Showing 18001 words to 21000 words out of 59418 words
Sa a ne?zagi da asshar ba Wanda bata durawa farhan ba sai sumbatu take.
Chak kukan nata ya tsaya kaman an dauke wutan nepa."wat did I just do?"tace tana tashi zaune tare da goge hawayen ta."I rise my voice to him in front of my parent,I cried in his present.oh shit"tace tana kaiwa pillow ta duka kaman shi ya mata laifin." abinda nake son yayi a gaban abba shi yasa nayi daga yau baxan kara kuka a gaban shi ba balle ya raina ni.I know by now he is celebrating ya sani kuka.kaman yanda ya sani na zubar da hawaye na,I promise sai yayi Wanda yafi nawa sai yayi nadaman taro wasa da yayi tare dani.I promise"tace tana kara goge hawayen ta.
9:30pm Umar ya sauke shi a cikin gidan yana cewa"dude wats ur next step?kasan fa ka debo da zafi"dariya yayi ya bude kofan motan ya leko ta window suna kallon juna,yace" don't worry I will handle it,I knw by now tayi bacci and zan San yanda zanyi Mu rage haduwa da ita"its impossible u know since a gida daya kuke."I know and I will try"yace yana juyawa cikin gida,"gud 9t"Umar yace yana Jan Motan shi.
Sallama yayi ya shiga parlour kaman yanda yayi expecting ba kowa sai t.v da yake ta ihun Sa shi kadai.dakin shi ya wuce yayi kwanciyar shi zuciyar Sa wasai,tsabanin farhat da ta kwanta zuciyar ta a cunkushe.
Cikin sati 2 abba da Yan uwan farhan suka tsaida magana akan nan da 2weeks za a sha biki.farhat na dawowa saga sch Ammi ta tare ta da zancen,aiko abin sai ya dawo mata sabo cos har ta manta da batun wani farhan sbd Rabon da tasa shi a ido tun ranan da ya shirya wasan sa.kuka ne yake son kubce mata amma haka ta daure ta shanye da ta tuna alkawarin da tayi,she will never drop her tears for him.murmushin dole ta kakalo ba tare da ta ce komai ba tayi hanyan stairs.
Zama tayi a bakin gadon ta,tare da rafka tagumi da hannu 2.tana son bawa farhan mamaki amma ta yaya?Dan bata son shawaran kowa shi yasa bata fadawa frnds din ta ba.
Cire tagumin tayi ta mike tana murmushi tace"yessssss.....hakan zanyi..."
Nace toh me farhat take shirin yine?π³
[11/28, 7:24 PM] Ummee Yusuf: π₯π₯π₯π₯πΉπΉ
FARHAT
π₯π₯π₯π₯πΉπΉ
Written by Ummee Yusuf (Maman Yusuf)
Page 20
Zaune suke a parlour dukan su bayan sunyi dinner amma har yanzu farhan bai dawo ba.in bata manta ba,kusan a week kenan basu hadu ba."what is he planing?ya kamata in San me yake shiryawa next b4 nima in nuna masa salon wasan".tace a ranta.
Sallama yayi a kofan parlour, Ammi ta amsa ya shigo ciki.dan razana yayi ganin ta a zaune parlour dan baiyi tsamanin ganin ta ba a wannan lokacin.amma da yake wayeyen guy ne sai ya mazge.gaishe dasu Abba yayi sannan ya samu waje ya zauna.
Fada Abba ya Fara masa kan ddadewa da yake a waje kwana 2nan,kamin ya amsa mishi sai jin muryan ta yayi tana cewa"Abba ba laifin shi bane,laifi na Dan muyi waya kuma ya fada min ya ba zai samu daman dawowa da wuri ba."ke fa wani sa'in shasha ce,mesa baki fada min ba?"Ammi ta katse ta tana hararan ta."mantawa nayi fa Ammi"tace a shagwabe."ya isa haka,ke meye naki na sai an fada miki?tunda ya fadawa kanwar Sa Ai shikenan"Abba yace da smiling face.sunne kai suka yi dukan su suna dariya kasa kasa.Ammi ma dariyan tayi tace "Ai shikenan kuwa na daina magana daga yau.
Farhan ya jinjinawa farhat a zuciyar Sa cos a zaton shi zata dauki wani mummunan mataki a Kansa shiyasa ma yake zuwa gida late kawai Dan kar su hadu but yasan yanzu ma she is up to some thing.
"Ya farhan ur food is on d table"tace tana masa kallon kasan ido.mazgewa shima yayi ya mike ya nufi dinning, cikin sauri itama tabi bayan shi tana "let serve me u"Abba ya bisu da ido cike da sha awa.
Ita ta ja masa kujera ya zauna,plate ta dauka ta cika mishi da tuwon semovita yasha miyan kuka Wanda aka burge naman kaza a ciki said kamshin man shanu yake.wani plate kuma ta cika shi da kammoniye Wanda yasha spices,ta tura masa plates din duka 2gaban Sa tana murmushi,ta xauna a kujeran da yake opp da nashi.wanke hannu yayi ya fara aikawa cikin Sa.har wani lumshe ido yake saboda santi.ita kuma sai wani yatsina fuska take Dan kyankyami miyan take.
"A villager will never change,yuks!look at u so disgusting".dagowa yayi yana kallon ta with his smiling face,yace"my future wife,I like ur style.da alamu kin Iya kula da muji and nasan u accept d defect".wajan su Abba ta kalla,taga sun Dade da barin parlourn.kallon banza ta mai tana nuna shi da yatsa cike da tsiwa tace"future wife indeed,huh! Sai kayi nadaman taro wasa da kayi dani,run wuri kuma tun dare baj maka kaje kace ka fasa auran da bakin ka b4 is too late 4 u.kaima kasan ko a matsayi driver baka isa ka shigo gidan nan ba,balle ka dubi tsaban ido na kace wai ni zaka aura.wlh wlh in har baka jenye ba akayi auran nan,kasani duk abinda ya biyo baya kayi kuka da kan ka bcs I have already warn u.
"Wow!miss ego yace yana tafa mata"irin wannan long lec haka?gaskiya zaki Iya lec a ko wani sch.but kin San me?da farko nasa zuwa gun abba in ce na fasa auran ki.dama naso taimaka miki ne sabida naga tunda nazo gidan nan ko kare ba zo gidan nan da sunan yana son ki ba,dan hallacin da Abba ya min shiyasa nima naso in danyi manage dake,cos baki da qualities da nake so matan da zan aura ta kasance da su.but furucin ki na yanzu da kike cewa akwai abinda zai biyo baya,toh gaskiya kinsa min kwadayin ganin ko menene.Dan haka ki fara shiri na fasa janyewa."yace ya mata murmushi kaman ba shi yayi furucun ba.
Farhat ta matukar fusata,tunda take ba a taba ci mata mutunci haka ba.ita da take gara maza shine wannan poor bagger yake cewa zai manage da ita.ita da take ganin duk guys din maid bata ga Sa an auran ba.a fusace ta dauki warmer mai cike da miyan kuka ta watsa mishi a fuska,in ba Dan yayi saurin rintse idon shi ba da ya shiga masa ido.
Cike da karaji tace"karya kake,kai din banza waye kai a garin nan?kai da kake karkashin mahaifina matalauci mabaraci har kake da guts din Dada min magan........."
Katse maganan nata tayi ganin ya nufo ta gadan gadan.fuskan nan nashi a murtuke kaman bai taba dariya ba,sai da yazo dab da ita har suna jin numfashin juna.wani kallo yake mata da yasa ta firgita"repeat wat u have just said now"yace idon shi cikin nata.a matukar tsorace take da yanayin shi amma ta daure tace"dallah matsa min in wuce duk ka cika ni da wari ,a rinka wanka pls"kara matso ta yake tana baya,yana binta har ta kai jikin bango.hannayen Sa duka 2 yasa ya mata rumfa har yanzu fuskan a murtuke take.duk a rude take tasan ko tayi ihu su Ammi ba jin ta zasuyi ba,balle ma ba zata yi ba Dan kar ya raina ta.
"Ina ruwan ki da wari ko kamshi na jiki na?ina ganin sai na koya miki yanda ake kula da miji,tunda naga dai sauran ki".yace yana goga mata fuskan shi Wanda ta bata da miya kan nata fuskan.runtse ido tayi tana cize lebe sakamakon zafin jajin miyan da shiga mata ido."let's share it wife"yace yana murmushin mugunta Dan sab yasan yajin ya shiga mata ido amma ta matse ita ala dole kar ya raina ta.bai barta ba sai da ya goga mata miyan tas a fuska da jiki,tana ji tana gani saboda ya tare ko ina ko kwakwaran motsi bata iyawa.
Kallon yanda take fama da idon ta yake,"so tell me something good b4 I go to bed"yace yana dariya kasa kasa.cikin dauriya ta dake ta bude idon ta daya canza launi daga fari zuwa ja,harara ta watsa masa tace"ban taba ganin talaka mai ji da kai irin ka ba,kana ganin har ka Kai matsayin da dani zan Iya gaya maka wani magana?any way I can say poor bagger stay.........ouch..."race tana Sosa bakin ta sanadin Dana mata yatsan Sa manuniya da yayi a baki kuma shi yayi sanadin katse maganan da ta fara.kallon Sa take cike da takaici,ji take inama zata Iya rufe shi da duka da tayi ko zata huce haushin ta.Ga radadin ido gana bakin duk a lokaci daya."next tym try and find a nice name to ur hubby ko kuma inta hukunta shi wannan somin tabi ne sauran sai a bedroom din Mu"yace yana kashe mata ido tare da shafa gefen fuskanta da miyan kuka har ya fara bushewa.juyawa yayi yana dariya cikin takun kasaita ya nufi dakin shi ya bar ta nan tsaye da kunan zuciya.
A zuciye tayi dakin ta,direct bathroom ta fada tana mai jin haushin zuciyar ta da take yaudaran ta na jin dadin yanda suka kasance tare a yau take Ga kuma hancin ta da yaki daina jiyo Mata daddan kamshin Sa.
Wanka tayi sosai wai duk Dan ta daina jin kamshin but still tana ji.sleeping dress tasa ta dauki turarenta ta kama fesawa sai da ta kusan feshe rabi tukun ta ajiye ta kwanta a gado tana tunanin yanda zata kuntatawa poor bagger a haka har sarkin barayi ya saceta.shima farhan haka ta kasance a wajensa ,sai wani murmushi yake tunda ya fito daga wanka Ga laptop yasa a gaba amma ya kasa tabuka
a komai.ganin bazai ya ba yasa ya rufe laptop din yayi kwanciyar Sa yana tuna moment din such na yau
A haka shima baccin Ya kwashe shi.
[11/29, 7:16 PM] Ummee Yusuf: π₯π₯π₯π₯πΉπΉ
FARHAT
π₯π₯π₯π₯πΉπΉ
Written by Ummee Yusuf(Maman Yusuf).
Zan rayu da Ku zan mutu,Abadan dani da kuzo Mu zauna masoya na.
Page 21~22
Washe gari ya kama Saturday ba aiki Dan haka gidan shiru kowa na bacci in ka cire mutum 2,farhat dama al adan tane every weekend tana motsa jiki.sai farhan kuma da yaki komawa bacci yana jiran yaga fitowan ta.fitowa tayi cikin shirin ta yanda ta saba wato 3 quarter black colour,white top and white facing cap.tayi matukar kyau tana rike da ball dinta while ladi tana rike da sauran kayan bukatun ta
A kan idon shi ta fara wasan yau yana nan tsaye a bakin window da phone dinsa a hannu, kawai sai ya tsinci kan shi da mata video yana smiling. yana nan tsaye har ta gama,yaga ta nufi
cikin gida.da sauri shima ya matsa daga window ya ajiye wayan ya fito tsokana.
Sauri sauri take tafe tana goge ruwan jikin ta,bata lura da shi ba sai da tazo dab dashi sannann ta ankara da mutum a gaban ta.ta taso da rashin mutunci taga ladi ta kusan isowa inda suke, rabawa tayi ta gefen shi ta wuce ciki ba tare da ta kula shi ba Dan bata son ya bada ita agaban masu aiki.murmushi yayi ya bita da ido Dan sab ya ya gane dalilin rashin kula shi da tayi.bedroom ya koma ya kwanta yana kallon videon da ya mata yana murmushi.
Sai 9 suka sauko Dan yin break fast,sun Dan jima kan dinning amma farhan bai fito ba.Ammi tace"habibty je ki kira yayan kj muyi break".bata so ba amma ba yanda ta iya ,haka ta daure ta nufi bedroom shi.
Knocking ta fara yi,jin shiru yasa ta bude kofan dakin ta shiga.wani irin kamshi mai dadin gaske ya mata maraba,kallon dakin ta faryi komai neat a tsafta ce.tabe Baki tayi irin dakin bai mata ba.karasa shigowa ciki tayi tana dube dube.ganin kan gadon ba kowa yasa ta juya da niyan fita, jin karan bude kofan bathroom yasa ta juyo.
Farhan ne ya fito daga wanka,daga shi sai Dan karamin towel a kugun Sa daya kuma yana goge gashin kansa dashi.baima San da mutum a dakin ba,ita kuwa ya fito a haka yasa duk ta daburce Dan tunda take bata taba ganin namiji haka ba.da sassarfa ta nufi kofan fita,sai da ta kama handle din kofan sannan tace"they are waiting 4 u at d dinning"ba tare da ta juyo ba kuma bata saurari abinda zaice ba tayi ficewar ta da sauri tana sauke ajiyan hrt.dariya yayi yana gurgiza kai,ya cigaba da shirin Sa a gurguje.
Fitowa yayi ya same su har sun fara cin abinci sakamakon karya da farhat ta tsula musu,cewa wai
yace shi ba yanzu zai ci abinci ba.dukawa yayi har kasa ya gaida su,amsawa sukayi cikin sakin fuska.Abba yace"Ai mun dauka baccin weekend din ne yayi dadi da kace ba yanzu zakayi break din ba".kallon farhat yayi da ta matse tana cin abincin ta hankali kwance,cos yasan aikin tane.kujera yaja ya zauna opp dinta sannan yace"eh abba naso taba baccin ne kuma sai na tuna ina da meeting"ok yana da kyau,ka kara himma"abba yace ya cigaba da cin abincin sa.
"Serve him" ammi tace ba wasa a fuskan ta.tashi tayi ta zuba mishi amma na mugun ta dan sai da ta cika plate din kaman cin mutum 2 sannan ta koma ta zsuna ta cigabs da cin abincin ta.
Bismillah yayi ya fara ci yana satan kallon ta,itama hakan ta kasance dan tana dago ido suka hada,bakin ta inda jiya ya dana mata yatsa ya dan taso yayi ja.alama ya mata da bakin yana mata dariya. duk haushi ya cika ta,bayan shi ya mata mugunta kuma ya zauna yana mata dariya.kwafa tayi tare da galla masa harara.dariya ya karayi, yakara nuna mata bakin shi ya mata alaman kiss.a zuciye ta mike tana cewa"ammi bari in shirya zan tafi islamiya"bata tsaya jin amsan ammi ba tayi gaba.raka ta yayi da ido yana dariya.
Juyawan da zaiyi yaga abba na kallon sa,sukuyar da kai yayi yana sosa keya tare da in ina sai kame kame yake, da yaga bazai fitar da shi ba shima tashi yayi ya fice daga parlourn gaba daya.dariya abba da ammi suke,abba yace swthrt ina ganin gata da muka saka date din bikin nan a kusa if not yaran nan?hmmmm"yace yana girgiza kai.ammi tace"ni da nake tare dasu kullum ina ganin drama kala kala,sai kauda kaina nake inyi kaman ban harbo jirgin su ba".
A bakin gate ta tarar dashi yana zaune a bencin bamodu mai gadi,suna hiran su da yaran kanuri.lbr mai ban dariya ba madu yake bashi dama shi ba dai surutu ba.shiko sai kyalkyala dariya yake.ko inda suke bata kalla ba a zuciyar ta tace da alama daga kyauye daya abba ya dauko su.
Da kafa take tafiya saboda islamiyan nan kusa ne bayan layin su dan haka bata daukan mota.
Tana cikin tafiya taji ta bayan ta ance"hi yam mata ji mana"a masifan ce ta juyo dan taga wani dan rainin sence din ne da yake mata magana a cikin anguwan su.a iya sanin ta duk guys din anguwan shakan ta suke,wasu dan kudin babanta.wasu kuma saboda rashin mutuncin ta yasa bada kula ta.
Arba tayi da kyakkyawan fuskan sa asual yana mata murmushin sa mai kara masa kyau.wara ido tayi ba shiri ganin shine ya biyo ta,shima wara mata idon yayi yace"ya kika fasa masfan?ko da yake kinga mijin ki dole ki nutsu".
Zataui magana ta fasa,ta juya ta kama tafiya sauri sauri,"hey easy mana,kar kije ki karya kafa ko kin manta hills ne a kafan ki"bata kula shi ba,duk yanda yaso tayi magana taki.har bakin gate din islamiyan ya rakota sannan ya koma.
Duk da anguwan nasu na masu kudi ne ba mutane sai daddaya.wayanda suka gansu tafe yana mata magana kuma bata mishi rashin mutuncin da ta saba ba.sun jinjina mishi kuma ya ciri tuta koda yake shima ya hadu koma ace ya fita haduwa.dalilin da yass taki kula shi kenan kar yan anguwan su su rainata.(nace toh su farhat abi a hankali dai).
Cikin tashin hankali ta kira frnds din ta akan su zo gida su same ta,tana cikin Matsala.nan ko sukace gasu nan zuwa.bata taba daukan zancen bikin da muhimmanci ba sai yau da taji ammi tana waya da kannen ta mata 2 game da bikin kan gobe zasu wuce da babbar yayar su zainaba zuwa dubai dan yi mata sayyan kayan daki dana kitchen.kuma taji yayar abban ta ba gaaji zata zo gobe ta tafi da ita gidan ta dan gyaran amarya.
Sai bayan azahar suka samu karasowa suma cikin tashin hankali dan sun san abinda zai sa farhat sanyi haka ba karamin abu bane.
Tana kwance idanun ta a rufe suka shigo suka same ta,ramlat tace"ba dai bacci kike ba star,ko baki da lafiya ne?"tashi tayi ta zauna idon ta duk ya canza kala zuwa ja."subhanallah wai beb meke faruwa ne?kin bar mu a duhu"rukky tace tana zama kusa da ita.nan ta kwashe abinda yake faruwa ta fada musu.ramlat har da dan ihun murnan ta,tace"kice ke dama kan ki kikayiwa tanadi shiyasa in na nuna kulawa ta a kanshi kike jin haushi"kefa wata banza ce when it comes abt boys sam baki da tunani.in ba haka ba ina ni ina wannan banzan"farha tace tana huci.Ruky tayi ajiyan zuciya tace"ni a ganina star ba abun tada hankali bane,tunda yabiyo tanan kema ki nuna mishi ruwa ba sa an kwando bane.kiyi amfani da wannan daman kiyi ta gasa mishi aya a hannu.in har kika bari ya ganki haka,zai ce kin tsorata da game din kar ki yarda yayi winning a kanki.kuma mu zamu baki tips na yanda zaki wana shi sosai yasan lalle yayi kuskure da ya taro wasa dake".
Haka suka zauna suna ta bata shawara da karfin guiwa,har taji yes zata iya.daga nan kuma suka fara tsara yanda bikin zai kasance.
[11/30, 8:31 PM] Ummee Yusuf: π₯π₯π₯π₯πΉπΉ
FARHAT
π₯π₯π₯π₯πΉπΉ
Written by ummee yusuf(maman yusuf).
Page 23~24
Ana sauran 10 days biki ammi da kanwar ta sukaje dubai danyi mata kayan daki dasu kayan kitchen.itama a ranan yayar baban ta tazo ta wuce da ita dan gyaran amarya.farhan shima ya koma can gidan yan uwansa da suka zo saboda biki acan dambuwa road. dan haka basu kara haduwa ba kowa harkan gaban shi yake but farhan yana nan yana fama da missing dinta amma haka yake ta