Showing 3001 words to 6000 words out of 8408 words
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
🅿️..........7⃣↔8⃣.
*BISIMILLAHI RAHMANU RAHIM DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJI MAƊAUKAKIN SARKI WANDA YA BANI IKO NA KAMMALA LITTAFINA MAI SUNA YAREEMA ASLAM SANNAN YA BANI IKO YAU NA KAWO MUKU SABON LITTAFINA MAI SUNA WAYE SHI ? INA FATAN ZAKU BIYONI DAN JIN SAƘON DANA ZO DASHI A WANNAN LITTAFIN.*
______________Nihla ce taji kukan Ammi ta shigo ɗakin da gudu tunda taga Anty Mimi ta juya ta fita dan tasan faɗa sukayi dan indai zasu zauna guri guda sai sunyi miƙewa Mimi tayi ta fita a ɗakin tsohuwar dan amsa kiran daya shigo wayar ta.
Wata hamshaƙiyar hajiya ce zaune gefen ta ƴan mata ne guda biyu dukkansu jikin su sanye da ƙananan riguna wanda basu wuce gwiwoyin su ba kana ganinsu kaga cikakkun ƴan bariki dukkan su suna manne a jikin hajiyar suna shafata yayin da ita kuma take lumshe ido tana amsa kira a wayar ta sallamar commender Halima ce ta karaɗe falon da sauri hajiyar ta ture ƴan matan ta saka hijabi sannan ta bada izinin shigowa fuskar Halima ɗauke da murmushi ta ce "ranki ya daɗe" ɗan taɓe baki Hajiya Aisha tayi ta ce "dame kika zo waye ya aikoki" cikin sigar yaudara Halima ta ce "alkhairi ne ya kawoni gunki amma fa idan kin ban haɗin kai" gaba ɗaya hajiya Aisha ta maida kallonta kan Halima dan bata wasa da yaran mijin nata bata doguwar magana dasu amma yau kuma har Halimcy ce tazo take mata magana a haka cikin haɗe rai ta ce "ina sauraren ki" kujera Halimcyn ta samu ta zauna ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ita dai Hajiya Aisha kallon ta kawai take kallon ta Halimcy tayi kafin ta ce"Hajiya Aisha taimako ne ya kawoni garunki akwai binciken da ake a kanki kuma ana zargin kina haɗe da matsafin nan jagus sannan kuma kina less mijinki yasan da cewa kina tare da jagus amma bai san kina harkar lesbian ba kina ɓoye wannan harkar saboda bakyason a sani amma ni kuma nasan komai da kikeyi inason ki nutsu kiji inason in taimake kine amma in kikayi ƙoƙarin cutar dani wallahi zaki gani kafin nazo gurinki akwai wacca na sanar wa komai akanki har bidiyonki na tura mata na sanar daita da zarar kin cutar dani ta watsa a social media zan zauna a gunki zaki zama ƙawata ta hakane kawai zasu kuɓuta ni kuma zan dinga basu bayanan ƙarya akanki har na goge zargin da suke miki amma dole zakina biyana duk wata sannan idan kikayi ƙoƙarin sanar da wani ta ƙaremiki don asiri baya cina kuma baya cin wanda suke bincike a kanki idan kina mamaki ki gwada yanzu".
gaba ɗaya gumi ya gama wanke wa hajiya Aisha fuska karo na farko kenan data tsorata a rayuwar ta rufe ido tayi ta fara karanta wasu ɗalasuman tsafi amma me ko gezau halimcy ba tayi ba dan haka saita sallama ta ce "yanzu ya kike so ayi maganar ki zama ƙawata bata taso ba saboda kamar cin Amanar ƙungiyar mu ne amma san dinga biyanki kaso me tsoka" SGS Funtua da ke sauraron su ta na'urar dake maƙale a kunnen halimcyn ya ce "ki ƙara ƙoƙari dole ta yarda ki zama ƙawarta ta hakan me kawai zamu samu bayanai akan ta" haɗe fuska halimcyn tayi ta ce "ok na fahimci bakya buƙatar taimakona kinga tafiya ta" da sauri hajiya Aisha ta ce " tsaya dan Allah karki min haka na amince da buƙatar ki amma da sharaɗin matuƙar kikaci amanata sai naga bayanki" duk da halimcy ta tsorata hakan bai hana ta yin murmushi ba ta ce "kema haka" sannan ta fice a gidan".
Cikin farinciki SGS Funtua ya ce "good job halimcy amma fa ki kula kar ki bari aga wata alama ta cewar mu kikewa aiki" ta ce "insha Allah yallaɓai zan iya bada rayuwata akan ceton Al,umma" ya ce "good za muyi magana anjima" ta ce "godiya nake yallaɓai" sannan suka katse kiran a gaggauce ya shirya ya bar gidan dan yamma tayi hakan ne yasa bai ƙarasa binciken da yake ba.
Zaune take ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya chart take da ƙawayen ta sai wani ya mutsa fuska takeyi shigowar sa harabar gidan ne yasa ta ɗago idanuwan su ya haɗu da na juna harara ta galla masa sannan ta murguɗa masa baki sakin baki Safwan yayi danshi rashin junyar Safna har mamaki take bashi yarinyar daya girme mata sosai batafi sa,ar ƴar autar su ba Nihla amma sai shegiyar rashin kunya haɗe fuska yayi ya tunkaro ta ai kafin ya ƙaraso gurin ta zuba da gudu har tana zubar da lemon dayake akan ɗan table ɗin dake gaban ta abin har yaso ya bashi dariya tsoron yarinyar yayi yawa amma kuma bata fasa rashin kunya........
*KASH LAIFIN DAƊI ƘAREWA KUDAI KU BIYONI*
*INA GODIYA A GAREKU MASOYANA*
*#ZAINAB KABIR JAEN*
*{GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟}*
3/7/24, 9:03 AM - my lovely sister: https://chat.whatsapp.com/CVoFH73vk0nCnVISlZC9uU
❤🩹 *WAYE SHI?*❤🩹
*MARUBUCIYAR LITTAFIN*
*1:-RAYUWAR ZAINAB*
*2:-RASHIN MAHAIFIYA*
*3:-YARIMA ASLAM*
*YANZU KUMA GAMU ƊAUKE DA SABON LITTAFI MAI SUNA WAYE SHI ?*
*STORY&WRITTING* *BY* *ZAINAB KABIR JAEN*
*{GARKUWAR*💪 *ROYAL STAR🌟}*
*FREE BOOK* 📚📖.
*Littafi mai d'auke da soyayya,Sadaukarwa,tausayi,ilimantarwa,har ma da nishad'antarwa,*faɗa karwa*ku dai ku biyo garkuwar taku*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
🅿️..........9️⃣↔🔟.
BISIMILLAHI RAHMANU RAHIM DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJI MAƊAUKAKIN SARKI WANDA YA BANI IKO NA KAMMALA LITTAFINA MAI SUNA YAREEMA ASLAM SANNAN YA BANI IKO YAU NA KAWO MUKU SABON LITTAFINA MAI SUNA WAYE SHI ? INA FATAN ZAKU BIYONI DAN JIN SAƘON DANA ZO DASHI A WANNAN LITTAFIN.
______________Murmushi yayi ya nufi part ɗin sa a ransa yana faɗin ina sonki amanata bayan ya shiga ɗakin kiran Abbas ne ya shigo wayar tasa ɗaga kiran yayi da sallama ɗauke a bakin sa amsawa Abbas ɗin yayi yana faɗin "ranka ya daɗe na samu labarin hajiya Aisha tayi bukin ɗin jirgi zuwa senigal gobe" zumbur ya miƙe daga kashin giɗar da yayi ya ce "mene dalilin zuwan nata ka nemo minshi kafin tafiyar ta" ya faɗi haka yana yanke kiran dafa kasan yayi ya rasa ina zaisa ransa yaji daɗi kewar mahaifiyar shi ta kama shi yasan daya na kusa daita damuwar sa zatayi sauƙi gashi wadda da ta maye masa gurbinta ta rasu hawayen daya gangaro masa ya goge ya ce "meyasa daddy meyasa ni baka sona kamar sauran tunda ka haifeni baka nuna min so kamar sauran na samu duk wani abu na more rayuwa amma na kasa samun mai maye min gurbin Mommah na wadda tamin haka ta rasu Allah sarki Mommy insha Allah zan riƙe miki amanar ƴar ki Safna kamar yanda kika riƙeni nima.
"Granny wai meyasa baki son zaman lafiya ne ke kullum kin fiso a dinga tashin hankali a gidan nan kawai kin kira daddyn mu sai faɗa kike masa akan ɗansa bai fiki son sa ba aka faɗa miki" Mimi ce ke maganar cikin ɓacin rai dajin haushin abinda kakar tasu tayi ma mahaifin su a gaban yara ita kuwa tsohuwar sakin baki tayi tana kallon ikon " kin gama nace kin gama mara kunya ni yarinyar nan narasa ubanwa kikayo a rashin kunya mahaifiyar ki ba haka take ba haka mahaifin ki amma shima Safiyanu tun yana ƙarami bayaji ko kaɗan kuma bari in gaya miki wallahi yarinya nafi ƙarfin ki fasa miki baki zanyi ni zaki yiwa rashin kunya" ta ƙarasa tare da fashewa da kuka tsaki Mimin tayi ta fice daga part ɗin ita kuwa granny kayan ta ta fara haɗawa tace wallahi sai na bar gidan nan Aliyu tun kan ƴaƴan ka su fara yimin duka Mommah ce ta shigo taga abinda tsohuwar take haƙuri ta samo bata tana rarrashin ta ta ƙyar ta haƙura tana faɗin " anci darajar ki da tafiya ta zanyi" zama Mommah tayi tana tayata hira har ta sake.
tunda ya ɗauko ta zai kaita makaranta ya fahimci akwai abinda ke damunta tayi shiru yau ba tsiwa sam sai yaji ransa ba daɗi har suka iso makarantar bata sani ba ta tafi kogin tunani cewa yayi " ranki ya dade mun zo" cikin sanyi jiki ta buɗe murfin motar zata fita muryar sa taji yana faɗin "sorry madam" ɗan satar kallon sa tayi ta fice daga motar haka kurin yaji shima duk ransa ya 'baci dan baya san ganinta a damuwa tafi kyau in tana tsiwa da rashin kunya...
*WACECE SAFNA*
*KASH LAIFIN DAƊI ƘAREWA KUDAI KU BIYONI*
*INA GODIYA A GAREKU MASOYANA*
*#ZAINAB KABIR JAEN*
*{GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟}*
3/7/24, 9:03 AM - my lovely sister: https://chat.whatsapp.com/CVoFH73vk0nCnVISlZC9uU
❤🩹 *WAYE SHI?*❤🩹
*MARUBUCIYAR LITTAFIN*
*1:-RAYUWAR ZAINAB*
*2:-RASHIN MAHAIFIYA*
*3:-YARIMA ASLAM*
*YANZU KUMA GAMU ƊAUKE DA SABON LITTAFI MAI SUNA WAYE SHI ?*
*STORY&WRITTING* *BY* *ZAINAB KABIR JAEN*
*{GARKUWAR*💪 *ROYAL STAR🌟}*
*FREE BOOK* 📚📖.
*Littafi mai d'auke da soyayya,Sadaukarwa,tausayi,ilimantarwa,har ma da nishad'antarwa,*faɗa karwa*ku dai ku biyo garkuwar taku*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
🅿️..........1️⃣1️⃣↔1️⃣2⃣.
BISIMILLAHI RAHMANU RAHIM DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJI MAƊAUKAKIN SARKI WANDA YA BANI IKO NA KAMMALA LITTAFINA MAI SUNA YAREEMA ASLAM SANNAN YA BANI IKO YAU NA KAWO MUKU SABON LITTAFINA MAI SUNA WAYE SHI ? INA FATAN ZAKU BIYONI DAN JIN SAƘON DANA ZO DASHI A WANNAN LITTAFIN.
______________Safna ƴace guda ɗaya tilo ga babban ɗan kasuwar nan mai suna Alhaji Abubakar matawalle ɗan kasuwane wanda yai shura a jahar mu ta kanon dabo Nigeria matar sa ɗaya mai suna Maryama, yana zaune lafiya da matar sa shekarar su goma da aure ko ɓatan wata bata taɓayi ba hakan yasa dangin mijin nata suka sako ta gaba da gori rashin asali dana haihuwa sam bata sakewa a gidan mijin nata koda yaushe yaran su da manyan su suna kan hanyar gidan gashi in suka zo suyi ta 'bata mata gidan haka take haƙuri saboda bata da kowa sai mijin nata ana haka suka haɗashi aure da ƴar uwar sa bazawara ce kuma tayi haihuwa biyu a gidan data baro dan haka suka ce tunda ita ba juya bace tazo ta haifa masa ƴaƴa abun mamakin kuma shine tunda akayi auren shekarar Amaryar tasa bakwai ba haihuwa dan haka sai duk surutun da suke sukayi shiru kuma sai da tasan yanda tayi tasa suka dena musu suntiri a gida dan ta lura in tayi wasa irin na Maryama zasuyi mata itada kishiyar ta sam basu da matsala suna zaune lafiya sun haɗa kansu yanzu Maryama ta samu natsuwa sosai a gidan mijinta dan Amaryar tata irin matan nan ne goggagu sam bata ɗaukan raini ita kawai duniya ce gaban ta business ɗinta take gari-gari ana haka Maryama ta samu ciki murna a wajan Alhaji matawalle ba,a magana haka Saratu dan ita ko a jikinta dan dama ita ba haihuwa ce a gaban ta a lokacin Safwan shekarar sa ɗaya da fara aiki a gidan kuma tun zuwansa Allah bai haɗa jinin sa da Amaryar Alhaji ba wato Saratu amma shida Mommy ya ɗauke ta kamar mahaifiyar sa.
Tare da Safwan ake rainon cikin dan in ya fita haka zai siyo ma Mommy su ɗata yalo da sauransu takan ce indai mace na haifa Safwan zan baka ita matsayin mata indai inada rai har mijinta saida ta faɗawa lokacin da cikinta ya isa haihuwa bata iya aikin komai wataran safwan ke mata har Allah ya sauketa lafiya yarinyar taci sunan mahaifiyar Alhaji matawalle ana kiranta da Safna cewar Mommy zata masa takwara sanda yarinyar ta fara wayo ta shaƙu Safwan sosai duk inda taji muryar sa ta sani in bai ɗauketa ba ta dinga kuka kenan shekarar safna biyar a duniya Allah yayi wa Mommy rasuwa sakamakon ciwon ciki datayi na dare ɗaya amma duk da tana cikin ciwo saida ta nana tawa mijin nata cewar indai Safna ta girma ya taimaka ta cika mata burin ta ya aurawa Safwan ita tasan zai riƙe mata Amanar ɗiyar tata sannan shima Safwan ɗin ta bashi amanar ƴar tata.
Mutuwar ta daki Safwan da Matawalle sosai nan riƙon Safna ya koma hannun Saratu wato Ammi kasancewar tana son yarinyar yasa take gatan tata kamar ƴarta amma sam bata yarda Safwan ya ɗauke ta tun yarinyar na kuka in ta ganshi har ta haƙura haka shima tun yana damuwa har ya haƙura sanda yarinyar ta girma gaba ɗaya sai halayen ta suka koma na Ammi har ma ta fita dan indai rashin kunya ne da rashin girmama manya kuma da izza Safna ta haɗashi kaf gidan Safwan kaɗai take shakka dan shi sam baya sake mata fuska amma sauran ma'aikatan gidan duk ta raina su ta dinga sasu aiki kenan sam ta tsani talaka a rayuwar ta dan a cewar ta duk ƙazamai ne wannan hali na Safna yana damun mahaifin ta danshi mutum ne mai son jama'a ga kyauta.
wannan shine labarin jarumar tamu a taƙaice
*CIGABAN LABARI*
*KASH LAIFIN DAƊI ƘAREWA KUDAI KU BIYONI*
*INA GODIYA A GAREKU MASOYANA*
*#ZAINAB KABIR JAEN*
*{GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟}*
3/7/24, 9:04 AM - my lovely sister: ❤🩹 *WAYE SHI*❤🩹
*NA ZAINAB KABIR JAEN* *{GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟}*
🅿️➡️1️⃣3️⃣
______________Yau tunda suka taho motar tayi tsit ita Safna ta ƙurawa gefan titi ido har suka iso makarantar bata sani ba, bai san abinda yake damunta ba amma sai yaji ransa duk babu daɗi dan bubbuga kujerar da take zaune yayi a hankali ta ɗago tsintar kansa yayi yana faɗin "Madam meyake damunki?" bata kulashi ba duk da dama ya tsammaci hakan.
Jakarta ta ɗauka zata fita yakuma faɗin "sorry Madam" still dai bata kulashi ba ta juya ta nufi ajinsu juya motar tasa yayi zuciyar shi sam babu daɗi, kiran Abbas ne ya shigo wayar tasa ɗagawa yayi yana faɗin "Abbas ya ake ciki kasamo wani evidence ne ?" a ɗaya ɓangaren cikin rashin jin daɗi Abbas ɗim ya ce " boss har yanzu shiru dai ni bama wannan ne yasa na kiraka ba dan Allah Safwan ka daure kazo funtua kodan saboda mahaifiyar ka....." cikin tsawa Safwan ɗin ke faɗin " wait Abbas na gaya maka babu ruwan ka da abinda ya shafi tsakanina da iyayena ka tsaya iya matsayin ka wannan ba matsalar ka bace" ya ƙarasa yana katse kiran jingina kansa yayi akan sitiyarin motar zuciyar sa na tafarfasa nan da nan idanun sa suka kaɗa sukayi jawur zuciyar sa sai tafarfasa takeyi bai san meyasa Abbas keson fama masa ciwon daya daɗe a zuciyar shi ba why Abbas why meyasa bazaka barni na zauna lafiya ba bana son zancen gidan bana so ya ƙarasa yana dukan sitiyarin a hankali ya lumshe ido rayuwar sa ta baya ta fara dawo masa tana tuna masa WAYE SHI.
Safwan Asalin ɗan garin Funtua ne mahaifinsa Alhaji Habib Funtua ɗan kasuwane wanda ba,a iya nigeria yayi suna ba a ɗaukacin duniya baki ɗaya Alhaji Habib mutun ne mai zafin rai da zuciya gashi sam baya son talakawa bashida taimako sam tsakanin sa da talaka yayi masa aiki ya biyashi Mami itace matar sa ta farko suna da yara shida Anty Suraiyya wadda take aure a kaduna itace babba tana kula da companyn Abbun nasu nacan sai Anty Shukura ita kuma tana aure a Abuja kuma itama ita take kula da companyn mahaifin nata sai Anty Saudat a lagos sai Samira ita kuma a gombe sai Safwan sannan Mimi ƴar auta duka matan suna kula companyn mahaifin su kasancewar duk ƴaƴan shi sunyi ilimi mai zurfi Safwan shine kaɗai ɗansa na Namiji saidai shi kuma Safwan sam babu abinda ya rage a halin Mahaifiyar su na son taimako da son jama,a sannan tun yana ƙarami bashida burin daya wuce ya zama soja.
Kowa a gidan nasu yasan da hakan shekarun sa sha shida a duniya ya kammala secondary kasancewar sa yaro mai matuƙar hazaƙa a lokacin me ya sanar da mahaifin sa ƙudirin sa nason aikin soja amma sai ya ce sam bai yarda ba business zai karanta kamar sauran ƴan uwan sa ya kula masa da babban companyn sa dake kano ya roƙi mahaifin nasa kan ya barshi yayi aikin sa saboda bashida wani interest akan business ɗin amma yaƙi sanin halin mahaifin nasa yasa ya haƙura Turkey aka turashi karatu amma me saiya juya akalar karatun nasa zuwa taraining ɗin sojoji a wata babbar makarantar ko yarda sojoji anan Turkey ɗin shekara biyu yayi yana training sannan ya fito da babban muƙami a makarantar sojojin kowa yana son Safwan saboda yanayin maida hankalin sa shiyasa suka so su riƙeshi anan ya musu aiki yaƙi yarda saboda shima ya bautawa ƙasar sa sanda ya dawo Nigeria bada sanin mahaifin shi ya dawo ba kasancewar course ɗin shekara shida aka tura shi mahaifiyar shi kawai tasan da hakan. dan haka sai ya wuce gidan sa na kano yake aikin sa acan a ƙananan shekarun sa da basu wuce ashirin ba ya taka matsayi da dama wanda duniya take alfahari dashi ba iya ƙasar sa ba SGS FUNTUA kenan ɓoyayyen matashin daya ɓoyewa duniya kamannin sa saidai aikin sa tantirai suna tsoron sa dan ko sunanshi aka faɗa a gaban mai laifi saiya razana.
a shekaru shidan nan ya taka matsayi da dama sannan yasamu kyaututtuka iri-iri cikin lokaci ƙanƙani yazama matashi mai kuɗi.
KASH KU BIYONI.
NGD DA ƘAUNAR DA KUKA NUNA MIN
INA NEMAN AFUWA MA RASHIN POSTING DA MAYI KWANA BIYU INSHA ALLAH DAKA YANZU MUN DAWO POSTING BABU KAMA HANNUN YARO NGD
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CVoFH73vk0nCnVISlZC9uU
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
TAKU ZAINAB KABIR JAEN GARKUWAR ROYAL STAR
3/7/24, 9:04 AM - my lovely sister: ❤🩹 *WAYE SHI*❤🩹
*NA ZAINAB KABIR JAEN* *{GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟}*
🅿️➡️1️⃣4️⃣.
______________Ranar daya cika shekara shida da tafiya karatu Walima mahaifin sa ya haɗa masa ta tarbar sa da kuma murnar damƙa ma ɗan nasa companyn sa yaran sa gaba ɗaya sun zo daga gidajen auren su kowa burin sa ya ganshi saɓanin mahaifiyar sa da zuciyar ta take cike da tsoron hukuncin da zai yiwa