Showing 159001 words to 162000 words out of 197468 words

Chapter 54 - ALKAWARIN MASOYA COMPLETE

13 Jul 2025

7797

ya baiwa uzaifa 200k tunda Sunsan Inda kudin ya fito lokacin da ya tura musu basuki amsa ba account ya Kai Nnenna ta bude ya zuba Mata kudin da shayibu ya basa nata kana ya Kara Mata 100k a ciki,Lahab a sannu sannu ya Fara Zama sannan ne a fagen kwallon kafa don sosai ya iya buga wasa hakan yaja Masa farin jini da daukaka har yasa wasu team Fara daukar sa haya Yana buga musu Wasa ba tare da sun damu da kankantar sa ba kudi kuwa sosai ya Soma damkarsu sosai Kuma Alhamdulilah Lahab mutum ne da baida gyashi kome ya samu sai ya tsamma Rahab dake India da uzaifa haka zalika zaisa wa Nnenna a account nata duk da Bata cin Koh sisi haka zalika Adewale don yanzun tuni Suka bar gidan da suke lahab ya Kama musu gida Mai zafi wadacece Suka koma ciki don wani sa'in sai afi wata Ade Bai hadu da Nnenna ba waje d'aya sai in ya shigo part nasu Lahab ga moto Lahab ya saya ya saima Ade duka rayuwa tayi Dadi bana Wasa ba tuni papan Ade yayi sanyi lokacin da ya kawowa Ade ziyara yaga yanda Allah ya daukaka Lahab Kuma Yana taimakon dansa har dawainiyar makarantan Ade yanzun Lahab keyi,Amma tuni ya manta da zancen wani Nabeel don tunda yazo kasan Bai taba kiransa ba saidai in Suna waya da Ade in Yana gun shine inya tambaye shi sai Ade yace gashinan su gaisa.





Lahab sun koma makaranta tuni har semester yayi nisa yaso yasa Nnenna a makaranta Amma babu Hali tunda Bata da shaid'an takardun Gama secondary,ga rigimar da take fama da ita nata na masifa ga yawan ciye ciyen kayan fruit don yanzun tabar apply ta koma kankana da mangoro Koh Kuma abarba.




Lokacin da labarin Lahab ya Fara zaga katsa tuni Yan nageria Suka Soma Jin labarin sa wani Dan naija best footballer Kuma very young a turai gashi da farin jini bana Wasa ba duk channel na sport ba'a rasa nasa a ciki,lokacin da labari ya Fara riskan Mami tunda ba kallon kwallon take ba sai Yan uwa ke kiranta Suna cewa sunga Lahab na ball a TV koransa tayi tana Masa fada akan an turasa karatu yaje ya Kama abinda bazai amfane saba Bata yarda ba,Aiko waya yayiwa Abbu ya sanar dashi dare da Masa Alkawarin insha Allah zai kammala karatunshi tare da sakamako Mai kyau daker dai Abbu ya sauko ya baiwa Mami hakuri ya cigaba da Wasa tunda sunga kokarin da yayi a karatu.






tun safe Lahab ya fita Bai dawo ba saboda Wasa da suke bugawa Mai zafin gaske bashi ya dawo gida ba sai kusan 2 na dare,shigowa falon yayi ba tare da ya kunna wutan ba ya wuce sait nasu bude dakin su yayi ya shiga da sallama,dan waro Ido yayi ganin wutar dakin a kunne ga Kuma Nnenna kwance a bargo"Kai amma yarinyar Nan bakiji taya Zaki kwanta da wuta a kunne"kashe wutan yayi ya zaro tafkeken wayarsa dake bag dake bayansa ya kunna hasken waya aje bag in yayi yadau towel ya nufi toilet wanka yayi kana ya fito,daure da towel in kayan bacci yasa ya fita a dakin kitchen ya wuce ya tare coffee nasa Mai zafi ya zauna a dinning dake cikin kitchen in ya Soma Sha Saida yasha Rabin cup kafun ya mike.




d'akin ya shiga tare da matsowa kusa da gadon hannun sa yasa ya warware blanket Inda ta lulluba zai kwanta da Sauri ya sake blanket in, saboda turirin da yaji ya fito daga cikinsa har yanajin wucin numfashinta Mai zafi Ashe idanunta biyu sai rawan d'ari take hannu yasa ya tabata da Sauri yaja baya zafi jikinta jaujau"subhanallah Labiba tun ba yauba nasan baki da lafiya amma rashin jin da Kika kakkabawa kanki yanzun ya hanaki Bari muje hospital"?kasa amsa Masa tayi bakinta ya bushe sosai hakoranta har haduwa suke da juna,mikewa yayi da sauri ya nufi wardrobe nata budewa yyi ya dauko Mata wando da riga amma irin bujennan masu Fadi yasa Mata hijab ya dauko cikin Wa'inda ya sai Mata duk da ba amfani yake dasu ba Kuma hijab in irin have Sunnah ne.






A daren nan Lahab ya dauketa sai Wani hospital Mai tsada, a cikin daren Nan aka amsheta zuwa lokacin zazzabine yaci karfinta sosai ruwa Suka daura Mata tuni tayi bacci sai gwaje gwaje da aka mata,a asibitin Lahab ya kwana tare da ita tana farkawa da safe ta Fara Neman abinci Kuma ta tashi garau abinta,fita yayi ya sai Mata abinda zataci taci kana aka sake daura Mata ruwa.




8:21pm zaune Lahab yake a Kan kujeran dake dakin dayake kowani mutum d'aya dakinsa ne guda ba'a had'a wani da wani zaune take ta tasa kaza a gaba tana ci hannun ta d'auke da ruwa a makale, don Koh barin a cire batayi ba ta Soma ci shi Kuma Lahab ya Barta Bai Kira nurse ba gudun kada ace ya kawo cinnedu amusu dariya,wayarsa ne yayi Kara zarowa yayi yayi picking up"Lau Ade Labiba ce babu lafiya Muna hospital amma karka damu fa jikin da Sauki sosai"yayi shuru Yana sauraran abinda Ade ke cewa sai Kuma yace"no ka tafi school kawai yauma sukace zasu sallame mu basai kazo ba sai Kuma ya katse wayar"Kara kallonta yayi ganin tana tauna kashin kaza"Amma wallahi kin chanja haba Dan Allah kece ci Kamar me Amma Baki karuwa sai ma rama da kikeyi sai haske amma dai ba kome hips da breast sun ciki"?





Kala batace Masa ba dan yanzun Sam babu irin kunyan da a tsakanin su bare taji kunyar sa Koh kunyar abinda yace"amma dai da ace bakicin nama har yanzun da anyi babu ke tsabar dadi har kashin cinya kike tumurmusawa,dan Allah kici Naman dake gefen plate in kibar kasusuwan Nan in Naman ya Kare Zan sayo Miki wani amma ace mutun ya aje nama ya kamacin kashi salon wani ya shigo muji kuny..................bai karasa ba aka bude kofar dakin da Sauri Nnenna ta sake kashin hade da boye plate in gudun Kar aga taunannun kasusuwan data aje a ciki.




Dariya kawai Dr tayi ta karaso cikin dakin,hade da turo kujera d'aya ta zauna kusa da Lahab kana ta kalli Nnenna ta kalli Lahab tace"Kamar u look familiar"dan murmushi yayi yace"Hassan Lahab the footballer"?oh oh really great footballer nice to meet,am Dr jeme John by name"hannu lahab ya Bata sukayi musabaha, don tsohowace ba yarinya ba,had'a fuska Nnenna tayi amma batace kome ba kallon ta again Dr tayi tace"gaskiya ya Kamata ki fito da abinki kici gaba daci,ba kunya ta dauko plate nata taci gaba dacin Naman Amma Bata tauna Kashi, kana tacewa Lahab wacec ita Nnenna a wajen sa"?





dan shuru yayi sai Kuma ya cije yace matarsa ce, waro Ido baturiyar tayi ya nuna Nnenna yace matar ka?gyada Mata Kai yayi, shuru tayi don ita duk zatonta Koh yar'uwa Koh friend ne Koh girlfriend,tunda taga irin kyau da Nnenna kedashi gashi zaman turai ya karbeta sosai tayi fresh da ita sai Kuma ta d'aga kafada kana tace,ok anyway congratulations ur wife is pregnant.



Ji kake karaaararam plate na nama ya Fadi a hannun Nnenna saiga hawaye Shar mikewa tsaye Lahab yayi da karfi yace"what?...........................






.






*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*




Cike da damuwa ya Kara Kiran Adewale amma sai ya danna Masa user busy,baiyi zuciya ba ya tura Masa message dan Allah ya d'auki wayar sa daker dai ya samu Adewale ya dau wayar sannan ya amince zaije ya dubo Nnenna amma daga wannan kada ya sake sakasa a shirgen Nnenna babu ruwan sa,katse wayar Lahab yayi Yana hamdala sannan ya koma cikin dakin har lokacin Rahab na zaune yana jiran sa,yana fitowa ya Mika Masa hannu wayan nasa ya basa sannan ya maida ruwan jikin sa ya kwanta.



da daddare Koh abinci Lahab ya kasa ci sai tsumayen Kiran Adewale yake amma shuru sai kusan 8 na dare Adewale ya Kira Rahab Rahab ya kawo Masa wayar amsa yayi da Sauri ya tashi Kamar d'azun ya shiga ban dakin Kara wayar yayi a kunne ya Soma mita sai yanzun Adewale zai kirasa tun d'azun Yana zaune Yana tsumayen Kiran nasa amma shuru"?yanzun zaka tsaya na fada maka abinda na ganone Koh zaka tsaya min mita na kashe wayata"?da Sauri Lahab yace toh kayi hakuri fadamin inji meya faru"?




Ajiyar zuciya Ade yayi yace ka duba WhatsApp na tura maka hoton ta kaga halinda naje na sameta a ciki zuciyar Lahab Saida ta buga cikin tsoro yace meya sametan,baidai basa amsa ba kawai ya katse wayar,jikinsa har rawa yake ya bude data ya shiga WhatsApp zubewa yayi a kasa ya zauna tabas saban shock Nnenna ya gani kwance Kamar gawa Ido a rufe jikinta gabaki d'aya ya sauya daga fari zuwa yellow sosai ga bakinta yayi jajer dashi rabin fuskarta har wajen wuyanta jijjiyoyine bakekkerin Suka fito rudu-rude jikinsa ne ya cigaba da rawa ya fita da Sauri wayar Ade ya Kira Yana d'auka ya Soma Masa magana"Adewale mutuwa tayi ne meya sameta"kaga Lahab karka sa kanka a matsala nidai goggoji tacemin yau kwana biyu kenan da Fara ciwon Nan nata sun tsorata ainun don numfashin tane kawai zai tabbatar maka tana da rai"innalilahi wa'inna'ilahu raji'un kawai Lahab yace ya katse wayar da gudu ya fito daga ban dakin wardrobe ya bude ya fito da kayansa sakawa yayi ya zaro takalmi zai sa yaga Rahab ya shigo da mamaki yace"Lahab sai Ina zaka a haka Kuma"?




"da Sauri Lahab yace fita zanyi"fita fa kace wani irin fita kake nufi Koh ka manta ne baka da daman fita a gidan Nan yanzun"da Sauri shima Lahab yace Ina da Kai Koh ka manta ne dan Allah Rahab kaje ka kwanta a matsayi na Ni Kuma na fita a madaden ka ka taimaka min wallahi akwai babban matsala"wani kallon tuhuma Rahab ya Masa sannan yace wani irin matsala kenan?



Nidai ka taimaka min kin taimaka Masa Rahab yayi daker ya samu ya shawo kansa kafun ya amince kwanciya yayi akan katifar Lahab yayin da Lahab Kuma yasa Kai yabar dakin Yana zuwa compound na gidan nasu security Suka tashi shiga mota yayi Suma Suka shiga aka jasu suka Soma tafiya gidan ya jafar Lahab yace a kaisa Suna Isa yace su tsaya a kofar gidan basai sun Shiga ba bude kofar yayi ya shiga gidan da Sauri ya nufi falo gashi yammane Kuma goshin mangari ba falon ya bude da sauri ya Shiga babu kowa sashen su Majid ya nufa Yana bude kofar yaga babu kowa Kamar falo sai kida dake tashi a dakin Majid bude dakin yayi da Sauri Majid ya juyo ya kallesa sai Kuma ya juya yaci gaba da rawansa.



Xama Lahab yayi a hankali yasa hannu ya kashe mp in a kufule Majid yace"kaga Rahab banson surutu tashi kabar min daki da Allah"Majid Lahab ne"zaro Ido majid yayi yace kana nufin kaida aka sawa Mari Kaine ka fito"?nidai ba wannan ba taimakona zakayi security na kofar gida so nake ka taimaka nabar gidan Nan ba tare da sun sani ba"kallon sa Majid yayi da mamaki yace"so kake nayi fiffige da Kai mu tashi ta samane Koh yaya Ni ta Ina Zan iya fiddakai"?




"Shuru Lahab yayi sai Kuma yace back door ka taimaka min"d'an dakata Lahab nifa karkazo ka sani a matsala munddin aka nemeka aka rasa Ni za'a zarga karka kiramin ruwa babu ruwana wallahi"dan Allah Majid ka taimaka min Dan Allah nace fa"dan shuru yayi sai Kuma yace Ina zuwa fita yayi a dakin Bai Jima ba sai gashi ya dawo da key yana cewa Lahab ya bari a Shiga sallan mangariba.




Ana shiga sallan mangariba backdoor Lahab ya nufa da Majid bude Masa yayi ya fita harda waya Lahab ya karba a wajen sa Yana barin layin Adewale ya Kira akan ya fito gida Yana bayan GRA,Bai wani Jima ba saiga Adewale daga Nan gidan su goggoji Suka nufa da yake darene babu Wanda ya gane Lahab Shiga gidan sukayi har dakin da Nnenna ke kwance abin tausayi gabaki d'aya kammanin ta sun sauya ta chanja hannu Lahab yasa ya bude kwayar idanunta Saida ya koma baya da Sauri saboda yanda jini ya taru a idanun tim goggoji ya tambaya garin Yaya ta Soma ciwon"wallahi Lahab kwana uku batacin abinci a kwana na hudun ne na matsa Mata akan saita d'anci abinda na kawo daga gidan ku daga saka abinci a Baki Koh hadeyewa bata gama yiba Naga ta damke makogoronta tana amai harda jini a ciki shikenan ta yanke jiki ta Fadi Ido ya rufu har yanzun bata budewa kwana biyu kenan.


Mikewa yayi da Sauri ya nufi kofar gidan Keke napep ya tare sannan ya dawo gidan da Sauri ya ciccibi Nnenna da jikinta ya bushe ta sandare,da Sauri Ade dasu goggo Suka Soma tambayar sa lafiya Ina zaije da ita gudun kada a ganeta a Kamata,kala baice ba yayi kofar gidan da Sauri Ade da goggoji Suka Shiga keken Suma aka bar faruq a kofar gida a tsaye,wani private hospital na kudi Lahab ya kwatantawa Mai keken directly Suka karasawa asibitin ya d'auketa sai ciki ganin halinda take ciki yasa likitoti rufuwa a kanta.




da misalin karfe 12:30am na dare Lahab da goggoji ne a asibitin don Ade tun 9 na dare papa ya kirasa yanata masifa akan ya dawo gida,likitane ya Kira su vayan sun shiga office nasa ya Soma musu tambaya Koh akwai abinda ke damun tane daya shafi iska-iska girgiza Kai goggoji tayi shidai Lahab shuru kawai yayi Yana Jin abinda Dr ke cewa Wai Basu gane Kan cutar ba sun saka Mata ruwa ma ruwan baya gudu haka Allurar ma sun saka amma ruwan yaki shiga a jikinta,su d'auketa kawai jinyan Nan bana asibiti bane,mikewa Lahab yayi da gudu yayi dakin da aka kwantar da ita Yana zuwa kuka kawai ya fashe dashi ya zauna a bakin gadon hade da kamo hannun ta Yana hawaye.



Goggoji ce ta turo kofar ta shigo ta zauna akan kujeran tana kallon Lahab sai Kuma tace"Lahab yarinyar Nan ta Fara bani tsoro gaskiya mezai Hana ta koma wajen danginta kaga halinda take ciki fa"hawaye ya share sanann yace"gaskiya goggoji bazan iya barinta a halinda take ciki ba gaskiya tunda yace abar musu hospital nasu da safe sai mu kaita wani"?



Kaga Lahab Kai suspect ne haka ma ita nasan dai ba kowa bane zai gane Nnenna tunda ita gabaki d'aya jijiyoyin fuskarta sun sauya Mata kamanni bai Kamata ana ganinka haka barkatai ha bugu da Kari Kuma halinda yarinyar Nan take ciki bana asibiti bane gobe in Allah ya kaimu sai muje nida faruqu kauyen mu akwai wani babban malami acan gaba da kauyen, insha Allah koma menene zai kawo karshen sa,d'an shuru Lahab yayi sannan yace"muje dai tare goggoji shi faruq ya zauna a gida bai Kamata na bar Miki d'awainiya haka ke kad'ai ba"




amma Lahab baka gani akwai damuwa na barin gari yanda tsaro yayi yawa a kankan Nan"?karkiji kome goggoji Allah ya kaimu goben"ameen ta amsa,washe gari tun asuba Lahab Suka bar cikin gombe Kuma cikin hukuncin ubangiji Basu samu wani matsala a tafiyar tasu ba,haka zalika baibi takan Kiran da Majid keta danna Masa ba sosai suke ta shiga cikin kauyuka wasu kauyukan ma da machine suka shigesa kafun su Isa kauyen da zasu Saida Suka hau kuran shanu kafun Suka iso wani rugan Fulani.



Zaune suke a gaban wani dattijo ne babba sosai tsohone ga farin gemun shi,Lahab da goggoji ne a gabansa a cikin bukkan sai Nnenna da aka shimfidar akan wani taburman kaba,magana ya Fara a hankali cikin nutsuwa yace"Alhamdulilah Ramatu naji dadi matuka da yanda Kika taimake wannan baiwar Allah Nan ba tare da kinsan wacece ita ba haka zalika Kai Lahab kayi matukar kokari Allah ya saka maka sannan ya kalli goggoji yanzun Ramatu inaso ki sanar dani menene ya faru da ita Koh Kuma me tayi ta Soma ciwon"a hankali goggoji ta rusuna tace abinci kawai na takura Mata taci"wani irine abincin"?shinkafa ne da Miya"a nutse yace dakwai nama a ciki"?gyada Kai tayi ganin haka yasa Lahab saurin cewa ai batacin nama"da mamaki goggoji tace Koh shiyasa Inna Bata abinci Mai nama sai takici amma Bata taba fadamin ba ranan ma nina matsamata taci bata gama hadewa ba abin ya faru.




Mikewa tsohon yayi ya nufi Kan Nnenna masowa yayi sosai yasa hannu ya bude kofar idanunta"sai Kuma ya girgiza Kai tare da d'auko wani magani ya bude xamxam ya juye a ciki ya zuba magani Addu'a yayi sosai ya tofa sannan ya Kira goggoji taxo ta Kamata ya bude bakinta ya Soma zuba Mata maganin tana Sha wasu na zuba sai kawai sukaga ta zabura ta Mike ta Soma aman jini babu gaggautawa harda guda-guda sai Nishi take amai tayi bana Wasa ba,har lokacin idanunta a rufe komawa tayi ta kwanta shi Kuma ya mike ya d'auko magani ya kwaba da man shanu yace ta shafa Mata aduk Inda jijiyar ya fito,Dole tasa Lahab ya fita waje shida dattijon don jijjiyar daga fuskarta ya gangara har wuyanta har Kan kirjinta na hagu ya sauka har kafarta na hagu,fita sukayi goggoji ta gama shafa mata kafun Suka dawo gaushi aka kawo a kasko ya zuba magani a ciki maganin na turnuke dakin Nnenna ta Mike tana wani irin ihu da surutai da Sauri goggoji ta Fadi kasancewar tana da marabai,ya aike Lahab ya Kira wasu sukazo Suka fita da ita shi Kuma ya cigaba da fama da Nnenna Harya samu ta natsu sannan ta koma ta kwanta Lahab kam na bare a waje duk abin duniya ya damesa ya kasa nutsuwa yasan war haka ana neman sa.





***************
Bayan sati d'aya Alhamdulilah jikin Nnenna yayi sauki sosai amma har yau Bata dawo hayyacinta ba gashi idanun nata yadan washe daga jini-jinin zuwa fari tass amma Bata tashi ba jinya dai ake Mata sosai goggoji ta koma cikin gombe tabar Lahab a kauyen su,duk sati faruq na zuwa ya dubasa sannn Yana kawo Masa labarin irin Neman sa da ake Kamar me,dayake garin babu Network

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login