Showing 192001 words to 195000 words out of 275307 words
masarautar Joɗa naji in ba aljanunta ba."
Cikin damuwa Ummi tace.
"To wake firgitata har hakane".
Cikin riƙo hannunta gam ganin yadda taketa fizge-fizgen tana rantsewa wlh ƙarya akeyi yana garin.
A hankali yace.
"Kawai fa Ummi al'janunta ne ke zuwa da wani sabon salo.
Kuma zanci musu mutumci, bazasu medamin gida sansanin ihu da kururuwa ba".
Cikin sanyi Ummi tace.
"Babu maijin ihunta fa Sheykh, kai dai ka ƙara bincike da kyau akan al'amarin."
Sai ta kuma kalli Aysha da har yanzu a gigice take.
"Ki nitsu ko Aysha gani gashi ga Saratu.
Babu wanda zai shigo nan zamu ganshi".
Cikin sanyi ta gyaɗa kai.
Jan hannunta yayi suka nufi falonshi.
Ummi kuwa wurin Saratu taje suka fara aikinsu.
Shi kuwa yana riƙe da hannunta ya zauna bisa kujera kana ya zaunar da ita.
System ɗinshi dake hannunshi ya ɗaura kan stoll ɗin dake gabanshi.
Tare da buɗe wa, ɗan juyowa yayi ya kalleta.
jin har yanzu jikinta rawa yakeyi, a hankali yace.
"Ke wai me ya miki".
Cikin rawan murya na tsoro tace.
"Abunda kakeyi min".
Da sauri ya juyo ya fuskanceta tare da zaro idanunshi woje cikin ɗan ɗaga sauti da haɗe fuska yace.
"Me nakeyi miki da yayi miki?".
Ya ƙarashe mgnar a fakaice.
Cikin takaici tace.
"Hannunshi yasa a rigata".
Jawota yayi jikinshi tare da miƙewa tsaye.
Cikin faɗa da zafi rai a ɓace na fatar baki yace.
"Zancen banza kenan.
Ko iskarki ce, ta isa in haɗa muhalli da itane, bare wani can Jahan da ba'a san asalin menene shiba menene addininshi ba.
Ke wacce iriyar yarinyace, da zaki tsaya har ya kalli abinda Muhammad Jabeer ya kalla har ya taɓa min kayana.
Lallai ya nemawarwa kansa masifa da yayi gigin kai hannunshi inda hannuna ya kuskura ya taɓa."
Juyawa yayi a fusace ya nufi.
Bedroom wayarshi ya ɗauka tare, da kiran Jamil wanda ma'akacine a ma'akatar su Jahan.
Cikin kausasa murya yace.
"Ka binciko min waye Jahan ina yake suwa yakewa aiki nanda rabin sa'a ina son amsoshi na".
Da sauri Jamil yace to.
Ita kuwa Aysha a inda ya tashi ta kwanta.
Bayan wani ɗan lokacin.
Jamil ya kira Hamma Jabeer ɗin ya shaida mishi cewa da tabbas Jahan baya nan.
Baya ƙasarma gaba ɗaya tsawon watanni biyu.
Kuma babu wani Jahan da ya sani."
Jin hakane yasa Sheykh, yin wani sihirtaccen murmushi da kyau.
Ko Jamil bai san komai kan Jahan ba.
Murmushi yayi tuno yadda yake cewa al'janin Aysha ke zuwa da salon iskanci.
Ranar dai a gida ya wuni, yana fakewa yaita murmushi lokaci zuwa lokaci.
Ita kuwa Aysha wurin Ummi ta koma.
Sai da Yamma Sheykh da Galadima sukaje suka samu Lamiɗo sukayi mishi dukkan bayanin tafiyar da sukayi da nasarorin da suka samu a ciki, da alamar matsalar da suka tarar, nan sukayi tattaunawa tamu sannan kan al'amarin.
Aysha kuwa sai washe gari Ummi ta mata jagora taje, Sashi Gimbiya Aminatu.
A can ta samu, Aunty Juwairiyya da Mamin Affan.
Nan suka zauna sunata hira.
Sai yamma ko wacce ta nufi Side ɗinta.
Yau sallan layya saura kwana uku.
Mutane nata shiryawa shirin ƙaramar salla.
Yau tunda safe da Sheykh ya fita bai dawoba sai dare.
Washe gari da Safe, Junaidun ya kira Aysha bayan sun sha hira yake cemata.
"Adda Shatu, jiya Dr Sheykh yazo Rugar Bani, wurinsu Arɗo Bani da Babanmu.
Sunata godiya dai sunce ince miki ki ƙara yi mishi godiya kan hidimar da yayi mana."
Cikin mamaki tace.
"Au dama shine likitan da ya maidaku asibitinshi ya kula daku?".
Da sauri yace.
"Eh amman nima ban san shine kuma mijinki ba sai.
Yau da yazo.
Ni nayi zaton wurinmu yazo sai naga su Baba da Arɗo Bani sunata murnar zuwanshi, sai na gane bafa wurinmu yazo ba".
Uhum tace tare da cewa.
"To ba matsala in sha Allah zan masa godiya".
Daga nan sukayi sallama.
Konciya tayi tana nazartan takun Yan Sheykh sai dai duk nisan da zurfin tunaninta kafin taje wuri a tunani ko bincike tuni ya wuce ta.
Abu ɗaya ta fahimta, yana bin diddigi akan abubuwa da dama shi mutumum ne bauɗaɗde mai algibata tako ina ka buga zaka sameshi.
A ranar bata ganshi ba.
Hakama washe gari.
Sai da asuba Ummi ta tasheta akan ta kai mishi.
Abun yin sahur sabida gobe za'a tashi da azumin arfa.
A tsaye ta sameshi a falo da waya a hannunshi.
Bisa alamu da Aunty Hafsat yake mgn.
Gabanshi ta ratsa ta ajiye mishi tray'n a kan stoll dake gabashin.
Ba tare da ya kalletaba ya kamo hannunta ya riƙe lokacin da zata juya ta fita.
Sai kuma yaci gaba da wayar.
"Aunty Hafsat wai har bikin ya isone?".
A can ɗaya gefen murmushi tayi tare da cewa.
"Sosai ma kuwa Sheykh saura wata ɗaya da kwanaki ne zulhajji na ƙarewa da kwana biyar na sabuwar wata za'a fara bikin".
A hankali yace.
"To kuma shine zakuzo tun bayan salla da mako ɗaya, yanzu ita Ramatu da wa zata bar mijinta ta taho wata kusan biyu".
Hannunta dake cikin nashin hannun ya ɗan ƙara matsewa.
Tare da janta jikinshi.
sai kuma ya ɗan gyara tsayuwarshi tare da cewa.
"A a Aunty Hafsat ku bari in bikin saura mako ɗaya ko biyu sai kuzo".
Da sauri tace.
"Sai dai biyun".
Uhum yace. Ita kuwa cewa tayi ina.
"Ya Ɗiyata Aysha kuma yar uwata aborso a rayuwarmu".
Murmushi yayi a hankali tare da lumshe idonsa yanaji wasu zafafan hawaye na tashin hankali na tsastsafo mishi yace.
"Gata".
Yana faɗin haka ya liƙa mata wayar a kunnenta.
Da sauri ta ɗago ta kalleshi.
Tsareta da ido yayi. Jin muryar Aunty Hafsat ne yasata ɗan murmushi tare da cewa.
"Aunty Barka da asuba".
Cikin tarin so tace.
"Barka dai Aysha yasu. Jalal da Jamil ya kewan Hibba".
Cikin murmushi tace. "Suna lfy Aunty ina kewar Hibba kam sosai ma".
"Kada ki damu mun kusan haɗuwa ai muma zamu zo ai. Ya Jazlaan yana lfy ko".
Cikin jin daɗi tace.
"Allah ya kawoku lfy Aunty".
Amin Amin tace.
Kana tace.
"Ya Jazlaan yana lfy ba wata damuwar ko".
Ɗago kanta tayi ta kalleshi,
Kwaɓe mata fuska yayi tare da mata alamun bata amsa.
Cikin sanyi tace.
"Uhum Alhamdulillah".
"Masha Allah. To sai anjima ko kada in hanaku yin sahur".
Ɗaga nan sukayi sallama.
Shi kuwa a hankali ya zauna tare da zaunar da ita gefe.
Kana yace.
"Kinyi niyar yin azumin arfanne?".
Kai ta gyaɗa mishi alamar eh.
Kauda kanshi yayi tare da cewa.
"To kin nemi izinine?".
Tura baki tai tare da cewa.
"Izinin wa?".
Kanshi ya gyaɗa tare da cewa.
"Ok haka kikace ko baki san izinin wanda zaki nema bama kenan ko?."
A hankali ta ɗan kalleshi sai kuma tace.
"Kayi haƙuri. Ina son yin azumin, ka amince inyi?.
Kanshi ya jinjina tare da cewa.
"Uhuumm ai da kinyi ba neman izinin sai da yamma in karyashi".
A hankali tace.
"Ka karya min shi kuma ɗura zakayi min ne?".
Kanshi ya kauda tare da cewa.
"Aikin wani ladan zanyi dai in Kauda naki da nawan, Ni na samu lada biyu na niyan azumin da ladan raya Sunnah".
Shiru tayi tana jin yadda yake murza yatsarshi ma nuniya cikin tafin hannunta.
Ganin lokacin sahur na tafiya ne yace.
"To tashi kije kiyi sahur".
Miƙewa tayi ta fita.
Shi kuwa sahur ɗin ya fara.
To Alhamdulillah Azumin Arfa dai yayi zafi sosai kowa ka gani kamar yayi azumi goma.
Kuma yaune Lamiɗo ya ware raguna aka bada duk cikin masarautar Joɗa ahilinshi da bayinshi da hadimai kowa da ragonsa.
Sheykh Jabeer kuwa shima yasa su Jalal sunje sun raba a cikin gari sadaka.
Da yamma suna zaune Aunty Juwairiyya ta shigo gefen Ummi ta zauna.
Ita kuwa Aysha tana kwance bisa kujera kamar sumemmiya. Azaban ƙishirwa da yunwa ne suka dabaibaye kuzarinta.
Cikin sanyi Aunty Juwairiyya tace.
"Aunty Aysha sannu fa, Azumin da daɗi kam yau".
A gyatsine ta kalli Aunty Juwairiyya, sabida zuwa yanzu zarginta da takeyi yamafi na baya.
Ummi ce ta ɗan kauda zancen da cewa.
"Ya shirye-shiryen aiyu kam salla".
Murmushi ta ɗanyi tare da cewa.
"Alhamdulillah Ummi wannan karon ai aiyukan zasu zo mana da sauƙin.
Dan nan za'a kawo ragunan Jamil da Jalal Amarya ta gyara musu."
Ni inji dana Ya Jafar da nawa dana Hajia Mama".
Cikin murmushin Ummi tace.
"A a kada ki mana wayo kinada masu tayaki aiki ga Ladi da Lami duk zasu tayaki."
"Ummi kuma ga Saratu ga Larai gaki ga Aunty Aysha".
Cewar Aunty Juwairiyya.
"Duk da haka aikin da yawafa anan ga na Sheykh ga na Mamey ga ganawa gana Aysha kana ga na Jalal Jamil. Kuma suma su Saratu sunada aikin nasu."
A hankali Aysha ta miƙe zaune tare da cewa.
"Ummi aiki ai ba abin tsoro bane, ba damuwa".
Tana faɗin haka ta juya ta nufi ɗakinta.
Tazo gab da bakin ƙofar shiga falonta kenan taga wani irin duhu ya rufe mata ido sai jiri da sauri ta zauna.
Sheykh kuwa da yayi al'walan la'asar zai fitone ya ɗan zuba mata ido tare da cewa.
"A azumi ɗayan ne kike neman faɗuwa zaki sune min ko".
Dariya Ummi tayi tare da cewa.
"Azumin fa da zafi Sheykh".
Kanshi ya ɗan juyo tare da cewa.
"Kaiya Ummi ragwanci dai".
Murmushi sukayi ya wuce ya fita.
Ita kuma da ido tabi bayanshi ƙeyarshi ta liƙawa wani mayataccen kallo.
Kana ta miƙa tsaye ta nufi ɗakinta.
Ummi kuwa cikin gyara zama tace.
"Gsky Juwairiyya aikin nasu Jamil ayishi a sashinki.
Kinfa San na Sheykh ma biyu ne".
Dariya Aunty Juwairiyya tayi tare da cewa.
"Kai Ummi to shi Sheykh ba a ana tashi sallan idi a wurin ake yanka nashiba, tunda shine liman baza'ayi layya ba sai yayi.
Yanayi kuma a wurin ake rabashi sadaka.
Daga nan kowa ya dawo gida yayi nashi".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Eh to ai akwai wanda Lamiɗo ke bashi kuma za'a kawoshi nan".
Miƙewa tsaye tayi tare da cewa.
"To shike nan Ummi a bar na Jamil tunda shi zaima je ya tayamu aikin ku ku gyara na Jalal".
"To shike nan". tace kana suka tafi salla.
Bayan sun idarne suka fito suka fara aikin buɗa baki.
Bayan sunsha ruwa sun hutane.
Suka shiga kitchen kimtsa kayan aikin da aka lodo musu sukayi.
Kana suka ɗan haɗa aikin da zai iya faruwa a lokacin.
Washe gari aka tashi ranar Sallan layya.
Yara da manya mata da maza al'ummar Annabi na duniya baki ɗaya anata shiryawa zuwa idi.
Babu wanda ya tsaya karyawa sabida duk suna azumi.
Wanda sai bayan an sauƙo idi anyi yanka mai layya yayi buɗa baki da hantar dabbarsa.
Sauri-sauri yake kimtsawa cikin wata kekyawar al'kyabbar mai taushi baƙa sai farar jallabiya da yasa a ciki.
Hiraminshi ya kimtsa kana ya fisa turare.
Sannan ya fito da sauri ganin lokacin nata gaba towa.
A falo ya samu Ya Jafar. Tare suka fito babban falon.
Nan suka samu su Ya Hashim, Jalal, Jamil, Imarn, Affan, Sulaiman. Da sai sauransu.
Nan suka rakaya suka nufi masallacin Masarautar Joɗa inda nan yake limancin Sallah idi.
Masallacin da ƙaton filin harabar masallacin duk ya cika yayi maƙil tako ina al'ummar Annabi ne keta shigowa.
Cikin shiga mai kyau ta al'farma da tsabtar addini.
Ita kuwa Aysha a hankali take kimtsawa sabida ciwon da mararta keyi.
cikin sanyi ta buɗe wodurob ɗinta.
Wani tattausan Boyel mai taushi da sheƙi mai ɗan karen kwai ta zaro, dinkin zani da rigace borno sitayel mai masifar kyau.
Kalarshi Sky blue an watsa mishi aiki da zare Pink color mai sheƙi.
Bayan tasa bra and pant wani tattausan ondawuya dan guntu iya guiwa tasa, kana tasa.
Ɗaura zanin ta dai-dai-ta shi.
Rigar ta zura a jikinta tayi mata cib-cib gwanin burgewa ƙirjinta ya zauna daɓas.
Ninke ɗan kwalin tayi tare, murza asetta ta ɗan karkatashi kaɗan jelan gashinta da bata kitseshi ba, ta barshi kwance a bayanta.
Turare mai masifar ƙamshi ta fesa.
Sannan tasa wani sarka da yan kunne masu kyau.
Gyale pink color ta yafa.
A hankali ta fito falo.
kiciɓis sukayi da Ummi tana cewa.
"Aysha mu tafi ko".
A hankali tace.
"Ummi kuje kawai. Bazan jeba".
Ɗan jim Ummi tayi sai kuma ta juya kawai ta tafi.
Ita kuwa Aysha kitchen ta nufa.
"Special Arish". tace a hankali kana ta.
Ɗebo dankali da sauran kayan da zata buƙata
SPECIAL ARISH
1.dankalin turawa
2.nama, kwai, tumatur
3.kabeji, bama , maggi
4.tafarnuwa ,man gyada.
Da farko dankalinki ta fara ferewa ba tare da daddatsashiba ta wanke saita-ta tafasashi da ruwa da gishiri kadan.
Sai ta kada kwai da albasa d curry da Maggi Tafarnuwa.
Daga nan saita dinga tsoma dankalin tana soyawa.
Sai ta kuma tafasa nama da maggi da gishiri da curry da tafarnuwa da al'basa har yayi laushi saida ruwan ya kusa tsotsewa saita kara wata al'basa da timatur suka nuna saita kwashe.
Ta yanyanka kabeji kanana sannan ta dafa kwai ta yanyan kasa da. Dan girma sannan ta zuba Maggi da bama ta gaura yeshi .
Sai ta samu Foodflaks ta zuba Irish a gefe sannan hadin namanki ta shina ta sashi a wani kulan shi kuma haɗin kabejinki ta sashi a wani kulan shima
Kasan cewar da yawa ta ɗan yi shi.
Tana gamawa taje ta jerashi a kan Dinning area.
Sannan tazo ta kimtsa wurin.
Tuni kuma an idar da salla.
Affan dake kusa da Sheykh ne ya ɗan matso tare da cewa.
"Hamma Jabeer gacan ragon an kawo mutane nata son tafiya gida suna jiran kayi yankan."
Da sauri yajuya tare da cewa.
"To muje".
Bayan yayi yankanne ya juya ya tafi.
Yasan na cikin gidanma duk shi ake jira.
Affan kuwa a gefen wurin ya tsaya saida aka gama fiɗan dogarin dake raba naman ya yanko hantan yasa a leda ya miƙawa Affan.
Daga nan Affan ya juya ya tafi cikin gida shi kuma yayi ta rabawa mutanen wurin naman.
Yayinda duk sauran mutane gari kuwa aketa tafiya.
A can mayankansu na cikin Masarautar Joɗa nan Sheykh ya nufa shida Lamiɗo da sauran manyan masarautar baki ɗayansu.
Daga nan ya fara yanka bayi masu fiɗa suna amsa suna feɗewa ko wanne ana kaishi sashin maishi.
Affan kuwa kai tsaye Side ɗin Sheykh ya nufa.
A falo ya samu Ummi da Aysha,
ledan hantar ya miƙa mata tare da cewa.
"Gashi a gasawa Dr Liman Sheykh Akarmakallu Hamma Jabeer kafin ya dawo.
Yanacan yanata yanka zai dawo a gajiye a yunwace".
Dariya Ummi tayi tare da cewa.
"Gsky kam Aysha amshi ki fara da wuri".
To tace kana ta amshi ledar.
Kitchen ta wuce. Ummi na biye da ita a baya.
Juyo naman tayi a roba, ta wonkeshi Sannan tasa wuƙa ta fara yankashi dogo-dogon yanka sala-sala.
Kara lallaɓesu tayi, kana ta tasashi a wata robar, al'basa ta yanka mai yawa, dai-dai yadda zaji mata, citta kanamfari Curry da maggi da ɗan gishiri ɗan mitsilili ta tarfa a ciki.
Ta gaggaureyasu.
Kana ta juye a tukunya sannan ta ɗauka a kan gas, tasa wutan dai-dai misali.
Ummi kuwa al'basan taketa gyarawa tana yankawa a wata roba. Attaru da basufa takwas ba ta, gyara kana ta jajjaga matasu.
Tuni naman kuwa yana tsilala yanata ƙamshi ya tsastsafo ruwan jikinshi, ya haɗe da kayan ɗan-ɗano dana ƙamshi.
Jajjageggen Attaruhu da al'basan da Ummi ta miƙa mata, ta amsa. Kana ta buɗe tukunyar, ta juyeshi ciki ta ɗan motsa naman.
Haɗin duk ya shiga ciki.
maggi da Curry ta ɗan ƙara.
Sannan ta rufe tukunyar nan take tafa bararraka bul-bul sai wani irin ƙamshi yake fesorwa.
Jamil da ya shigo da bayi uku ko wanne da roban kayan ciki a ciki an wonkesu fes, hanji an kitsesu gwanin kyau.
Shima ajiye robar hannunshi yayi tare da cewa.
"Wannan ƙamshi shine ƙungiyar yunwa."
"Allah ko Jamil". Ummi ta faɗa tana kallonshi.
Shi kuwa, kanshi ya jinjina tare da cewa.
"Sosai ma Ummi, gashi wannan nakune Sheyky Aunty Ayshan, Mamey ke, Jalal ya kwautar da nashi wa abokinshi".
"To yayi kyau, bari mu fara aikin."
Cewar Ummi juyawa yayi ya fita yana cewa.
"Afa ajemin wannan gashi na Sheykh da yake ta zuba ƙamshi".
"Kaɗan ba". Cewar Aysha dariya yayi tare da cewa.
"Kai Aunty Aysha rowa ba kyau fa".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Yoh naji Affan yace Hammanku zai dawo a yunwace".
Dariya yayi ya fita.
Ummi kuwa tukwane ta ɗauka kana ta kalli Saratu da yanzu ta shigo tace.
"Yanka min al'basan da yawa.
Ke kuma Larai zoki riƙe min mu yayyanka tunda a gyare suke".
To sukace kana duk suka fara aiyukan da tasasu.
Aysha kuwa buɗe tukunyar tayi ganin. Yadda yayi kauri romon yayi yadda takeso. Yanata ƙamshi sai ta ɗauko wani kekkeyan ɗan Foodflaks karamin.
Ludeyi tasa ta rinƙa korfe romon tana sashi a kular da zafin shi.
Saida ta korfeshi kab.
Kana ta rufe kular sannan.
Ta matso kusa da tukunyar ta fara, motsa naman wuta yanaci daki-daki tana motsashi tana gaurayashi.
Yana ɗan kame jikinshi yana ɗan zama kamar gashi wuta.
saida taga ya tsane yadda takeso.
Ta kwasheshi da zafinshi tasashi a kula kana tasa wani a ɗan madaidaicin kula mai ɗan karen kyau.
Rufeshi tayi sannan ta raba romon biyu, a ƙananan kulan.
A tray'n ta jera Foodflaks masu ɗan karen kyau ɗin kana tasa plate spoon and fork, sannan ta ajiyesu gefe.
Kana ta ajiye mai yawan shima gefe.
Inda Ummi take ta matso kana ta fara taya wonkewa tana tsaneshi tana zubawa a tukunya.
Tare da turbuɗeshi da al'basan da citta kanamfari Curry da maggi tafarnuwa da a dai sauran kayan ƙamshi dana ɗanɗano, saida suka gama komai cikin ƙanƙanin lokaci kana.
Su Sara suka kullace wuri.
Sannan Ummi tace to suma suje suyi nasu aikin.
Ta basu duk wani kayan haɗin da zasu buƙata duk da tasan ana kaimusu.
Falon suka dawo suka zauna.
Bayan Ummi ta zubo musu hanta gashin tukunyar ta yarfa musu romon a samanshi.
Plate ta miƙa Aysha.
Da sauri ta jujjuya mata kai tare da cewa.
"Bana cin kayan ciki".
Cikin mamaki tace.
"Allah sarki Aysha am na manta, da ban haɗaki da aikinshiba".
Shiru tayi ganin ta rumtse idanunta tare dasa hannunta ta kama mararta.
"Sannu baki da lfy ko?".
Ummi ta tabayeta cikin kulawa.
Kai ta jinjina tare da cewa.
"A a ba komai ai da sauƙin".
Jalal, Jamil, Affan, Imran, Sulaiman, Y Jafar ne suka shigo a jere.
Kai tsaye Dinning area suka wuce.
Da sauri Ummi tabi bayansu tana cewa.
"Sannunku an gama yankan ne?".
Baki Jalal ya tsuke tare da cewa.
"Inafa aka gama gajiya kawai mukayi muka gudo .
ALLAH ko Hamma Jabeer har tausayi ya bani mutun kusan awa biyu a sunkuye, ba hutu, fuskarshi kayanshi duk sun cika da jini".
Jamil ne yace.
"Ummi da Allah zubo mana abin ci".
To tace tare da shiga kitchen ɗin gaseshen naman ta ɗauko musu.
Ta zuzzuba musu kana Special Arish ta saka musu da haɗin naman da kabejin da Aysha tayi musu.
Sannan ta ɗauko Drinks ta jera musu, nan suka faraci.
A hankali Aysha tace.
"Shine kuka gudo kuka barshi shi ɗaya a can ko?".
Murmushi Affan yayi tare da cewa.
"No Madam Jabeer ba gudowa mukayi ba shi yace mu dawo da Ya Jafar".
Sulaiman ne yayi dariya tare da cewa.
"Yo gskyanta taga an bar mata miji shi ɗaya duk mun gudo".
Dariya sukayi duka.
Sha ɗaya da rabi. Dai-dai ya shigo, cikin tarin gajiya.
Da sallama a bakinshi, da sauri ta buɗe idonta dake rumtse dan ciwon da cikinta keyi.
Su Jalal kuwa daketa hira suna cin abinci da korawa da Drinks mai sanyi ne suka juyo suka kalleshi tare da cewa.
"Sannu Hamma Jabeer sai yanzu kanshi ya ɗan jinjina kana ya wuce.
Cikin kula Ummi ke ce mishi sannu.
" Sheykh sannu da aiki Allah ya maimaita mana".
"Amin Amin". yace kana ya wuce.
Ita kuwa da ido ta rakashi.
Ɗan juyowa