Showing 270001 words to 273000 words out of 275307 words

Chapter 91 - GARKUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

24416

da kyar ta iya saita numfashinta cikin karkarwar jiki da rasa abin cewa ta ce, "Wannan wanne irin yabo ne haka har sai ka haɗa da sarautar gidan nan?"
Yanayin ta ya kalla ya yi Murmushi, wanda ya ƙara tunzirata kana a nitse yace.
"Dan na tabbatar miki da ƙimarta da darajarta ne, ina son kuma hakan ya zauna a cikin ƙoƙon ranki har illa masha Allah..."
Cikin takaici tace.
"Wannan kuma ka yi kaɗan ka sani adana shi a raina"
Kallon da yake mata ne ya hana ta ƙarasa zancen, don daga inda take tana iya jiyo sautin hucin da yake, muddin ta ƙara sa maganarta tsab zai iya wanka mata marin da zai sa ta rasa jinta na awanni.
Da hannu ya nuna mata ƙofa alamar ta fice mishi a gida.
Kamar munafuka ta wuce simi-simi tana gunguni.

Juyowa yayi ya nufi cikin, sai kuma ya ɗan juyo ya kalli cikin falon jin alamun akwai mutun a ciki.
Juyowa yayi cikin falo.
Cikin nitsuwa ya kalli Ummi da Shatu.
Da alamun Ummi lallaɓata take taci abinci,
Idonshi ya ɗan lumshe, haka nan yaji wani irin sanyi har cikin ransa yake jin daɗi.

Wani ɗan guntun Murmushi yayi bayan ya kalli fuskar Shatun data ke kwaɓe har da turo baki.
Wayar Ummi ce ta fara suwa juyowa tayi ta ɗan jawo wayar,
tana dubawa taga Umayma cikin farin ciki ta ɗaga, tare da karawa a kunne kana tace.
"Assalamu alaikum, Umaymah Sheykh."
Cikin tarin jin daɗi Umaymah tace
"Wa alaikassalam Ummin Sheykh ina yaran naki? Ya jikin ɗiyar tawa"!".
Murmushi Ummi tayi kana tace.
"Alhamdulillah suna lfy, ɗiyarki jiki da sauƙi gatasu ma kusa dani".
Cikin kula tace.
"Bata wayar".
To Ummi tace kana ta miƙawa Aysha wayar.
Tare da cewa.
"Ga Umaymah".
Amsa Aysha ta yi ciken jin sanyi tace.
"Assalamu alaikum Umayma barka da rana."
Cikin tsananin kulawa Umaymah tace.
"Waalaikumus salam Habibty, sannu Aysha Addana, Allah ya yi miki albarka, Allah ya saka miki da al'khairi, na ji daɗi sosai, in sha Allah al'khairi da haske yanzu zai bayyana, sannu kin ji my dear, ki kula da kanki sosai, ki dinka shiga ruwan dumi akai akai, sannan kada ki yi wasa da kunun nan da Ummi take miki, kin ji ƴata ki yawaita cin gashin naman da zatanayi miki da shan kunun har na tsawon kwana uku kinji ko Aysha."
Wata azababbiyar kunya ne ta rufeta.
A kunyace tasa ɗayan hannunta ta rufe fuska tana jin inama ƙasa ta tsage ta shige cikinta.
Da ƙyar ta iya ce wa,
"To Umayma."
Jin Muryarta ya sa Umayma yin dariya don tasan kunyace irin na ƴaƴan Fulani ne yasa ta yin shiru.
Cikin murya mai baiyana jin daɗin da take ciki tace.
"Yauwa Aysha, Allah ya yi miki al'barka."
Cikin sanyi da jin daɗi tace.
"Amin Umaymah".
Kana daga nan
Suka yi sallama ta kashe.

Sunkuyar da kanta tayi tare da mikawa Ummi waya, don izuwa yanzu kunya ta gama jiƙeta, kallonta Ummi ta yi tana jin dadi aranta tana kuma addu'ar Allah ya nuna musu ranar da ƙwai zai fasha, don ga alamun nan suna ta tabbata.
Shi kuwa Sheykh ajiyan zuciya mai sanyi ya sauke kana ya juya ya nufi falonshi.

Ummi kuwa Kitchen ta wuce da tray'n a hannunta.


Ita kuwa Aysha Anan falon ta zauna tana tunani kala-kala musamman akan masarautar sam ta kasa gane mata.
A kullum da kalar surƙullen da zai bayyanar mata, ko meye ma'anar zantukan da suke yawan yi wanda bata gane masa ba?.
Dazu tajiyo Gimbiya Saudatau da Sheikh maganganunta sun bata mamaki, lallai akwai wani babban al'amari a cikin gidan nan, wanda da sannu zata fahimci menene wannan abu.
Kuma zata tambayi Ummi wani abu ko zata gaya mata, ko ta samu sauƙin Tsarkakkiyar dakw cinnzuciyarta.
Tana nan zaune har aka kira sallar la'asar ta tashi daƙyar don har yanzun bata jin dadin jikinta.
Bedroom ɗin ta ta wuce.
Kai tsaye Bathroom ta nufa.

Al'wala ta ɗauro don har masallacin masarautar sun tada kabbara.

A hankali take taku sabida har yanzu tanajin jikinta na mata zafin rabuwa da budurci.
Sallaya ta shimfiɗa kana itama ta tada kabbara.

Bayan ta idar da sallah ne,
ta kuma miƙewa a hankali ta fito falo, sabida ta gaji da baccin kwanciya tayi bisa kujera da wayarta a hannunta, tana mgna da Junaidu.

Ummi kuwa tana kitchen.

Murmushi ta ɗanyi jin Junaidun na cewa.
"Dan Allah Adda Shatu kicewa su Bappa su dawo haka nan, zamansu a waccar ƙasar ya isa.
Ina kewar Junainah, Rugar Bani gaba ɗaya muna kewarsu dan Allah su dawo".
Gyara konciyarta tayi tare da cewa.
"To Junaidu in sha Allah zan gaya musu, su dawo maka da masoyiyarka dan nima nayi kewar Junnu ina kewar Ummey na".


Ummu dake kitchin ne ta ɗan tsagaita daga motsa naman da take fasawa Aysha
Sabida jiyo sallamar Hajiya Mama da Aunty Zuwairiyya.
Haka yasa ta fito tai musu barka da zuwa kana suka gaisa tare.
Sannan tace su isa Aysha na ciki.

To Juwairiyya tace kana tai gaba Hajia Mama na biye da ita a baya.

Ita kuma Ummi ta koma Kitchen dan kawo musu ruwa.

Ba a jima ba sosai Ummi ta debo drinks ta fito da nufin kai musu.
Sai kuma sukayi kiciɓis a bakin ƙofar falon Ayshan. Sun fito falon Shatu fuskarsu a murtuke, da alamun ransu a ɓace, suka wuce ta.
A hankali ta bisu da ido, tare da tambayarsu.
"Har kun fito ko ruwa baku shaba".
Dukansu babu wacce ta kulata suka fice.
Ajiyan zuciya ta ja ciki da mamaki, sai kuma ta juya ta nufi falon Ayshan.
Tana gab da shiga falon ta ji sautin muryar Aysha na faɗa da ɗan ɗaga murya take cewa. "Mitssssss munafukan banza masu fuska biyu mugaye masu baƙaƙen zuciya. In sha Allah sai Allah ya toni asirinku!".
Da sauri Ummi ta ƙaraso gareta tare da ajiye tray'n hannnunta bisa stoll cikin kula tace.
"Lafiya dai Shatu Meya faru?".
Girgiza kai Shatun ta yi cikin jin haushi ta ce
"Ummi nace bana son su, bana son ganin sun shiga rayuwata, bana son su rinƙa zuwa inda nake saboda na tsani mu'amala da mai fuska biyu."
Ajiyar zuciya Ummi ta yi tana jujjuya zancen Shatun, da kuma tsananin mamakin takun sakar dake tsakanin Aysha da Hajiya Mama.
Numfashin ta ɗan fesar tare da dafa kafaɗarta kana a hankali tace.
"Shike nan ki yi hakuri yanzu ai sun fita."
Ƙwafa Aysha ta yi tare da kishingiɗa sosai tana mamakin yanda mutanen gidan suka kasa fahimtar komai tana matuƙar mmkin in ance wai Hajia Mama itace Mamansu Sheykh kuma ita har yau bata yardaba bata kuma jin zata yarda har gaban abadan.


Bayan ta idar da sallar isha har yanzun jikinta ba kwari haka tana jin ciwo a gabanta musamman in ta miƙe tana tattakawa, miƙewa ta yi a ciccije, "Wash Allah na!".
Ta faɗa haɗe da miƙewar ta fara tafiya tana gwale-gwale kamar ƴar kaciya, kallonta Ummi ta yi tana nazarinta, bayan ta shige ɗaki ta tashi ta bita ɗakin.

A tsaye ta sameta gaban drower'nta.
Juyowa tayi ta kalli Ummin dake matsowa kusa da ita tare da cewa.
"Aysha kin sake shiga ruwan ɗumi kuwa?".
Kai ta jujjuya mata a hankali tace.
"Ɗazu da yamma dai na shiga".
Kai Ummi ta jinjina kana tace.
"Yauwa to kije yanzuma ki shiga ruwan ɗumi zakiji sauƙin abin sosai."
Ya mutsa fuska ta yi irin na mai jin ba daɗi kana cikin sanyi tsce.
"Ummi bana jin daɗi kwata-kwata."
Kusa da ita ta matso cikkn kula tace.
"Na sani, amma shiga ruwan ɗumin zai tai maka kwarai wajen jin daɗinki, don zaki sake sosai, duk wannan ciwo-ciwon zaki daina ji." Kwafe fuska ta yi kamar zata yi kuka.
Yanayinta Ummi ta kalla, ta so yin dariya sai dai kuma danne tare da cewa.
"Yi haƙuri kin ji Ayshs, daure kada ki zama raguwa mana."
"Uhmm".
kawai tace ta miƙe ta shige cikin bathroom.

Ita kuma Ummi ta wuce kitchen tare da ɗauko haɗaɗɗen kunun gero wanda ake yinsa na musamman kuma shi ake bawa amaren masarautar haɗe da farfesun farararen tattabaru, wanda shi ma wani haɗi ne na sirri mai tsuma mace, da yajin da ake barbaɗawa akan tattabarun wanda yake ƙarawa mace wani ɗanɗano na musamman.

Ita kuwa Aysha ta daɗe cikin ruwan ɗumin tana jin wani irin daɗi na ratsa ta, lumshe ido ta yi, tare da miƙewa tayi wanko fes kana ta fito.

Tana buɗe toilet ɗin ta ji ɗakin na ƙamshin wannan gashin tattabarun da Ummi ta kawo mata su har ɗaki.
A hankali ta matso gefen Ummi dake cewa.
"Yauwa kin fito ko Aysha?".
Kai ta gyaɗa mata tare da cewa.
"Eh Ummi".

"To yanzu ya kikaji jikin naki?".
Ummi ta kuma tambayarta.
A kunyace tace.
"Alhamdulillah naji sauƙin".
Cikin gamsuwa Ummi tace.
"Toh zo ki zauna ga wannan kici duk za su ƙara miki ƙwarin jiki." Girgiza kai tayi alamar bazata ciba.

"Yi haƙuri ki daure kici." Ummi ta daɗi mata cikin lallami.
Zama Ummi tayi tare da janyo flask ɗin ta zuba mata mai ɗan yawa.
Kana ta turo mata plate ɗin gabanta, kunu ta tsiyaya mata a cup mai ɗan girma ta miƙa mata tare da cewa.
"Yauwa maza kici zakiji daɗin jikinki".
A hankali ta gyaɗa mata kai, dan bacci ya fara kashe mata jiki.
Cikin lumshe ido ta fara sawa a bakinta.
Jin wani irin ɗanɗano mai daɗi ya ziyarce harshenta ne yasata, lumshe ido tare da haɗiye tsinkekken yawun bakinta ta cigaba da taunawa tana haɗiyewa tare da korawa da kunun geron.

Ummi kuwa tana ganin ta faraci ne ta wuce ta fita.

Bayan ta gama ta shanye kunun don shi ma ya yi mata daɗi sosai.

Cike da bacci ta ɗaura plate ɗin kan kofin ta turasu gefe kana a kasalance.
Ta wonke hannunta.
hamma mai sanyi tayi kana ta kwanta nan bacci ya yayi awon gaba da ita.

Shi kuwa Sheikh yana dawowa daga sallar isha ɓangarensa ya wuce kai tsaye.
Yana shiga bedroom ɗin sa ya zare al,kyabbarsa tare ta ajiye hirami gefen gadonsa ya zauna, yana ajiyar zuciya tare da lumshe idonsa.
Wayarsa ce ta yi suwa,
Ido ya zubawa wayar yana kallon mai kiran, kamar ba zai ɗaga ba,
Sai kuma dai ya janyota hade da murza screen ɗin wayar.
Da sallama ya amsa. Cikin zolaya Haroon ya ce.
"Barka da dare angon Shatu."
Wani ɗan guntun Murmushi Sheikh ya yi, haka nan yaji sunan yamishi raɗau yayi masa a kunne a zahiri kuwa ɗan gajeren tsaki yaja tare da cewa.
"Bana son surutu fa." Cikin Murmushi shi ma Haroon yace.
"Kasan dai ba ƙarya na yi ba, balle ka fara yi min wa'azi."
Gyada kansa yayi tare da cewa.
"To ina jinka menene zaka kirani da daren nan?".
Murmushi nan Haroon ya cigaba da tsokanarshi har ya gaji ya katse kiran.

Dai-dai lokacin kuma ya ya fara jin yunwa haɗe da zazzabi mai zafin gaske wanda ya jisa atake.
A hankali ya miƙe yana jin zazzaɓin tamkar wanda ake ƙarawa tun daga kan yatsansa har zuwa saman kansa, cikin tafiya a hankali ya fito daga bedroom ɗin zazzaɓin na cigaba da fisgarsa da ƙyar ya kai tsaƙiyar falon ya zauna kan kujerun dake falon, a hankali ya kwantar da kansa jikin kujerar yana furzar da numfashi mai zafi, lumshe ido ya yi, saboda ƙugin yunwa da cikinsa ke yi, zaman da ya yi, so yake ya ji dama-dama ya ci abincin ya kwanta, tun yana iya jujjuya jikinsa har ya gagara yin hakan saboda ilahirin gaɓoɓinsa sun amsa da zazzafan zazzaɓin ji yakeyi gaba ɗaya gabban jikinsa kamar allurai ake sokawa mushi, yana nan kwance har wajen ƙarfe ɗaya na dare jikinsa na karkarwa.
Cikin rawan sanyi daƙyar ya lallaɓa ya samu ya shiga bedroom ya kwanta a kan gadon a gicciye, hannunsa na rawar ɗari ya janyo blanket ya rufe dukkan jikinsa, shi kansa yana jiyo hucin numfashinsa da zafi, yana yi yana ɗan nishin azaba ƙadan,
a haka ya samu yayi baccin wahala mai cike da rikitaccen mafarki mara kan gado.

Kiran sallan farko ne ya tashe shi, cikin yanayi wanda bai saba tsintar kansa ciki ba ya miƙe, kasala-kasala gajiya-gajiya, ga mamakinsa zazzaɓin ya sauka, don yana ga ɗumin da jikinsa ya fitar da gumi alamun sauƙan zazzaɓi duk da akwai sanyi ac, addu'a ya yi ya miƙe a hankali ya shige toilet sai da yayi wonka da ruwa mai sanyi sannan yaji jikinsa ya yi masa daɗi.
Da sauri ya fito ya fara shirin zuwa masallacin masarautar don har sun fara kiran assalatu.

Bayan sun idar da sallan acan ya yi zamansa don gabatar da azkar da sauran addu'o'in da yake gabatarwa a dai-dai lokacin, sai da gari ya yi washe sannan ya dawo ya wuce falonsa kai tsaye.

Da hantsi ya fito daga falon. Cikin shigarsa ta yau da kullum.
A nan ya taradda su ita da Ummi suna zaune.
Da alamun Ummi nata lallashinta akan ta yi breakfast ne.

Tsayuwa ya ɗan yi gefensu tare da cewa.
"Ummi yunwa".
murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Dama yanzu nakeso Aysha taci, sai ta kai maka nakan."

A hankali ya ɗan yi taku biyu zuwa uku, ya kana ya zauna bisa kujerar dake fuskantar tasu.
Ido ya ɗan zuba mata, tare da jingina kansa jikin kujera.
Cike da wani irin mayataccen shauƙi.

Ita kuwa Aysha yatsun sawunshi ta zubawa ido, tare da shaƙan ƙamshin turaren jikinshi dan tun da ya shigo daddaɗan ƙamshin turarensa ya cika wajen har sai da Aysha ta lumshe ido, Allah ma ya sani tana masifar son ƙamshin turarensa.

Idonshi ya ɗan buɗe tare da ƙanƙancesu kana ya tsira mata su yana kallonta, a nutse sai kuma yayi wani gajeren.
Murmushi cikin nutsuwa da jera kalami yace.
"Me zai sa ace ba za a ci abincin safe ba? bayan kuma shi ya fi kowanne amfani a jikin ɗan adam?".
Kallon shi ta yi tare da kwaɓe fuska kana ta ɗan tura bakinta tare da fara magana ƙasa-ƙasa can cikin maƙoshinta.
"Dama ba dole kace haka ba, tunda kai ne sanadiyyar ciwon, kuma ba ajikinka yake ba." Ummi dake gefenta ta jita sarai duk da ba kalmomin duka ta ji ba amma tasan abinda take nufi.

Shi kuwa Sheykh Jabeer lumshe ido ya kumayi tare da sauke sassayan numfashi kana ya buɗe idon ya zubasu kan bakinta.
Kallon bakinta yayi ba tare da ta gama haɗe lips ɗintaba yace.
"Kika ce kin yi yajin cin abinci?".
Ya faɗa da zolaya duk da ba halinsa ba ne, ba kuma ɗabi'arsa bane.
Shima kanshi bai san ya aka yi zuciyarsa ta raya masa faɗin hakanba.
Lips ɗinsa ya ɗan laso da harshensa lokacin da yaji tana cewa.
"Uhmm ni ba haka na ce ba."
Gyara zamansa ya yi yana mata wani irin kallo mai cike da fassara, kallon nasa ne ya sa mata mutuwar jiki da kasala, don sai da ta ji wani iri a jikinta sabida wani irin kallone mai tsada da masifar ratsa jiki da zuciya.
Shi kuwa cikin tsareta da idon yace.
"Uhumm to muna jinki Aaaaishhh!".
Kiran sunanta da yayi da wata siga haka ya sa ta ɗago kai ta zuba mishi ido.
Sai kuma ta kauda kanta da sauri tare da sauƙe numfashi,
kwarjininsa ne ya cika mata ido sai wani Murmushi mai tsada da yake mata.
Cikin narkekkiyar murya tace.
"Cewa na yi na ƙoshi."
Ta ƙarashe mgnar tana kauda kai aranta tana jinjina kwarjini da haiba irin ta shi.

"Yarinyar goye a ke yiwa dole ta ci abinci fa, ko kema sai Ummin ta goyaki zaki ci? Tunda naga nima mancewa sani takeyi sai ke".
Dariya Ummi tayi tace. "Idan zata ci sai na goyata".
Cikin jin kunya ta sunkuyar da kai ƙasa tana nanata zancensa wai agoyata.
"Yi haƙuri ki ci abincin kin ji." ta kuma jin muryarsa a bazata.

Janyo flask ɗin yayi gabanta,
flask ɗin ta ɗan kalla tana jujjuya kwayar idanunta, cikin ranta take jin kwarjininsa ke yi mata barazana da ta ji shakkarsa, ban da haka ba zata iya shan da ruwan zafi acikinta ba sabida ɗazu da sassafe Ummi ta sata cin sauran naman ji data ɗumama mata.
Sama-sama a haka ta ci abincin da ɗan yawa duk da bata so cinsa ba.

Tana gamawa Ummi ta kwashe kayan kwanukan, shi kuma Sheikh ya wuce falonsa.

Yana shiga Jamil ya shigo, shi da Juwairiyya, zama suka yi suna hira Ummi ce ta ɗan kalli gefen da Aysha ke zaune tare da cewa.
"Yauwa Aysha tashi ki kaiwa Sheykh abincinsa".
Cikin sanyi tace.
"Ayyah Ummi bawa Jamil ya kai mishi".
Sai kuma ta kalli Jamil tare da cewa.
"Jamil ɗauki ka kai mishi".
Ta ƙare mgnar tana ɓoye ainihin tsoron sake shiga inda yake da takejin.
Murmushi Ummi tayi dan ta ganota, tray'n ta miƙawa Jamil dake cewa.
"Ummi kawo dai in kai dan ke".
Murmushi sukayi, kana shi kuma ya kai mishi sannan ya fiti.
ba su daɗe ba Yah Ja'afar ya shigo shi ma ya zauna kusa da Jamil nan suka ɗan ci gaba da hirarsu

Haka dai sukayi wunin wannan.
Ranar cikin farin ciki suka yini don anan falon suka ci abinci dukansu.


Da daddare ba yanda Ummi ba ta yi da Shatu ba akan ta kaiwa Sheikh abinci ta ƙi, sai da kanta ta kai masa.
Don Aysha tsoron zuwa ɓangarensa take, saboda har yanzun tana jin jiki.

Washegari ma da safe Ummin ce ta bawa Jamil ya kai masa, don fir Aysha ta ƙi zuwa.

Bayan yayi wanka ya fito, ya shafa mai ya kimtsa cikin wani tattausan yafi boyel mai taushi da kyau, Sky blue ne sai aikin da akayi mishi da farin zare sosai yayi kyau sai ƙamshi yake zubawa.

A haka ya fito falonshi
breakfast ɗinsa Wanda yana kimtsawa ya jiyo muryar Jamil ɗin na ce masa ga breakfast ɗinka Hamma Jabeer.

Zama yayi bisa kujera, yana mai mgnar zuci. "Rabon Aiiish da side ɗinna tun shekaran da safe yau kwana biyu kenan ana na uku rabon data shigo nan". Murmushi mai yelwa yayi wanda bai san dalilinsa ba.
"Uwar raki da tsoro".
Ya faɗi a fili lokacin da ya fito babban falon ba kowa a falon haka yasa ya wuce yana girgiza kai ya wuce dan sauri yake Asibitinshi zaije.


Bayan ya shiga asibitin ɗaki ɗaki ya bi duk marasa lafiyan ciki suna gaisawa tare da basu taimako na musamman yana duba lfyarsu wanda dama hakan al'adarsa ce kyautawa marasa lafiya, bayan ya gama da shiga ɗakunan suna binsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login