Showing 18001 words to 21000 words out of 71312 words

Chapter 7 - BINTUN BATUUL

10 Sep 2025

3164

da fadin

BashPrince00: My princess!

A take wani murmushi ya fita a fuska ta, har cikin zuciya ta nake Jin wannan sunan princess da yake Kira na da shi

BinGin: next week Zan koma makaranta fa!

Ai tuni Naga typing, se nayi relaxing baya na akan pillow na Fara jiran amsar shi, Babu jimawa se ga sakon

BashPrince00: wacce makaranta Kuma? Baki Gama secondary ba?

Ina murmushi ganin how curious he's nace

BinGin: ban Gama ba Ina SS2.

BashPrince00: wacce school ce?

A take na fada masa, ya Fara mitar how badly he's going to miss me, to shi ya zaiyi ma dai da farko Babu ni. Se nace masa kada ya damu Samiha na zuwa da waya, we'll try to be in touch!

A Haka ya roki na bashi number ta, Ni kuwa yadda yake on and off akaina Babu musu na tura masa, wa yaga farin shiga. Daga Haka muka Fara waya da shi, kafin wani lokaci shakuwa da Kuma soyayya me karfi ta shige ni, shima Ina da yakinin Yana so na sede abin da ya faru a karshe baiyi min dadi ba. Kafin wannan lokacin nasan na samu kulawa da Kuma farin ciki Wanda ba shi da algus babu mix ko kadan.

Har na koma makaranta da wayar Samiha muke chatting da shi, Amma duk da yadda muke communicating ban Bari ya taba karatu na ba, shi ma kuma he make sure Bai Shiga lokacin da ya kamata ace na Yi karatu ba. Amma duk wannan abun da kuke gani Bayan sunan shi Bashir, kasancewar shi dan kaduna sannan Kuma Yana karatu a Abuja Babu wani Abu Dana sani, not even his picture, Haka shima Bai San komai a tare da Ni ba ban da abun da ya fada min a kanshi. Na manta cewar I can be criticized over my figure and looks, Amma gani nake mutanen da suke narrow minded su ne Suka damu da irin wannan abubuwan.

Muna ta soyayya, Muna ta zuba kaina har akai hutu, wannan karon Kano naje, unlike sauran hutum. Tun da nayi wanka na tafi wajen Mamaa, Bayan mun gaisa naci abinci na karba wayar ta nayi logging 2go account di na. Kamar kullum kamar Kuma ko da yaushe Yana jira na online ya Kuma bar min offline message.

BashPrince00: princess kinje gida lafiya?

BinGin: nazo lafiya! Na Kuma samu kowa lafiya

Ya turo min emoji me zuciya tare da fada min irin yadda yayi kewa ta daga lokacin da mukai magana karshe zuwa yanzun.

"Ke Bintu murmushin me kike Yi?"

Nayi saurin dagowa Ina tamke fuska nace

"Ba komai!"

Tace

"Kije ki kwanta kiyi bacci!"

Na Mike Bayan na amsa ta ba, na fice ba tare da na Bata wayar ba.




I'm very busy with some stuffs here, I'm sorry for the late post
[1/3, 20:27] Maman: BINTUN BATUUL

Top-notch season 3

Ayshatuuu

013





Hakika soyayya wata aba ce me Dadi, duk yadda zuciya da baki zasu Kai ga kwatanta ta yadda feeling din yake bana tunanin zasu iya succeeding wajen yin hakan. Soyayya zata saka kayi duk abin da ka gama cika bakin ba zakai ba, kayi shi Kuma ka kasa gane dalilin da yasa kayi shi. A rayuwa ta nasan ban ji Dadi ba, nasan ni I was an example of mutanen da suka samu tabo cikin zuciyar su, Amma Kuma soyayya da nayi na Dan lokaci ta kasance wani likaci ne da naji dadin rayuwa, nayi cherishing kasancewar ta mutum Kuma mace.

So, fast forward rayuwar na tafiya, Kun San wani lokacin idan ka Fara girma akwai abubuwan da zaka ga Yana raguwa, to Haka tsangwamar da ake min, caba min magana, punishing di na akan laifin da ba nawa ba. Abubuwan sun Dan lafa se yadda suke takura min akan kurajen fuskata, Adda ta kawo min wani magani na tube akan na dinga shafawa, na Fara shafawa Amma tamkar an sake watso min su akan fuska ta Haka sukai, da naje na fada Mata se tace min

" Ba Kya using din shi correctly Bintu, idan kinsan munin da fuskar ki take karawa day by day da ba zakiyi Wasa ba"

Jiki a sanyaye na dauki tube din na tafi Abu na, daga nan Kuma kullum se ta kwaba min nescafe da kwai da Kuma kurkum, kullum se naje na shafa kafin ta fita aiki, na yamma Kuma naje wajen Mamaa, kamar ibada Haka wannan mulke mulke da shafe shafen nake. Amma Kuma ko kadan Basu bar fuska ta ba, in fact Kara fesowa suke yi.

Wani yammaci Ina kwance a daki, hutun mu ya kusa karewa. Ina ganin yadda ake Italian frosting dan already na Fara Saida cake da snacks duk da babu customers Amma dai a Haka nake Yi Dan hannu na ya fada. Tun safe ban ga Batuul ba, so duk tunani na taje gidan daya daga cikin siblings din mu. Se gata ta shigo kamar an jefo ta, na dago na kalle ta nace

" Ban gan ki ba yau"

Ta samu guri ta zauna gefe na, se Kuma ta Mike Wanda yasa na kalle ta Ina karantar yanayin da take ciki, she looks obviously nervous, ta tura kofar dakin sannan ta dawo ta sake Zama tare da Ciro wata Leda da ta kudundune a veil din ta. Ta Miki min, na saka hannu na amsa kwalin waya ne sealed ko bare shi baayi ba, na jujjuya ta Ina kallon ta, ban taba ganin wayar ba, ban ma taba jin sunan ba. Naga dai a jiki an rubuta iPhone 4S. Na dube ta Ina jiran Karin bayani Amma se Naga hannun ta kamar Yana tawa, cikin kwamtar mata da hankali na Kama hannun nata nace

" Menene Batuul? Me ya faru?"

Ta sake mikewa ta rufe window sannan ta Kara volume din food Network din da nake kallo tace

" Bintu ki fada min abin da nayi is wrong ko?"

Na kalle ta confused nace

" Ki kwantar da hankalin ki, idan kina ganin Baki son disclosing maganar, Zaki iya rufe bakin ki"

Ta girgiza min Kai tana sake ruke hannu na, tunda nake da Batuul ban taba ganin ta tsorata Haka ba, ita mutum ce me dakiya da karfin zuciya, akasin yau se Naga kamar an canja ta

" Twin!"

Kun taba Jin Batuul tace min twin? I can't remember idan ta taba fada gaskiya, na Kara Bata dukkan hankali na tace

" I did a mistake! I was so stupid Bintu. Ya zanyi?"

Na Fara kosawa, Nafi son ta fada min menene saboda zuciya ta wani irin bugawa take

" To tsaya kiji Bintu, wannan wayar tayi wajen N200k..."

"N200..?”

Na katse ta Ina kwalalo idanu na waje, se Kuma na kalla kwalin wayar, wannan bitten Apple da na gani se ya tuna min I some how heard about wayar.

"Waye ya Baki ? Suleiman ne?"

Ta girgiza Kai ta Fara fada min

Sunan shi Mahfuz, Bata San ko shi Dan waye ba, kamar yadda bansan Bashir Dan waye ba. Sun hadu through social media, if I can mention Facebook precisely. So suna tare duk da a gida tasan kowa Suleiman ya sani Kuma Suleiman zaa Bata, Amma wani lokacin mu Kan Yi wani Abu Wai shi black market, mu hada maza fiye da biyu ba tare da wani ya San da zaman wani ba. Suna ta soyayya se kwatsam jiya yace Mata Yana son ganin ta, kunsan dai Suleiman a gidan mu yake kusan dukkan al'amuram shi. Se ta nuna Masa hakan ba me yiwuwa bane ba, shi Kuma se ya nuna Mata ai haduwa da mace a gidan su old fashion ne, beside Yana son ta kawo Masa bedspread da Kuma snacks. Da farko ta nuna tsoro take ji Amma daga baya se ya yaudare ta da kalaman shi har ta dauki sabon bedspread din Adda, ta duba freezer ta kwashi snacks din da nayi ta soya sannan ba tare da kowa ya sani ba ta wuce ta same shi a wani top hotel a Kano. Shi ya fita ya Shiga da ita har dakin shi, sannan ya Fara Jan ta da hira har ta saki jiki, ya Bata juice Wanda tace min daga shan shi bacci ya dauke ta, Bata San me ya faru ba se Bayan azahar ta tashi, ta samu Kan ta Babu ko dankwali shi ne fa hankalin ta yayi mugim tashi ta Fara tuhumar shi da ko yayi Mata wani abu, yace shi ban da caressing gashin ta babu abin da yayi Mata, ta dinga shafa jikin ta to make sure cewar Babu wani Abu da ya cire a jikin ta, in fact shi Batuul tayi Masa kankanta. Tayi saurin gyara jikin ta, ta dakko dankwalin ta ta daura, shi ne ya Bata kyautar wannan sabuwar iPhone 4S.

Na saki ajiyar zuciya me nauyin gaske nace

" Batula Fatima Hamisu Ginsau! Wannan abin da kikai kuskure ne babba, kiyi kokari kada ki kara. Ina hankalin ki yake da yace kije hotel ki same shi?"

Ta Kara kallona worriedly tace

" Bazan Kara ba Bintu, nayi alkawarin ba Zan sake ba, Amma ya zanyi da wayar nan?"

Anan fa ake yin ta, na rasa yadda Zan fada mata saboda nasan duk yadda muka Kai da boye boye akan wayar se gaskiya ta bayyana. A karshe dai bansan yadda akai ba har Batuul ta Fara amfani da ita ba, kawai Naga tana ta harkar ta da sabuwar wayar ta abin ta, Suleiman kadai ya tambayi yadda ta samu wayar se tace Masa mijin sajida ya aiki mata daga Lagos, shi kenan magana ta wuce kamar daukewar ruwa.

Bayan na koma makaranta, Muka Shiga final year din mu, a wannan karon Bayan mun sake komawa gida na samu Kawu saboda career guide nace Masa

" Kawu zanyi registering jamb, shi ne nazo nace maka wanne course Zan saka?"

Ya Dan rage volume din radio din shi yayi kadan sannan yace

" Ki zaba abin da Kika San Kan ki zai iya dauka, kinsan bana son failure a gida na"

Na gyada Masa Kai sannan nace

" Na saka architecture?"

Yayi dariya yace

" Waye zai iya architecture Bintu? Amma ba ke ba ko?"

Na Dan Bata fuska nace

" Zan iya Kawu!"

Ya gyada Kai tare da fadin

" Then carry on'

Na fita zuwa dakin Yaya Auwal na fada Masa architecture zai cika min, da Kuma makarantar da nake so, ya danyi dariya yace

" Bintu kin San menene architecture kuwa? Ke din ce Zaki iya wani architecture? To Ni Adda cewa tayi na saka Miki education na biology Kuma na Riga har na coke"

Na dube shi wani Abu ya kawo min wuya nace

" Biology education Kuma? Ni me yasa ba zaa ji raayi na ba? Haba Yaya"

Ya shige ya barni a wajen, na koma daki kawai na Fara kuka, nayi me isata sannan na wanke fuska ta na karbo wayar Mamaa nayi dialing number BashPrince00 Wanda na Riga na haddace a Kai na. Ina magana yace

"Princess me ya same ki? Kuka kikai?'

Na gyada Kai na nace Ina Kara sakin wani kukan, ai se ya rikice gaba daya ya Fara tambaya ta abinnda ya faru, aikuwa Ina kuka na fada Masa duk abin da ya faru, se da nayi shiru yace

" Are you sure zai iya architecture din?"

Na gyada Kai na kamar Yana gaba na nace

" I'm determined!"

Se yace

" To Ni Zan turo Miki kudi kije ki sake registration a nearby jamb office!"

Nayi shiru Ina tunanin Anya kuwa na karba kudin shi? Ai Bai kamata ba, se na girgiza Kai na nace

"A'a ka bar shi, I can't accept it!"

"Saboda kin Raina ko? Me yasa kike min Haka ne Bintu? Baki dauke ni yadda na dauke ki ba ko? Kinsan yadda nake son ki kuwa? Ina Jin kamar akan ki I can move the mountain for you and I can melt the snow for you!"

A take fuska ta ta cika da wani annuri me kayatarwa, bansan menene love language din ku ba, Amma nawa love language din is "words of affirmation" Ina son mutum constantly ya din ga tuna min Yana fadin how much I mean to him, yadda yake ji na cikin zuciyar shi, tamkar kuwa Bashir ya sani ko fahimta yayi he always does yadda nake so!!!



Ta_kwalam ce



BINTUN BATUUL, NAZNEEN da Kuma GEN NASIR ZAKI rubutu ne na kudi, Wanda N1300 kawai ta ishe ka subscribing...
[1/3, 20:27] Maman: BINTUN BATUUL

Top-notch season 3

015...Last free page

Ayshatuuu



*Kece me kallon mutane kice musu sun Yi kiba ko? Kece me kallon su kice ke Kinga ranar da kikai? Kun San illar bakin ku kuwa? Kunsan me maganar ki take jawowa?*




"I finally got to see my BinGin"

Ya fada Yana sake matsawa gefen da Samiha take, yayin da ko second glance Bai bani ba balle na saka ran zaiyi min magana. Wani irin Abu naji ya zamo min wuya na ya tsaya min tamkar an samo katon dutse an saka a gurin. Nayi shiru Ina kallon Samiha dake murmushi from ear to ear, na kalle shi ya lumshe idanun shi duk lokacin da wannan jijiyar ta goshin ta ta bayyana, there and then naji, I've lost this battle, wannan ba fadan da zanyi nasara bane ba, Amma se zuciya ta ke cemin

" Bintu tafiya zakiyi? Ina Zaki je Baki fada Masa kece ba?"

Se na tsaya saboda har lokacin Samiha taki tace ita ce BinGin, ta Kuma taki denying hakan, na cigaba da kallon yadda suke ma juna killer smile Kai ka rantse da Allah kace dama can sun San juna, kamar Zan Yi hakuri Naga gudun ruwan su, Amma a yau se hakuri na ya kare, na gagara yin hakan, Babu shiri nace Masa

" Habiebie na!"

Se ya juyo da sauri, I'm sure ya Gane murnar da Kuma salon da nake amfani da shi duk lokacin da Zan Kira shi da hakan, se Kuma ta juya ya kalla Samiha da murmushin fuskar ta ya Fara daukewa, ya kalle ni wani irin kallo na kada kice kece BinGin, na gyada Kai na nace

" Nice Bintu Ginsau wato BinGin"

"Kece?! How?"

Ya fada cikin wata murya me wani irin amo, nayi shiru na rasa me zance masa, shima se yayi shiru yayun da nakan ga Yana stealing glance din Samiha wadda tayi shiru kamar ruwa ya cinye ta, ko kadan ban taba kawowa Samiha zata iya yin abin da tayi min ba, ko da Wasa ban taba kawowa hakan ba. A hankali yace

" I'm sorry Bintu but..."

Se yayi shiru ya kasa karasawa, Kun taba Jin bugun zuciyar ku ya karu har Kuna tunanin Anya wannan zuciyar tawa ba kokarin balls kirji na take ta fito ba? To Haka naji, I was so scared da zuciya ta ta kasa controlling bugun da take, nayi kokarin rike kirjina Wai duk kokari na, na kada zuciya ta ta fito

" Bansan Haka kike ba, kiyi hakuri but you're not my type, bana son Mata masu *KIBA* "

Ya fada idanun shi na Kan Samiha da lokaci daya murmushi ya Kara bayyana akan kumatun ta da fuskar ta. Na kalle shi sosae, na Kara kallon shi a Karo na biyu kafin Kuma na samu brain Dita ta Gama processing maganar da yayi min. Se na fahimci Yana nufin ni Bintu by type din shi bace ba, type din shi Samiha ce, beside baya ma son mace me kiba. Ai ina Gama tantance hakan ban jira wata magana ba, na juya na Fara wulla kafata, a wannan lokacin wallahi na manta cewar visiting akeyi, ko kadan na manta Wai hall din a cike yake da mutane, idanu na ba abinda suke gani, idan kuka dauke memory cells Dake taimakawa kowanne Dan Adam wajen tuna abin da ya Riga da ya sani, to bana tunanin Zan iya Kai kaina hostel. Na manta Wai bana son mutane, na manta wai bana sakewa idan mutane na guri, all that matters shi ne na kadaice. Ina zuwa hostel na Fara cire kayan jiki na, se da na cire tas na bar towel Dake daure a kirji na sannan na zumbula hijab na fita, Ina zuwa waje na samu drum ana Kone kone, a take na zuba dukkan kayan a ciki sannan na dawo, ba Wai Ina cikin hayyaci na ba ne ba, a lokacin I've completely lost my sense, bana cikin hayyaci na ko kadan. Ina zuwa toilet na tsaya gaban katon mirror Dake corridor kafin ka Shiga cikin toilet, nayi ta kallon Kai na, Ina juya Ina kallon tun daga fuskata down to my feet, Ina dadewa ban ga Muni na ba, Amma a wannan lokacin se Naga duk duniya Babu mummuna, Babu wadda batai dacen figure ba iri n, gani nake Babu wani Dan Adam da yafi Ni Bintu kiba a duniya, na wuce toilet na zauna saman toilet seat na Fara wani irin kuka Wanda har yau bana son na tuna wannan ranar

" Shike nan? Ya Kare? Shike nan har an gama? Yanzun da gaske na barwa Samiha BashPrince00 kenan?"

Kai a cikin zuciya ta nace Samiha ba zata taba yimin hakan ba, ba zata taba son abin da nake so ba...lol! I was too innocent, I was too softhearted, I was too kind-hearted also! Ban kawo ko wildest dreams dina Samiha zata iya son habiebie ba. To Amma se na ayyana ya akai har yanzun Bata biyo ni ba, kenan itama ta yadda ta Kuma karbe shi a matsayin saurayi

To dai na Jima Ina kuka, kukan da yasa hanci na Fara zuba, kunne na ya toshe kamar kurma, sannan Kai na yayi wani irin nauyi kamr idan na tashi Zan Fadi. Ban dai na kuka ba se da naji hawaye ya daina zuba daga idanu na kafin na sakarwa Kai na ruwa na wajen minti na ashirin kafin na Mike zuwa daki, Ina zuwa na Fara karkarwa saboda sanyi da ke ratsa jiki na, hakora na suka Fara karkarwa kamar an saka ni cikin kankara. Haka na kudundune cikin blanket Ina wani irin karkarwar sanyi, ku tuna I was only sixteen years old, Kuma dama duk rayuwa ta na kasance bakin ciki kawai nake kunsa, Samiha da BashPrince00 su ne mutanen farko da na Fara samun solace wajen su, se gashi Ashe su ne zasuyi betraying di na, Kuna ganin kuwa Zan iya sake trusting mutane easily? Ai Abu ne me wuya.

Ina nan kwance bansan har lokacin da na Kai a kwance ba, rufin asiri na period nake shiyasa har lokaci yayi nisa bansan karfe nawa bane ba. Ina nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login