Showing 183001 words to 186000 words out of 197468 words
shekarun nan..........................................
*Naga complain na mutane akan mutuwar Rahab Amma fa kuyi hakuri littafina na riga na tsarasa akan hakan ne,Kuma Inna bite na cire wannan bar wannan daga baya Zan rikice ne kawai in ban mantaba shekaran jiya nayita samun magana akan character in Lahab wasu sunce zasu bar karantawa saboda Babu Wanda Lahab yakejin tsoro kaza kaza kana jiya ance kunci zaima Lahab yawa* 🤧🤧🤧 *
*Kunga ai Inna sake nawa na Kama naku karshe nazo na makale a hanya Ina zare ido Daman shi rayuwa ba kome akeso ake samu ba Daman haka rayuwa take aka rasa uwa ma Kuma mutum ya hakura*
*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*
Wani irin murmushi Lahab ya sake yana gyada Kai ganin Wanda ya Jima yanason gani ya bayyana a bayan Ade wato abokinsa Barrister khamal najib,tsawa alkali ya buga da guduman sa don da yawa sun mike tsaye cikin su harda ummu da Addayiya,natsuwa kotun ta danyi kad'an kafun sulaiman ya mike Wai hawan jininsa ya tashi zai koma gida hanasa fita akayi a ciki code in ganin Kamar akwai bayani a bakin Wanda ya shigon,Koh zaka sanar da kotu Kai wanene da Kuma dalilin shigowarsu a irin wannnan lokaci ana tsaka da Sharia"Zama Ade yayi mutumin da sulaiman ya Kira da buba sai Brr daya gabatar da kansa a matsayin lauya Mai zaman kansa Kuma mataimakin lauyan dake Kare Wanda ake zargi,kotu sosai yayi tsit sai ummu dake da zufa sai yanko Mata yake"Kara natsuwa khamal yayi ya gyara zaman rigansa kana ya nemi izinin Fara gabatar da hujojinsa na Kare Wanda ake tuhuma"an baka dama"shine abinda alkhali yace"nagode ya Mai shariya sai Kuma ya juya yace"Kiran buba yayi ya fito ya tsaya a inda masu bada shaida Koh masu laifi ke tsayuwa tambaya Brr ya Soma Masa Kamar haka"Malam Koh zaka iya sanar da kotu cikekken sunan ka"eh Sunana Adamu ja Amma anfi kirana da buba ja"Masha Allah Koh zaka sanar da kotu menene alakanka da family dogo Mai naira da Kuma son halartar shariya tayau daka nema"?
Kamar yanda nace Sunana bubaja Ni ainahin dan nijar ne kamar yanda kowa ya gani Ni buzune,Neman kudi ya kawomu NAGERIA nida iyalina,bamusan kowa a kasar Nan ba tunda mukazo wahala mukesha sai dai mu samu bayan shago Koh gida mu rabe mu zauna muna kwana Ni Kuma Ina Saida shayi.
A hakan wata Rana Allah ya hadani da Alhaji Alhassan Harya daukeni aikin gadi a gidan sa nida iyalina mun koma gidan sa da Zama Kuma Babu abinda Muka nema muka rasa rayuwa ta Mana dadi dayake matar Alhassan macece Mai fada Amma tana da kyauta hakan yasa Muka kashe zuciyar mu dagani har matata Muna cin harziki harda yaron mu.
Nafi shekara ishirin Ina gadi a gidan Alhaji hatta makarantan d'ana shike biya,mun Zama Kamar Yan uwa,yayansa sun giggirma har wasu sunyi aure.
Bayan wasu shekaru zuwa lokacin gidan ya Kara cika ga aure da Alhaji ya Kara ya auro Amina,tunda Alhaji ya auro Amina kullum sai sulaiman yazo kofar gate yayiita min magiya Akan na Kira Masa Amina Koh Kuma ga wasika na Kai Mata amma Koh daya ban amince ba duk yanda yayi ta hadani da Allah naki,ana haka sai kanwarsa ta Fara zuwa gida tana baiwa Amina wasika daga baya Allah ya tona asirin abin Alhaji ya ganosu shikenan sai yasa security a gidan tsaro ya ninka nada.
Shikenan tun daga lokacin bankara ganin sulaiman ba Ni harnama manta da labarin sa,kwasam wata rana saiga yarona ya shigo gidan da gudu ya Kama hannu na Dana mahaifiyarsa Muka nufi sashin mu don yanzun mun Jima da barin bakin gate,hankalin mu ya tashi da abinda ya sanar damu kwata kwata bamu taba kawo hakan a ran mu ba cameran daya dau kome ya bani kana yace in nunawa Alhaji,Kuma ya Kamata mu gudu mubar gidan don Sun gansa dumu dumu Yana musu vedio"shin yanzun kana tare da kemeran ne tsahon shekarun Nan Koh yaya Kuma ya Kamata kama kotu bayani dallah dallah suwa dan naka ya gani"?
Eh dama Yana karatun jarida ne da Alhaji yadau nauyin sa yace min wata Rana sun fito makaranta Suka biya gidan abokin su zai dubasa kutsam sai yaga Khadija(ummu)ta shiga wani gida dake unguwan shikuma yayi zaton Koh gidan Yan uwantane yace Bari ya shiga ciki ya gaidasu saiya bita cikin gidan Yana kokarin bude kofar dakin ya shiga sai ya Fara Jin magana na tashi Nan ya zagaya ta window yasa hannu ta baya ya bude labule wa'inda ya gani a ciki yasa sa daukar camera sa yayi record na kome Yana tsaka da daukane Mutumin ya gansa harma da matar suka bisa shine ya fito a cikin gidan.
A ranan yarona yabi ya rikice akan mubar gidan nace Masa Ni sai na nunawa Alhaji Kuma na Masa sallama bazaiyu nabar gidan baby sallama ba kuma in Muka koma nijar Banda sana'a Koh wani aiki Amma hakan yaron Nan yace sai dai mu tafi shi haka kawai yaji tsoron Zama a gombe,mahaifiyar sa tace ya shirya kayansa zata tafi dashi in yaso inya samu natsuwa sai su dawo in Kuma Basu dawo ba Nina bisu,haka Koh akayi a ranan Suka bar gidan,nayita jiran ganin fitowar Alhaji Amma bansamu ganawa dashi ba Ina zaune Khadija ta dawo tazo ta shiga gidan.
Washe gari abin mamaki saiga Alhaji ya tashi da ciwon kafa hankali na ya tashi naso naje na sanar dashi Amma Kuma saina kasa Koh shiga cikin falon gidan a hakan yayita ciwo wata da watan Ni duk lokacin da na yunkura Zan sanar dashi sai na kasa, har Allah ya dauke rayuwar sa, a Randa ya rasu na tattara kayana bamma kowa bankwana ba nabar gombe na koma kasarmu Amma abin ciwo iyalina Basu zo kauyen muba na tsorata sosai hakan yasa na dawo cikin gombe Babu irin yawo da banyi ba Amma bansame suba duk Inda nasan Zan gansu na duba Amma bangansu ba hakan yasa na Kama shago Ina xama a ciki Ina dan sana'a,maganan camera Kuma memory na saya Ina chanja record na vedio duk bayan shekara biyu duk abin kallo daya fito na yayi saina saya na tura a ciki na aje don nasan wata Rana xai min matukar amfani.
Kusan a Yan kwanakin Nan sai na ringa mafarki akan yarona Yana cewa na nemi gidan Alhaji naje nakai abinda ya bani,Koh bayan shekaru darine indai Ina da Rai unguwan bazai bace min ba saidai Kuma na kasa gane gidan dayake anyi gine-gine na zamani Kuma masu kyau don ashekarun baya kaf unguwan gidan Alhaji ne Mafi kyau sauran duk na talakawa ne Amma yanzun Naga ba haka bane,kutsam wata Rana Allah ya hadani da wannan yaro Adewale nake Masa kwatance gidan yace min yasan gidan don dan gidan abokin sane saidai babu lafiya don yaron gidan yasha guba Allah ya Masa rasuwa Nan yake bani labarin abinda ke faruwa,haka kawai naji hankali na ya tashi Kuma naji yaron ya kwantamin a rai anan nake basa labarin abinda ya kawoni,amma yace gaskiya zuwana gidan yanzun akwai hatsari, Inna yarda dashi muje ya nemamin gida na zauna zasu daukaka Kara akan lamarin ayi kome a gaban Sharia abi musu hakkin su, salati jama'ar dake code in suka sake,buga guduman sa Alkali yayi kowa ya nutsu,Neman ganin vedio akayi Mika musu wayan sa yayi aka zare memory,had'a kayan kallo akayi babba yanda kowa dake zaune acikin code in zai gani,ummu Kam sharkaf tayi da zuba,haka uzaifa hankalin sa ya tashi, wato mutumin da ya nuna baya kaunar wani Koh ance yama wannan Abu baza'a Yi mamaki ba da ace Mamu ce Babu Wanda zaiji dar don ansan Bata son mami Amma Wai ummu mikewa tayi ta Soma rantse rantse,malama Khadija Nan kotune ki kiyaye komawa tayi ta zauna hankali a tashe.
Haskene irin na films in da Babu colour amma ras ake ganin fuskar mutane,falone irin na da Alhaji sulaiman na tsaye sai Khadija daken zaune akan kujera cikin dari dari Suna magana"gaskiya kaf duniya Babu Wanda na tsana irin Amina"Kuma Zan iyayin kome don Naga bayan ta"gyada Kai Alhaji sulaiman yayi sai Kuma yace"karki damu nida kike ganina innan tsohon saurayin tane amma ganin Mai kudi yasa ta auresa ta barni don haka nima fansa nakeson d'auka a kanta Kuma Koh nawa Zan iya kashewa don ganin bayanta Ni aguna kudi ba kome bane"gyara Zama Khadija tayi tace watoh yanzun ka nemenine dan mu had'a hannu dakai mu raba auren nasu Koh yaya don nidai kome Zan iya Amma Banda kisa bazan iya kisa ba"
Karkiji kome Ina dai kin amince Zaki had'a hannu Dani"eh na amince"toh ke mekike so ayi Mata"Ni bani da buri daya wuce Naga Babu ita a cikin gidan, haka cikin dake jikinta babu shi shine burina,itace tazo a baya sannan tana kokarin mallake kome na gidan Kuma Ni na tsaneta so nake mu Kulla Mata sharri Wanda zaisa Alhaji da kansa yaji ya tsaneta Kuma ya saketa tabar gidan cikin jikinta Kuma so nake ya zube Babu shi"an gama karkiji kome basai an Mata sharri ba ni Ina da malami Kuma harma yamin aiki akanta,waro Ido Khadija tayi tace malami Kuma nida nace ayi Abu na sharri Kuma a samu maganin zubda ciki"?
Karkiji kome wannan zaifi yin aiki farat daya sai Kuma ya shiga daki ya fito hannunsa dauke da wani laida fito da wani yadi yayi ya Mika Mata Amma ba'a ganin wani kalane saboda Babu colour a vedion Amma sunajin tambayar da Khadija ta Masa"wannan Jan Kellen fa malam"?Mika Mata wasu layu uku yayi again bai Bata amsa ba ya sake Mika Mata wani sweet"karba tayi tana jujjuyawa a hannunta kana ta sake jefo Masa tambaya"wannan Jan sweet in ki tabbatar Alhaji yasha shi Koh a abinsha Koh a hakansa wannan kelle Kuma Zaki shimfida ne a kasan zanin gadon da zai kwanta saiki jera wannan layun duka uku a kasan filonsa ki tabbatar Babu Wanda ya kwanta akan shimfidar Koh Shan abinnan sai shi kadai"
Toh meye ma'anan hakan Kuma Ni a zatonsa ai Amina ce za'a ma magani ba Alhaji ba"wannan kikayi abinda nace Miki toh shikenan kaf duniya Babu Wanda Alhaji zaiji ya tsana sama da kome a duniya...............sai Kuma Sukaga Alhaji ya juyo ya kalle window Yana cewa waye a wajen sai Kuma Sukaga camera na gudu Yana haska kasa shikenan Kuma saiya dauke"innalilahi na shiga uku salati kawai ke tashi a kotu sannan lauya ya nemi ganin Khadija fitowa ummu tayi sai hawaye take tazo ta tsaya tambayar da aka jefo Mata yafi kome daga Mata hankali"watoh menene gaskiyar alakarsu da sulaiman Kuma zargin da ake gaskiya ne abinda sulaiman ya sata shita aikata washe gari Alhassan ya tashi da ciwon kafa"?
Tabbas nasan irin wannan Rana na zuwa shiyasa tun farko naso na sanar da hakikanin gaskiyar abinda ke damun Alhaji tun kafun yabar duniya amma sulaiman yayimin barazana da rayuwata mundin na furta ainahin abun saiya ga bayana"kotu ta tambaye ki hakikanin Al'amarin batace ki kamo wata jawabi ba"shin Menene alakarki da sulaiman? gaskiya bamu da wata alaka a tsakanin mu asali ma wata Rana Dana fita a gida ya tareni yace Yana so muyi magana naji tsoro ainun Amma lokacin da naji yacemin saurayin Amina ne nada, Kuma aiki yake so muyi tare zai biyani kudi masu makudan yawan gaske Jin zancen kudi yasa na amince muka saka rana da waje Muka hadu a Randa muka zauna muna tattaunawa yaron bubaja ya ganmu Kuma muka gansa munso ya tsaya amma haka yaki tsayuwa ya gudu hankali na ya tashi shiyasa nace Nina fasa aikin Amma yace Dole nayi abinda ya sani zancen d'an bubaja Kuma in zuba Ido zancen Nan babu Wanda Zai sani.
dana dawo gida nayita dari-dari dasu bubaja gani nake Kamar zasu tonamin asiri Amma hakan bai hanani narkar da sweet Inda sulaiman ya bani a shayin surkina ba haka zalika na shimfida Kellen Nan da laya a daren na langwabe da sunan rashin lafiya na dau uzaifa na kaiwa Addayiya a daren ta kwana dashi don nasan tabbas ba kwanan Amina bane Kuma Amina bazata yarda ta karbi uzaifa a hannun Addayiya ba Kuma haka zalika Addayiya bazata kwana da uzaifa ba daki d'aya da mijinta duk da lokacin yarone karami,Aiko hakata ta cimma ruwa washe gari ya tashi da ciwon kafa Amma haka ya d'aure yaje masallaci daman Ina fakonsa Yana fita na shigo sashen nasu Alhamdulilah Babu Wanda ya ganni harna Shiga na Ciro abinda nasa Masa sauran shayin ma na zubar a toilet,lokacin da nazo fita a dakin karaf Muka hadu da Addayiya Nan na Soma Kame Kamen Mara gaskiya kana nace Mata nazo duba uzaifa ne Yaya kwana"dayake ita Bata kawo mummunan Abu a ranta ba Kuma Bata tambaye ni Jan Kellen dake hannuna a nannade ba tace min in zanzo duba yarona Saida asuba zanzo uzaifan dan yayene,kana ta daukesa ta bani nabar sashen su.
Hankali na ya tashi lokacin da Naga surkina sai ciwa ce ciwa ce yake tun ranar dana saka Masa abubuwan Nan, hankali tashe na koma wajen sulaiman anan yake cewa ai maganin haka yake Nan da wata uku zanga abinda zai faru Aiko Nan da wata uku Alhaji ya rasu, hankali tashe naje na samu sulaiman akan gaskiya Ni Zan tona asirin gaskiyar abinda ya faru kudi sulaiman ya bani bana Wasa ba Kuma ya rantse da Allah Ina fadan gaskiya sai yayi ajalina,Ni Kuma haka na amshi kudin nazo naci gaba da rayuwata na watsar da kome Amma daga baya na fahimci dalilin amfani dani da sulaiman yayi watoh saboda Amina ta dawo garesa.
Uhmmmm ummu na gama bayani lauyan su Adewale ya mike Yana cewa" ya Mai shariya wannan Sharia da muke da Wanda ake yanzun Yana da banbanci an shigar da Sharia ne cikin shari'a Babu alakar kisan Abraham da Kuma wannan gabatar da shaidu da ake,gyada Kai Alkali yayi yace a tsare Masa sulaiman kana a cigaba da shari'an su Lahab shin lauya nada hujoji dazai Kare Wanda ake zargi"kwarai ma kuwa Ina dasu,toh Bismillah ka gabatarwa da code hujojinka"Kiran Nabeel lauya yayi dam dam haka zuciyar sa ta amsa mikewa yayi a dake yazo ya tsaya a Inda aka tanada"code zataso sanin cikekken sunan ka"Sunana Nabeel Muhammad"zaka iya sanar da kotu alakar dake tsakanin ka da Wanda ake tuhuma dasa hannun sa a kisan Abraham"abokina ne"abokin ka nada Koh na yanzun"Kamar ya nada Kona yanzun"calw down Mana Nabeel Wai nace abotar taku har yanzun anayi Koh an daina"?
Kaga Brr karka kawo wata manufa ta daban kawai in zaka min tambaya kamin abinda ya shafe kaina ba wani ba"kotu ta bashi dama kuma tana umurtar ka daka amsa Masa duk tambayoyin da zai jefa maka"a gaskiya Ina bukatar lauya nima Mai girma Mai shariya a d'aga shariyar Nan harsai na d'auki lauya" da murmushi brr yace"haba Nabeel tambaya ce fa Kamar yanda akama Khadija haka za'a maka ka koma ka zauna kaima toh, menene na d'aukan lauya Kuma"?dan shuru yayi sai Kuma yace eh abokina ne har yanzun.
a ranan............. Koh zaka iya sanar da kotu a wannan dare a Ina ka kwana"?dan rikicewa Nabeel yayi kafun yace kamar ya bangane a Ina na kwana ba"?eh a wannan daren dai a Ina ka kwana"gaskiya bazan iya tunawa ba don ya Jima sosai"toh shikenan tunda kace ya Jima sosai bari na tuna maka a ranan baka kwana a gidan ku ba Kama iyayen ka karya da sunan zaka kauyen su mahaifiyar ka zaka je ka gaida kakan ka ta wajen uwa sai Kuma da misalin karfe 1:23am na dare ka fito daga cikin gidan Godwin dake saman layin ku Kuma a daidai lokacin aka kashe Abraham Koh zaka gayawa code meya kaika gidan a daidai wannan lokaci?
Wallahi karyane Babu Inda naje Ina gidan mu wallahi karya ake min wannan ai kazafine"malam Nabeel ka kiyaye a kotu kake"shuru Nabeel yayi cikin tashin hankali ganin wankin hula nason kaisa dare,Dr Colin's kutu nason ganin ka don amsa wasu tambayoyinta mikewa wani magidan cin Cristian yayi yazo ya tsaya"Koh zaka sanar da kutu hakikanin abinda ka gani a wannan rana"kwarai ma kuwa a wannan Rana bayan na taso daga aikin dare da aka kirani na nufo gidana dake kusa da gidan Godwin tunda na sharo kwanar layin mu wutar mota ta ta haskamin mutum Kuma akwai hasken nepa duka, ya fito daga gidan hankali tashe jiki duk jini fuskarsa a rufe nayi matukar tsorata hakan yasani niyar juyawa na koma Inda na fito sai Kuma motar ta mutu yaki tashi wutar motar ma ta d'auke Nan nayi ta kokarin kunnata amma na kasa Saida yazo daf dani cikin duhu kawai saiya gwaru da motar tawa ba tare daya kula akwai mota a wajen ba Nan ya buge kafarsa da Sauri ya tsunguna Yana mammatse kafar Kana ya mike yabar wajen Saida yabar wajen nayi Sauri na bude motata na sauka Nan na kunna wayata Zan haska hanya na wuce gidana kawai saina ga wayarsa a kasa ya Fadi da Kuma mask na fuskar sa alamu ya cire mask inne,da banyi niyar d'auka ba amma daga baya saina d'auka kawai nayi gida tunda na koma gida haka na kasa natsuwa kwata kwata Saida na kunna wayan Nan amma wayar da lock a ciki sai dai screen in wayar akwai hoton shi Nabeel da Kuma yayarsa sun dau hoto tare Kamar ranan sallah ne ma hoton aka daukesa,lokacin dana ga hoton saina aje wayar da yakinin taima ya Kira yanason wayarsa,washe gari da safe saiga labari ya karade gari an kashe Dan Godwin babu Wanda naji ina zarginsa a Raina sai Nabeel amma Ina tsoron karna sa kaina a rikici bani da gamsheshen hujja Kuma naji tsoro Kar wani bincike yasa a bi diddigin layinsa,na kashe wayar gabaki daya,wata sabuwar labari danaji shiya dagamin hankali shine Wai Nnenna da Lahab su ake tuhuma sai dai ba'a Kama yarinyar ba har Shiga code nasu Lahab na farko naji labari da Kuma fitarsa Lahab na fita da kaina naje