Showing 15001 words to 18000 words out of 91982 words

Chapter 6 - Dangin Ubana

Milhart   

15 Jul 2025

3878

da shirmen ku babu Wanda yayi tunanin karb'ae jakar sa"

Ma'isha saurin karb'an jakar hannun da tayi tace "Laa sorry daddy wallahi farin cikin ganin sa ne yasa na manta"
Haisam yace "Hakane mummy 2 weeks fa dad baya Nan Dole muyi kewar sa"
"Naji yanzu dai ku bari idan yaci abinci ya samu ya huta sai kuyi hirar taku"
A tare sukace toh.

Karb'an jakar hannun Ma'isha tayi, Ma'isha Tace "Mummy ki bari Mana na kai Masa d'akin sa"
"Anki d'in mijinkine ko mijina?"
Ma'isha hannu tasa ta rufe bakin ta Tace "mummy abin harda gorine Kuma?"
Hararar ta mummy tayi ta bi bayan Daddy da tun d'azu ta wuce d'akin sa.

Zama Ma'isha tayi a Kan couch d'in dake gefen na Haisam bakin sa ya kawo dai dai kunnen ta yace "kinji abinda mummy Tace ko dama maza ki Nemo miji in yi miki aure idan bakya son Gori"

Dariya tayi Tace "Na baka huka da nama yaya ka Nemo min mijin aure na maka alkawarin ko wane ne ka kawo zan aure shi"
"kamar dagaske, confidence d'inki dariya yake bani wallahi kina nufin ko Mai gadi na kawo miki zaki aura? "
"Da gudu ma, ai Mai gadi mutum ne kamar kowa ko?"
"Shikenan tunda kince haka Zaki Sha mamaki."
Dariya kawai tayi suka cigaba da kallo.

Umma ce ta Shigo parlor Tace "Kun samu sana'a ku Kam, a haka za'a samu likitocin?"
Haisam yace "Ai gobe ba school ne Umma Sunday ne fa ranar hutun d'an boko"
" Gafara Chan ka zauna kana kallon zeeworld kamar wata mace"
"Wallahi umma ba laifina bane, laifin Yar kice itace ta koya min Kallo"
"nasan abinda zakace Kenan ai" wuri ta Samu ta zauna suna kallon tare.


Daddy ne da mummy suka fito baka Jin abinda suke cewa Sai dariyar su kawai, Haisam kasa kasa yace "Kin gani ko princess kiyi aure ki Rika samun farin ciki abunki"

"sai na fadawa Daddy abinda kace yanzu"
"a a yi hakuri nayi shiru"
Dinning suka nufa, Umma, Ma'isha da Haisam Suma suka wuce dinning d'in Tuwon shinkafa da miyar kuka mummy tayi yaji daddawa da citta sai nama da kifi da suke ta shawagi a ciki, suna ci suna Hira har suka gama suna gamawa Haisam ya Mike yace "Yau bacci nake ji sosai zan kwanta"
Ma'isha a take ta 'bata Rai Tace "Yaya but kace min zamuyi Kallo tare fa"
"Am sorry Kanwata wallahi a gajiye nake akwai gobe wuni zamuyi muna Hira kinji?"


Bata so hakan ba Dole ce tasa ta hakura yayiwa su mummy sai da safe ya wuce part d'insu Yana tafiya Ma'isha itama tashi ta shige d'akin ta.


Haisam na shiga d'aki ya ban d'aki ya fad'a yayi wanka ya sanya vest da d'an gajeren wandon sa ya d'ale Kan gado ya bud'e datar sa ya Fara chatting, emoji da stickers na kuka ya Fara cin karo dasu Ma'isha ta jero Masa dama yasan za'a Rina Nan ya shiga rarrashin ta suna cikin chat d'in ne bakuwar number ta kirasa.

Yana picking Tace "Haba yallab'ai kasa ina ta jiran ka, nan ne ma ya tuna cewar yace zai kirata dafe kansa yayi yace "Am so sorry Aysha na d'anyi busy ne gafar ce ni"

Murmushi tayi ko ba komai bai manta sunan ta ba, tace "Bakomai yallab'ai Ni da na damu da nayi magana da kai ai na kiraka"
Murmushi yayi yace "Afwan ina jinki"
"ummm dama ba wani abu bane ba, so nake Dan Allah ka Zama Tutor na"
"Tutor dai? 'dan Ni d'in Nan bani da wannan ilimin ai Ni dolo ne fa"
Yar karamar dariya tayi Tace "na amince ka koya min dolon cin naka, duk da nasan Kai ba dolon bane ba sai dai in rowa zaka min Kar na karu da kai sai na hakura"

Murmushi yayi yace "Toh yaushe kike so mu Fara?"
Tace "Ko gobe ma"
"A a gobe Sunday ba inda nake zuwa ina gida, ki dai bari idan muka had'u Monday mayi maganar"

Cikin murna Tace "Toh nagode sosai"
"Bakomai sai da safe"
Ya katse wayar Aysha bin wayan tayi da kallo tace "Mtssw ya katsewayar kamar shi ya Kirani" wurga wayan tayi akan gado ta kwanta ta fara sharar baccin ta dama ta Riga ta shirya cikin kayan baccin ta.


Ma'isha kuwa ganin bai mata reply ba tayi tunanin ko bacci ne ya d'auke sa, ta shiga kiransa Amma busy, ji tayi kamar ta kurma ihu, cikin sanyin jiki ta tashi ta shiga wanka ta d'aura da alwala,bayan ta fito tayi shafa'i da wutiri bayan ta idar ta shiga rokon Allah da ya yaye Mata sayayyar da take Masa in shi d'in ba alhairi bane a gareta ba, in ko alhairi ne yasa ya Sota kamar yadda take son.

Wayar Tace ta fara ringing tana dubawa taga yayana Yar karamar tsaki tayi Tace "wato ya gama waya da ita"
Sai da ya kusa yankewa ta sa hannu ta d'aga ta Kara a kunnen ta, yace "Haba princess kin shanyani bacci Kika yine?"
"a'a wanka na shigane"
"Shine baki fad'a min ba?"
"gani nayi kana wayar da tafini muhimmanci"


" Ki daina fad'in haka princess waya nake da wata course mate d'ina"
"Oh mace ce ma ko?"
Yace "Eh"
"Na sani ai"
"Me Kika sani?"
"Babu komai"
" To hau online d'in mu cigaba da hirar mu"
Tace "Nikam bacci zanyi kaina ke ciwo"
Babu yanda baiyi ba ta hau Amma taki hakan yasa ya kyale ta,katse wayar yayi, yayi wurgi da ita Yana tsaki yace "Yau na kasa gane Kan yarinyar Nan ko me ya same ta oho"
Da wannan tunanin bacci yayi awun gaba da shi.


Ma'isha kuwa kasa bacci tayi, tana kuncewa sa sakawa idan har bata mallaki Haisam a matsayin miji ba zata iya samun matsala, Kila ma ta rasa rayuwar ta a dalilin hakan, Amma meyasa haryanzu bai nuna Yana sonta ba? A bayyane Tace "Ya Allah kasa Yayana Yana Jin abinda Nima nake ji akan sa, Allah yasa ba Ni kad'ai nake haukataba" a Haka har bacci ya d'auke ta.

WASHE GARI

Ma'isha tunda tayi sallar asuba ta koma bacci bata tashi ba har sai da aka Fara Kiran sallar azahar, tana farkawa wayarta ta fara dubawa taga missed calssy da dama, amma na haisam yafi yawa harda texts shi a tunanin sa fushi ta Kuma yi dashi.


Murmushi kawai tayi ta tura Masa text *"am sorry Yaya na bacci nake , wayar na silent ne shiyasa banji ba"*

Yana gani ya Mata reply da *"okay idan kin shirya ki Sanar dani Ina d'akina sai na kai ki saloon d'in"*

Ta amsa reply da *"Alright"*

tashi tashiga wanka,sai da tayi sallar azahar kana tashirya cikin wasu lallausar riga da siket na voyel less dark blue wanda aka mata ɗinkin tamkar ajikinta aka dinka yayinda adon jikin kayan pink ta yafa pink din mayafi da takalminta hill da kuma handbag ɗinta pink yar karama ,ta saka wayarta aciki ,Batayi wani kwalliya ba abisa dabi'arta na rashin damuwa da ɓata fuskar ta wajan ciki masa hayaniyar kwalliya ,Ta fesa turaren ta mai kamshi ta fito.


Tana fitowa ta samu mummy da Umma a parlor suna Hira sannan suna Kallo sama sama Umma tace " masha Allah daughter kinyi kyau" Ma'isha kanta akasa tana murmushi tace
"Nagode umma "


Mummy Tace "Yau sai ina Haka?"
"Saloon zani"
"uhmnn" kawai Tace
Tace "Sai mun dawo"
Mummy kallon ta kawai tayi Umma Tace "A dawo lafiya,Allah ya tsare"

Ta amsa da Ameen, part d'insu Haisam ta shiga Kai tsaye d'akin sa ta nufa,ta tarar ya gama Shima hakan yasa basu 'bata lokaci ba fita sukayi atare, sadaddiyar mota suka shiga da Alama sabuwace an wanke ta sai sheki take.


Bayan sun shiga motar ya kalleta ta yace "Princess irin wannan kyawu Haka, kamar Zaki je gasar sarauniyar kyau"

Turo baki tayi cikin Shagwab'a tace "Sai yanzu ka ganni?"
Dafe Kai yayi yace "kefa na lura Sam bana Miki gwanin ta ko?"

"Ni dai bance ba, ai tun Shiga na d'akin yakamata kace nayi kyau"for
"kyau din naki ne yayi yawa baki ga sai kallon ki nake ba na kasa magana,Kuma nayi maganar baki ji bane, yanzun ma dakyar maganar ta fito"

Dariya kawai tayi tana Jin dalilin kalaman sa masu sanyaya zuciya, shiyasa Bata gajiya da magana dashi bataki ace tana tare dashi ba a ko wani lokaci ba.


Sunyi tafiya kusan na minti uku sai Tace "kaima fa kayi kyau sosai Yaya"
"Au ramawa zakiyi? Sai yanzu Kika ganni Kennan?"
"A a na Isa ramuwa Kuma, tun d'azu nake son fad'a maka cewar kayi kyau sosai Amma ya kasa fita yanzun ma dakyar sai da na dage na furta"

Dariya ya Shiga yi, itama tana dariya tuki yake a hankali har suka Isa saloon ta fita shi Kuma ya zauna a mota Yana jiran ta.
Fitar ta ke da wuya wayar sa ta Fara ringing Yana dubawa yaga Aysha, picking yayi bayan sun gaisa ta Fara Jan shi da Hira har ta a ka Gama wanken Kan nata suna waya da Aysha bud'e motar tayi ta zauna, yace "Aysha am sorry please zan kira ki anjima"
Tace "Tohm bye" ya katse wayar.

yace "Princess har kin Gama?"
" yau Kuma Yaya? "
"Yau Kuma me? "
"To ai ka Saba cewa na dad'e ne,yau Kuma nayi sauri ko?"
Dariya yayi yace "Wallahi Aysha ce ta ke ta bani dariya"

"Wace ce Aysha Kuma?"
"course mate d'inace"
" Wato da ita yake waya Kennan jiyan ma koma wacece ke baki Isa ki rabani da Yayana ba,baki Isa ki rusa min ginin da na dad'e ina ginawa ba" take ayyanawa a ranta.


Tafi yayi Tace "Na'am"
"Lafiyan ki kuwa tunanin me kike haka?"
"Bakomai bacci nake ji yaya"
"Shopping d'in fa?"
" Na fasa mu koma gida kawai"
"Ikon Allah yau wa
zai Mutu princess ce tace Bata son shopping"
Kirkirerren Murmushi tayi yace " Your wish is my command"
Ya tada motar suka bar gun.

Suna Isa gida bata tsaya jiran sa ba ta bud'e motar ta fita, tarar da su Mummy ta musu sannu ta shige d'akin ta.

Umma Tace "mutanen ki sun fara"
Mummy Tace "Chan ta matse mu Basu da damuwa ne ko kad'an"
__________________________
Please comment and share
Milhat ce
Yar Terawa


🍃 *DANGIN UBANA*🍃

Story & Written
By

Milhaart

Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*


```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*

Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

Page

19 and 20
Haisam na shiga parlor cikin girmawa ya gaidasu mummy suka amsa, Umma kallon tuhuma take Masa Tace "Haisam me kayi wa 'yata?"
Cikin rashin fahimta yace "Umma ce Miki tayi na mata wani abun"
"Gidan ku Haisam ina tambayar ka kana maida min amsa da tambaya?"
"Wallahi Umma Ni ba abin da na Mata, sai dai Kuma in sharri ta fara yi"

" Wani irin sharri yarinya ta fita tana walwala da farin ciki ta dawo cikin 'bacin Rai ka dai..... "
Mummy ce ta dakatar da ita tace "Ki daina shiga maganar yaran Nan wataran Zaki ji kunyane Tohm"
"To ai abun ne da mamaki daga fitan su ta dawo Haka?"

"Da dai kinyi shiru da kin taimaka wa Kan ki sabida kunya zakiji, Ni da ranar na shiga maganar su ba kunya tani sukayi ba, ina Nan ina goyon bayan Son Ashe ya lallab'a sun shirya, kawai nazo wucewa naji Muryar su suna Hira suna dariya tun daga Nan na fita harkan marasa kunya"

Haisam yace "Ma'isha dai akwai abinda ke damin ta nayi nayi da ita ta Sanar dani taki daga bisani ma kuka tayi tamin dakyar na rarrashe ta"
Mummy tab'e baki tayi Tace " Kwaji dashi"
Umma Kuma Tace "Nikam ai baza taki Sanar dani ba" mikewa tayi ta shige d'akin Ma'isha ta tarar tana kuka ta kwanta ruf da ciki, Bata ma San da shigowar Umman ba.


Dafe ta tayi had'e da Kiran sunan ta cikin murya Mai sanyi "Daughter!!!
A firgice ta tashie ta zauna tasa hannu tana share hawayen dake fuskar ta, kirkirerren Murmushi tayi Tace "Umma kece ban ji shigowar ki ba"

Ganin irin kallon da Umma take mata yasa ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsunta Umma tace "Ma'isha me ke damun ki? Yayan ki ya Sanar dani kina cikin damuwa Kuma kin ki fad'a Masa sannan yace min kina kuka na d'auka shirmen sane Ashe da Gaske ne tunda na gane wa Ido na, me ke damun ki? Ki saki jikin ki Nima tamkar mahaifiyar kice"

Murya na rawa tace *
"Ba ... Babu komai fa Umma"
"Baza dai ki fad'a min ba, ko kina ganin ban Kai ki fad'a min bane?"
"A'a Umma har kin wuce ma, kawai ban San ta ina zan fara Sanar dake damuwata bane"
"ki fad'a min ta ko ina zan fahimta Kuma Insha Allahu zamu samu mafita"

"idan na fad'a mata dalilin kuka na tabbas nasan zata Sanar da Haisam sannan idan na 'boye Mata Kuma baza taji dadi ba Dole ma nasan yadda zanyi, na gwammaci nayi ta dakon soyayyar a zuciya ta har izuwa ranar da zai bud'i bakin sa yace Yana so na"

Dafe kafad'ar Ma'isha Umma tayi hakan yasa ta dawo daga tunanin da take Umma Tace "Ki Sanar dani matsalar ki"
"Umma...... Ina.... Ina son... "
"Kina son me?"
"Inaso na Sanar dake Amma this is not the right time idan lokaci yayi Zaki ji Insha Allah, Amma for now ina bukatar addu'ar ki please"
"hmmm Shikenan Daughter Allah ya yaye Miki damuwar ki"
"Ameen Umma"
"To tashi muje parlor muyi Kallo"
"Ya Haisam na parlor ne Umma?"
Mikewa tayi Tace "Dama zan karb'i sako a wurin sa"
"Ai na d'auka fushi kike da yayan naki"
"Umma ai ni da Ya Haisam sai Allah"
"Allah ya muku Albarka"
Ta amsa da ameen.

Suka fice, suna isa parlor ba taga Haisam ba Tace "Mummy Yaya na fa?"
Wani irin Kallo ta mata Tace "Sandan kiwon sa ya 'bata"
Turo baki tayi zatayi magana Umma Tace "Jeki d'akin sa maybe yana chan"
Tace "To umma" da saurin ta ta fice.


Mummy ta bita da Kallo kana ta maida kallonta ga Mummy Tace "Kinga abinda nake fad'a Miki ko?"
Umma Murmushi tayi Tace "Na gani."
Babu Wanda ya sake cewa komai suka cigaba sa kallon su.



Tun daga Baki kofar d'akin sa take ji yana waya yana dariya d'an tsayawa tayi Tace "Waye Yaya samu haka?"
Jin ya ambaci sunan Aysha yasa taji kamar an soketa da kibiya a kirji, shiru tayi har ta juya xata koma sai Kuma ta dawo ta bud'e kofar had'e da sallama, Yana ganin ta yace "Am Sorry zan Kira ki anjima" ya katse wayar, Ma'isha Murmushi tayi har cikin ranta taji dad'i ko ba komai tana da muhimmanci a gun sa, sai wata zuciya Tace Mata "idan Kuma 'boye Miki wani Abu yake fa?"
Yace "Princess ya dai kin tsaya kina kallona ki zauna Mana"

"Yaya meyasa ka katse wayar da kake yi?"
"Sabida princess d'ina ta Shigo lokacinta ne ba na kowa ba"

Taji dad'i sosai hakan yasa ta zauna Nan fa suka fara Shan hirar su sosai suna cikin farin ciki.

Aysha kallon wayan ta ke Tace "Ya Rabbi gayen Nan zai bani wahala, a hakan zan samu soyayyar sa? Amma ba komai insha Allah sai nasan hanyar da nabi na sa ka Fara Sona ko ta wani hanya ne"



*MONDAY*

7:45am
Kiranta yayi a waya murya cikin fad'a fad'a yace "Wai me kike haryanzu ne? So kike na makara?"
"Am sorry gani n...... "
Kitt ya katse wayar cikin sairi ta fito ta bud'e motar ta shiga tana Zama bata ma rufe kofar ba ya ya tada motar tana rufewa ya jaaa motar suka nufi hanyar school kana kallon fuskar sa zaka gane ransa a 'bace yake cikin sanyi murya Tace "Yaya Dan Allah kayi hakuri wallahi na tashi da ciwon Kaine"

"Dama kin tab'a rasa abin fad'a ne? Inaga ma Dole na bar driver ya Rika kaiki aini ba driver d'inki bane ba"
"Yaya har abun ya kai ga Haka?"
"Wuce Nan ma"
"Ai Yaya naga lectures d'in naka karfe 8 ne Kuma haryanzu da sauran time"

"Malama test nake dashi Kuma malamin Nan ba imani bane dashi, 8 na cika yake rufe kofa ba Mai Shiga ba Mai fita, sabida Kinga baki da lectures sai 9 yasa Kika 'bata min Lokaci"

"Wallahi ba haka bane Yaya"
"Hakane Mana, wallahi ki ka Kuma maimata irin haka tafiya zanyi na bar ki"
"Insha Allah bazan sake ba kayi hakuri"
"Da kuwa kin taimaka wa Kanki, don Kanki kika taimaka bani"
"Kayi hakuri"
"Naji" kawai yace Mata har suka Isa cikin makaranta babu Wanda ya ce uffan a cikin

Saida yayi parking Tace "Yaya ka saki ranka Mana in ba haka ba test d'in bazai maka dad'i ba"
"Kin San da hakan ai Kika bata min raai? Fita yayi a motar ganin zai iya kulleta a ciki itama tayi saurin fita jakarsa kawai ya d'auka a back sit yayi tafiyar sa ba tare da yace Mata komai ba.


Ma'isha mamaki ne ma ya kamata bata tab'a ganin sa haka ba, "ko da yake ni na 'bata Masa raai zuwa anjima nasan zai huce tunda hakan ba halin sa bane ba."




Haisam sauri yake sosai sabida saura minti biyu kachal time ya cika, Yana Shiga LT zaman sa kenan zai ga shigowar malami, ai kuwa yana Shiga yasa aka rufe Masa kofofin, Nan ya Shiga arranging d'insu zaman da sukayi babu Wanda zai iya magana da wani inko kayi za'a jika sanan baka Isa Kati satar amsa ba layin medicine ba wasa kwata kwata su sha Tara ne a ajin bayan mutum sama da talatin ne suka samu admission sauran tun a aji d'aya aka zubar dasu GSU Kenan ba wasa.


Alhamdulillah test yayi wa Haisam dad'i mintuna 30 aka basu Amma shi a cikin sa'a ya gama cikin mintuna 20,bayan sun gama duk suka fita, wurin motar sa ya nufa jin an Kira sunan sa yayi saurin juyowa Murmushi yayi yace "Kaga manyan mutane"
"Su ku Kenan ko?"
Hannu suka Sha yanda samari suke Haisam yace "Ya test d'in dai?"
Yace "Alhamdulillah"
"Masha Allah, Allah ya bamu sa'a ya amsa da amiin.


Haisam yace "Dama cafeteria zanje ban samu na karya a gida ba muje Mana"
"Wallahi Nima ban karya ba muje d'in"
Sai da ya ajiye jakarsa a mota kana suka wuce suna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login