarsa a tafin hannunnata yana sakin
wani irin kuka da yake bayyana tashin hankalin da zuciyarsa take ciki… Da wani irin zafin nama ta janye
hannunta ta kuma kafe shi da idanunta kafin ta furta “To hell with you Moddibo, me zaka ce min sau
nawa naja maka kunne akan hakan Amma ka nuna min bakomai… gashi nan abinda ake gudu ya faru…
na tabbata ko rantsuwa zan yi ba zan yi kaffara ba k’ungiyar matsafa ka shiga, su suka ‘dora ka akan haka.
Ka cuce mu, ka cuci yaranka ka cuci kanka, ka kuma cuci Didi da ta d’au dukkan kulawar ta ta d’ora a
kanka, ga sakayyar da ka mata nan na tabbata wannan ne zai zama ajalinta. Zan d’auke Uwata zan bar
asibitin nan da ita bana son kuma koda wasa kazo inda take, yaranka kuma ka san yarda zaka yi da su, ga
abinda ake gaya maka nan wannan loakcin ake gudu gashi yazo…” Daga haka ta fice daga motar da sauri,
kamar zata tashi sama. Zuciyarta wani irin zafi take ga tausayin Amani da take ji a ranta. Me Moddibo ya
aikata shikkenan ya rusa rayuwar Amani waye zai aureta da wannan bak’in painting da Ubanta ya shafa
mata? Tafiya kawai take bata san inda take saka k’afarta har zuwa sanda ta isa d’akin da aka kwantar da
Didin da Amanin. Tana shiga ta kalli Haulat da Iman don bata son yin zancen a gabansu ta ce su tafi waje.
Idanunta Ya rufe ta nufi wajen Amanin ta jata da k’arfin gaske ta fara zuba mata dundu tana furta
“Hankalinki ya kwanta Ama? Mahaifinki Ya kusanceki ko ga tsarabar sa nan a cikin ki? Sai ki fara shirin
abinda zaki fuskanta nan gaba.”
Da sauri Mommy ta isa wajen tana furta “Aa Umma T, kada ki mata lahani, ki bi a hankali duk da an San
abin da ciwo Amma ai k’addara ta riga fata…” Wani irin kallo Fateema ta jefa mata tana furta “K’addara?
K’addara kike kira Safna?” Sai ta cije bakinta ta isa wajen Didi da ta ji tana nishi da k’yar. Hankalinta a
tashe kawai ta zube a wajen tana sakin wani irin kuka. Shigowar Umma D. ne yasa ta ‘d’ago tana kallon
Umma D D’in da ta nufi wajen Safna tana furta “Me ya faru ne?” Safna taja ajiyar zuciya kamar gaske ta
furta “Wannan tashin hankalin bai kamata ki ji shi ba.” Wani kallo Dijatu ta mata kafin ta isa wajen Didi
tana furta “Ya Ilahi wai me ke faruwa ne?” Safna ta jijjiga kai a ranta ta furta “Ai yanzu zan gaya miki
asararriya burina yau ya cika…” a fili ta furta “Abin dai ba da’din Ji, Amani ce da cikin mahaifinta a jikinta
……” Dijatu ta juyo da sauri tana zubawa Safna wani gigitaccen Mari kafin ta furta kada ki k’ara gaya min
wannan banzar maganar, Har abada Jinin Muhammadu Moddibo ba zamu aikata irin wannan fasadin
mara da’din ji ba, ta fa’di dai Uban da ya mata ciki ba Moddibo ba, sau nawa nake fa’da a sakawa yarinyar
nan ido rawar kanta tafi k’arfinta, yanzu Fateemah kin yarda da abinda na fa’da, Har kuke jin haushi na da
na hana yaron wajena aurenta, yanzu kun ga Hujjata ai dama na fa’da da wata a k’asa gashi kuwa ta
fito….” Fateemah ta ‘d’ago a hankali tana kallon Dijatu abin mamaki sai taga kamar Dijatun farin ciki ne a
cikin idanunta kamar Moddibon ba D’an uwanta da suke ciki guda ba…. Ba tun yau ta san Dijatu bata son
Zuri’ar Moddibo ba ba, ta kuma rasa dalili.. cikin b’acin rai ta furta “Adda D, kamar abinda kike bai kamata
ba, ya kamata mu samu mafita ba kuma a samu na Yaya tawa a gari ba…” wata dariya ta yi kafin ta
kalleta ta ce “Ai zancen Duniya ba zai tab’a b’uya ba….

JIKAR NASHE★✍️HADARIN GABAS…..



NAZEEFAH SABO NASHE★✍️






_*BRIGHT PENS...*_
2nd batch
Zazzafar tafiya mai abin ban mamaki, tawayen jerin marubuta huɗu a sabuwar tafiyar ta second batch.

*HADARIN GABAS*
Nazeefah Sabo Nashe

*ƘARFE A WUTA*
Ayushercool

*ZAYTOON*
Zee kumurya

*MUTALLAB*
Nimcyluv Sarauta.




4️⃣



Shiru Fateema ta yi tana kallonta cike da mamaki. Duk da ba yau ta saba hakan ba Amma na yau kam ya
bata tsoro. Jininka fa uwa d’aya uba d’aya wannan babban bala’i Ya same shi amma ka nuna kai farin ciki
ma kake.. Didi kallonta itama kawai take tana zubar da hawaye, bata San lamarin na Dijatu ya yi zafin
haka ba. Ta k’arasa gadon da Amani take fuskarta a d’aure tamau ta zuba mata ido tana furta “Ke fa’di
Uban da ya Miki ciki, don ko duk jikina kunnene ba zan yarda Moddibo bane, dama can kin saba yawon
banzanki, mara kunya fitsararriya yanzu ga guzirin abinda kika aikata nan.” Shiru Amani ta yi ta kuma
runtse idonta ba tare da ta bata amsa ba, don sam bata son Dijatu kamar yarda itama take nuna mata
tsana muraran. Idanun nata a lumshe ta dinga ganin Flash back na abinda ta San Ya faru, Wanda ta
tabbatar ba zai tab’a goge mata ba…..



____________

Bata manta ranar da rayuwarta ta fara sauyawa daga Amani zuwa wata can daban da k’addara take juyin
waina da ita. Zaune suke a d’akinsu ita da Imaan suna shirya yarda zasu tari Dada da zai dawo daga Spain
a ranar. Murna ce fal cikinsu ba don komai ba sai don Dadan ya musu alk’awarin kawo musu wayar da ake
ya yi a lokacin IPhone 14. Basu tab’a rik’e waya ba don Dadan nasu bai basu dama ba hakan yasa murna
ta kasa barin fuskokinsu. Dama tuni suka gama masa duk wani girki da suka son zai so zai kuma yi
marmarinsa musamman ganin cewa watansa biyu cur baya gari. Tun asuba da suka tashi basu zauna ba
duk da yawancin girkin Imani ce ta yi Amani kuwa ko cangal bata yi ba sai damunta take da d’an banzan
surutu. Haushi Iman D’in take bata ta yarda ta bari Mommy ta mayar da su jakai tana can a kwance bata
aikin fari balle na bak’i shi yasa sai k’iba take kamar ana zuba mata yeast.


Amani kwalliya ta yi sosai ta tsuke cikin Riga da wandon da ya bayyana duk wata sura ta jikinta. Tana da
cikakkiyar surar da duk namijin da Ya kalleta sai ya ji ta burgeshi komai nata gwanin sha’awa kamar ita ta
halicci kanta. Ba kwalliya a fuskarta illa lip balm da ta sakawa d’an bakinta. Gashin kanta kuwa ta matse
shi a tsakiya hakan ya sake mata kyau kuma kamanninta da Rabi Mukherji Ya sake bayyana. Kallonta
Imaan take tana furta “Amani ba zaki daina saka wa’dannan matsatstsun kayan ba?” Amani ta juya tana
kallon kanta a mudubi rigatta d’af jikinta ko cibiya bata wuce ba. Ta d’an ja tsaki tana furta “Zan ga sanda
za ki waye, me ye a cikin shigata gidan nan duk ba wani Wanda ba muharrami na ba, idan ma akwai me
za’a gani a nan?” Imaan ta ware ido tana furta “Mhmn ke ce kuwa mai abin gani, wallahi ki daina irin
wannan shigar zaki d’au hak’kin mutane da yawa…” Murmushi kawai Amani ta yi a zuciyarta tana jin ba
komai game da shigarta. Shigowar motoci yasa ta yi saurin d’aga labulan windown d’akin tana sakin ihu
da k’arfin gaske tana furta “Yeeeeah, Dada.” Sai kuma ta fita da saurinta ba tare da ta saka Hijab D’in da
Iman take ta mik’a mata ba…. Tana zuwa bata yi wata wata ba ta fa’da jikinsa wata irin runguma ta masa
rungumar da ta jita har tsakiyar kanta. Da sauri ta lumshe idonta tana jin wani irin bugun zuciya abinda
bata tab’a ji ba a duk sanda zata rungume shi. A hankali ta janye jikinta tana zuba masa ido. Shima
kallonta yake with a smilling face ya lokaci kumatunta yana furta “Baby girl how are you?” Ta d’an yi
murmushi tana karb’ar jakar hannunsa. Tana kallon yarda Mommy take zabga mata harara bata wani
damu ba don lamarin matar sam baya gabanta ya daina damunta. Hannun Dada ta kama zuwa cikin
parlor sai hira take masa shi kuma yana d’aga mata kai kawai idan da sabo Ya Saba da surutun Barbie.
Imaan da take gefe ta kai masa side hug. Itama ta ja hancinta yana furta “Pretty how fa?” Ta sakar masa
murmushi kawai suka zauna side by side d’insa. Hannu ya saka ya bu’de jakarsa ya ciro bunch of
chocolates ya mik’awa kowa tasa. Sai kuma ya ciro guda yana kallon Amani ya furta “Your’s.” Ta yi wani
irin tsalle ta cafe chocolate D’in. Favorite choco d’inta ce don haka ta yi saurin b’arewa ta saka a baki.
Dada ya d’an lumshe ido yana furta shazumamu… Oya ku bar ni na huta ku tafi maza.” Ba su wani ja ba
musamman ganin ya mik’a musu chocolates da IPhones d’insu da sauri suka tafi da gudu suka shige
sashensu….

A daren komai ya fara faruwa don tana kwanciya barci ta fara wani irin mafarki da Dadan yana
kusantarta abinda bata tab’a yi ba, shikkenan sai abin ya zame mata jiki kullum a cikin tunanin Dada da
wata muguwar sha’awarsa take…. Tun tana b’oyewa Iman Har Iman ta fara ji a duk sanda take mafarkin
tana kuma kiran sunan Dadan…




Ba zata tab’a mantawa ba da rana ta biyu da Iman ta San yanayin mafarkin. Imaan ta tashi hankalinta
kuma tun a lokacin taso su kai maganar wajen Didi sai dai Amani ta hanata.




ASALIN LABARIN……..


★★★
A cikin wani irin yanayi take a cikin barcin, yanayin da ya zame mata dole duk dare sai ta kasance a
cikinsa, yanayi ne na saduwa tsakanin namiji da mace cikin tsananin soyayya da zakwa'din juna. Irin
nishin da take saki a cikin barcin zai tabbatar maka da cewa tana jin da'din abinda ake mata. Zuwa wani
lokaci ta saki wani irin nishi mai kama da ihu sai kuma ka ji d'if ta koma barcinta kamar ba ita ba ce a
wancan yanayin mai kama da na ma'aurata suna saduwa a cikin wani irin yanayi mai nuni da shauk'i.
Mik'ewa Imani ta yi tana kunna bed side lamp idanunta akan fuskar y'ar uwarta da suka kasance y'an
biyu ne wato uwa guda ce ta haifesu a kuma rana guda abin da ake wa take da biyu kyautar Allah.
Hannunta ta saka ta share mata gumin da ke tsatstsafa daga jikinta duk da sanyin a'cn da take d'akin. Ta
kuma ja rigarta da ta yaye duka cinyoyinta a waje. Karatun Kur'ani ta saka a d'akin sai kuma ta d'ebo
ruwan zamzam d'in da take adane da shi a gefen gadon ta karanta ayoyin tsari a ciki ta tofa sannan ta
saka hannu ta dukan y'ar uwartata a hankali. "Amani tashi ki sha ruwa..." Amanin ta bu'de idonta da ya
mata nauyi da k'yar tana kallon glass cup d'in kafin ta saka hannu ta amsa ta shanye sai ragowa ka'dan ta
bari. Imani ta zuba ragowar ta shafe mata fuskarta da shi. Daga haka Amani ta san ta yi abinda ta saba.

"Na yi ko?" Ta fa'da tana kallon y'ar Uwar duk da a jikinta ta ji ta yi d'in don ga feeling d'in nan tana ji har
a lokacin tana jin kuma danshi sosai a k'asanta. Runtse idanunta ta yi tana tunano kwamacalar da ta afku
a cikin barcinta Mahaifin ta dai still a wannan karon ma yana saduwa da ita irin saduwar ma'aurata.
Runtse idonta ta yi hawaye masu zafi suna saukar a k'uncinta da saurin gaske, gefe guda tana dafe
k'irjinta saboda yanayin yarda zuciyarta take wani irin bugu da k'arfin gaske. Menene haka ne? Me yake
damuna? Me yasa duk duniya na rasa mutum guda da zan yi mafarki da shi irin wannan sai mahaifina?
Me yasa yake zuwa min a haka? Ta fa'da fuskarta na bayyana matsananciyar damuwa. Iman ma kukan
take tana kuma rik'e da hannun y'ar uwarta ta furta "Amani ki cire Dada a ranki kin saka shi a zuciyarki ne
shi yasa kike irin wannna mafarkin da shi... Ki tuna ke da kan ki kika ce kina jin kina yiwa Dada son aure a
ranki? Me yasa zaki saka haka a ranki? Sannan duk masu son ki da aure kin kasa bawa kowa dama me
yasa?" Shiru Amani ta yi tana ha'diyar wani irin zazzafan yawu don ita kanta bata san dalili ba ba kuma ta
da amsar da zata bawa Imani abu guda ta sani ta na yiwa Dadansu wani irin so mara kwatance sau tari
idan ta gan shi sai ta yi da gasken gaske take cire ranta daga son ta rungumeshi ko ta yi kissing lab'bansa
da suka fi galabaitar da ita a cikin mafarki. "I LOVE HIM IMANI..." Imanin ta ja addu'a a ranta tana tunanin
da gaske akwai wani Aljanni da ya auri y'ar uwarta yake Kuma zuwa mata da fuskar Dadansu idan banda
haka ta ina wannan kwamacalar zata yi yu ya zama dole su samu Inno da zancen nan tunda ba su da
wacce ta fita su d'in marayu ne mahaifiyarsu tun bayan haihuwarsu ta mutu kallo guda ta musu ta yi
kalmar shahada ta rasu. Ta sauke ajiyar zuciya da yasa Amani ta d'ago ta zuba mata narkakkun idanunta.
Cikin kasalalliyar murya ta ce "Ki yi hak'uri na san abinda nake yana damunki, na kuma hanaki ki gayawa
kowa ba don komai ba sai don ina tsoron irin fassarar da mutane za su yi min. Imani wace amsa zan basu
a lokacin da idanunsu suka dawo kaina da tarin tambayoyinsu? Shi yasa na hanaki gayawa Didi, don Allah
ina son ki cigaba da daurewa ina kuma rok'on Allah ya kawo auren mu shine zai kauda duk wannan
matsalar." Imani ta saka idanunta cikin na Amani kafin cikin murya data bayyana rauninta ta furta "Kin
gama making decisions d'in? Kin amince zaki auri Mahmud?" Amani zuciyarta ce ta buga sosai a duk
sanda aka mata maganar aure hakan ce yake faruwa da ita, don haka ita da kanta take danganta
al'amarinta da matsalar jinnu. "Zan aure shi ba don ina son sa ba Imani, ba don ya yi min a matsayin
Mijin da zan so shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login