Showing 114001 words to 117000 words out of 213059 words

Chapter 39 - GURBIN IDO COMPLETE

Huguma   

27 Oct 2026

214

/>
ke gaya miki ba kowanne jagwalgwalon masu aiki da sunan abinci nake ci ba?,take note please,kada ki sake shigomin daki ba tare da izini na ba" ranta ya sosu kamar kullum,ta kuma kasa hadiyewa

"Amma dai kasan ni matarka ce ko?,sannan kuma ko yaya ne ina

da hakki a kanka" qas yayi da kansa,murmushi nason kubce masa amma kuma ya hana kansa faruwar hakan,don baya son raini,daga bisani ya kuma daga kan nasa ya dubeta kai tsaye

"I know,i already know, that's why na baki zabi ai tuntuni,a mutunce zan baki ta

kardarki ki qara wuta,i assure you zaki samu dai dai dake" wani qullutun baqinciki ne ya tokare mata wuya,wanda ta kasa riqeshi,sai ta saki kuka kawai ta juya gudu gudu sauri sauri tabar dakin,yayin da shi kuma ya bi bayanta da wani kallo da tsarabar tsaki

,kana ya miqe a hankali yana sanya hannunsa cikin sumarsa yana maidata baya saboda yadda ta cakude,bawai bashi da feelings ba,ko kuma feelings dinsa ya mutu ba,aah.....yana nan a yadda yake,lafiyayyen namiji,wanda wannan dalilin ya sanya ko a baya ya riga

jabir aure,amma dai for now bayajin komai akan kowacce diya mace,musamman unaisar da sai a yanzu yake gano fuskarta ranar da qaddara ta fara hadasu da ita a wani club sanda yake aviation school,zuwansa club na farko kenan a rayuwarsa,shima baisan can zasuj

e ba,daga wajen cin abinci suke shida abokinsa kuma abokin karatunsa muslim,yace yazo ya rakashi wajen wani abokinsa,as'ad zubair,dan gida wani babbban qusan gwamnati a nijeria,acan ya gansu tare da ita,wanda shikam kallo daya ya yiwa fuskarta ya dauke kai

,abinda yasa ya kasa shaida fuskarta kenan da wurwuri sai daga baya,duk da ba shigar banza ko wani abu yaga tana sha ba amma abun ya tsaye masa a rai,don yana da tabbacin cikakkiyar mace mai cikakkiyar kunya ilimin addini da tarbiyya ba zaa sameta a wannan

wajen ba.

Ruwa mai dumi sosai ya sakarwa kansa,bayan ya gama yayi brush ya feshe bakinsa da turaren mouth mint mai qamshin strawberry,ya dauki babban towel yana tsane jikinsa daya jiqe da lema sosai saboda yawaj gargasar da yake da ita saman l

afiyayyar fatarsa.

Cikin wasu lafiyayyun kaftan ya shirya kansa farare qal,duk motsin da zaiyi jikinsa na fidda wani irin qamshi mai taushi,ba kasafai ya fiya sanya hula ba,don haka ya riqeta a hannu bayan ya laluba key din motar da yake son

fita da ita,ya kalli agogo yana duba lokaci,sai ya sanya wayoyinsa a aljihu bayan yayi kiran daya daga cikin drivers dinsa yaji yana kusa don qyuyar tuqi yakeji,har yanzu kasalar bata sakeshi ba,yayo waje cikin takunsan nan dake dauke da wani salo na daba

m da zaka tsammaci tsabar jin kai ne ko izza.

Sai da suka tsaya sukayi sallar magariba da isha'i a hanya sannan suka qarasa a asibitin,a sannan har yayi waya an musu take away na abinci awa daya kafin ya isa,qarfe takwas da wasu motsi,driver ya

yi parking motar tasu,ya balle murfin motar ya ficw cikin nutsuwa,iskar

asibitin tana kadashi,tana kuma tuna masa wasu abubuwa sa suka shude cikin rayuwarsa.

Babu yawan jama'a sosai a asibitin,hakan ya bashi damar isa qofar dakin kai tsaye,tun ba

i shiga ba ya tabbatar akwai mutane a ciki,sai ya tura qofan a nutse da sallama.

su hudu ne 'yammatan gidan nasu,sai baba tabawa ta biyar dinsu,sallamarsa ta sanya su duka yin dif,yayin da wuta ta daukewa maimunatu dake zaune ta jingine bay

anta da filo tana sauraren hirar tasu,sanye take da doguwar rigar atamfa wadda ta zauna mata sosai a madaidaicin jikinta,ta kuma fidda mata shape dinta saboda yadda breast curve din aka yishi cif da cif,ya kuma zauna mata sosai,dogon hannu aka yiwa dinkin

saidai an yayyanka shi ya koma kamar spaghetti sleeve,tayi tayi sanda ta sanya kayan a bata baby hijab dinta data saba sakawa amma fa'iza tace a'ah,su da su waye a dakin da sai ta sanya hijab,baba tabawa ma tace

"Ki barshi kawai maimunatu,kada kije ya d

ameki ma ya gotar miki da canola din" kasancewar sun cire mata ruwan da ake qara matan don ta huta.

A ladabce suka gaidashi bayan baba tabawa ta miqe ta bashi kujerar da take kai ta matsar da ita gaban gadon maimunatu,maimunatun da tunda ya

shigo tayi qas da kanta,ko sau daya bata dago ba,idanunta nakan Canola din hannunta.

Takalmanta baba tabawa ta jawo tana sanyawa,dai dai sanda anni ke fitowa daga bandaki

"Yaushe ka shigo?" Da hannu ya nuna mata yanzu yanzu

"Zamu wuce,dam

a shirin tafiya muke"

"Akwai driver?" Ya tambaya a taqaice da muryarsan nan me cike da ginshira

"A'ah a'ah,salma ta tuqomu,gani nayi tafiyar babu yawa" cikin salma ya duri ruwa,ita anni me yasa ba'a sirri da ita?,kawai tace masa eh driver dinne,na me

ye saita bashi labari?.

Qarasa dibibicewa tayi sanda ya watsa mata wani kallo na gargadin kinyi na farko kinyi na qarshe,baa baau mota su tuqa a gidan,saidai idan kinyi aure mijinki ya baki,suk inda zasu driver ke kaisu

Da daya

da daya suka fice a dakin suna yima maimunatu sallama tare da cewa zai gobe,murya can qasa take amsa musu,gabanta na wani irin faduwa,tana jin kamar tabi bayansu sanda suka fita,dakin ya rage daga ita saishi daya sanya waya a gaba yana dannawa

[11/24, 10:

10 PM] Safiyyatulkiram: 44

Ba wani qura sashen nata yayi sosai ba,saboda yanayin ginin gidan dama unguwar,amma duk da haka baba tabawa ta zage ta gyare mata sassan nata tas,ko ina ya dauki qamshi da qyalli,aikin da ada ita ke abunta duk sanda ta

dawo hutu,abu nafarko data lura dashi,babu wani daki da

maimunatun ta ware da sunan dakin maigidan,hakanan bataga wani abu ko guda daya daya danganceshi ba a sassan,koda agogo bare akai gasu hula,tsoronta daya kada dai ace fa yarinyar tana gefe suna rayuwa

rsu shida unaisa,kada suyi amfani da qanqantarta su cutar da ita,abinda bata sani ba duk kanwar ja ce,har gwara gwara maimunatun,yana tsayawa ya dubeta da idanunsa,yana mata kallon quruciya sometimes har yakanji abar tausayi ce a ransa (hmmmmm,ya manta duk

qanqantar allura qarfe ce,mace babba da yarinya duk sunanta mace).

Baaba tabawan batace dai da ita komai ba,taci gaba da sanya ido a fakaice,har zuwa sanda ta gama kintsa ko ina,sanna ta dora musu abincin dare saboda yammaci sosai yayi,sun ku

ma yi 'yan ciye ciyensu kafin ta gama aikin,babu kuma mejin yunwa a cikinsu,duk da maimunatun taso ta barta tadan dafa musu koda jallop ce kafin baban ta gama aikin amma ta hanata.

Gab da magariban akayi knocking qofar falon,baba tabawa ta leq

a,sai gata ta dawo tana gaya mata yaron gidanne da siyayyar kayan abinci,ta saba,kusan duk sanda ta dawo hutu zai aiko da cefane da kayan abinci a zuba mata a store,duk da ba rasa komai takeyi ba,hasalima kayan abincin kamar ba'a tabasu,saboda ita daya ce

iya cikinta,ba kuma kasafai take wani girki ba,don idan tayi breakfast sai takai har rana bataji yunwa ba,bata sake dora girki sai na dare,ta riga data saba zama da yunwa,banda yanzun ma da cikinta yake komawa normal irin na mutane.

Baba tabawa

ce ta bude masa can qofar baya ta kitchen din,ya shiga ya zuba komai ya fitar da wanda zai fidda kamar yadda aka saba,sai daya tafi ta kulle wajen sannan ta dawo

"Niko nace,kuna gaisawa kuwa da abokiyar zamankin nan?" Kanta maimunatu ta daga daga qoqar

in jona chargy da take a wayarta

"Ina shiga duk sanda na dawo a makaranta mu gaisa na gaya mata na dawo"

"Amma duk xaman da kikayi asibiti ban ganta ba" ta tambaya cikin mamaki,don ko yanzun ma taji motsinta,sun kuma hadu da masu aikinta a kitchen di

n gidan,saidai babu wanda yace mata kanzail a cikinsu.

Shuru maimunatun tayi,don itama bata da amsar da zata ce,ta kuma fuskanci kusan ita kadai dince bata zo dubata ba,tasan kuma ta sani,koda mai gidan bai gaya mata ba sanda su laila sukazo d

aukar mata kayan sawa sun hadu,sun kuma gaya mata abinda ya kawosu,duk yadda taso kada taji babu dadi aka abun wannan karon sai dataji ranta ya sosu,ita din batasan ciwon kanta ba kenan da take shiga har sassanta duk randa ta dawo ta gaidata ta gaya mata t

a dawo,badon komai ba sai don zaman lafiya dake da dadi,bawai rashin sanin ciwon kai bane,duk mutumin da zakayi ciwo ya kasa dubaka to lallai rashin qauna yakai iyaka,a take nan taji a cikin ranta itama tabar taka sassanta.

A nan waje ta watsa

r da batun,kamar yadda baba tabawa bata sake daga batun ba,ta wuce bedroom dinta tayi wanka,ta shirya cikin dinkin doguwar rigar atamfa A shape,ta dora baby hijab dinta saman kanta bayan tayi sallar magariba,tasha magungunanta sannan ta fito falon,tana ji

a ranta zuwa yanzu wayarta ta cika da chargy.

Ta samu baba tabawa ta gama shirya musu abinci

"Na zuba sauran yana dumama don kada ya huce kafin yazo ci" baba tabawa tace da ita,sai ta amsa mata da to,ba tare data fuskanci ma'anar maganarta

ba,tare suka zauna da ita sukaci abincin,suna ci suna hira,baba tabawa na bata labarai iri iri da suka shafi rayuwa,zamanta da kishiyoyinta da kuma mijinta,yadda mijin ke ji da ita saboda tafi duka sauran kula dashi,a fakaice take shigar mata da darasi.

Sosai take jin dadin labaran,tunda take tsahon watanni sai yau ne takejin gidan a matsayin gida,sai yau ta taba jin dadin zaman gidan,sun jima sosai suna hira,harta soma jin bacci yana fusgarta,don haka ta miqe ta bada faralin sallar isha'i,ta du

bi baba idanuwanta na lumshewa

"Inajin akwai maganin dake sanya barci cikin magungunan da nasha"

"Bacci ko?" Kai ta gyada mata

"Eh wallahi,zan je na kwanta"

"To Allah ya tashemu lafiya" da kallo tabi maimunatu sanda take shigewa dakinta,tana ji

njina kai tare da sake tabbatarwa kanta akwai matsala,bata ga ya shigo ba,bata ga taje nemansa ba,koda kuwa ba kwananta bane,tana kuma da tabbacin zuwa yanzu ai yana gida,don ba mai yawon dare bane shi tun asali,amna zatabi komai a sannu,koda yau da gobe b

a kwananta bane,dole jibi ya zamanto kwananta,jinjina kai tayi tana ci gaba da kallonta,saidai kuma gefe guda na zuciyarta tana ayyana mata yadda zata tafi da komai.

******washegari ta kunna wayarta,ta kuma dauko number afra fatima da ayman t

a sanya,tayi saving number kowa,sannan ta fara kiransu daya bayan daya,duk wadda ta kira sai ta yi mamaki,cike da murna da farincikin samun number aminiyar tasu,afrah ce a qarshe,don tasan dole sufi dadewa da juna akan kowa.

Da tsiya afra ta fara

yi mata

"Kin yiwa kanki fada kenan?" Dariya maimunatu tayi

"Na gaji da kewarku ne" hira sosai suka sha da afrah din,har sai da katinta da hisham ya taba lodawa layin ya qare,afran ta biyota

"Ina fata kin fara shawo mana kai captain" dan shuru tayi

tana son tuna waye captain,sai kuma tadan saki fuska

"Manta da wannan batun"

"Seriously you are doing wrong fa maimunatu,kina nufin a haka zaki yita zama,meye ma'anar auren kenan?"

"Karfa ki damu,ni dashi duka bamu damu ba"

"Amma kin sauke aman

ar anni da amma kamar yadda suka baki?" Tambayar da ta sanya maimunatun yin shuru kenan,har sai da afrah tace

"Qarshen term na ss 2 nima za'a karbi kudin aure na da farid,lalurar abba tasa uncle kamal yace a daga,amma abban da kansa yace a karba,babu wa

ta damuwa,sannan hajja ma tace itama tafi nutsuwa nayi auren,naci gaba da karatun a dakina,tunda shima farid din yana da ra'ayin karatun"

"Allah sarki,Allah ya bashi lafiya kafin lokacin bikin,Allah yasa za'ayi damu,qawata kice na fara shiri tun yanzu"

hararar gefanta afrah tayi,kamar maimunatun tana kusa da ita

"Nifa mun kusa raba gaari dake,muddin ba zaki tsaya kiyi abinda ya kamata ba" murmushi maimunatun tayi

"Nifa baki fahimta ba,wai ta yaya kukeso na mu'amalanci mutumin da babu soyayyata ko d

igo a ransa sai ta marigayiyar matarsa,sannan kuma nima din babu qaunarsa ko qanqani a rai na,hasalima ni wani kallo na daban nake masa,ko inuwa daya idan muka hada Allah Allah nake yabar wajen ko kuma ni nabar wajen,infact ma kallon mugu nake masa,tunda n

a ganshi yana smoking,bansan ta inda zan fara sonshi ko sakashi ya soni ba" wata qaramar dariya afrah ta saki

"Ban yarda dake ba,ban kuma yarda da dukka hujjojinki ba,kece number one a cikin mu hudu da kika fi kowa son kallon k-dramas na soyayya,har tur

kish drama kin koya kallo....."

"Kin tunamin ma,akwai wani da naga talla,zanje na kalla" taka katse afran tana miqewa daga kwanciyar da tayi

"Ahaf,kyaji dashi,kici gaba da zama,zaki mamaki idan kk ga wata tayi muku wuf dashi" dariya maimunatun ta sak

i,idan hakan ta faru batajin tana da asara,saidai unaisa,don ta fuskanci tana da damuwa sosai a kanshi.

Agogo ta kalla sanda suka gama waya,sai taga lokaci yaja,abinda ya sanyata miqewa kawai ta shiga wanka,so take ta shirya ta fita su gaisa da

baba tabawa.

Dai dai lokacin da yake shigowa sassan nasu,cikin shirin office kamar kullum,slim fit three pieces suits ne a jikinsa Dim gray color dake da ratsin butter color,kwantacciyar fatarsa dake nuna zallar hutu da gayu tayi kyau cikin s

higar,jikinsa ba abinda yake sai fidda sassanyan qamshin turaren prive rose George armani dan qasan turkey,kwantacciyar sumarsa sai fidda qyalli take kamar qura baya tabata,komai nashi me kyau tsari da kuma tsafta ne.

A nutse baba tabawa dake gya

ra abinci saman dining hannunta kuma maqale da carbi tana ja ta waiwayo tana amsa sallamarsa

"Barka da fitowa" ta fada tana sakin murmushi,taji dadin ganinsa sosai,don ya soma wanke zato da zargin dake ranta,kadan ya motsa fuskarsa,abinda ke alamta yana

yin nasa murmushi ko fara'ar kenan

"Barka da asuba"

"Barka kadai manya,mun tashi lafiya?"

"Alhmdlh,jiya na gaji sosai,kuma na dawo late,ban leqo ba" murmushi tayi

"Ai babu komai,ta warware ma" agogon daure a tsintsiyar hannunsa wanda yake mix d

a zallar ruwan gwal ya kalla

"Zan wuce office,akwai wani abu da kuke buqata?" Kai ta girgiza

"Babu komai,amma ga abinci ko zaka ci" wajen ya kalla,ya sani baba tabawa is the best cook a duk gidansu,tana cikin list din mutanen da yake iya zama hankali

kwance yaci abincinsu,amma yanzun sai yakejin bazai iya zaman ba,baima saba cin abinci cikin gidan ba, infact ma bai taba ba

"Ina sauri ne,zan makara"

"Amma akwai kunun gyada irin wanda kakeso,ka daure ko cup daya kasha" ta fada tana hada masa da sa

uri,bayan ta saka madara da suger madaidaita,don tasan bai cika sonsu ba

"Na gode" ya fada yana karba,har cikin ransa yaji dadin hakan,yayin da baba tabawan ke karantarsa a fakaice,babu wadda ke girki a cikinsu ta bashi kenan?,abinda ya fara zuwa kanta

kenan,lallai akwai aiki jazur a gidan,akwai kuma gyara.

"Tana ciki,ina tsammanin ta tashi,zan shiga ciki na watsa ruwa" tayi masa tayin shiga wajen maimunatun a fakaice,tanason haifar da kyakkyawar alaqa a tsakaninsu,tanason tayi wani aiki da a

nni zataji dadinsa,sannan kuma ba zata manta dashi ba. Bashi da wani sauran zabi face soma takawa a hankali zuwa dakin,tunda har ta fahimci bashi da nufin shiga,bayaso ta zargi wani abu a ranta game dashi,ya kuma tabbatar kome yayin kamar yayishi ne gaban

idanun anni,tunda da ita da anni duka abu daya ne,hannunsa guda daya cikin aljihun wandon suit dinsa,daya hannun kuma cup din kunun ne yana sipping a hankali,ya masa dadi qwarai,ya kuma yi masa yadda yakeso.

Daure da babban towel ta fito daga b

andakin,ta dora qarami saman kanta da yadan jiqe ya kuma bawa sumarta daman kwanciya a bayanta da gefan fuskarta,yau din sakayau take jinta,da alama lafiya tana sake samuwa a gareta,kai tsaye ta isa gaban mirror taja dressing chair ta zauna tana kallon fus

karta data yi wani irin haske ta kuma yi fresh har ita da kanta abun yana bata mamaki,kamar zaka taba ta jini ya fito,ta canza totally,irin canjin da ita da kanta yake bata mamaki.

Towel din saman kan nata ta cire ta fara goge fuskarta dashi tan

a maida sumartata dake son shige mata idanu baya,bayan ta miqa hannunta ta jona hand drayer amma bata kai ga kunnata ba,tana goge gashin nata tana dan rera karatun qur'ani,haddarta ta qarshe da bata baiwa ya shaik nasu ba,saboda zazzabin da ta dinga fama d

ashi kafin tafiyarsu hutu,ta miqe tsaye tana ture kujerar baya,ta kunna hand drayer din ta soma busar da kanta in a low heat.

Dai dai sanda ya murda qofar dakin ya kuma turo cikin cikakkiyar nutsuwa,tashin farko qamshin hair mist dinta dana hai

r oil da take amfani dashi wanda ya cika dakin saboda zafin hand drayer din dake kadoshi,ya kuma cakude da qamshin turarenta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login