Showing 27001 words to 30000 words out of 47989 words

Chapter 10 - NI DA GIDANA Complete Hausa Novel

15 Jul 2025

4143

iya furuci ne, ban da a aikace.

Banyi zaton za'ta kai mu da nisa haka ba, domin zatona duk wata d'awainiyar aure zai bani damar nayi masa, iyakaci ya k'aurace min, tun da baya Sona.

Komai kenan bazan yi ba, hoto zan zama.

Gaskiya da sake. Na dad'e a daren ranar ban iya samun bacci ba, ina tsara salo salon yarda zan fitowa Yariman kawu na, mai wuyar Sha'ani da tsadadden samuwa.

Idan yasan wata ai baisan wata ba. Nayi wayewar sanin komai, da iya komai. Zan fito masa duk ta inda bai zata ba. Kuma cewar da yayi na rink'a kallon'sa a matsayin Kawu Sulaiman zan kuwa fitine shi, duk shagwab'a da tab'arar da nake yiwa Kawu Sulaiman tun ina yarinya, har girmana zai shata salo salo, bashi da k'orafi ko sababi, idan yayi zance ai shi yace na rinka kallonsa a matsayin kawu na, zan ce shi yaja, tun da shi ya ban damar hakan, sai duk a binda zai faru ya faru.

Da ace ban riga na aure shi ba, ya furta min kalaman nan, to tabbas zan yi zuciya na barshi. Amma tun da yayi saken da igiyar aure ta sark'emu, to wallahi bazan hak'ura da shi ba, Sai inda k'arfina ya gaza.

Bani ba, ko wacece ma a binda zatayi kenan, in dai ta samu nasarar mallakar miji irin Ancle Fa'iz. Baza ta yarda ta canza shi da wani ba sai dai tayi k'ok'arin canza shi zuwa ga yarda takeso, idan zata iya, Ko taci layar hak'uri ta
zauna da shi da halinsa.

A ranar dai nayi ta bak'i amma yawanci k'awayena na jami'a saboda su na gayyata a yinin biki na, saboda bana son tsofaffin k'awayena na secondry su san na auri malam Fa'izu, terere za'ayi tayi, ana kwazawa.

Daren ranar Ancle Fa'izu ya shigo falona, amma ba muyi hira ba doguwa. Duk yarda naso ya saki jiki ya jima yak'i, ya kawomin uzurin wai a gajiye yake, na kuma karb'a. Ko minti biyar bai yi ba, yayi min sai da safe ya wuce d'akin sa.

Da safe na a jiye bak'unci gefe d'aya, tun da nayi sallar a suba ban koma ba. Ancle Fa'iz nema ya tasheni sallar a suba bai san nima gwanar tashi bace k'arshen dare nayi nafilfili har zuwa a suba, to Sai yazo ya tarar dani zaune Ina lazumi, Sai ya juya.

Tare muka Shiga hada hadar girkin safe da su Khairat, duk da Khairat tayi tayi na bar aikin sayi nak'i.

Ta hak'ure, Sai gashi muna aikin tare cikin armashi, har 'yar hira mu keyi. Ita kuwa Muhibbat baya ga gaisuwa bata sake cemin komai ba. Bayan miskilanci, ma da
naga tana fama dashi da jin kai ainun, ko irin yanayin yayan tane da ita ban Sani ba. Amma shi Ancle sanadin aure ya d'an sauya,tun da har yana 'yar hira dani. Ta yiyu ita ma ta sauya idan an Kwan biyu, amma fa a zatona.

Muhibbat dai tafiyar ta tayi ta barmu da aikin, kuma na lura sanadin zuwa na ne. Khalifa ne ya lek'o kichean d'in ya soma yiwa Khairat Maganar ta dafa masa ruwan wanka idan ta gama.Sai kuma yayi Jim, da ya ganni, in da ya sake bina da mayataccen kallo, Sannan ya miko gaisuwarsa gareni.

Na amsa da sauri na kau da kai na ci gaba da a binda na keyi. Zuciyata bata sak'amin komai ba, game da Khalifa, Kawai banajin dad'in kallon da yake yi min ne, ko santaran nake babu aure. Ban Sani ba, ko shi kuma tasa d'abi'ar Kenan, ko kuma wani k'uduri ne a ransa. Amma yaya zanyi, tun da k'addara ta cilloni gidan'su.

Bayan ya tafi, Khairat tace .

"Yaya Khalifa ya cika matsawa mutane idan yaga a na aiki. Da da wutar nefa ma Sai na jona masa a Heater ko electric cooker. Amma tunda yaya Fa'izu ma zaice na dafa masa ruwan wanka, Sai kawai na had'a musu wuri guda." Nan nasan itace ke yi musu hidimar komai shi da khalifa, nasan zuwana kuma bazai Ancle Faiz ba zai sauya hakan ba.




_This is just the begining👌🏻_









_Taku_


_Zainab ilyas mazawaje_


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe




*NI DA GIDANA*



_Zainab ilyas mazawaje_


_Best brilliant interlligent writer_... 🖋️










*page 13*




Nace da Khairat, bayan tafiyar khalifa. "Bari na d'ora musu a gas cooker d'ina, idan yaso sai ki d'ebarwa khalifa nasa, kin san yanzu ruwan sanyi ba zai zububa a jiki, dole sai an d'an dafa, tun da da ragowar sanyi, tun da kuma safiya ce, kije kiyi shirin makaranta, kar ki makara, naji kina tambayar lokaci, na k'arasa soya dankalin."

Tace "Gaskiya kam. Kin hutashsheni ma, na gode Anti Sumayya. Dama na kusa latti wallahi, wannan yaya Khalifan zai sake b'atamin lokaci. Na gode."

Nace. "Kai Khairat, ina a bin godiyar, ai an zama d'aya."

Cikin mintina kafin ta shirya, na dafa ruwa, ta mik'awa Khalifa nasa.

Ban bata na Ancle Fa'izu ba, nace na a jiye masa, duk da na fahimci ita ke yi masa wannan aiki, ba kuma fasa bata zai yi ba na sani saboda baya son na yi masa hidima kowacce.

Ni kuma na Hak'k'ak'e aikin ya dawo hannu na duk runtsi.

Da na gama na zuba komai a mazubin da ya dace. Daga Sama na jiyo muryar Momi, nan nasan ta tashi Kenan.

Na nufi benen domin na gaishe su har Abban.

Amma gyaran muryar Abban da naji yana saukowa daga benen na dakata.

Saye yake da babbar riga babu ta ciki. Nan nasan iya k'ofar gida zai fita.

Na tsuguna na gaisheshi. Cike da farin ciki sosai ya amsa, ya tambayi lafiyata da yarda na kwana. Ya sake jero adduoi masu kyau
gareni kamar rannan.

"Allah ya shi albarka, ya baku zaman lafiya 'yata." Ba kad'an ba naji dad'in addu'ar nan tasa. Ko ba 'ace ba,kana ganin sa kaga mutumin k'warai mai karimci. Fara'a Kam a fuskar sa kamar gonar auduga.

Nasa kai da nufin d'aga labulen mai kauri da ba'a ganin na ciki, na tsinkayi maganganun, kuma farko Sunana naji an kira, shine dalilin da gabana ya fad'i na kasa shiga, in da maganganun suka yi ta tururuwar shiga kunne na.

Muryoyin Khalifa ne da momi.

"Sumayyan ai babu laifi Itama Khalifa.Tana da hankali da nutsuwa ga alamu ga ladabi. Gashi tana karatu, amma banga alamun wayewar banza a tare da ita ba kamar wasu."

Yace.

"Momi, bafa a saurin yabon d'an kuturu, Sai ya mutu da yatsu."

Ta karb'eshi.

"Haka ne Khalifa sai ya mutu da yatsu."

Ya sake cewa.

Momi, ni fa tun kafin ma na ganta na tsaneta. Da na ganta Sai nafi tsanarta. Kallon k'urillama nayi tayi mata, domin naga me Yaya Fa'izu ya gani, a jikinta har ya zab"i auren'ta, amma bangani ba, ba kalar auren sa bace ma ko da a kaddarar aure.
Momi kuma naga mai kafirin wayoce fa yarinyar nan, da iya kissa, daga zuwa har ta zama 'yar gida?anya bazata d'auke miki hankalin d'aba a gaba?".

Da bata ce komai ba ya zarce.

"Momi amma fa Yaya Fa'iz ya kwafsa, kan a bu kad'an yayi wani auren huce haushi, kodai k'arawa kai haushi, tun da na tabbatar Salima kad'ai yake so a duniya. Laifin mominta ai
bai kamata ya shafeta bako?".

Nan momin tace.

"Shima ai ba Salimar yayi nufin b'atawa ba, nufin sa na kan mamanta, amma dole ita zata fi kowa jin ciwon hukuncin da ya zartar na yin aure.Nasan labarin bai same ta ba, tun da kaji shiru.Amma dai ya aikewa da iyayenta katin d'aurin aure, ta yiyu bata ji ba.Nima banji dad'in a binda yayi ba na zartar da hukuncin yin aure, a matsayin ramuwa. Nafi son sa da Salimar sau dubu. Babu yarda banyi ba, na hanashi auren nan, amma ya dameni da magiya da lallami, kullum har Sai da na
saduda.
Ni kunyar had'a ido nake da Salimar ma wallahi. Yarinyar da take mutuwar son'sa, duk in da d'an uwan sa yake, Sai da ta nemi Sani. Bata gajiya da yi mana d'awainiya, jikinta bai huta ba, haka ma kud'inta. Amma a ce sakayyarta kenan? Gaskiya Sai yanzu nake jin ciwon auren ma, bayan anyi. Ko a waya kunyar mu gaisa nake ji. Kasan kusan kullum tana bugowa ta gaisheni."

Khalifa yaja dogon tsaki.

"Dole ma yarinyar nan tabar gidan nan Momi, dole ya sallameta, ko bai shirya ba."

Momin tace"Wani irin furuci kake yi Khalifa? Kai kake auranta, ko kana da wani k'arfin iko ne a kan mai auranta? ai babu maganar dole, tun da Shima ba sonta yake yi ba, yarda na fuskanta , kama hutar da kanka. Idan d'an koli yaci kasuwa, ai gida yake komawa ko?".

Khalifa yace. "Haka ne Momi. Ni dama babbar damuwata, kar ta ritsa dani. Saboda Salima tace za'ta samomin babban aiki na acounter a kamfanin babanta. Kinga idan auren ta da Yaya Fa'izu bai yiyu ba, taji yayi auren nan, yaya kike zaton makomata Momi? ni za'ayiwa buk'ulu fa. Ai dole na shirya
Munak'isar da zai saki yarinyar nan momi, idan naga bashi da niyyar sallamarta da wuri."

Ban tsaya naji me momin zata ce ba, na juya a hankali na sauko, saboda idan na Shiga za'su tsargu. Idan kuma na ci gaba da tsayuwa, za'su iya fitowa su ganni.

Nayi zaune a d'aki, damuwa duk ta baibayeni. Maganganun Khalifa su sukafi zafafa k'wak'walwa ta. Bansan zan fuskanci Wata matsala ba kuma a gidan, bayan ta b'angaren Mijina da nake tunanin ita kad'aice da zan ji da ita.

To A she bayan matsalar da nake da ita ta Mijina, duk gidan ma Ina da matsala da su, babu mai yi dani a she duk sun fison Mijina da Salima. Gaskiya naga Muhibbat Sai wani fizga fizga take min. Momi farin cikin Ancle, Fa'iz tace ta fison Salima sau dubu dani. To ko iya nan matsala ta ta tsaya, ai da aiki gagarimi a gabana. Ancle baya had'a kaunar momin sa da ta kowa. To ni kuwa da wanne zan soma? ta Ina zan fara? da yaya zan soma warware matsalolin da suka yi min k"awanya hagu da dama?.

Duk da wad'annan matsaloli dake gabana, amma domin k'arfin hali wai b'arawo da sallama, Zuciyata Sai rad'amin take da cewa.

Sumayya karki kaya, ba"a sanin maci tuwo, Sai miya ta k'are, kuma mai zabarin nema, yana tare da nasara, wataran, musamman mai nagarta.

Ni dai nasan, bawai nacin son Ancle Fa'iz ko ya soni, shine babbar matsalata ba. A ra'ayina, a tsarina, babu a binda nak'i jini irin a ce nayi aure ya mutu, Sannan a ce ma ban dad'e ba. Sam! ban shiryawa Zaman zawarci ba, ban kuma shiryawa amsa sunan bazawara ba. Domin Muddin wa'adin aure na da Ancle Fa'izu ya cika ya sallameni, ban isa na goge tambarin sunan bazawara a goshina ba.

Nasan samarina ma zasu samu labari, suyi min dariya, musamman Usman, da ya tab'a yab'amin magana da karin magana, yace wai k'arshen a lewa dai kasa ce, suna nan suna zuba ido kuma, suga k'arshen'ta.

Shi zaton'sa wani mai iko sosai na samu na barshi.

Bayan wani lokaci, na koma na gaishe da Momi. Sam banga wani sauyi a tare da ita ba, sai ma bangajiya, da tayi min, da cewa, wai taji nice jigon aikin komai, na karin kumallon ranar.

Khairat dama ita ta kwashe komai, ta kaiwa kowa. Nima har d'aki ta biyo ni dashi.

Tace min.

"Anti Sumayya, na tafi makaranta. Fuska ta cike da fara'a nace
"To, a dawo lafiya, K'anwata.

"Khairat, ita ce na tabbatar tana k'aunata da zuciya guda. Kuma nima ta shiga raina, tashi d'aya.

Har lokacin, banga Ancle Fa'iz ba, ya fito daga d'akin'sa ba. Bacci yake ko menene, ban Sani ba. Kamar na Shiga na gaisheshi, na kasa.

Na had'a ruwan wanka mai zafi dai dai dai, nasa turarrurukan wanka, na rufe da murfin babban bokitin wankan,mai kyau.

Sai da na gama shiryawa, na zauna a falo, Ina karyawa, Sannan na jiyo muryar Ancle Fa'iz shida Khalifa a tsakar gida suna magana. Nan nasan a she Khalifa, ba fita yayi ba. Kafin na farga naji sallamar Ancle Fa'iz. Amma daga bakin K'ofa ya coge, muka
gaisa.

Nace.

"Ancle ga ruwan wankan ka can na kai maka toilet. Nan naga yayi dan jim, kamar bazai ce komai ba. Ni kuwa nasan shammatar'sa nayi, shi yasa na sashi a kwanar nazarin yarda zai yi da katsalandan d'in da nayi, na binda bayaso nayi. Wato yi masa d'awainiya ko Wacce iri.
Nace.

"Ancle, Fa'iz kajini kuwa?".

Yanayin sa kamar amsar rashin bukatar hakan zai nunamin, amma sai ya canza niyya, ta yiyu nauyin ya wofuntar da kyautatawar yayi, ko kuma wani dalilin ne.

Ya shafi, kyakykywar
bak'ar sumar'sa da take a kwance ta soma fesowa, daga askin da yayi mai suna SKIN, da yay masa kyau kuwa sosai.

Yace. "Naji ki Sumayya."

Daga haka bai sake cewa komai ba, ya tafi. Nasan da bai a mince ba, zai fad'amin ba ya so, tun da bashi da rufi, ko alkunya.

Naji dadi kuwa sosai da bai gwasaleni ba.

Ranar nayi bak'i sosai. Baba Talatu da Hajiya mariya suka fara bud'e fage. Da Tsokanar wasa na tarbesu nace.

"Ku kuma tsofaffun nan Sai yau za ku gamo kai, Ku ringid'o kuzo? Ko ku lek'oni jiya? Kuma naga duk mazajen nan ku ai naga duk sun tsofe, babu sabon jini, sun zama jagwal, ballantana kuce tarairayar'su tasa kuka kasa lekoni jiya kuka shantake".

Baba talatu tayi jagale tana kallona na shegantakar da nayi musu, nasan kulla kalmomin daukar fansa ta tsaya yi.








Taku a kullum_

_Zainab mazawaje_

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe


*NI DA GIDANA*





_Zainab mazawaje_


_Best brilliant interlligent writer...✍️_





*Page 14*




Hajiya Mariya tayi 'yar dariya tace.

"Shak'iyyar wofi. Kwana biyu dai munji kunne, da kika yi gaba, yanzu kyayiwa mijinki kuma."

Baba Talatu, tace"Sa'a ma kika yi muka zo yau. Dama idan dad'i yayi wa Mutum yawa, Sai yace Allah kasheni na huta. Da Kawunki Sulaiman cewa yayi, kar muzo, a bari an d'ebi lokaci tukun. Kakan kine, ma yace sai munzo mun duba masa ke lallai, duk da dai bake kad'ai bace ma a gidan, ko menene ai da wasu, amma shine za kiyi mana godiyar mayu ko?".

Naji nauyi, na saddakai k'as nace kuma.

"Yaya Kawuna yake?".

Baba talatu, tace.
"Dama nasan shine a layin farko. To Lfy Lau yace a gaisheki da kyau."

Na yi murmushi kuma nace.

"Allah sarki tsoho mai ran k'arfe, yaya yake, kina kulamin da shi kuwa? (kakana). Tace

"Tace.Ko ke albarka.Lfy Lau yake, yace na gaisheki."

Hira sosai muka yi, daga bisani, na kaisu
wurin Momi. Momi ta karb'esu da daraja kam, suka yi tama hira, har Hajiya Mariya tace da Momi. Ina Angon yayi, bamu ganshi ba?".

Momi, tace. "Sun tafi ziyarce ziyarce, shida Khalifa, d'azu. Tace"Ai nayi zaton jin za muzo ne, ya waske, gudun kar muzo muyi masa d'iban Karan mahaukaciya,saboda ya Samu, Sabuwa, ya ya damu gefe."

A kasa dariya, a tare.momi tace cikin dariya. "Ina zai ya daku, ai da tsohuwar zuma ake magani, kuma da sabon gini gwara yabe".

Hirar barkwanci tsoffin nan sun Shashi da Momi. Hakan yay min dad'i kam, sosai. Nuriyya tazo a ranar, kuma da ita muka yi ta tarben bak'i har girke girke, duk da momi ta aiko da nata daron tace a bawa bak'i.

A Sati na na d'aya a gidan, Ina zaune gaban mudubi Ina taje kaina, Wanda yasha washing da retourching, yana ta shining ya kwanta lamb'am. Ba kuma wani tsawo ne da shi ba can, iya saman kafad'ata yake tsayawa. Ina kuma alfahari da a bina a hakan.

Half vase ce a jikina, da under wear na siket iya gwiwa, domin kwalliya na gama nasa turarurruka na jiki, zan saka kaya na kenan, naji an banko k'ofa da sauri, an shigo. razana nayi, bawai ga yanayin under wear kawai
dake jikina ba ma, saboda nasan babu mai iya shigomin d'aki kai tsaye haka ba, domin ko Ancle Fa'iz mijina iya kacin'sa falo, bai tab'a Shiga cikin d'akina ba.

Wanda na yanke tsammanin zai shigo, shid'in ne ya shigo.

Ancle. Sau d'aya ya dubeni, sai naga ya yi saurin juyar da kai, ta yiyu yanayin da ya ganni ne bayaso idanunsa su sake sauka a kai. Da ya shigo ya wuceni ya isa kan gado, ya zauna.

Na Samu sauk'in razana, ganin shine. Naja dogon Hijab na sallata nasa da sauri domin bansan me yake faruwa ba, na sake kai duba gareshi, cike da Mamaki. Da ganin'sa kasan daga wanka ya fito. Silk d'in sumarsa da bata taru da yawa ba, jik'e take da ruwa. Zulaika ce gajera a jikin'sa, da towel fari, sol, da ya sak'ala a kafad'a.
Nace. "Lafiya kuwa, Ancle?" .

Kafin yace komai, k'ofar d'akin da take a bud'e ya tashi ya jawo ya rufe. Sannan
Yace.

"Mutum, domin ya shigo d'akin matar'sa laifine?".

Na girgiza kai.

"Ko kusa, my Ancle. Gani nayi baka tab'a shigowar bane"

Yace. "To, yau na shigo, then so what?".

Nayi shiru, Ina kallon'sa.

Ya sake zama kan gadona, ya cire towel d'in da ya sagala a kafad'a ya ajiye gefe.

"Sumayya, wani a bune ya faru, nake so, Kije falo ki zauna, ko da Momi ta aiko kirana, kice bananan".

Toh! wata Sabuwa Inji 'yan caca. Kallon da nayi masa galala, yasan tambayace zan masa na dalili, ya katseni.

"Karki tambayeni dalili. Just ki aiwatar, kyaji komai daga baya. Yanzu babu lokaci, kiyi sauri Kije" .

Na ja zani zan d'aura, kasan Hijab yace. "Kisa kayanki mana, tun da kin d'ebo. Kiyi sauri amma".

Bani da zab'i face bin umarnin'sa da nasan zai iya jefani a matsala babba, idan a kasamu kuskure a ka gane gaskiya. Amma k'arya kuma ba'halin Ancle Fa'iz bace, ko mai amfani ce. Tun da yau yayi kuwa, nasan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login