Showing 48001 words to 51000 words out of 213059 words

Chapter 17 - GURBIN IDO COMPLETE

Huguma   

27 Oct 2026

240

dama dai

ta samu foundation me dan kyau ba laifi daga makarantar primary din da tayi a gembu.

Gab da magariba suka gama karatun kamar kullum,tana goye da amna da barci ke dibanta suka shiga cikin gidan,ta taras dasu laila duk sun dawo,sun sha qunshi d

a gyaran kai tubarkalla,kowacce cikinsu tana da suma dai dai gwargwado irin na fulani.

Duk yadda suke daukin amna tazo gurinsu taqi kowa,kowa da kalar wayon da zaiyi mata amma ta qiya,murmushi maimunatu ta sake,har fararen haqoranta suna fitowa

"Saiku haqura,yau dai kam ni ta zaba" sunata yiwa yarinyar tsiya ta wuce da ita dakinta ta kwantar da ita saman gadonta,zuwa lokacin bacci yayi awon gaba da ita.

Washegari amnan tana barci maimunatu ta wuce islamiyya,sanda ta farka bata ganta ba

ta saka rigima,rarrashin duniya kowa yayi mata amma ta qiya,hatta da anni da amman da suke dasawa yau taqi,saboda sun bari hisham kafin ya fita aiki ya nata allura,basu samu lafiya ba sai da maimunatu ta dawo,da gudu ta taryeta kuwa tun daga bakin qofa,ma

imunatu ta dagata tana taba jikinta,ta samu zazzabin ya sauka,baki ta tura gaba cikin murya irin ta yaran da suka samu gata

"Ba uncle hisham bane yayimin allura"

"Ya salam,sannu kinji,kiyi haquri" maimunatu ta fada tana shafa bayanta,saita kwanta luf

a jikinta tana bata labarai har suka qarasa cikin gidan.

Cikin kwanakin wata irin shaquwa ce sosai ta shiga tsakanin amna da maimunatu,ta maisheta tamkar uwarta,duk gidan a yanzu babu wanda take dafewa kamarta,kowa yasan hakan cikin gidan,gaba

daya ma ta dawo da kwananta dakin maimunatu,hakan yayiwa maimunatu dadi sosai,saboda tafi sakewa da amnan akan kowa cikin gidan,zasuyi zamansu a daki suyita hira da amnan kai ka dauka da wata babba take magana,sosai amnan ke jin maganarta,da gaske yarinya

r qaunarta take,amna yarinya ce me wayo da surutu,haka zata zauna ta yita baiwa maimunatu labarin mommynta da twin sister dinta da ta rasu,takan ce

"Ummu(mamam shaheeda)amma/anni sunce sunje maka,zasu dawo,zasu siyomin tsaraba me yawa ko?" Sai maimunatu

ta gyada mata kai cike da tausayinta

"Amma me yasa ni mommy bata tafi dani ba?,kuma ta tafi da amra ta barni?" Ire iren maganganun dake karya zuciyar maimunatu kenan akan yarinyar,yake qara mata sonta da kuma tausayinta,sau tari takan faki idanun yarin

yar ta share hawayenta,saboda ita da yarinyar dukkaninsu suna cikin jarabawar

maraici,har gwara amna,tana da gata gaba da baya,saboda tsabar gata ma kowa so yake a bashi ita ya riqeta,ita kuma fa?.

Idan ta gama wannan kuma sai ta koma zancan m

ahaifinta,wanda maimunatu batasan wayeshi ba,saidai da alama yarinyar tana kewar mahaifin nata kewa me tarin yawa,a zuciyarta take jin tunda yana raye bai kamata ya nisanci yarinyar haka ba,tana da buqatarsa a kusa da ita,duk randa ko ta samu yin waya dash

i,ranar gaba daya labaranta nasa ne,maimunatun takan bata lokacinta ta biye mata suyita yi,abinda ya qara sabonsu da shaquwarsu kenan da ita.

Yammaci ne sosai,wanda yake dauke da lullumi sosai da zakayi tsammani damina ce zata fara,saidai maimak

on daminar ana dakon zuwan zafi ne kafin gabatowarta.

A irin wannan lokacin gidan yakan kasance shuru,rana ce da babu makaranta both islamiyya da boko,yawanci a wannan lokacin 'yammatan gidan sunfi kwanciya suyi barci idan basu da abinda zasuyi,

idan kuma suna dashi kowa yakan kama aikin gabansa,zuwa dare kuma su hadu zaman hira,ma'aikata kuwa na kitchen na sassan biyu,sassan dr marwan ko na hajiya anni.

Maimunatu ce ta dage dan qaramin falon da anni kan zauna ta huta lokaci zuwa lokac

i,hannunta dauke da zobo data dafawa annin tsurarsa,babu suger bare kayan hadi sai citta da kanunfari kawai,tun zuwanta gidan takan dafawa anni shi akai akai,saboda qarin jimi da kuma gyara zuciya da sauran cututtukan hawan jini,sosai anni takejin dadinsa,

don tana ganin amfaninsa a jikinta.

Tashi xaune anni tayi tana amsa sallamar cikin sakin fuska,idanunta nakan maimunatu,a duk sanda ta kalleta tana jin dadin sauyin da ake samu tattare da ita,zuciyarta kuma a kullum tana gaya mata kamar lokaci

yayi da zata bayyanawa maimunatu qudurinta.

"Sannu da hutawa anni"

"Yauwa maimunatu,ke zaa yiwa sannu" murmushi tayi ta zauna ta fara zuba mata zobon,annin ta karba tana godiya ta fara kurba,jifa jifa suna hira.

"Maimunatu......qarasa jik

in soket ki ciromin wayar can da Allah" amsawa tayi ta ciro kamar yadda ta umarceta

"Yauwa laluba ki kamomin ja'afar" maida dubanta tayi ga numbers din dake kan wayar,ta fara laluba sunayen,har takai ga sunan da annin ta nema

"Gashi anni"

"Yauwa k

iramin shi" ta fada tana ci gaba da kurbar zobon,zuciyarta na ayyana mata tunani kala daban daban.

A nutse la latsa icon na kira,kiran kuwa ya tafi kai tsaye,take daga qasan sunan number wayar qasar waje ya bayyana,kuma sunan TURKEY ya fito d

aga gaban number kadan

*TURKEY*

*TURKEY CAPITAL*

_ANKARA yanimahalle_

_Green forest mahalle_

Cikin babban ginin me dauke da apartments apartments,hawa na biyu,madaidaicin falo ne da ba zaka kirashi tangamene ba,kamar

yadda ya wuce ya amsa sunan qarami,me dauke rantsatsun kujeru irin na asalin qasar turkey din,lafiyayyen carpet da curtains ash color light and dark dukka na qirar qasar,sai rantsatsiyar wallpaper kalar kayan dake falon,qananun sideel table da babbansu da

ga tsakiya,dining space da aka maqalawa fridge dukkansu kalolin kayan falon ne.

Daga gefan fridge din lafiyayyen matashin saurayi ne jingine da fridge din,hannunsa riqe da cup daya cika da tataccen ruwan kayan marmari kala daban daban da aka m

arkada aka kuma tacesu a mazubi guda,dogo ne me murjajjen jiki,yana sanye da shirt mai dogon hannu da kuma trouser,yayi crossing qafafunsa hannunsa daya soke a aljihun wandon nasa,daya hannun kuma yana riqe da cup din da yake kaiwa bakin nasa lokaci bayan

lokaci.

Kana kallonsa zakasan yayi nisa a tunani da kuma nazarin inda idanuwansa suke kallo,gaba kadan dashi inda aka tsara rukunin kujerun dake falon.

Mutum biyu dake zaune cikin falon,daya farar fata ne,bature sosai,mr denis evoy

dan asalin qasar Belarus,yayin da dayan ya kasance baqar fata ne,wanda ya mallaki wata sassalkar fata me kyan gani da kuma burgewa ko cikin jinsin masu baqar fatar da ake kira da chocolate color,CAPTAIN JA'AFAR MARWAN KHALID AKKO qwararren kuma sanannen ma

tuqin jirgin sama wanda ya ajjiye aikinsa,ya kuma yi switching kansa ya zuwa babban dan kasuwa,mamallakin kamfanoni dake samar da manyan gine gine na manyan ma'aikatu jami'o'i da manyan kamfanoni tituna dama gidaje,manyan gine gine masu ban sha'awa da qaya

tarwa.

Kyakkyawa ajin farko,irin kyan nan da a hankali yake bayyana kansa,wankan tarwada ne,a very husky man built like a football player,dukka qirar jikinsa na nuna alamun qarfi dake bayyana cikar mazantaka,yana da tsaho da kuma kauri dai dai

misali wanda ya taimaka wajen sake boye ainihin tsahonsa,wasu irin shanyayyun idanu masu matuqar daukan hankali da kuma tafiya da imanin diya mace ko wacece ita,lafiyayyen qasumba ne dashi wansa bata rabo da saisaye da kuma gyara,gyaran da yake dacewa da k

yawawan labbansa hancinsa me tsaho da tudu da kuma cikakkiyar girarsa,akwai wata suma ta musamman saman kansa mai sulbi da kuma sheqi ta asalin bafullace,wadda batayi yawa ba hakanan ba kadan bace.

Iya lafiyayyar fatarsa da kuma zara zaran yatsu

n qafarsa da na hannu kadai idan ka kalla zakasan cewa a huce yake cikin cikakkiyar wadata da kuma hutu,sau tari qannensa na sha'awar yanayin qafarsa dake luwai luwai kamar ta mace,saboda yadda ta samu hutu da kuma gyara,tako ina ja'afar ya cika cikakken n

amiji,wanda ya samu kusan cikar komai na rayuwa......saidai abu biyu daya rageshi,na farko mutum ne shi miskili na gasken gaske,irin miskilancin dake baiwa mutane da dama mamaki,ake kuma

tunanin lokaci zaizo da zai sauya,saidai har zuwa lokacin da aka tsam

maci zai sauya din yazo bai sauya ba,lokacin kuma ya sake zuwa ya hade masa da baqar qaddarar rasa matarsa da kuma diyarsa mafi soyuwa a wajensa,abinda ya sake canzashi kenan,ya kuma sake cillashi duniyar miskilanci.

Sosai yayi relaxing bayans

a da jikin kujerar da yake zaune,very calmly yake kallon Mr Denis,sai kayi tsammanin duk duniya bashi da wata matsala a rayuwarsa dake barazana ga farinciki da kuma ci gabansa.

[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 19

*Arewabooks:Huguma*

https://arewaboo

ks.com/chapter?id=6351005edace9b957e575eaf

Saidai shi din haka yake,komai nasa a nutse yake cike da tsari da kuma nutsuwar,yana duban mr denis ne jabir dake jingine da fridge shima yana nazarinsa,cikin kwanakin nan gaba daya aikin ja'afar din k

enan,ya dawo da dukka hankalinsa akan kamfaninsa,ganawa yake tayi da mutane daban daban duka akan kamfanin,wani irin huge change yake gani tatare dashi a dare daya,sau tari yakanyi sha'awar inama ace ja'afar din ya tabbata a haka?,wasu lokutan a baya sai y

ayi kamar zaici gaba da rayuwarsa kamar kowa,sai kuma abun ya sake tabarbarewa,but surely a wannan karon yana ganin yanayin kamar ya banbamta da na baya,ko wannan din zai dore?.

Murmushi jabir ya saki,yana dora cup din saman fridge din sanda ya

ji mr denis na complain kan cewa

"Sir, you didn't say anything since we start the negotiation" a ransa yake cewa da alama mr denis ja'afar din baqo ne a wajensa,sai ya fara takawa zuwa inda suke zaunen,gab kuma da zai qarasa wayar ja'afar din ta dauki

ruri kiran anni ya shigo.

Da idanu kawai ya kalla wayar,sai da yaga sunan me kiran sannan ya miqa hannu a nutse ya dauka,ya kalli mr denis

"Excuse me" ya fada da wata deep and husky voice,saidai kuma akwai taushi da laushi daya cika muryar.

Shi ya fara yiwa annin sallama cikin ginshira da nutsuwa gami da wani irin kamun kai kamar mace,daga can sashen anni ta amsa tana sauke ajiyar zuciya

"Anya?,anya babban mutum?" Anni ta fada tana nuni da yatsanta kamar yana gabanta

"Barka

da warhaka anni" yayi fatali da zancanta ya maye gurbinsa da gaisuwa

"Barka kadai,kuna lafiya?"

"Alhamdulillahi,fatan kowa yana lafiya"

"Lafiyar dai da sauqi" anni ta fada zuciyarta fal kewa da kuma rashin dadi kan sauyawarsa

"Subhanallah,wani

abu ya faru ne?" Ya tambayeta yana gyara zamansa kadan gami da yamutsa fuskarsa,abinda yasa girarsa dake cike da gashi ta kusan hadewa waje daya

"Mene ma bai faru ba ja'afar?,fisabilillahi.....yanzu ace haka rayuwa zata ci gaba da tafiya" qaramar ajiyar

zuciya ya sauke,shi kansa yana damuwa,yana damuwa kan yadda ya kasa moving forward yadda ya kamata,yana damuwa kan damuwar da mutanen nan masu muhimmanci a rayuwarsa ke shiga damuwa saboda shi,yana damuwa da yadda kowa hankalinsa yake kansa,to amma ya zai

yi?,shaheeda ta daban ce,tayi masa wani mummunan tasiri me matuqar qarfi da kaifi a rayuwarsa

"Aci gaba da tayamu da addu'a, everything will be okay in sha Allah" nannauyar ajiyar zuciya ta sauke

"Addu'a kam ita aketa yi babu fashi,babu kuma kama han

nun yaro.....sai yaushe ka shirya dawowa qasarka?" Ta jefa masa tambayar da shi kansa baisan amsarta ba,gani yake kamar bashi da wani sauran zama da zaiyi a qasar

"Ban shiryama hakan ba anni,har yanzu da sauran lokaci" fuska tadan hade kadan

"Kamar y

aya ja'afar?,bakasan har yanzu zamanka a nan bashi da wani amfani ba?,idan kuma akwai ka gayamin"ta masa tambyar da salon titsiye,maimakon ya amsa mata sai ya sanya hannu saman kansa yana shafa lallausar sumarsa

"Ina amna?" Kamar tace masa sai yanzu zai

tuna da ita?,sai kuma ta bari,don a yanzun babu abinda take da buqata irin dawowarsa

"Dazun maimunatu ta kaita wajen Aishatu"

"okay.......aci gaba da yimin addu'a,ita nafi buqata,am little busy,zan kiraki anni"

"Ja'afar!" Ta kirayeshi da kakkausa

r murya

"Naam"

"Ina jiran kiranka,akwai magana me muhimmanci da nakeso muyi dakai,ka tabbatar kome kakeyi ka kirani bayan ka kammalashi" kai ya jinjina,domin annin mutun ce me kima a idanunsa,ba kasafai yake mata kallon kaka ba,yafi mata kallon uwa

"In sha Allah" daga haka suka yanke wayar,yana dan tunani cikin ransa wacce magana zasuyi da annin?,duk da jikinsa ya bashi tatsuniyar gizo dai ba zata wuce ta qoqi ba.

Sanda yake qoqarin kiran ammansa yaji annin ta kirayi jabir,baisan me t

ake ce masa ba,saidai jabir din ya tashi daga wajen ya fita yana amsa wayar annin.

Saida amma ta sauke ajiyar zuciya sanda taga kiranja'afar din nata,abune me matuqar wuya ta daga waya ta kirayeshi,saboda zallar kara da yakana irin tata,zamantow

arsa dan fari a wajenta,ta ajjiye rigar amna da take ninkewa wadda yarinyar ta cire yanzun ta dauki wayar.

Kamar ko yaushe cikin girmamawa da qanqan da kai ya gaidata,ta amsa masa cikin nuna kulawa tare da tambayarsa jikinsa,wanda daga nan bata

iya qara cewa komai ba,sai shine ya tambayi amna

"Yanzun nan maimunatu tazo ta dauketa suka fita"

"Okay amma" yayi mata sallama yana ajjiye wayar

"Maimunatu,maimunatu dai?,wacece haka?" sai yaji ransa yadan sosu,don yaso jin muryar yarinyar,yayi m

atuqar kewarta har baisan iyaka ba,yanason yazo ko don ita,amma duk sanda ya ganta tana karya masa gwiwa ne,don tana tuna masa da mahaifiyarsa da kuma 'yar uwar tagwaitakarta.

Last time da ya kira haka akace tana wajen maimunatu,har kusan sau uk

u yana kira amma ana sake gaya masa tana wajenta,abinda ba al'adarsa bace maimaita kiran waya,wacece ita din ma?,amsar da baisan ta ba,haka kawai yaji kansa ya dauki zafi,sai ya dubi mr denis

"I heard everything you said,i need a time to think about wha

t we discuss,i will contact you " kai mr denis ya kada masa,sannan ya bashi hannu sukayi musabaha,me denis ya tattare takardunsa ya masa sallama ya fice zuwa qofar gidan,inda PA dinsa ke zaune cikin mota yana jiransa.

Zazzafar iska ya furzar d

aga bakinsa wadda ta fito hade da sassanyan qamshin alawa me taste din mint da baya rabo da ita,hannunsa a saman goshinsa yana murzawa a hankali,ya daga shanyayyun kyawawan idanunsa ya aza kan agogon dake manne a falon,wanda yake nuna lokaci daga qasa kuma

kwanan wata.

Duk rana irin ta yau rana ce da yake tafiya Istanbul ya kwana,washegari ya shiga ziyartar guraren tarihi da suka shafi annabawa da sahabbai,da wahala yayi missing ranar ba tare da yaje ba,abune me muhimmanci cikin rayuwarsa,yana

daya daga cikin ababen tarihin da shaheeda ta barwa rayuwarsa,ita ta koya masa hakan,ita ta sanar dashi wanzuwar wajen,sai ya miqe da hanzarinsa dake nuna zallar lafiya da kuma cikar kuzari,ya dauki wayarsa da kuma agogon hannunsa dake saman table ya nufi

dakinsa,dai dai lokaci jabir ya dawo falon,yabi hanyar da kallo,sai kawai ya rufa masa baya.

Goye yarinyar take a bayan maimunatu,suna takowa. Ahankali daga sassan amma zuwa wajen anni,tun sanda ta fuskanci anni waya zatayi ta zame daga dakin,ta

kuma fake da dauko amna,hakan tafi nutsuwa da hakan,ko babu komai annin zata sake tayi wayarta yadda ya kamata,tun annin tana qorafi harta saba,indai wannan ne halin maimunatu ne.

Dariya yarinyar keta yi abinta,hankali kwancw tana jin dadin laba

rin da maimunatu ke bata.

Kusan minti goma kenan da dawowarsa cikin gidan,amma bai shiga ciki ba,ya tsaya daga bakin motarsa yana amsa waya,hannunsa dauke da briefcase dinsa da kuma lab coat,harda qarin baqar leda.

Siririyar muryarta d

ake cike da wani irin taushi ce ta ratso ta inda yake tsaye,abinda yaja hankalinsa kenan,ya daga kansa a hankali yana dubansu daga inda suke takowa.

Sanye take da skert high waisted wanda ya kama qugunta ya kuma baje sosai daga qasa,sai wadatacci

yar rigarsa me hannu wanda ya tsaya mata iya gwiwar hannunta,kanta lullube yake da mini hijab wanda shima ya taimaka wajen suturce jikinta,saidai kuma yayi matuqar haskata kasancewarsa peach color.

Samun kansa yayi da binta da kallo,dan qaramin ba

kinta me siraran tausasan labba suna motsawa,tana da wani irin kyau me sanyi da fusgar hankali,tun ranar da ya fara ganinta ya tantance hakan,ta dauki hankalinsa ta kuma burge shi qwarai,duk da kasancewarsa mutum da ba kasafai mata ke burgeshi ba,bama shi

kadai ba,kusan duk haka mazan gidansu suke,dalili da ya sanya ake musu kallon masu jin kai kenan

"La la la,kika yarda kike goyata a bayanki saita karya miki baya?" Maganar haisam ya ratsa kunnenta sanda take shirin giftashi ba tare data kula da tsaiwars

a a wajen ba,hada idanu sukayi,ya bita da murmushi,sai tayi maza ta janye idanunta tana sakin wani qaramin murmushin ba tare da tace komai ba.

Gyara tsaiwarsa yayi,yana maida wayarsa gaban aljihun rigarsa tare da sake cewa

"Baki gani ta kusa ka

moki a qiba?,amna bakisan yanzun kin girma ba,saura kadan ki cika 4years

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login