Showing 54001 words to 57000 words out of 71312 words
rayuwa ta kwana biyu, Ina ayyana dalilin hakan se Kuma na tuna irin gudunmawar da Akram ya bawa rayuwa ta, for unknown reason se kawai na Fara murmushi Ina Jin wani nishadi me dadi Yana shiga ta. Mamaki sosae ya Kama ni na yadda lokaci daya nake Jin kamar rayuwa ta tana canjawa. A hankali dai bacci ya tafi dani.
Washegari na tashi da wani irin kuzari, for the first time naji na tashi da annashuwa da Kuma walwalar. What has gotten into you Bintu? Haka na dinga tambayar Kai na lokacin da nake kitchen Ina hada meaty spaghetti da akai order. Bayan na kammalla nayi wanka naci abinci kamar kullum na Sha abubuwan da nake ganin zasu saka kiba ta ta ragu na Zama yadda nake so. Bayan na shirya na sako wani atamfa me kyau da Mamaa ta Dinka Mana, normally duk kayan zuwa makaranta ta materials ne Amma yau se naji Ina son na saka wani kayan daban. Bayan na saka na Fara kokarin daura Dan kwali se na kasa, Batuul dake shafa Mai akan gado tace
" Haka saurayi kikai Naga har wani rawar Kai kike"
Ban ce Mata komai ba balle na Bata amsa, a karshe na samu na daura dankwalin na dakko wani veil da ya shiga da atamfar na yafa se naji dukka I'm uncomfortable. Nan ma Batuul ta Fara dariya tana fadin
" Wallahi gwara ki saka hijabin ki kinfi kyau, Kinga yadda tumbin ki ya fito kuwa?"
Na juya a fusace Ina kallon ta, ta karasa yafa karamin veil din ta ta fice ta barni tsaye Ina harar ta, se Kuma naji I'm demoralized bani da confidence din fita da shi, kilan idan na fita da shi mutane suyi tayi min dariya nayi wani irin, cikin sauri na maida shi wardrobe sannan na dauki hijab na saka na dauki jaka ta na fita, dakin Mamaa naje nayi Mata sallama sannan naje dakin Adda wadda ta Gama shiryawa alamar fita zatai, tace
" Muje na sauke ki. Kin dai ki Suleiman ko? Naga Wanda Zaki aura ai. Har ni zance Miki kiyi Abu ki kiyi"
Wani irin yanayi naji marar Dadi nace
" Adda ya zanyi? Kema kin San Suleiman baya so na, so kike na dinga cusa Kai na wajen shi?"
Ta fusata zata Kai min hannu nayi saurin matsawa Wai na Yi Mata rashin kunya, har Ina mayar Mata magana. Na Bata hakuri sannan nabi Bayan ta zuciya ta kamar zata fito. Batuul na gaba ni Kuma Ina baya muna tafe suna Hira wadda kusan dukka labarin saurayin ta take bawa Addar ita Kuma tana ta saurare tare da murmushi.
A school suka sauke ni, na Mata godiya sannan na tafi class, gaba daya mood di na ya baci, yadda na tashi da safe cikin farin ciki ne da zumudin zuaa makaranta amma a yanzun se naji duk Raina ya baci. Bayan zuhr aka zo yin test din, yau Bai zo inda nake ba Wanda yasa naji rashin Dadi, bai Kuma tambaye nu ko naci abinci ba kamar yadda ya saba, duk se naji kamar an kukkunce min knots din Kai na. Fuskar shi Babu annuri ko kadan ni Kuma saboda zakewa Wai se nake Jin Babu dadi, guys imagine my audacity! Haka ya rarraba question papers din ko kallo na baiyi ba da yazo wajen bani, duk se naji idanuna sun cicciko da kwalla, ko dai shima ya gaji Dani he find me boring and unattractive again? Me yasa bani da sa'a ne cikin rayuwa ta? BashPrince00 ma da ya Fara so na he chose Samiha over me! Kuma a take se na tuna samihan, I'm sure tana can tana farin ciki a rayuwar ta, wannan tunanin sun da nayi se kawai na Fara kuka a hankali Wanda ko mutum na kusa dani ba lallai ya fahimci hakan ba.
Duk abinda nake Ashe Yana kallona, ban gaya muku how observant gayen nan yake ba ko? To shi mutum ne me kula da Kuma lura. Har aka kammalla test dinnan banyi cikin dadin Rai ba Bai Kuma kula ni ba, sannan na kasa fahimtar ma abin da yake tunani daga fuskar shi, Dan kuwa expression din shi was very blank!
Ayi hakuri a Kuma Kara hakuri... we're almost there. Thank you for hanging around 😊❤️😘
Ta_kwalam ce
[1/3, 20:28] Maman: 036
Ko da Muka kammalla test din nayi tunanin kamar yadda aka Saba zai bimu ne one on one ya karba, Amma se yace Mana duk wanda ya Gama kawai ya kife sheet din ya fita, the class is over. Haka kuwan nayi na goge fuska ta sannan na sake dage hijab di na ya rufe kusan rabin fuskata kafin na fita, duk tunani na zaice na tsaya Amma shiru kake ji baice min ba, hakan ya sake tunzura ni naji kamar irin I'm worthless dinnan, na Fara tunanin ko dai shima he finds me boring kamar yadda kowa yake gani.
Ina fita napep na.sauke wata Dan Haka na tare Dan tafiya gida, sede kafin na Kai ga Shiga sajida ta fara Kira na. Se da na shiga sannan na dauki Kiran, Muka gaisa ta tambayi ko na gama lecture nace Mata na gama se tace tana son nazo gidan ta na zauna da yaran ita Kuma zata je biki da Batuul! Wato Ni na Zama Nanny kenan? Kowa idan ya dakko wahalar yaran shi se ya Kira Ni nayi babysitting ko? For the first time nace
" Na karba order cake yanzun zanje nayi suna jira na"
Na fada Ina sake tamke fuska ta, tace
" To kizo ki tafi dasu gida idan yaso idan na dawo se na biyo na dauke su!"
Nan ma nace
" Ai na kusa zuwa gida, sede ki biyo ki kawo su"
Nasan yau zatai mamaki saboda ko kadan ban taba Yi musu musu ba, duk wani abu da zasu saka ni Ina Yi dukda ba godiya ake yi min ba. Haka na kashe wayar Ina jiyo ta tana cewa Batuul ai nace na wuce ita Bata San yadda zatai da yaran ba. Ina zuwa gida na wuce daki kamar yadda na saba, kwamciya nayi zuciya ta ko kadan Babu dadi. Kawai hango dull fuskar shi nake da yadda ko kula ni baiyi ba, zuciya ta se ta Fara tuhuma ta da Wai me yasa na damu tun da kuwa nasan ni da shi Babu wani Abu da ya hada mu, he's just my lecturer, whereas I'm his only female student. To se menene Dan Bai kula ni ba, Naga Yan gidan mu karewa da muke related by blood ba kula ni suke ba shi ne Zan damu Kai na. Maimakon wannan tunanin yasa naji Dan Dadi ko na watsar da tunanin shi, a'a se ma wani bangare na zuciya ta ya Fara kokarin Kare muradin ta da nuna min, shi fa Akram mutum ne me muhimmanci cikin rayuwa ta shi din therapist di na ne, ta Yaya zaai naji Dadi idan therapist di na ya daina kula ni? Shi fa ya Dan Fara boosting confidence di na ya nuna min Nima mutum ce like all other person.
Ina nan kwance se sallah kawai ke tashi na har na Fara jiyo muryar hajja, kamar an tsikare ni Haka na mike, ita hajja mahaifiyar Mamaa ce, da gudu na fita na fada jikin ta Ina dariya, ta rungume ni tana fadin
" Ja'ira! Karya ni kike so kiyi?"
Nayi dariya Ina Zama kusa da ita nace
" Hajja Baki ce min Zaki zo ba Kuma? Sannu da zuwa! Me Zaki ci?"
I find comfort and love a wajen wannan tsohuwar, Mamaa da Adda se murmushi suke ganin yadda muke da ita, ita dinma sosae take sakin jiki da Ni ko jikokim ta albarka. Na tashi naje kitchen cikin zobon da nayi na kawo Mata, na dauki Jakar kayanta zuwa dakin mu. Cikin hour daya nayi Mata grilling kifi na kawo Mata hade da abincin da akai a gida. Se da Naga taci sosae kafin na bar ta ta tafi wajen Mamaa sannan na dawo daki Ina Jin dadin zuwan ta, ko ba komai zuwan nata ya saka hankali na ya dauke daga tunanin Akram. Bayan maghrib hajja ta dawo daki na Muna ta hira har na kasa karatu, Babu jimawa Kuma se ga Iyan KT, ban sani ba ko Kun tuna ta? Idan ba ku tuna ta ba to mahaifiyar Adda kenan. Ai murnar da nake se da ta bawa kowa mamaki, ita ko dakin su Adda da Mamaa Bata je ba, yadda na karbo kayan ta dakin mu na wuce da su, na hada Mata ruwa tayi wanka sannan na hada musu abinci ita da hajja suna ta yabon girkina, Wai ko iayye na albarka. Abin da nayi zai tabbatar maka how lonely my soul is, I'm yearning for love and attention.
Su Adda har Kawu anan Suka zo suka gaishe su. Wajen Tara na Gama musu shimfida anan nake Jin ai kudin Batuul zaa kawo shi ne dalilin zuwan nasu. Adda Dake zaune Bata tafi ba, hajja tace
" Asiya Ina Batula Kuma?"
Se Kuma Adda ta dube Ni tace
" Bintu Ina 'yar uwar ki? Me ya faru Bata dawo ba?"
Na dubi Adda da mamakin tambaya ta Inda shalelen ta take nace
" Tana gidan sajida!"
Se kuwa Iyan KT ta Fara fada
" Yanzun Asiya har Baki San inda budurwar Yar ki ta tafi ba, karfe nawa yanzun? Har yanzun Baki daina sakar ma yarannan suyi abin da suke ba. Ki wasu irin iyaye ne? Ke kawata.."
Ta fada Wanda nasan dani take, dama kokarin fita nake tace
" Wuce kije ki Kira min kawun ku da Maman ku"
Ita fa Haka Iya take, matsawar idan tazo gidannan to se kowa ya koma hankalin shi, bana mantawa akwai wani zuwa da tayi ta samu ana ta zabar kayan sallah Ina daki a zaune, ta Fara tambayar Mamaa ni Kuma fa? Se tace ai Ni bana zaba saboda Kaya na daban kawu yake kawowa tunda ni baka ce. Ta bude idanun ta, Ina Gaya muku katsinancin nata ya motsa. Ta Fara fada tana tambayar su ko sun bawa Allah wani Abu ne da yayi su farare, dama har wani dadi ne ko afuwa ne Akan zaman ka fari. Kusan ranar yini tayi tana fada har kayan da aka kawo min se da aka mayar kasuwa aka canjo min, danma dai shagon Kawu ne.
To daga hajja har Iyan KT dukka basu shiri da Batuul, dukda tafi zuwa inda suke Amma Basu shiri saboda wani dalili da ban sani ba. Haka naje na Kira Mamaa da Kawu, suna tare ma tayi Masa serving abinci. Tunda suka Shiga suka zauna take fada akan Batuul saboda dukkan su sunsan ta tafi makaranta Amma Basu ma San ta tafi gidan sajida ba. Karshe da lallami kawu ya Kira sajida wadda ta tabbatar Masa tun maghrib Suka rabu da Batuul ta taho gida
" Kun bani kunya, har yaushe yarinya daya ku kasa kula da ita, wannan ya tabbatar min cewar Haka take kullum, Kuma Baku ma sani ba. Yaushe lalacewar ku ta Kai haka Hamisu, Asiya da Rukayya! Batular nawa take da zata gagare ku?"
Dake hajja Bata da fada, shiyasa maganganun ta ko fada take to kamar nasiha take, Kawu da kowa dukka sukai shiru ga shi sun kasa samun ta a waya, Nima Kuma Ina parlor se Kiran dayar number ta da duk gidan Ni kadai nake da ita, Nima wani birthday party zaayi na friend dinta shi ne ta Kira Ni da shi da suna min kwatancen in da zaa Kai musu cake shi ne Dana gane contact din ta ne nayi saving.
"Wai menene kike damu na"
Shi ne abin da ta Fara fada da ta dauka, kawai Dan bani da saurin fushi, Kuma Ina da hakuri bacin Haka da tuni gaba ce tsakani na da wannan marar mutuncin. Nace
" Batuul kina kallon lokaci kuwa? Ina kike?"
Daga yadda take maganar nasan ranta a bace yake tace
" Ina gidan sajida Mana yanzun Zan taho"
Ban Karya ta ta ba saboda ni bansan an Kira sajida ba, nace Mata tayi sauri ta dawo saboda Kawu na neman ta, ai shi Bata Gama Raina shi ba. in no time zakuga ta dawo!
" Sannan me yasa auren Batula kawai zaayi Banda Bintu?"
Hajja ta tambaya, Adda tace
" Batuul ce kawai ta samu miji, ita kawar taku ko saurayi Bata da shi, sannan wannan yaron Suleiman muka so hada ta da shi Amma tayi ta Masa wulakanci..."
Ai kuwa Adda Bata San ta ballo ruwa ba, Iyan KT tace
" Ita din BINTUN ba Yar ku bace ba? Tsinto ta kukai? Dan me zata Yi soyayya da abin da Yar uwar ta ta Bari? Wai ku a gidannan kanku daya kuwa? Wanne irin rayuwa kuke? Kun bani kunya, ta Yaya zaku fifita wasu daga cikin yaran ku Akan wasu wannan ba daidai bane ba. Itama kawar tawa tana zaune mijin ta tsalale na idon duniya zai fito, Kuma ba Baki nayi muku ba Allah ya sakawa Bintu kada kuga Kun haife ta, akwai hisabi tsakanin iyaye da yaran su. Ku fita ku bamu waje!"
Dukka suka Mike suka fita jiki a sanyaye, har lokacin Ina parlor Ina jiran Batuul wadda ta sake Kira na Akan Ina Kawu, nace Yana daki tayi sauri ta shigo. Cikin rashin saa tana shigowa suna fitowa su kuma, sukai kicibis akace Wai kicibis mugun gamo! Ran shi dama a mugun bace yake, Ina fata Baku manta kawu da zuciya ba dukda ba sosae yake nuna hakan ba, Yana zuwa ya dauke ta da mari Yana fadin
" Daga gidan uban wa kike? Ina Kika je se goma kike dawowa?"
Marin ya girgiza ta ba kadan ba, Dan har Jakarta da Bata Gama rufewa ba Bayan ta karba kudi hannun honorable ta Fadi a kasa, a take kudin Suka fito, dukka Mamaa da Adda Suka bude bakin su suna fadin wannan wanne irin tozarci ne cikin dare. Kafin ta Kai hannu ta dauka har ya dauka, mint ne na 1k wrapper guda biyu, ai Ina Gaya muku wannan Daren kusan kashe Batuul yayi, duka dai seda hajja da iya da Kuma wani makwabcin mu suka so kafin aka kwaci Batuul hannun shi, kawu Bai hakura ba ya shigo dakin mu Dan ita se rusa kuka take ta gudu dakin Auwal, Ina tsaye Ina kuka saboda hankali na ya tashi na Kuma tsorota da dukan yace
" Ina ne wajen kayan ta!"
Hannu na rawa na nuna Masa, aikuwa ya bude ya dinga watso da kayan kasa, kudi Nadi Nadi Haka Suka din ga fadowa, kunsan se da aka hada kudin sun Kai 900k, ai Adda se ta Fara kuka, ana bude Jakar ta se ga mukulin wata Benz ya Fado, innalillahi wa inna ilaihil rajiun! Munga tashin hankali wannan Daren Wai Saar mu saya sirikan kawu na nan, se da suka ji inama Basu ce Ina Batula ba da kilan hakan Bai faru ba. Tun da yaga key din motar ya ciri igiyar shanya ya nufi dakin Yaya Auwal ya fito da ita, tana ihu ga lokacin gari yayi shiru Bayan dare Kuma layout ce, kunga kowa na gidan shi, anan tsakar gida yace a gaban kowa ta Fadi motar waye? Da farko tace ta kawar tace, da ya zuba Mata wannan igiyar guys se tace
" Kawu wallahi tawa ce, tawa ce !"
Yace
" Uban waye ya siya Miki?"
Tana ihu Yana tafkar ta tace
" Honorable ne!"
Lokacin dukan yayi yawa har ya samu fuskar ta, nayi ta maza ganin kowa tsoron magana yake masa, na rike bulalar na tsugunna har kasa nace
" Kawu Dan Allah kayi hakuri, Dan Allah!"
Kilan shima jira yake wani ya Hana shi, kunsan dai yadda kawu yake son Batuul, Dan da amincewar shi Batuul ta ruguza maganar Suleiman Dan abokin shi. Ya yarda bulalar sannan ya wuce dakin shi, Nima naja hannun kawaye na muka tafi, kowa jikin shi a sanyaye yake. Muna zuwa har sun kwanta se ga Batuul ta shigo har lokacin kuka take, tana shigowa Ina tattare Mata kayanta, warcewa tayi daga hannu na tace min
" Munafuka kawai!"
Sannan ta nufi gadon ta kafin ta hau ta hangi iya da Kuma hajja a gado na dake nawa na da girma tace
" Anan zasu kwana! Aikin banza uwar shishigi duk se kin da dakin mu yayi warin tsofi!"
Tana fadin Haka ta fice ta barni da Jin kunya, hajja tace
" Wannan yarinya iyayenta sun lalata ta da yawa!"
Ta_kwalam ce
Be reminded that BINTUN BATUUL is not free, NAZNEEN and GEN NASIR ZAKI! They're still ongoing with as low as N1300.
[1/3, 20:28] Maman: 037
A wannan Daren bana tunanin a cikin gidannan akwai Wanda yayi bacci me Dadi kowa bacci dai se barawo Wanda sukai Kuma cikin dare da sun farka abin da ya faru zai Fado musu. Washegari da wurwuri nayi ma kawaye na breakfast, ba tare da na jira kowa ya tashi ba nayiwa su hajja sallama na tafi makaranta, ranar ta Kama Friday amma Zan fita saboda akwai lecture daya da nake da ita. Se Bayan na fita sannan na duba waya ta Naga message din Alamin Akan the class will not hold so it will be a free day! Wani rashin Dadi naji saboda bayan na fita abubuwan da Suka faru a class din Dr Akram se Suka dawo min, rudanin jiya da yasa na manta komai se gashi ya lafa yanzun se Kuma asalin damuwa ta ta dawo! Haka na koma gida badan na so ba. Na samu Kawu Bai fita ba, Haka Adda ma, dukkan su suna parlor an rutsa Batuul ta Fadi inda motar take, could you imagine motar tana gidan zuhra, Ashe can ta maida ta. Nan kawu ya Kira mijin zuhra akan su zo Yana neman su, Haka shima honorable din Kawu ya Kira shi sede baya gari yabi earliest flight to Lagos, Dan Haka Kawu yace Masa to ya fadawa masu kawo kudi su wuce Hadejia Kuma biki ya fasa saka watanni shida kamar yadda Honorable din ta nema, ya maida shi wata biyu.
Ita Kuma Batuul hatta school din ta sede Auwal ya Kai ta ya dakko ta, duk wani Wanda zata hadu da shi ya kasance a gida ne. Har lokacin kuka take yi, ta bani tausayi sosae da sosae yadda Baku tunani, Koda dai ta