Showing 15001 words to 18000 words out of 59418 words
yar mutane tasha iska haka nan zakewan nawa yayi yawa"yace a sarari yana gyara kwanciyan shi
Washe gari Tuesday bata da morning lec,Dan haka tana tashi ta kwashi kayan ta zagaya can baya ta kama wanki.abinka da sabon shiga ko yanda ake wankin ma bata Iya ba duk ta jika jikin ta tayi jina jina da ita.kayan ma dai jika jika ta musu ta shanya.
Cikin parlour ta shigo zata wuce bedroom dinta har wani layi take tana hada hanyan saboda gajiya.Sam baya kula dasu Ammi dake parlourn ba ,Ammi tace"son gaskiya naji dadin abinda kayiwa daughter, nasan yanzu koba komai tasan yanda masu yi mata aiki suke wahala kuma dole suyi dan shine hanyan cin abincin su.ka ganta nan ko kayan ta bata Iya ninkewa ba"kallon ta yake ya rasa bakin magana cos ta bala in bashi tausayi.but deep down him yaji dadin hakan saboda yasan yanzu atleast ta koyi how to respect others.yake ta musu kawai tayi wuce ciki Dan tana Iya fashewa da kuka in ta bude bakin ta.
Kan gadon ta fada da jikakkun kayan a jikin ta,tana maida numfashi ,har wani zazzabi 2 take ji a jikin ta a haka wani wahalallen bacci ya dauke ta.sai kusan azahar ta farka jikin ta zafi rau,Ga wata juwa dake diban ta saboda ko break fast batayi ba.tana nan kwsnce ta kasa tashi Ammi ta turo kofa ta shigo"baccin me kike haka ne ko kin manta kina da lec by 2"Ammi tace tana zama a baking bed din.hannun ta taba taji zafi rau,a rikce tace "baby re u sick?"kan ta kawai ta Iya gyadawa.fita Ammi tayi,sai gata ta dawo da wani mug mai Dan girma.tea ne ta hada mai kaurin gaske,taimaka mata tayi ta zauna sannan ta fara bata tean a baki.tas ta shanye,pain relieve ta dauko ta bata Wanda da kyar tasha dama akwai ta da kin magani.da kan ta Ammi ta shiga bathroom ta hada mata ruwan dumi tayi wanka sannan taji Dan dadin jikin ta.
A zuciyar ta ta yanke shawaran zuwa ta bashi hakuri ya fita a rayuwan ta ko zata ji dadi.bata sauko ba saboda zazzabin da gaske ya kwantar da ita,bayan isha I ta daure ta sauko ta nufi dakin shi da kyar.a baking kofan ta tsaya tana shawaran ta shiga ko ta koma,ta Dade a wajan daga baya kuma naga ta fasa shiga ta dawo daki tayi kwanciyar ta.
D next day Wednesday duk da taji sauki amma bata je sch ba.a wajan break fast farhan yaji ashe farhat bata da lafiya,duk ya rude yana ganin shine silan rashin lafiyan ta.koda Yaje office kasa zama yayi duk hankalin shi yana kan farhat Dan haka yana sallahn azahar ya dawo gida.a parlour ya iske su dukan su zaune suna kallo,zama yayi shima yayi yana tambayan ta ya jiki.duk ta fada kaman tayi sati tana jinya.murmushi kawai tayi ta sunkuyar da kai,sai wani blushing take.she was acting so strange kodai ta shiryu ne take cewa a zuciyan shi.shiru suka yi gaba dayan su suka maida hankalin su akan wani wa azi da ake haskawa a sunna t.v.wayan Ammi ne yayi kara,ganin Abba ne yasa ta mike tayi hanyan sama tana amsa wayan.
Su kadai ne a parlourn kowa yayi shiru sai dai suna hada ido sai su sakarwa juna murmushi.can dai farhat ta fara magana kan ta a kasa tace"ya farhan tun jiya nake son Baja hakuri amma bansan ta inda zan fara ba,pls ka yafe min for what I have coursed u"cikin wani yanayi farhan yace"no farhat ni ya kamata in baki hakuri,I'm so sorry I made u feel sick"don't worry komai ya wuce"tace still idon ta a kasa.cikin jin dadi yace"tanx dear"sai a lokacin ta dago da ta kalle shi.nan ya gane irin katobarar da yayi,kame kame ya fara ganin ba zai fidda shi ba ace"ermmmm ina zuwa"cikin sauri ya wuce bedroom din shi kaman zai kifa.bayan shi tabi da kallo tana smiling har ya shige sannan ta dawo da idon ta inda ha tashi taga bai dauki komai nashi ba,phones da jakan laptop din sa duk suna nan.dayan wayan sa da yayi mata kyau tasa hqnnu ta dauka tana swiping taga ya bude Dan baisa security ba.pic din shi na kan wallpaper ta kurawa ido tana Murmushi,suite ne ash colour a jikin Sa hannun shj daya a cikin aljihun wandon shi yana murmushin nan nashi mai kara mishi kyau da kwarjini.Dan latse latse tayi a wayan ta mayar ta qjiye.haka ranan farhat ta wuni sukuku da ita,kuma duk inda ta hadu da farhan kuma ta rinka blushing kenan.Ammi na ankare da su sai dai baya ce musu komai ba amma a kasan zhciyar ta tana add uan Allah yasa farhan ya zama silan shiryuwan tilon yarta.
11:45pm farhan ne zaune a tsakiyar bed dinshi ya Lankwasa kafafun shi,yana aiki a laptop dln shi.wayar Sa yaji tana kara koda ya duba yaga bakuwar no ce Dan haka har ta katse bai daga ba.kara shigowan wani kiran ne yasa shi daukan wayan ganin no dazu ne yasa shi receiving ya kara a kunne ba tare da yace komai ba.muryan mace yaji tana kuka harda shashsheka,cire wayqn yayi a kunne q kunnen Sa ya kara kallon no yaga dai bai San no ba.yana kokarn kashewa yaji amce"yafarhan!"hello farhat"yace da alaman tambaya a muryan Sa.cikin kuka tace"ya farhan zan mutu wayyo kaina"a rude yace"stop crying pls meke damun ki?"tace"kaina duk jiki na ciwo suke min na kira way an Ammi a kashe Kuma bazan iya tashi ba,pls ya farhan help me.ta karashe magqnan tana kara rushewa da wani Sabin kuka.cikin kidima yace"it was all my fault. In naja miki ,I'm sorry.ta INA dakin ki take?in ka hay sama first door at ur right"tace tana cigaba da kukan ta."owk gani. Nan zuwa"yace tare da katse kiran.cikin Saudi ya diro daga kan gadon ya fito parlour a Dari.duk da yaune farkon hawan shi sama bai sha wahalan gane kwatacen taba.yana taba kofan yaji ta a bude,Shiga yayi ya ganta kwance kan gado sai juye juye take duk gashin kan ta ya barbaje ya rufe mata fuska.a rude yq karaso gare ta yana mata sannu tare da tambayan ta ko akwAi magani a dakin ya dauko mata.
Tashi tayi ta zauna tana masa murmushin gefen baki,kamo hannun Sa tayi tana shafawA a hankali tace"kace min mai donkey head but u re a dump ass if not how can u come to my room at this time?naji Hiran ka da abokin ka last 9t wai Ashe ni make fooling.zan nuna maka u re nothing a tafin hannu na kake har ni zaka wulakanta a cikin gidan mu,kasa iyaye na suka fifita ka akaina dan haka yau zan kulla maka sharrin da har ka mutu baza manta dani ba kuma a yAu ba sai gobe ba za ka bar gidan Wanda za a mAka Koran kare tunda kaki tafiya ta girma da arziki...dole a koma kauye
.."tunda ta fara magana farhan ya bushe a wajan ko motsi ya kasa balle ya Iya kwace hannun Sa.kuma lalle ya yarda he is d biggest fool in d world tunda har ya karamar yarina kaman farhat Zata Iya maida shi kwar kwar ko tunanin ya akayi ta samu no shina bai tsaya yi ba.
Zuciyar sace ta wani irin bugawa ganin Ammi ta shigo dakin ladi na bite da ita a baya.farhat tana ganin Ammi ta kara rushewa da sabon kuka.farhan na kokarin kwatan hannun Sa amma ya kqsa,jikin Sa ne ya fara rawa ganin Ammi ta tukaro su gadan gadan fuskan nan nata kaman anyi mata mutuwa.
Hmmmm farhan cikin tsaka mai wuya pls kuyi masa add Ua
[11/26, 5:35 PM] Ummee Yusuf: π₯π₯π₯π₯πΉπΉ
FARHAT
π₯π₯π₯π₯πΉπΉ
Written by ummee yusuf(Maman Yusuf)
I dedicated this page to my sweet sis Ameena adam.luv u soo much.
Page 18
Farhan ya gama saduda yana jiran yaji hukuncin Ammi tana karasowa bakin bed din tace" haba farhat ke dai bazaki taba canzawa ba?abu qalilan zai saki cika mutane da raki?Allah ma yasa alh baya nan da bansan yanda zakiyi ba.son kai ma ta taso kako?yi hakuri wlh haka take da rakin tsiya dan in bata da lfy haka zata ishi mutanen gidan nan."
Shi dai farhan ya rasa bakin magna sai bin Ammi yke da ido da take gyarawa farhat kwanciya.cire hannun farhan Ammi tayi tace"go and sleep son"har yanzu dai ya kasa motsawa Dan ganin abin yake tamkar mafarki.gefen wani drower Ammi ta wuce dauko mata magani,kallon this is the beginning tayi mai tare da gallawa ladi harara.sum ya mike dan sai yanzu ya dawo daga suman zaune da yayi.bai Iya furta komai ba illa ficewa saga dakin,biyu 2 yake hada steps din saboda sauri.shi bai sAmu natsuwa ba sai da gan shi cikin bedroom din shi.
Zubewa yayi a kan Gadon shi yana maida numfashin wahala kaman wanda yayi tseren doki.allah ya so shi Ammi batayi masa mummunan fahimta ba,if not da ya shiga uku .wace hujja zai bayar wanda zai gamsar da iyayen ta cewa yana da gaskiya.tunani yake ta ina ma ta samu no shi?ajiyan zuciya ya sauke mai karfin gaske dan yanzu kam ya yarda kaidin mata azimun ne."Allah ka raba Mu da kaidin mace"ya furta a fili."I have to leave dis house or dis silly gal will make go crazy"murmushi ya fara shi kadai yana juyi a kan gado da ya tuna yanda ya ganta cikin night wear da lokacin da take wani shafa mishi hannu."she already made me crazy"yace yana lumshe ido.
Ammi sai mita take har ta bata magani,sannan ta sassauta murya tace "haba mana habibty kin fa girma yanzu ya kamata ki rinka hakuri watarana haibuwa fa zakiyi,so pls ki rinka daurewa.kinji?"kai kawai ta Iya dagawa,Ga wani hawayen takaici da take zubarwa.anytime zatayi Abu amma shine da nasara.shiru tayi tana sauke ajiyan hrt.ammi tacewa ladi ta zauna a wajan ta tana zuwa.tana ganin fitan amni ta taso a zuciya ta kwashe ladi da wani wawan mari cikin takaici tace mata"me nace miki?magana nake kin wani zuba min ido kaman ki cinye ni.ke da nace miki ki taho da ammi bayan kinga ya shigo kaman da 20mins ba.duk kin rusa min plan.pls ki fita min a daki kamin in miki wani mugun abun."sum sum ladi ta fice mata a daki.komawa tayi bakin bed ta zauna tana tuna yanda yau ta zauna ta tsara abinta tun safe kuma Allah ya taimake ta ta samu no shi cikin sauki a lokacin da ya bar way an Sa a parlour. But bari Abba ya dawo I know what to do cos nasan da shine yazo ya gan shi haka toh tabbas sai ya kore shi a Daren nan kuwa.ta wani bangaren kuma hankalin ta ya kwanta Dan taswn ya tsorata Iya tsorata cos taga hakan a kwayar idon shi.haka tayi ta nazari da kyar bacci yayi nqsaran daukan ta
Da washe gari da yamma Abba ya dawo daga abj.and yanzu jikin farhat da sAuki sosai.on Friday morning sunq zaune a dinning suna break fast ,fa rhan duk haΓ±kalin na kan farhat da ko kallln inda bata yi.can ta ciko bakin ta da potatos ball tana taunawa.dago idon da zatayi suka hada ido da farhan daya zuba mata ido.kashe mata ido 1 yayi yana mata alama da wai loman yayi yawa,murguda mishi baki tayi tare da kauda kai gefe.murmushi abba yayi yacigaba da cin abincin sa dan duk abinda suka yi kan idon shi aka yi.
Wannan ne karo na uku da yake dago kai ya kalli Abba da niyan mgn amma sai kuma sunne kai kasa yana murmushi,Abba ne ya lura dashi yace"ya dai farhan kaman bakin nan naka akwai magana"..
Sunne kai ya karayi yana murmushi sannan yace"Abba ka tambaye lil sis tasan abinda zan fada maka Dan wannan wani babban burin ta ne nake son cikawa,ta Dade tana gaya min tun farkon zuwa na gidan nan.ni kuma a matsayi na,na Dan uwan ta naga ya kama ta in cika mata wannan burin Dan ta samu farin ciki da kwanciyar hankali.da dai banyi na am da zancen ba amma da naga ta dage shiyasa nima na bata goyon baya.
Wani irin sanyin dadi ne ya lullube farhat lokaci daya da taji furucin farhan,sai dai kuma tana tsoron me iyayen ta zasu ce.but koma menene zata Iya daurewa tunda finally ya yarda zai bar musu gida da kan Sa,dama tasan za ayi haka Dan yanda rannan ta tsorata shi.
Abba ne ya katse mata zancen zuci da take yace"mama na ki fada min wani irin buri ne haka da ni ban sani ba,bayan a baya ni ke fara sani"ta budi baki da niyan magana kuma tayi shiru.a ranta take cewa ta ina zata Iya gayawa abba cewa bakon sane bata so,ta Yaya zata fada masa cewa talakawa da yake ja a jiki ne bata so?ta San in yaji daga bakin ta hukuncin da zai yi mata sai yayi sauri dayawa.wannan dalilin yasa taja bakin ta tayi shiru.tana sunne kai itama.
Dariya suka bawa abba ya Dan dara yace"ina sauraron ki mama na"abba in fa na bar zancen tuntuni amma tunda shi ya tado ta sai ya fada maka"tace tana kallon kasa.dariya ya karayi yana kallon Ammi da tayi shiru kaman bata wajan,yace"yau kuma ni ake kunya kuma mama na?"juyowa yayi saitin farhan yace"kaga kanwar taka ta kasa fada Dan haka kai ya kama ta ka daure ka fada ko.......?"
Da kyar farhan yace"ammmm dama.......Dama....
Dama me kayi magana mana INA jinka"abba yace yana kallon Sa.kara sunkuyar da kai yayi sannan yace"abba dama mun daidaita kan Mu ne ni da farhat......."sai yayi shiru yana murmushi da Sosa keya.
Masha Allah!!! Abinda abba yake maimaitawa kenan kana ganin fuskan Sa zaka Ga Balkan farin ciki daya kasa boyuwa"shiken nan tuwo na main a,hjy kinga ikon Allah ko"?itama cikin tsananin farin ciki tace"wlh alh inaga na fika jin dadin wannan hadin".
Bin kowa take da kallo Dan bata San Inda zancen Nash ya dosa ba,ita da take jiran taji an rufe ta da fada amma gani tayi ma suna ta farin ciki.muryan Ammi taji tana cewa"Ai biki zamuyi na ban mamaki a Maiduguri,da nawa ya tawa".zuciyar ta ne yayi wani irin bugawa Dan sai yanxu ta gane inda zancen nasu ya dosa.cikin kidima da tashin hankali ta mike tace.
Tab farhan ya debo da zafi.muje zuwa yanzu aka fara wasan.
[11/27, 7:04 PM] Ummee Yusuf: π₯π₯π₯π₯πΉπΉ
FARHAT
π₯π₯π₯π₯πΉπΉ
Written by Ummee yusuf(Maman Yusuf)
Gaskiya ina jin dadin comments da mahawaran da kuke ,yana kara min karfin guiwa.gaisuwa ta musamman ga MUSLIM IBRAHIM, ina yin Ku sosai masoyana.
Page 19
"Wlh Abba karya yake min,yaushe mukayi haka da kai?"jikin ta har rawa yake,idon ta kuwa sai ambaliyan Hawaye suke.kana ganin ta kasan tana cikin matukar tashin hankali .farhan kanshi sai da ya firgita ganin yanayin ta kuma ya tabbatar tsanan da take masa ya wuce misali amma yayiwa kan Sa alkawari zai koya mata zazzafan soyayyar Sa in dai aka aura masa ita.fargaban shi daya kar iyayenta su gane karya yake suki bashi ita.
ihun tane ya dawo dashi daga zancen zuci da yake sanadiyan buge mata baki da Ammi tayi.
Cikin fushi Ammi tace"bana son zancen banza,ca nake da amincewar ki ya fada kuma shekaran jiya da daddare da baki da lafiya wa kika kira?INA tare nazo na iske ku".
Cikin kuka mai tsuma zuciya tace"ni......Ammi ba wannan maganan nace ya fada ba".toh me kike son ya fada mama na?"Abba ya jeho mata da tambaya,fuskan shi dauke da murmushi.ta ina zata fara fada musu kudirin tq akan farhan?shiru kawai tayi tana shesshekan kuka.
Abba yace "borin kunya ne haka mama na uhum?Ai ba wani abin damuwa bane Dan ya ce ke kika fara ra ayinsa Dan ko ba komai Ai Dan uwan ki ne.nima kuma shaida ne"yace yana dariya kasa kasa"dazu da ido na,na gan Ku kuna ta soyayyar ku ,har kun manta ba Ku kadai bane a dinning din".
Mikewa farhan yayi yana Sosa kai ya fice da sauri, irin wai shi yaji kunyan nan.Ammi da abba suka bishi da dariya.
Kara volume din kukan ta farhat tayi,yanda take jin zuciyar ta kaman ya fashe.har wani daci daci take ji a bakin ta,farhan ya gama da ita wai ita ta fara cewa tana son shi,Ga iyayen ta sun yarda da karyan da ya tsula musu.Ammi tasan sarai karya farhan yayi amma taji dadi Dan ba Wanda zaki farhan a matsayin surki saboda kyawawan halin Sa.and above all da alamu ya nuna zai Iya zama sanadiyan shiriyan ta.
Cikin lallashi ammi ta bata baki,tashi tayi da gudu tayi banyan stairs tana cigaba da kukan ta.
Abba ya dubi Ammi fusakan dauke da tsantsan damuwa yace"anya swthrt ba kya ganin kaman mama na da gaskiyan ta?ban taba ganin ta cikin wannan yanayi ba.kema kin San bans son bacin ran ta cos ita daya gare ni".Ammi da har yanzu fuskan ta dauke yake da zallan farinciki tace"haba dear kasan fa habibty har yanzu kuruciya na damun ta,a yanayin da na fahimta itama tana son shi kawai dai taurin kai ne irin nata.and beside farhan ba zai taba yi maka karya ba,da anyi auran zasu sasanta kan su.just mu taya su da addu a tare da fatan alkhairi.
Abba ya sake fuska yana murmushi tare da gyada kai alamun gamsuwa da jawabin matar Sa,yace"hakane allah ya sanya alkhairi.ameeeen....."
Farhan na fita kiran Umar yayi yaji ko yana gida yaje ya same shi,Umar yace"bana gida inama kusa da anguwan Ku,ina cikin government house bari in karaso "OK"farhan yace tare da fitowa bakin gate ya tsaya.baya son su shiga ciki su hadu da farhat Dan yau yasan ya tsokono tsuliyar dodo.shiyasa zai bar gidan ba zai dawo ba sai ya tabbatar tayi bacci cos in ya tsaya haduwar su bazata yi kyau ba ko kuma ta rusa masa plan.yana nan tsaye har Umar yazo ya tsaya a gaban shi.bude gaban motan yayi ya shiga ya zauna,Umar yana zolayan shi da in jerry sa."tana ciki muje in baka lbrn abinda ya faru.kai man me kayiwa yar mutane?"Umar ya tambaye yana shan
Kwana"muje zan fada maka ".
Farhat tana kwance kan bed din ta sai rusa kuka take kaman ranta zai FIFA,mesa akan farhan kwata kwata bata da