Showing 78001 words to 81000 words out of 93605 words

Chapter 27 - GELLE ƁINGEL COMPLETE BY UMMU NASMAH

15 Jul 2025

3387

Mamma dai ba dawowa zatayi ba kaga daga ita sai Zizah sai suyi abinda suka ga dama.

" hmmm!!! Shikenan Bro Allah ya bani ikon cinye jarabawa ta, am Anya kuwa Momy zata yarda ka tafi Aunty Zarah gani nayi itace ta hanaka sauya gida bana tunanin zata yarda."

Murmushi Ya khalil yayi tare da cewa.

" Ta ma yarda ai an gama, domin kuwa munyi Magana da ita tace ba damuwa muje."

" Okay Allah ya kaimu."
.
Yayi Maganar yana sauƙe numfashi, sun juma suna hira har akayi sallar magaruba, bayan sun idar ma zama sukayi sanda akayi isha'i kafin suka rabu Shetima da Khabeer suka zo suka ɗauki Ya Garkuwa zasu masa rakiyar ɗaki sanda ya tsaya a hanya suka sayi gasasshiyar kaza da fresh milk sannan suka tafi Shetima na famar tsiya yake masa.

"Kee!!! Wai mijin naki bazai dawo bane kam, ni fa na fara gajiya 9:30 har yanzu ango bai shigo ɗakin Amaryar sa ba, bana son dare yamin banje gida ba, kinsan na cewa Abba yau zan dawo bana son yamin faɗa, yawwa wai nikam anya kuwa kin sanar da ƙawarki bikinki Safreena maman Abdul."

Da sauri Jummo ta ɗago kanta tare da dafe goshinta ta ɗauki salati


" Ya Allah!!! Kai wallahi bani da kirki ko jiya ma naga miss Call ɗinta wallahi ban sanar da ita ba, kwana nan bani da sukuni shiyasa na manta da ita itama kuma bawai kirana take ba sai afi sati biyu bata kira ba sai randa taga dama zata kira amma dai koma menene dai ya kamata na sanar da ita bikina, insha Allah gobe da safe zan kirata yanzu dare Ya fara."

" Gaskiya ya kamata ki faɗa mata, tana sonki kuma da alamu ita irin matan nan ne wanda basu damu da shiga Rayuwar mutane sosai ba, kuma kina kallon idanunta zaki fahimci tana tare da wani ɓoyayyen lamari amma........"

Sallamar su Ya Garkuwa itace ta kana meenat ƙarisa Maganar da tayi niyya, amsawa tayi suka ƙaraso a bakin gado ya zauna su Shetima na tsaye cike da tsokana Meenat tace.

" Au ashe dai zakazo ai nayi zaton sai gobe ne zaka shigo, tunda Gashi dai dare harya tsula."

Dariya khabeer yasa tare da ɗaurawa da cewa.

" Shi wannan uban zumuɗin ne zai iya bari sai gobe, ai kuwa ya dinga sambatu kafin gari ya waye domin ba haƙuri garesa ba."

Dariya Ya Garkuwa yayi tare da cewa.

" Kuyi sauri ku gama Maganar ku tafi, ko kuma na koreku na rufe gidana."

Zaro idanunta Meenat tayi tare da cewa.

" Eyyye!!! To ku tashi mu rufawa kanmu asiri mu tafi kafin ya koremu, ni dai ga AMANAR ƙawata na baka dan Allah a riƙe Amana Allah ya baku zaman lafiya."

Da ameen Dukkan su suka amsa ita dai Jummo kanta na ƙasa, suma su Shetima Sosai suka yiwa Garkuwa nasiha irin na abokai kafin ya rakasu suka tafi, ya bawa mai gadi UMARNIN ya rufe gidan ya juya zuwa ciki.

Kusa da ita ya zauna tare da saka hanunsa ya kamo hanunta, da ɗayan hanun ya ɗaga hijabin da ta ruhu dashi, yana murmushi yace.

" Alhamdulillah godiya ta tabbata ga ubangin daya bani ke a matsayin mata, ina farin cikin Kasancewa dake waje ɗaya Jummo Allah ya bani ikon riƙe amanarki, ina cikin farin ciki yau."

Murmushi Jummo tayi itama ba tare da tace komai ba haka kawai yanzu kuma take jin kunyar Ya Garkuwa, murmushi yayi ganin bata da niyyar Magana yace.

" Dear yau kuma kunyata kikeji hmmm!!! To tashi muje muyi alwala muyi Sallah mu godewa Ubangijin mu."

Da to Jummo ta amsa tana miƙewa tsaye, ta nufi tollet yana nan zaune tayi alwala ta fito, shima shiga yayi yayi tasa alwalar sukayi nafila raka'a biyu, bayan sun idar ne ya kama goshinta yayi mata addu'o'i sosai, Ya Garkuwa sosai ya yiwa Jummo tambayoyi game da addinin ta, yasha mamakin yanda ta amsa masa dukkan tambayarsa, tashi yayi tare da ɗauko ledar daya shigo da ita da kansa yaje kitchen ya ɗauko plet ya juye kazar duban Jummo yayi yace Bismillah.

" Girgiza masa kai tayi a hankali tace.

" Na ƙoshi."

Murmushi yayi yace.

" Ina ai baki isa ba dole sai kinci kazar nan dan nasan babu abinda kikaci."

Yayi Maganar tare da haɗe fuska, duk gardamar Jummo sanda ya Garkuwa yasa taci kaɗan bayan sun gama da kansa ya fitar da plet ɗin sauran kajin kuma ya saka a frich dawowa yayi ya buɗe wadrop ɗinta ya ciro mata sleeping dress wata ƴar ƙarama, ya ajiye mata tare da cewa.

" Ki shiga tollet kiyi wanka, ki saka wannan kayan bari naje ROOM ɗina."

Bai jira yaji mai zata ce ba ya fice, Jummo rigar ta ɗaga tare da taɓe bakinta a zuciyarta tana furta wannan rigar kuma kamar ta arna zansa, tashi tayi ta ɗauki kayan ta shige tollet, wanka tayi ta saka kayan tare da saka katuwar hijabin ta, ta fito mirror taje ta feshe jikinta da turare tare da humra lungu da saƙo na jikinta kwanciya tayi ta duƙunƙunu bata juma ba bacci ya ɗauketa.

Ya Garkuwa bai shigo room ɗin ba sai sha ɗaya da rabi, tana kwance tana bacci cike da nutsuwa, murmushi yayi tare da saka hanu a hankali ya cire mata hijabin lumshe idanunsa yayi yana ƙarewa yanda sleeping dress ɗin ya mata kyau, kamar dan jikinta aka yisa, suffar jikinta duk a waje fuskarta ya shafa tare kai mata kiss a lips ɗinta, murmushi yayi ya shafi fuskar tata, hanu ya saka ya jawota jikinsa tare da mannata da jikinta hanunsa na yawo a bayanta, Jummo kamar cikin mafarki take jin ana wasa da jikinta wani irin miƙar daɗi take cikin barci, hanu yasa ya buɗe botin ɗin rigar ya cire mata shi, breast ɗin ta ya zubawa idanun a hankali ya kai bakinsa, jin abin na neman wuce gona da iri domin kuwa ji take kamar ana tsotson breast ɗin ta, a hankali ta buɗe idanunta ɗan zaro idanunta tayi tare da ƙoƙarin turesa zata miƙe ya zuba mata nauyinsa a jikinta yana girgiza mata kai idanunsa sunyi jajur sha'awarsa ta bijiro dama Garkuwa ya lafiyar kura, cikin sarƙaƙƙiyar muryar sa ya ce mata.

" Karki min haka Jummo karki haramta min abinda ubangiji ya halatta min, idan banji daɗi a jikinki ba, a ina kike son naje naji, kina son nayi zina ne bayan ina dake wacce Ubangiji ya halitta min, karki zamo irin matan da Allah ke fushi dashi saboda toyewa mijinta haƙƙin shimfidar sa."

Sosai jikin Jummo yayi sanyi, tare da sakar masa jikinta, ganin haka yasa nima ficewa domin bazan tsaya ganin abinda yafi ƙarfin idanuna ba.


Kiran sallar farko shine ya tashi Ya Garkuwa daga nannauyan baccin da yake mai cike da nishaɗi, Jummo dake kwance saman ƙirjinsa ya duba wanda take baccin wahala fuskarta kwance da bushashshan hawaye na azabar da taci daren jiya, cike da so da ƙauna ya manna mata kiss a fuskarta tare da furta.

" Na sameki yanda nayi tsammani harma kin zarce haka tabbas ina alfahari dake a matsayin mata kin kawo mutuncin ki, wanda yake matuƙar wahala a wajen ƴan a wannan zamanin na godewa Ubangiji da bai jarafceni ba saboda zunubin dana aikata"

ya ƙarisa Maganar a hankali yana zameta daga jikinsa ya saka kanta saman filo tare da jawo mata blanket, tashi yayi ya shige tollet wankan tsarki yayi tare da yin wanka yayi alwala, ya fito ya hau sallar nafila yana godewa Ubangijinsa da arzikin matar da ya masa sanda aka kusa shiga sallar asuba sannan ya miƙe yaje ya haɗawa Jummo ruwan zafi kitchen yaje ya ɗebo kishiri kaɗan a hanunsa ya zuba cikin ruwan tare da fitowa yazo ya ɗaga Jummo caɗak dake bacci ba tare daya tashe ta, domin kuwa yasan zata masa gardama, cikin ruwan ya ajiye ta, a firgice ta buɗe idanunta tana runtse idanunta tare da cije baki, zata miƙee ya dannata cikin ruwan yana riƙe da kafaɗarta, Jummo kuwa sosai take jin azaba a ƙasanta gashi ya danneta ba halin tashi, idanunta ta runtse tun tana jin azabar har ta fara jin ruwan ya fara mata daɗi jin ta sake jikinta yasa Garkuwa fahimtar ta daina jin zafi sakinta yayi tare da raɗa mata a kunnenta.

" Sorry Dear"

Ya miƙe ya rataye mata towel tare da ficewa daga tollet ɗin, zanin gadon ya yaye tare da ficewa dashi, ya dawo ya shimfida wani, harya gama ya fita Sallah Jummo bata fito ba, ko kafin ya dawo Jummo ta fito ta saka kayanta har tayi Sallah ta koma bacci, shi kuwa bai shigo gidan ba har sai da gari ya fara haske, tana kwance tana bacci, murmushi yayi shima ya kwanta tare da jawota jikinsa, bacci ne mai nauyi shima ya ɗaukesa, sune basu farka ba har sai wajen 11:10am nan ma ya Garkuwa ne ya farka falo ya fito turus ya tsaya ganin Zizah tsaye ta na zaune cikin kujara.

" Zizah yaushe kika shigo gidan nan?"

Ya jefa mata tambaya cike da mungun mamaki yana duban falon yanda akayi mopping aka gyara ko ina har turaren wuta aka kunna kuma shi dai bai ɗauki ƴar aiki ba, Zizah murmushi tayi tare da cewa.

" Tun goma na shigo naji shuru shine nace ina ga bacci kuke harma na gyara falon baku tashi ba, abinci na kawo muku."

" Abinci Kuma keɗin waye yace ki kawo mana abincin.?"

Ya jefa mata tambayar cike da tsarguwa, ɗan murmushi Jummo tayi tare da cewa.

" Kai Ya Garko sai tambaya kake min tamkar wata ɓarauniya, ni babu wanda yace na kawo, nine na ce Aunty Zarah ta zuba na kawo muku, ina Aunty Jummon bata farka bane, bara naje na duba ta."

Ta ƙarisa Maganar tana miƙewa tsaye zata shige ROOM ɗin Ya Garkuwa yayi saurin shan gabanta tare da cewa.

" Ke baki da hankali ne, uban me zaki shiga kiyi a ciki, bacci take ki ɗauki gyalenki ki koma gida, na gode."

Zaro idanunta Zizah tayi cike da jin haushi tace.

" Ya Garko korata kake a gidan ka, dan nazo wajenka, Allah ya baka hkr, amma dai zan shiga mu gaisa sai na tafi."

Ta yi Maganar tana ƙoƙarin shigewa tsawa Garkuwa ya daka mata tare da cewa.

" Ba fa na son iskanci, karki kuskura ki shiga ki tashe ta tana bacci ki shige ki koma gida bana buƙatar ki a gidana."

Bakinta Zizah ta cije cike da takaici sanin halin Garkuwa ya sata ɗaukar gyalenta tace.

" Allah ya huci zuciyarka ban san me na maka ba kake korata, ka gaishe da Aunty Jummon ni na tafi."

Tayi Maganar tana ficewa cike da haushi tsuka Ya Garkuwa yaja tare da sawa ƙofar key ya Kitchen ya shiga da kansa ya dafa musu lipton tare da soya ƙwai ya ajiye a daining ya shige ROOM ɗinsa, ko da Zizah ta fita cike da takaicin rashin Nasara ta kira Momy ringin ɗaya ta ɗaga tare da cewa.

" Zizah anyi Nasara, kin ajiye layar kuwa a ROOM ɗin nata.?"

Cike da haushi Zizah tace.

" Momy yau dai anyi rashin Sa'a, domin kuwa Ya Garkuwa ya hanani shiga, ina hango rashin yarda dani a fuskarsa, amma karki damu Momy idan ba'ayi Nasara yau ba akwai gaba, alwashi naci miki sai nayi sanadin wannan Auren kuma zan cika Alwashi na, yanzu zanbi gidan Su Halilah, shiyasa na kiraki."

Momy tamkar zata kurma ihu tace.

" Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!! Kai Garkuwa akwai ɗan durun'uwa nacacce wannan yaron kamar bani na haifesa ba, ba damuwa nasan zaki iya Zizah sai kin dawo."

Tayi Maganar tana katse kiran Zizah shigewa tayi cikin zuciyarta tana ayyana bazata koma gidan Ya Garkuwa ba sai nan da sati biyu.


Ita kuwa Jummo ko da ta farka wanka tayi tayi brush tare da shiryawa cikin wata koriyar atamfa jikinta yasha turare batayi wani kwalliya ba powder ta shafa a fuskarta sai lipstick, ta fito falon tana ɗan ɗingishi a zaune ta samu Ya Garkuwa kusa dashi ta zauna tare da cewa.

" Ina kwana."

Tayi Maganar cike da kunya, dubanta Ya Garkuwa yayi cike da so da ƙauna ya jawota jikinsa yace.

" Wai ke kunyata kike jine, ah to kuma Kunyar me zakiyi wani dare ne jemage bai gani ba, a sai dai daren mutuwarsa, da alamu dai kunyar ce ban gama fitar da ita ba, tashi muje na cire sauran kunyar."

Kafaɗarsa Jummo ta ɗan daka tare da cewa.

" Ni wa yace maka kunyarka nake ji, yunwa nake ji."

Murmushi yayi tare da kwaikwayon muryarta.

" Yunwa nake ji" dukkan su dariya sukayi yace.


" Ga can lipton na dafa na soya ƙwai, muje muyi breakfast, amm Momy ta Aiko Zizah da abinci amma bazamu ci ba gaskiya gara muyi amfani da wanda na dafa."

Kallonsa Jummo tayi tare da cewa.

" Ba zamu ciba kuma, to meyasa, Momy ne fa ta aiko sannan kace bazamu ci ba, gaskiya ni na Momy zanci."

Girgiza mata kai yayi tare da cewa.

" Ba fa zakici abincin nan na faɗa miki, kiyi amfani da wanda yayi da hanuna bana son musu."

" Ha'a My Love ba musu nake ba, baka yarda da Momyn bane.?"

" Eh ban yarda da ita ba, aii uwata ce ko, na kuma fiki sonta tunda nace karki ci, to ki haƙura."

Numfashi Jummo ta sauƙe tare da kallon sa tace.

" Na yadda da ita, kuma zanci, Momy bazata cutar damu ba, dan Allah ka daina zargin mahaifiyarka."







*UMMU NASMAH CE*
[5/29, 4:19 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY*




➰➰ *66 to 67*




" Hmmm!!! Okay Bismillah ga can abincin tunda ina hanaki kina cewa zakiyi, Momy dai uwata ce kuma baki fini sonta ba, na kuma fiki sanin waye Momy, amma tunda kince zaki ci Bismillah."

Ɗan tura bakinta Jummo tayi tare da shigewa tayi gaba abinda daining ta zauna tare da jawo basket ɗin da Zizah ta kawo, Chief ɗin dankali ne da kuma soyayyen ƙwai sai ɗaya plast ɗin mai ɗauke da farfesun kayan ciki, murmushi Jummo tayi kasancewarta tana son farfesun kayan ciki.

" Ya Garkuwa kamar Momy tasan ina son farfesu, zanci abinci na koshi."

Tayi Maganar cike da farin ciki zuciyarta ɗaya, girgiza kansa Ya Garkuwa yayi tare da zama yana jawo plast ɗin ruwan zafin sa, abincin da ya haɗa da hanunsa ya ci bai ci na Zizah ba, ita kuwa Jummo cike da farin ciki ta dinga kwasar farfesun ta, tea ɗin da Ya Garkuwa ya haɗa ta jawo tana kanne masa idanu alamun tsokana ganin ransa ya ɓaci, ta hau shan tea ɗin kauda kansa gefe Ya Garkuwa yayi tare da haɗa wani yasha yana gamawa ya tashi ya dawo falo ya cigaba da kallon tashar alzajira.

Jummo murmushi tayi, tare da jawo wayarta numbern Safreena ta kira ringin ɗaya Safreena ta ɗaga tare da cewa.

" Dukkan mu bamu da kirki, amma dai nace kiyi haƙuri karki min ƙorafi."

Dariya Jummo tayi tare da cewa.

" Maman Abdul, bazama ki bari nayi Sallamar ba kenan, to dai a wannan lokaci nine na miki laifi domin kuwa nayi Aure ban sanar dake ba dan Allah kiyi haƙuri wallahi abubuwa ne suka min yawa kuma gashi ba'a nan akayi bikin ba, a ƙauyenmu akayi."

Shuru Safreena tayi cike da jin haushi sai kuma tace.

" Amma gaskiya baki kyauta ba, nasan da ni ce duk rashin kirki na wallahi bazanƙi sanar dake AURENA ba koda kuwa ba'a ƙasar nan za'ayi ba, baki kyauta min ba."

Ɗan murmushi Jummo tayi tare da cewa.

" Na sani Wallahi ban kyauta ba, amma dan Allah kiyi haƙuri."

" Shikenan ba damuwa ya wuce amarya, yanzu kuna ina kenan."?


" Mun dawo cikin Gombe tun ranar da aka ɗaura Auren, ina nan cikin shango Estate."

" Ayya masha Allah, to Allah ya sanya alkairi ya baku zaman lafiya insha Allah nima zanzo amma sai na dawo daga Egypt saboda gobe nake son zan tafi akwai abinda zai kaini insha Allah ina dawowa zanzo, ya kamata ki buɗe WhatsApp saboda a ringa zumunci tunda kiran wayar yana bamu wahala amma insha Allah kafin ma na dawo zanyiwa Zee Magana zasuzo ita da Abdul suga gidan naki."

" To shikenan insha Allah zan buɗe na gode sosai ki gaishe da yarona Abdul da ƙawarki Zee."

" Insha Allah zasuji na gode ki gaida angon."


" Zaiji na gode."

Jummo ta ƙarisa Maganar tana katse kiran, tashi tayi ta tattara plat ɗin da sukaci abincin ta kai kitchen sanda ta wanke sannan ta dawo falon yana nan zaune inda ta barsa, har yanzu da alamun ransa a ɓace yake."

Zama Jummo tayi tare da kwantar da kanta a kafaɗarsa a hankali ta furta.

" Kayi hkr dan Allah, wallahi bansan ranka zai ɓaci haka ba, da bazanci ba, amma ni a tunanina Momy Uwa take garemu bazata bamu abinda zai kashemu ba, duk ƙiyayyar da Momy take min, nasan kai tana sonka, bazata saka Wani abu a cikin abincin nan ba saboda tasan zaka ci bazata so ka cutu ba, da wannan hujjar naci abincin amma wallahi da nasan ranka zai ɓaci haka bazanci ba."

Hanu Yasa ya rungumota jikinsa tare da cewa.

" Hmmm!!! Na sani Momy uwace garemu, amma a yanda na fahimci Momy a halin yanzu babu abinda bazata iya aikatawa ba, akan ƙiyayyar da take miki, nasan halin Momy zata iya cutar dake ta ko wacce irin hanya koda kuwa nima zan cutu, shiyasa na hanaki ci amma bana fushi dake dan Allah ki dinga kaffa kaffa da Momy tana da hatsari a rayuwarki."

" Bana ɗaukar Momy a matsayin hatsari ga rayuwata amma insha Allah zan kiyaye, akwai ƙawata Maman Abdul munyi waya da ita tace tana gaisheka."

" Ƙawarki dama kina da wata ƙawa ce bayan Meenat.?"

" Ehh akwai Maman Abdul mun haɗu da itane a super market sai dai bata taɓa zuwa gidan mu ba, waya dai kawai muke amma fa tana da kirki Sosai."

Murmushi Ya Garkuwa yayi tare da cewa.

" Yayi kyau ina amsawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login