Showing 3001 words to 6000 words out of 10546 words

Chapter 2 - WA YAFI K'AUNATA

12 Jul 2025

958

cibiya sai d'an k'aramin wando iya gwaiwa mijinta yafi son yaga mace kullum da k'ananun kaya, shi yasa kullum itama tana k'ok'arin ganin ta faranta masa rai, parlo suka fito sai da ta ciyar dashi abincin safe sana suka dawo parlo suka zauna suna fira jefi-jefi har lokaci ya d'anja, d'agowa tayi tana binsa da kallo cike da sonsa tasa hannu tana shafo fuskarsa ta ce "ya kamata my kaje yau wajan Hajiya tunda ta ce cikin satin nan take son ganinka ya kamata kaje yau kawai" kallon matar tasa yake cike da so, ya sakar mata murmushi ya ce "insha Allahu yanzo dana fita sallah zan wuce unguwar tamu" ya idasa maganar zuciyarsa na d'an bugawa, lumshe ido tayi cike da jan hankali ta ce "to yau mi kake so na dafa ma da rana uhum?" murmurshi yayi ya ce "komi kika dafa zanci ai bari na tashi naji an fara kiran sallah", tashi tayi daga jikinsa, yana gaf ficewa ta kira sunansa tsayawa yayi, k'arasowa tayi kusa dashi kamar yadda ta saba ta had'e bakinsu waje d'aya wani irin kiss ta aika mai dashi ai ko yaji sakon har tsakiyar kansa, ya lumshi idonsa yana k'ara rik'eta sun dad'e a haka sana ta sake shi tana cewa "mijina Allah ya kare min kai ya dawo min da kai lafiya ya kareka da dukkannin sharri ya dawo min da kai cikin aminci", sosai yaji addu'ar tata, duk da ta saba mai haka amma koda yaushe da kalar addu'ar da zata mai shi yasa kullum sonta k'aruwa yake bawai raguwa ba.


Haka suka rabo zuciyoyinsu cike da begin juna,


Yana fita ta d'an tsaya tana cewa "to mi zan dafa mai?," can kuma saita d'an girgiza kai tana murmushi.


Kitchen ta shiga ta d'akko b'arzazzar shinkafa ta d'akko roba ta juyeta a ciki ta wanke ta fas, sana ta d'akko tukunyar ta zamani sitima, tasa ruwa a k'asanta, tasa hawa na d'aya, ta d'akko mai da magi fari da d'an gishiri kad'an, duka tasa a cikin b'arzazzar shinkafar nan data wanketa, tasa mai fari mai d'an dama-dama, sana tasa farin magin nan da gishiri, sai tasa ludayi ta motsa ta had'esu, sai kuma ta d'an taro ruwa kad'an tasa a ciki, sai ta d'akko tukunyarta mai hawa-hawa ta fara zubawa gida uku ne ko ina tasa sai kuma ta d'akko gyad'a wadda ta daka ta sama-sama tasa a ciki, ko wanne gida sama-sama ta barbaza ta, ta had'a su waje d'aya ta rufe saman tukunyar da marfinta, ta d'ora akan gas.

Tana gama wannan ta d'ora wata tukunyar ta d'akko d'anyan naman kaza dake cikin firiza tasa a tukunya, ta yanka al'basa a kai ta d'ora a d'ayan gas d'in, sai kuma ta d'akko tafarnuwa ta dakata da kayan k'amshi tana gama dakawa ta juye a tukunyar data d'ora naman kazarta a ciki, sai da naman kazarta ya tafasa ya fara k'amshi ta d'akko markad'ad'd'und'on kayan miyarta ta juye a ciki ta rufe, sai da miyarta ta fara dafuwa, sana ta bud'e tasa kayan d'and'ano, danda nan gidan ya fara d'omewa da k'amshin girki, sai da miyar taja sosai sana ta d'akko manja tasa a miyar ta rufe, sai kuma ta rage gudun gas d'in, ta koma ga danbun shinkafarta ta bud'e sama tasa cukali ta d'ebo, ya daho yayi wara-wara ta sauke ta juye a kula, sai da ta kai darning sana ta dawo ga miyarta, tana bud'ewa har mai ya fito sosai ta kashe gas d'in, ta juye ta itama a kula, ta kaita darning, ta dawo kitchen d'in ta gyara ko ina, sana ta bud'e firiza ta d'akko ayarta da dabino da kwakwa ta wanke su ta tsaftace su tasa a bilanda ta had'esu ta markad'e sai da ta tabbatar sunyi laushi sun markad'u, sana ta juye su, ta tace su ta d'akko wani jok mai tsawo ta juye a ciki, sai kuma ta d'akko madarar da ake yin iloka da ita, guda d'aya ta juye rabi a ciki, tasa cukali ta motsa ko ina ya had'e, saita d'akko k'ank'ara ta fasa ta ta juye a cikin kunun ayarta, ta aje gefe guda ta k'ara gyara kitchen d'in ko ina yayi kyau, sana ta fita ta aje shima kunun ayar akan darning.


D'an zaunawa tayi tana rik'e k'ugunta saboda ta gaji sosai, sai da ta d'an huta sana ta shige bathroom tayi wanka ta sake fashe jikinta da turare tasa turaran wuta tasa hijabinta ta rufe kanta dashi sai da ta tabbatar ko ina na jikinta ya d'au k'amshin turaran wutar, sana ta aje shi a gefe yana ba d'akin k'amshi, sallah tayi ganin har hud'u tayi, tana gamawa ta fito parlo ta zauna jiran mijin nata.



RAMADAN POV

Sai da ya gama sallah a masallaci sana ya shiga motarsa ya nufi unguwarsu, yana zuwa mai gadi ya wangale mai get ya shiga harabar gidan nasu yayi parking d'in motar yana kallon harabar gidan naso a cikin zuciyarsa yana tunanin da Abbansa yana raye da duk wannan matsalolin basu faru ba, sai da suka gaisa da mai gadi sana ya nufi cikin gidan naso.


A babban parlon gidan nasu ya tadda duka y'an gidan da k'annansa guda biyu sai Yayyansa guda biyu Ya Aysha ce kawai babu itama dan tayi aure su kuma Inteesar da Nawwara Auntys d'insa kenan basuyi auran ba sai k'annansa guda biyu Hasana da Usaina.


Suna ganinsa suka gaida sa shi kuma ganin Yayyan nasa mata na mai wani kallo yasa ya murtuke fuska yana gaida su badan yaso ba.


Amsawa sukai ba yabo ba fallasa Hajiya ce ke sakkowa, d'aga kai yayi yana kallonta ganin irin kallon da take aika mai dashi ne yasa yayi k'asa da kansa, tana k'arasowa har kasa ya duk'a ya kwashi gaisuwa, sai da ta zauna ta d'ora kafa d'aya kan d'aya tasha mur ta bud'e baki cike da isa ta ce "sai yanzu kaga damar zuwa ko kuma sai yanzu y'ar gwal d'in taka ta baka umarnin zuwa?" ta idasa maganar tana tsaresa da ido, shi kuwa cike da mamaki yake bin Hajiya da kallo, shikam ba duka jiya ne Ya Ayshar ta zo ta gaya mai sakon Hajiyar ba, katse mai tunani tai da cewa "koma dai minene ka sanar da ita cewa nanda wata biyu masu zuwa zaka k'ara aure, nanda sati biyu kuma zanzo har gidan naka da amarya, zata zab'i inda yayi mata koda d'akin da Munnirar take zaune ne kuwa, idan ta nuna nan ne yayi mata dole ta kwashe komatsanta taba amarya waje, kaji na gaya maka karma kace ban sanar dakai ba", wani irin kallo mai wuyar fassarawa yake bin Hajiya dashi wannan k'iyayya har ina kai jama'a ta ina zai fara ne, Hasana ce ta buga tsalle dama ba kunya ne da ita ba tana cewa "haba ai gara ta matsa taba amarya waje duk ta kanainaye komai dama... Kamin ta idasa maganar Ramadan ya tashi a zuciye yana d'auketa da wani gigitaccan mari ji kake tasss tasss, su duka sai da suka tashi tsaye, Hasana sai hawaye tana b'oyewa bayan Hajiya ganin yadda yake huce kamar zai rufeta da duka, Hajiya cike da masifa ta rufesa da fad'a tana cewa.........✍️



*Washhh Allah na gaji mu had'u zuwa gobe idan Allah ya kaimu*



ZAHRA ROYAL STAR CE



SHARE FISABILILLAHI🥰🙏


*👩‍❤️‍👨💞 WAYAFI K'AUNATA 👩‍❤️‍👨💞*
(Love Story)




PAID BOOK #500






MALLAKIN
*©ZAHRA ROYAL STAR*





*Littafin kud'i ne wadda ya shirya yin tafiyar dashi zai iya turo kud'insa, ko katin MTN ko hoton katin saika turo shaidar biya #500 ne kacal*




8130479973
*FATIMA RABI'U OPAY BANKA*




Zaka turo shaidar biyanka ko hoton katin ta wannan number d'in,
(08130479973.08035023054)





Free Page 5-6



بسم الله الرحمن الرحيم العالم



Muka ji saukar maganar ta akanmu cike da masifa tana cewa "kai dai Hafiz ban san irin ka ba wallahi, shin wai mika gani wajan wannan yarinyar mai kama da aljanu?, ka wani mak'ale mata, to tun wuri bari na gaya maka idan wani abunne a zuciyarka wallahi kayi gaggawar cire shi a ranka" ta idasa maganar tana hararara ta gaida ta nayi ina cewa "Inna Rabi ina wuni" wani banzan kallo data yi min tana cewa "da ban wuni ba kin ganni uwar iyayin tsiya, kai kuma bita zai-zai sai ka ciga ba da bin bayan ta kamar wani jelar doki, ai shi yasa d'an uwanka yake birgeni ya za'ai ma ya tsaya da wannan kucakar yarinyar", ta idasa maganar tana jan wani dogon tsaki tayi gaba abinta.


Shi kuwa girgiza kai kawai yayi yana kamo hannuna ganin nayi k'asa da kaina ya ce "Maryam" ya kira sunana a hankali d'agowa nayi ina dubansa cike da sona ya sake cewa "am so sorry my Maryam... Da sauri na katse shi da cewa "kai Ya Hafiz miye na bani hakuri to?, ai itama uwata ta ce dan tayi min fad'a ba wani abu bane" murmushi ya sakar min yana k'ara kallon kyakkyawar fuskata, shi dai Allah ya sani ina matuk'ar birgesa.


Ganin lokaci naja na ce "Ya Hafiz bari na shiga daga ciki kar Iya taga na dad'e" saki na yayi yana cewa "Ohh na ma manta aiken mu fa aikai oya jeki ina nan shigowa sashin naku" da to na amsa inayin gaba.


Da sallama na shiga Iya na zaune, ta tasa fulawar da zatai d'an wake a gaba tana jira na, murmushi na saki ina zama kusa da ita, tashi tayi tana d'ebo ruwa ta zauna tana cewa "yanzu fisbilillahi Maryam tun d'azo na aike ki sai yanzu kikaga damar dawowa saura masifaffan can ya shigo duk ya damu mutane" tana maganar dai-dai ta gama kwab'a d'an waken tashi nayi ina cewa "kai Iya wallahi a hakama nayi sauri kuma harda shi ya tsayar dani yana faman min tsiyar daya saba min yanzu dai kawo na jefa d'an waken" sakar min tayi, tana zama a tabarma, dama tuni ta d'ora ruwan zafi harya tafasa, zama nayi gefen murhun na fara jefa d'an waken, Iya dake kallona ta ce "yanzu sabo da Allah shi dai duk inda ya ganki hankalinsa bazai kwanta ba saiya jaki fad'a, ni na rasa wannan k'iyayya taku keda shi, to idan Allah ya k'addara zaku zauna inuwa d'aya fa..... Kamin ta idasa maganar da sauri har ina shirin zubar da kwab'un d'an waken na ce "kai Iya wannan wane irin fata ne kike min dan Allah ki daina ma wannan maganar karma mala'iko suji su amsa ina dalili ina zankai rigimar Ya Abbas kashe ni zaiyi wallahi", dariya ta sakar min tana cewa "ke ki bimin sanwa a hankali karki zubar min da kwab'i , wasa nake miki koni bazan bari a had'a ki da wancan mai bak'ar zuciyar ba".


Tashi tayi bayan na gama jefa d'an waken na d'akko roba da ruwa a ciki ina tsamewa ina cewa "yauwa Iya ta ai nasan baza ki bari ba Allah sarki da Kakana mai shano na nan ai da mai wannan bak'ar zuciyar bazai min duk wannan abubuwan ba", Iya dake zaune cike da damuwa da kewar mijin nata yau kusan shekaru bakwai da rasuwa, ta ce "Allah dai ya jik'an Malam" da amin na amsa nima zuciyata ba dad'i Allah baya barin wani dan wani yaji dad'i.



Bayan na gama Iya ta ce nasa mai nashi a kula, sai da nasa masa na aje gefe, na had'a mana nida ita muka zauna muka fara ci d'an waken yayi mun dad'i sosai saboda yaji kayan had'i an yanka su tumatur dasu albarsa harda kwai a ciki.


Bayan mun gama na shige d'aki nayi alwala ganin har mangaruba tayi ina cikin sallah naji muryarsa ya shigo suna gaisawa da Iya data idar da sallah, jawo mai d'an waken tayi ta zuba mai, saida ya fara ci yana tand'e hannu sai da ya gama ci tas ya wanke hannu yasha ruwa ya goge baki, da kamar bazai tankama Iya ba can kuma sai ya ce "na ce dai Iya ba wannan k'azamar yarinyar taki ce kika ba ta jefa min d'an wake ba" wani dogon tsaki Iya taja tana cewa "kai Abbas bafa nason rashin ta ido ka kalli zabar ido na sai da ka gama lashe abinci zaka zo kana kawo min wani suki burutsu, to ita ce tayi, kaga saika amayoshi ko", ta idasa maganar cike da gatse tashi yayi yana murmushi wadda Iya ce kawai take ganinsa zaro kud'i yayi zasu kai dubu uku ya aje mata yana cewa "haba Iya ta kar aji kanmu mana yanzu ga wannan ladar yimin d'an wake da kikai ne" tashi Iya tayi tana washe baki dan Iya akwai son kud'i ta ce "yauwa d'an albarka yanzu kayi zance mai kyau to na gode Allah shi k'aro bud'e" da amin ya amsa yana ficewa daga sashin.


Ni kuwa dake cikin d'aki, fitowa nayi ina sane nak'i fitowa yana nan samu nasan bazamu kwashi ta dad'i ba nida shi kamar wuta da ruwa ne.

Zaunawa nayi ina zunb'uro baki gaba ina cewa "Iya kinji fa mi ya ce wai ni ce k'aza ma" na k'arashe maganar cike da jin haushinsa a raina tashi Iya tayi tana d'aure kud'in daya bata a hab'ar zaninta tana cewa "ke kinga ni bana son wannan sokiburutsin naku keda shi wadda baya k'arewa ba kinsan halinsa ba?, fad'a yayi fa dama dan kiji haushi ai", tashi nayi ina cewa "yauwa Iya candynmu fa ya kusa na gama secondary school kuma kinmin alk'awari zan wuce ko ina so nima nayi karatun likitancin nan", Iya dake zama kusa dani ta kunna rediyon ta tana cewa "eh nima ina son haka amma dole sai mun zauna da Iyayanki kinsan dai bake kad'ai zaki gama makarantar ba bansan mi suka yanke a kanku ba idan aure suka yanke a kanku haka zakiyi hakuri kiyi shi banda ta cewa tunda bake kad'ai ce ba" hankali na yayi mugun tashi matsowa nayi kusa da ita ina cewa "Iya aure kuma?, ni dai gaskiya wallahi Allah ban shirya mashi yanzu ba dan Allah Iya karki bari a durkusar min da rayuwata duka nawa nake da za'a ce wai aure", tashi Iya tayi tana janye ni daga jikinta itama kanta zata so na wuce d'in sai dai kuma abun zai zama abun magana a cikin gidan ta ce "Maryam bawai bana so kiyi karatu bane a'a abunne zai zama abun magana dama yanzu ana min surutu nida ke cewa nafi sonki, ke kuma kin tare ko ina kin hana sauran jikokina suji d'umin jikina, kuma ba haka bane ke kad'ai ce marainiyar babu wadda zaki rab'a kiji dad'i idan ba niba, ina suke so kije to? shi yasa nake k'ara jawoki a jikina dan bana so kiyi kukan maraici amma gani ake kamar son kai ne nake nunawa a kanki gani suke kamar soyayyar da nake ma Mahaifinki ce ta dawo kanki, Maryam Mahaifinki sadda yana raye kwata-kwata baya so yaga kuka na ko b'acin raina yana min biyayya sosai koda zai cutu kuwa , duk cikin y'ay'ana nafi jinshi a raina badan komai ba sai dan harga Allah zuciya na son mai kyautata mata, Mahaifinki kullum cikin kyautata min yake, to taya za'ai bazan so jininsa ba?, kawai kiyi hakuri muga miye suka yanke komi Allah ya tsara miki Maryam a rayuwa ki karb'esa hannu biyu-biyu kinji?", shigewa nayi kawai jikinta ban k'ara cewa komai ba dan baki na yayi min nauyi.........





*KADUNA* POV




Hajiya cike da masifa ta rufesa da fad'a tana cewa "kai kai kai tsaya daga nan na ce, dukanta zakai akan waccar abar akan ta fad'i gaskiya, ai gaskiya ta fad'a, uban miye take a cikin gidan naka inba taci ta kwanta ba, tabi ta kanainaye komai, sai abunda ta ce shi kakeyi, dan haka karka sake ka k'ara kai hannunka akan yarana indai akan waccar matar taka ce", ficewa yayi daga gidan gaba d'aya ranshi idan yayi dubu ya b'ace.


Yana fita Nawwara ta ce "ai wallahi kin min dai-dai wallahi waccar matar ba'a banza ta barshi ba kina ganin daga anyi maganarta ance tayi kaza harya tashi a hargitse", zaunawa Hajiya tana jawo Hasana dake bayanta ta ce "ke kuma gobe ki k'ara shiga harkarsa idan yayi miki illa ke kika sani" k'unkuni ta farayi tana zama kan kujera Inteesar ce da har yanzu bata sa baki ba tana danne-dannen waya ta ce "nifa wallahi wani lokacin ban ganin laifin Munnira saboda tsantsar kulawa ce take bama mijinta kun kasa fahimta ne ba wani asiri a ciki", da sauri Hajiya ta ce "kinga Inteesar ki fita ido na rufe ki fita samgar wannan sha'ani tunda naga kema ta shanye ki ta gama dake, dan haka karna k'ara jin bakinki a ciki, tunda naga keda Ramadan d'in kamar an canza min ku, ke Nawwara maza idan kin gama abunda kike ki kira min Halima", da to ta amsa Inteesar kuwa tab'e baki tayi tana tashi tabar masu parlon dan ita Allah ya gani bata ga wani abunda Munnira take na rashin kyautawa ba kawai dai dama can Hajiya ba son Munnirar take ba.





Ramadan yana isa gida ya saita kansa baya so ya shigar mata da b'acin rai bata ji ba bata gani ba,

Amma duk da haka Munnira na ganinsa tasan ransa a b'ace yake, ruwa mai sanyi ta kowa mai ya sha yana sauke ajiyar zuciya bata ce mai komai har sai da ta taimaka mai yayi wanka ta kaishi har darning ta zaunar dashi sai da ta zuba mai abinci, yadda k'amshin girkin ya bigi hancinsa yasa ba shiri ya lumshe idonsa har miyan bakinsa na tsinkewa zama tayi kusa dashi tana d'an tsotsar alawa dake bakinta kallonta yayi ya ce "minene kika ta tsotsa ne wai?" murmushi ta sakar mai, mai tsada ta ce "alawa ce fa" jawota yayi jikinsa yana cewa "oya zan sha bani nima" turo mai d'an k'aramin bakinta tayi, ta had'e da nasa ta tura mai alawar cikin bakinsa sai kuma ta d'an kamo harshansa tayi mai wata irin tsotsar da yasa lumfashin Ramadan d'aukewa na wucin gani, can kuma saita sakar mai bakin har yanzu idonsa lumshi yake yadda yake jin zak'in alewar da miyan bakinta sai suka bashi wani irin gard'i kamar karta saki idonsa harya canza launi murmushi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login