Showing 6001 words to 8408 words out of 8408 words
ɗan nata inya gane yana aikin soja suna zazzaune a palourn suka fara jiyo jiniyar motoci mamaki ne ya kama dukkannin su suna mamakin waye yazo haka da jiniya gaba ɗaya suka fito harabar gidan dan ganin wane baƙon sukayi.
shi kuwa Safwan tunda suka shigo gidan zuciyar shi ke tsananin bugawa har motocin su suka gama parking wani security ɗin nasa ne ya zagayo ya buɗe masa ƙofar motar a hankali ya zuro ƙafafun sa kafin ya gama fitowa gaba ɗaya haɗaɗɗan matashi ne ya bayyana jikin sa sanye da kakin sojoji kansa babu hula saidai sumar kansa dake a kwance luff tasha gyara tayi masa kyau sosai baƙin glass ne a fuskar sa fari ne soll irin farin nan da babu sirkin ja a ciki cikeda da dakewa ya fara takowa a hankali ya nufi wajan da mahaifin sa dake tsaye yayi mutuwar tsaye ganin abinda ya gigitashi da sauri Safwan ya tafi zai rungume shi cikin wata iriyar tsawa ya dakatar dashi "dakata karka taɓani Safwan ni zaka tozarta ni zaka kunyata a idon duniya" cikin sanyin muryar ya ce "sorry Abbu" wanke shi da mari yayi yana faɗin "baka isaba wallahi baka isa ka tozartani ba wallahi kaje ka barmun gida babu ni babu kai na cireka a ƴaƴana banida wani ɗa namiji a yanzu" zubewa yayi kan gwiwoyin sa yana bawa mahaifin nasa haƙuri amma cikin zafin rai ya tureshi daga riƙon daya yiwa ƙafar tasa.
Idanun Safwan ɗin sun kaɗa sunyi jawur ganin irin tozarcin da mahaifin sa keyi masa a gaban security ɗin nasa kasa tashi yayi a gurin cikin wata tsawar yaji mahaifin nashi na cewa " zaka fita ko sai na sa an fitar da kai ta ƙarfine eyeee?" a hankali ya tashi ya hau jikin sa a matuƙar sanyaye da sauri Mamin sa ta biyoshi tana faɗin ka dakata yarona dan Allah karka tafi ka zauna tare damu ta ƙarasa cikin kuka shi kanshi Safwan ya kasa daurewa ganin hawayen mahaifiyar tashi shima hawaye kawai yakeyi kamar ba soja ba cikin zafin rai mahaifin nasa yace "Halima indai kika ƙara taku ɗaya daga inda kike a bakin auren ki na yanke duka igiyoyin auren dake kanki" cak ta tsaya ta durƙushe a gurin tana kuka sauran yaran nata suma sunayi da matuƙar sauri Safwan ya shiga mota suka bar gidan zuciyar shi na masa ƙuna tsanar mahaifin shi da halayen shi suka rufe kai tsaye gidan sa na kano ya koma inda yake zaune a kwana kin nan damuwa tayi masa yawa kewan mahaifiyar shi da halin daya bar ta a ciki sun lulluɓashi dan haka ya yanke shawarar ya nemi aiki a wani gidan ko ya rage damuwa in yana ganin sa tare da mutane shine ya nemi aiki a wajan Alhaji matawalle kuma yaci sa,a ya ɗauke shi a matsayin driver sai dai sam baya baiyyana asalin sa ya buɗe company kala-kala a na kula masa dasu ya tara dukiya dashi kansa bai san yawan su ba dan a yanzu companyn sa yana na biyu a manyan companys na Nigeria daga na mahifinsa sai nasa kasancewar ya samu ma,aikata masu amana suna kula masa da dukiya sosai shi kuma yama cigaba da aikin sa na soja duk da dai ba wanda yasan asalin mai companyn nasa kawai dai kowa yasan SSG Company. wannan shine asalin abinda yasa jarumin namu ya fara aikin driver.
WANNAN KENAN.
cigaban labari.....
ku biyoni dan jin yanda zata kaya ngd
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CVoFH73vk0nCnVISlZC9uU
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
3/7/24, 9:04 AM - my lovely sister: ❤🩹 *WAYE SHI*❤🩹
*NA ZAINAB KABIR JAEN* *{GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟}*
🅿️➡️1️⃣5️⃣.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CVoFH73vk0nCnVISlZC9uU
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
_____________A hankali yaja motar shi yafara driving a hankali duk zuciyar shi babu daɗi sam baya son tuna abinda Mahaifin nashi yayi masa ya kamata ko yaya ya masa uziri a hankali ya koma gidan zuciyar sa babu daɗi sam kansa yana matuƙar sara masa idanun sa sunyi jawur a haka ya ƙarasa gida kan ƴar katifar sa dake gidan ya kwanta bacci kuwa nan da nan ya ɗauke shi bai farka ba sai gab da za,a tashi su Safna dan haka da cikin hanzari ya tashi ya fito makarantar tasu ya nufa yana zuwa ana tashin su hango su yayi su uku sun fito suna taho wa inda ake ɗaukan ɗaliban zuba mata ido yayi kawai saiya tsinci kansa da sakin wani tattausan murmushi a hankali ta ƙaraso gaban motar ta buɗe murfin ta shiga sai dai ko kallan sa batayi ba shima bai damu da hakan ba suka kamo hanyar gida.
yau ta kama weekend tun safe Safna take shan aiki saida ta gyara ko ina tsaff sannan tayi wanka ta shirya cikin wani material maroon colour da adon milk wanda akayi misa ɗinki doguwar riga harabar gidan tafi to wayar tace tayi ringing ɗaga kiran tayi tana cewa "baby tun ɗazu fa nake jiranka" a ɗaya ɓangaren shima Mahbub ɗin yace "sorry princess ina bakin gate ɗin gidan ku" cikeda murna ta ce "are you serious darling" murmushi yayi yana faɗin "yess of course yanzu ma zaki ganni" yana faɗin hakan motar sa ta shigo gate ɗin gidan duk abinda sukeyi akan idon Safwan ne dake zaune ɗan nesa dasu kaɗan.
mamaki ne ya cika zuciyar sa yaushe Safna ta fara kula samari kuma waye ma Saurayin da take kulawa mamakin sa ne ya katse sanda yaga managern companyn sa Mahbub ya fito a mota ransa ne ya ɓaci matuƙa me yarinyar nan take nufi bazai yuwu ba ya faɗa cikin zuciyar sa ransa kam duk inda yake yayi dubu ya ɓaci yana kallon su suka isa garden sai wani shagwaɓa take zuba masa da suka isa wajan zaman garden ɗin yana kallo Safnan ta jawowa Mahbub ɗin kujera ya zauna cikin wani baƙin kishi ya taso daga inda yake ransa a matuƙar ɓace sam ya ma manta matsayin sa a gidan wajan su ya nufa gadan-gadan suka suna zaune suna shan soyayyar su bama su lura dashi ba Mahbub ne idon sa ya sauka akan SGS ya nufo gurin s, zumbur ya miƙe zuciyar shi tana tsananin bugawa ita kuma Safna mamaki ne ya kamata ganin Mahbub ɗin ya zabura har yana taka ta bai sani ba.
Shi kuma SGS kafin ya ƙaraso hankalin ya dawo jikin sa da sauri ya dai-dai ta natsuwar sa ya ƙarasa ya miƙa ma Mahbub hannu yana faɗin "barka da zuwa ranka ya daɗe" sanin waye Safwan ɗin da yanda yake ƙoƙarin ɓoye kansa kansa yasa shima Mahbub ɗin sakin murmushi yana faɗin "barkan mu dai kana lafiya" ya ce "Alhamdulillah" haushi ne ya kama Safna ta ce " baby wa kake cewa ranka ya daɗe wai driver nawa bana son irin haka fa" murmushi Mahbub ɗin yayi mata a zuciyar sa yana faɗin baki da hankali baki san dawar garin ba a fili kuma ya ce "oh baby Sorry bazan ƙara ba", kallon Safwan Safna tayi cikin tsiwa da rashin kunya tana faɗin "kamin tsaye aka ka kauce ka bani guri zanyi magana da mijina" ji yayi kamar ta soka masa wuta da tace mijinta amma saiya dake ya ce "to ranki ya daɗe" a fakaice kuma yayi Mahbub in kiya da ya bashi minti biyu yana jiran sa a waje sannan ya bar gurin......
Wannan kenan.
Kudai ku biyoni.
Taku ako da yaushe Zainab kabir jaen
GARKUWAR ROYAL STAR
3/7/24, 9:04 AM - my lovely sister: ❤🩹 *WAYE SHI*❤🩹
*NA ZAINAB KABIR JAEN* *{GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟}*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
🅿️➡️1️⃣6️⃣.
______________Ko minti ɗaya Mahbub kasayi yayi a gurin saboda son cika umarnin ubangidan nasa yana barin gurin shima ya miƙe yana faɗin "Beb saƙon gaggawa daga office ana jirana zan dawo next week insha Allah" bai jira amsar ta ba ya bar gurin a ranta taji ba daɗi sosai amma sai tayi masa uziri da kiran daga office ne a waje ya taradda Safwan ɗin buɗe gaba motar yayi ya shiga sannan yayi masa umarni da su tafi har suka fita a unguwar ba wanda ya ƙara cewa ƙala sai can Safwan yaja numfashi ya ce "menene haɗin ka da Safna?", ɗan sosa kai Mahbub ɗin yayi kafin ya ce"ranka ya daɗe she's my girlfriend" ɗan kallon sa yayi kafin ya ce "auren ta zakayi?" ƙasa da kai yayi kafin ya ce "No Oga ai na kusa aure ma da yarinyar ancul ɗin mu auren family za,a mun" cikin ɓacin rai Safwan ɗin ya ce "kenan yaudarar ta kake?" ƙasa da kansa yayi saboda ya fahimci ran ogan nasa ya ɓaci.
Shi kuma Safwan cikin faɗa ya ce "kar na ƙara ganinka a gurin ta as from today babu kai babu ita" cikin ladabi ya ce "insha Allah oga".
Dai-dai lokacin suka iso ƙofar gidan Safwan ɗin sauke sa yayi shi kuma ya tafi.
To tundaga ranar Safna bata ƙara jin Mahbub ba ko wayar sa ta kira sai dai ta ƙaraci ringing ɗinta ba,a ɗaga ba in tayi masa text message ma ba zai mata reply ba ta damu ƙwari kafin daga baya ta watsar da lamarin sa dan yanzu tayi wani sabon saurayin Ameer ɗan gidan ministan kuɗi yaron bayaji yana wasa da ƙudi sosai class ɗin su ɗaya ya daɗe da cewa yana sonta amma bata yarda sun fara soyayya ba sai yanzu.
exam ta ƙarato su Safna sunyi busy da yawa kasancewar jarabawar da zasu zana itace shaidar su ta kammala Secondry wato Neco da waec karatu suke babu ji babu gani domin son su samu nasara duk da a ɓangare ɗaya sam bataji daɗin zana jarabawar don ba zata dinga ganin sahibin nata ba koda yaushe.
To sun zana jarabawa lafiya kuma sakamako yayi kyau sosai yanzu Safna babu abinda tasa gaba sai soyayyar ta Ameer dan daddy ya ce bazata fara karatu ba sai tayi aure yanzu Ameer har gidan yake zuwa kuma koda yaushe akan idon Safwan ne abun yana ɓata masa rai sosai dan yana ganin wannan zubar da mutunci ne yasa Safna kula wannan yaron da, da kaɗan zai girmeta a ransa ya ce dole inyi wani abu ya kamata inyi gaggawar auren yarinyar nan tun kan yaran nan su ɓata mata tarbiyya dan haka ya samu Alhaji da maganar yaji daɗi sosai ya ce " dama Safwan jira nake naji kayi magana nima nayi tunanin ya kamata a cika alƙawarin mahaifiyar ta tunda yanzu ta gama makarantar ta amma safwan ya kamata ace zuwa yanzu ka sanar mana da iyayen ka" sosa kai yayi ya ce "Alhaji iyayena ne zasu neman mun aure gidan nan ni asalina ɗan ƙauyen funtua ne nazo birni ne neman kuɗi sai Allah ya haɗa ni da kai daddy zanje ƙauye in turo magabata na" ya ce "Allah sarki to shikenan sai ka turo sun bama lokaci da yawa za,asa ba ai" ya ce "to daddy".
Safwan da kansa yaje dangin mahaifin sa wanda mahaifinsa ya wulaƙanta dan yana ganin su talakawa ne ya wofantar dasu Safwan ɗin ya gina musu rayuwa ya taimake su yaje ya faɗama yayyen mahaifin nasa duk abinda ke faruwa kuma ya sanar dasu idan sunje neman auren kar su sake su faɗi asalin mahaifin sa. .
Sunji daɗi sosai kuma a satin sukazo nemar wa ɗan nasu auren Safna Alhaji matawalle ya karramasu sosai kuma anan akasa ranar biki wata huɗu a cewar sa baya buƙatar komai daga hannun Safwan ɗin sai sadaki.
ita kuwa goguwar sam batasan abinda ke faruwa ba tana can tana shan soyayyar ta da Ameer ɗinta sai da biki ya rage wata biyu sannan mahaifin nata ya sanar daita a gigice cikin tsananin tashin hankali take faɗin "daddy wallahi bana sonsa bana ƙaunar sa bazan iya zama dashi ba wallahi daddy bazan iya ba" cikin tsananin ɓacin rai Alhaji matawallen ya ce "Safna indai har na isa dake ki amince da auren nan idan kuma ban isa dake ba kije na zare hannuna akanki" hankalin ta ya matuƙar tashi dajin kalaman mahaifin nata cikin kuka ta ce "daddy kayi haƙuri na amince wallahi na amince" ɗan sassau towa yayi yamata nasiha sannan ta bar gurin tunda ta shiga ɗakinta kuka take yanzu ita Safna za,a haɗa aure da wannan matsiyacin da bai da komai drivern ta inalillahi wainna ilaihi raju'un shine kawai abinda take maimatawa biki ya rage wata ɗaya aka kawo lefe a cewar Safwan zaiyi wa Safna komai na aure da akeyi akwatuna biyu ne sai dai kayan cikin duk masu araha ne atomfofi shidane duk ledoji sai wasu dogayen riguna na gwanjo guda biyu sai takalmi da jaka masu araha guda biyu sai ƴan kayan kwalliya wanda ba, a rasa ba sanda safna taga lefan jitayi kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu.
Sam bata yarda su haɗu da Safwan dan gaba ɗaya bata son ganin sa wata irin tsanar sa ce ta mamaye mata zuciya sai da biki ya rage sati ɗaya suka haɗu gaba ɗaya ta rame tayi baƙi duk gayun nan yanzu batayi gaba ɗaya tausayin ganin ta a haka ne ya kamashi sai yaji zuciyar sa sam ba daɗi kuɗi ya bata dubu biyar ya ce in akwai abinda zatayi wani murmushin baƙin ciki ta saki ta ce " bawan Allah kana tunanin akwai wani abu da zanyi a wannan auren naka ina kayi kaɗan ai wallahi babu abinda zanyi kuma ka ɗebe kuɗin ka bana buƙata dan ni ɗin kasan ba matsiyaciya bace"......
Wannan kenan kudai ku biyo ni dan jin yadda zata kaya.
ayi haƙuri da rashin posting ɗin da bamayi kwana biyu insha Allah daganan zuwa azumi zamuyi ƙoƙari muga munyi abinda mukayi.
Na gode da irin kulawar ku gareni inajin daɗin yanda kuka nuna dauwar ku akan wannan littafi.
Wannan littafin na sadaukar dashi ga duk wani member dake cikin group ɗinnan.
SANNAN INA MIƘA GODIYATA A GAREKI ƳAR UWA KUMA ƘAWA AMINIYA A GARENI SISTER MUKARAMMA BISA YANDA KIKE ƘARAMUN ƘWARIN GWIWA DA KUMA KULAWA NA GODE SOSAI ALLAH YA BAR ƘAUNA YA KUMA BAR ZUMUNCI NA SADAUKAR DA LITTAFIN NAN GAREKI KACO KAM.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CVoFH73vk0nCnVISlZC9uU
TAKU AKO YAUSHE GARKUWAR ROYAL STAR .