Showing 6001 words to 9000 words out of 9932 words

Chapter 3 - SAWUN GIWA 2 by Autar Alheri

31 Oct 2025

1568

LOKACI. SEKIN GWADA ZAKI TABBATAR HAJIYATA INADA TABBACIN IDAN KIKA FARA BAZAKI BARIBA DOMIN KOWANNE BAKI YASON DAƊI GA KUMA BIYAN BUƘATA CIKIN SAUƘI,

MUNADA INGATTUN KAYAN MATA DA KUMA MAGANIN MAZA MUNADA KAYAN GYARAN JIKI SABULUN DILKA DADAI SAURANSU DUK ABINDA KIKESO HAJIYATA ZAKI IYA SAMUNSHI AWURINMU AKAN FARASHI ME SAUƘI.

GAME BUƘATAR GARIN BOBOTIC SABAYA ZE IYA NEMAN WANNAN CONTACT ƊIN 👉07073092176 KAYANMU BASUDA NABIYU💃💃💃


Washe gari da sassafe maisoon da yah muhseen sukayiwa Anty meenah sallama a airport kana jirginsu yaɗaga zuwa Nigeria...seda sukaga tashin jirginsu tukkunna suka koma gida sedai suna isa saka samu fawan na jiransu, sosai suka gaisa cikin mutunci kana yace "meenah ina autar mom? "Laa bata gayamaba yah fawan wlh juya taɗora rigimar ita bazata zaunaba seta tafi hakan yasa yah muhseen yace tashirya sutafi yanzu daga airport muke wurin rakasu har jirginsu yatashi inaga kafin yamma autar mom kam tana gida....wani irin kallo yakebin anty meenah dashi tunda tafara magana zuciyarshi na tsinkewa "mikenan ake nufi? Maisoon muhseen tabiya bayan tasan ita yazo ɗauka a ƙasar? Tana nufin son muhseen takeyi akanshi kome? Inaaa wlh sam bazata saɓuba yafaɗa Aranshi kafin yajuya fuuuu yabar gidan ko sallama beyiwa anty meenah ba...ita kam mamaki sosai yanayinshi yabata sadai batace komaiba tashige warta gida itada yaranta..

Fawan nafita airport yanufa domin yin cuku cukun tafiya domin yayiwa ƙanshi alkawarin da isa Nigeria zegaya mata asalin abinda keranshi gameda ita kana yagawa abbey domin ayi gaggawar yin komai yariga muhseen ɗin...sedai duk yadda yaso yabar Saudiya aranar abin yaci tura doline se bayan kwana biyu zesamu jirgin zuwa Nigeria ahakan doli yasiya ticket ɗin wancan jirgin yakoma masaukinshi zuciyarshi na ƙunar doline yajira nanda 2 days tukunnah yatafi.


Nigeria

Jirginsu na sauka suka hango jafar yazo ɗaukarsu tare da A'isha, dagudu A'isha tazo suka rungume juna itada maisoon suna murna. Shi kuwa muhseen Jafar yabawa hannu cikin girmamawa ga yayan nashi yace "munsameku Lafiya yah Jafar? "Lpy qalau bro y ibada? Alhmdlmulillah, "yah Jafar inawuni cewar maisoon kanta aƙasa..uhmm sannu autar mom yan saudiya to y ibada? "Alhmdllh yah Jafar y su anty sofy da baby's na? "Duk suna lpy, yafaɗa yanayi gaba shida muhseen. Amotama hakan suke ta fira cikin nishaɗi da farin ciki daga A'isha har ita maisoon domin sune abaya yah Jafar da yah muhseen suna agaba. "Ƙanena wane hukunci yakanye akan zancen da Abbey yayimuku kauda su fawan? "Humm aini nasamu tawa yaya in sha Allah nanda ɗan lokaci zan bayyana ta gareku. "Tofa 🤔 Masha Allah amma naji daɗi wlh.."yah muhseen matace kasamu? Kai mana naji daɗi wlh sweetheart Kinga daga mungama wannan bikin senasu yaya ko ya fawan yace yasamu mata gaskiya wannan abin Yamin daɗi, Maisoon tafaɗa cikin farin ciki. "Wlh kuwa sweetheart Nima naji ai kamar nataka kan ɗanda anty sofy zata haifa sabida murna, cewar A'isha suna taɓewa da Maisoon. "Please my one bro wacece wannan me sa'ar agaya muna ita domin tunyanzu agabatardamu agunta amatsayin cikakkun ƙanen miji domin tafara tattalinmu koba hakaba sweetheart? Hakane wlh, A'isha tafaɗa tana dariya...Humm ai kuna tare da koma wacece domin kuwa sa'arnan bazatabar gidanmu ba taje wani gidan tabbas doline takasance acikin ahalina kuma ina matuƙar sonta wlh har cikin raina, sekuma yayi shiru can yace "rabbi kabani muradin raina idan samunta alkhairi ne agareni kuma idan ita ɗin matatace Allah ka mallaka min ita cikin aminci...gabaki ɗaya baki suka saki suna kallonshi cikin mamakin kalamanshi musamman ƴammatan da dasukayi kamar andasasu sabida lulawa duniyar tunani. Yah Jafar kuwa cikin mamaki yace....!


Saura page ɗaya free yaƙare kuhanzarta biyan naku domin kusamu damar karanta SAWUN GIWA har ƙarshe 💃



SAWUN GIWA paid book ne akan 1k kacal 👌 banyadda kowa ya karanta mun abuna batareda yabiyani hakkinaba idan kinshirya biya zaki iya tura kuɗinki a wannan account ɗin 👉 2276776261 sha'awanatu ƙasim UBA Bank kana kitura shaidar biyanki awannan nomber 👉 07037092176 🙏














Autar alheri ✍️

🐘🐘🐘 *SAWUN GIWA*🐘🐘🐘


🐘
🐘🐘
🐘🐘🐘
🐘🐘🐘🐘
🐘🐘🐘🐘🐘


Romantic love story 💋💓💞


Daga alkalamin✍️👇

Dr Yasmeen Ahmad

(Autar alheri ✍️)



Marubuciyar 👇


SIRRI

SOLDIER'S FAMILY

INGARMAM NAMUJI

MEJO NAJEEB

WAYE MIJINA

TANTIRANCI SABON SALO

IZZAR MULKI

BIG LADY'S

MY LITTLE SISTER

JEJI GIRL

JIKAR IYA DELU

SHUGER DADY

And NOW 👇

SAWUN GIWA LABARIN GIRMA AKAN GIRMA SOYAYYA MULKI ISA FINƘARFI RIKICI BAN MAMAKI DADAI SAURANSU DUK ACIKIN BOOK ƊIN *SAWUN GIWA*


Free

Book 1

Page 19 & 20

"Tofa 🤔 wannan wacece ƙanena? Kodai ƴar gida zakayi acikin ƴammatan gidanmu zaka ɗauka? Murmushi yayi kana yace tabbas kuwa yaya aciki zan ɗauka domin nasamu zaɓin raina.."wow Masha allah Amma kuwa da su abbey sunfi kowa farin ciki da wannan al'amarin koya kukace sister's? Yatambaya yana kallon su maisoon..ajiyar zuciya suka sauke atare musamman maisoon da zuciyarta ta tsananta bugawa, kana suka ce "hakene yaya aikuwa zamuso musam ko wacece antyn tamu acikin family...zaku ganta soon, cewar muhseen adede lokacinda yah Jafar yayi Perking a cikin gidan Dady, wato gidansu maisoon.

Cikin zumuɗi suka fito itada A'isha suka nufi cikin gidan da hanzarin su...da kallo muhseen yabisu har suka ɓacewa ganinshi kana yasauke ajiyar zuciya. "Miyafaru ne ƙanana? Kodai acikin waƴannan yammatan ne kafaɗa irin wannan kallo hakan? Gayamin wacece acikinsu? Yafaɗa yana sakin murmushi. Lumshe kyawawan idanuwanshi yayi kana yace "maisoon yaya ina mugun son yarinyar nan Allah yasa ta amince dani, yafaɗa cikin rauni. "Wow Masha allah gaskiya kuwa idan kasameta kayi dacen mata bro Allah yasa ta karɓe ka amma kayi gaggawar fito mata da asalin buƙatar ka domin kuwa inba hakanba wani ze iya riganka..dam ƙirjin muhseen yabuga cikin fargaba yace "in sha Allah yaya zan yi ƙoƙarin hakan. To Allah yasa mudace,. Ameen y Allah, yafaɗa kana suka nufi cikin gidan.

Sukuwa yammanta suna shiga suka samu mom zaune a perlor, wani mugun ihu maisoon tabuga tanayi kan mahaifiyar Tata cikin cikin farin ciki da ɗauki ganinta. "Oyoyo my lovely I miss you so very much wlh, tafaɗa alokacinda ta maƙalƙaleta tana manna mata kiss a fuska. Cikin farin ciki mom tace "ikon Allah maisoon karyani zakiyi wannan murza hakan? Ashe dai kunma iso yanzu nake waya da Ameenah tace ai tunɗazu kuntaso keda muhseen yana inane? "Ta tambayeya tana waigen bayanta, Murmushi A'isha tayi cikin sanyin halinta tace "mom yah muhseen yana waje zeshigo yanzu, inawuni. ",Eyee Uwar Muminai kice tare kuke aibangankiba wannan sarkin figar hankalin duk ta maƙalƙaleni, to y kk y hajiyarki? "Tana lpy qalau mom. Masha Allah maza kuje ciki to kuyi wanka kuhuta sekuzo kuci abinci. "To mom suka faɗa atare suna barin perlor akuma wannan lokacin muhseen da yah Jafar suka shigo. Cikin girmamawa suka gaisa da mom. Aiko taji daɗi sosai domin yaran nasu suna da kirki kuma tanajin daɗin yadda suke nuna kulawarsa ga autar Tata. "Mom ga little sis nan naɗaukewa meenah please dan Allah tadena irin wannan tafiyar menisa ita kaɗai koba komai a gaya mana inbazamu iya zuwaba samu saka arakata sabida awannan zamanin mutun baya sakeda abinda yake dashi please. "Kaji ƙanen sojoji aidoli kam kace hakan, cewar yah Jafar. Murmushi mom tayi cikin sakin fuska tace "in sha Allah kuwa muhseen idan ma tace zataje to takiraku ta tagaya muku tukkunna, tafaɗa tana Murmushi. "Yawwa my sweet mom hakan yasace Bara muƙarasa gida yanzu. "To shikenan agaida min Hajiya, Jafar agaidamin ƴata..in sha Allah zataji mom, daga haka sukabar gidan.


Su maisoon kuwa seda sukayi wanka suka huta tukkunna sukaci abinci daganan suka shiga firar yoshe gamo A'isha nabata labarin yadda bikin ƙasarsu maimoun zekasance, haka suka wuni aranar har Dady yadawo yasamesu, sosai yayi farin ciki jin cewar muhseen ne yaje har Saudiya yazo da,ita...aiko tazuba taɓara sun ranta agaban Dady domin maisoon ƴar lelece agun iyayen nata. Sedare liss tukkunna yah jawwal yamayarda A'isha gida.


Washe gari dasafe tana kwance akan makeken bed ɗinta tana bacci, wayarta tadameta da ruri, cikin maganin bacci taɗauki yawar batareda tadubaba taɗora akunne. Tana faɗar "hello. "Hi beautiful lady y kk? Taji saukar muryar da take tunanin tasani. Ai babu shiri tamiƙe zaune tana wartsakewa tare da cire wayar akunnenta tana duba nomber, nomber Nigeria ce sedai batasan kota wayeba, kafin Takoma yin magana akace "hello beauty kinajina? "Waye ne? Yatambaya atsaitsaye. "Humm bakiganebako? Nasan dama bazaki ganeba.."luck kagayamin kowaye banason shirme kona kashe wayana, tafaɗa cikin ɗan hasala. "Uhm I'm very sorry please yaseer ne wanda kuka haɗu a saudia. "Niban haɗu dakowa ba a saudia idan zakayi bayanin kokai waye kayi idan bazakayi ba shikenan tafaɗa tana ƙoƙarin yanke wayar..."Karki kashe please sunana yaseer wanda kika temaki kakarshi a saudia acikin masallacin harami itace tace kibani contact ɗinki domin idan kindawo Nigeria kizo gidanta, to shine yanzu tace nakiraki naji idan kindawo kuma yoshe zakizo? "Humm aisakeyimin bayanin cewar Hajiya ce tace kakirani tun farko, shikenan kace mata nadawo kuma in sha Allah zanzo cikin kwana kinnan ina gaidata please, tafaɗa cikin alamun gajiya da zancen.."okay in sha Allah zataji please kiyi save contact na mana ƙanwata Kinga Hajiya bazata dena sakani kirankiba nikuwa bazanso duk nakira kicemun wayeba. "Okay I'll do it in sha Allah daga hakan batajira cewarshiba tayanke wayar...daga gefen yaseer kuwa murmushi yayi yana faɗar "agaskiya Muryar yarinyar nan kaɗai abin so ce balle Gara kyakkyawa, uhmm Allah ya karkato min dake my beautiful lady. Yafaɗa yana manna wayar a ƙirjishi..

Saudia


Kwana biyu dayin rigimar Basam da kursum Sheikh sudais yashirya komawa Dubai, ba yadda Sarki Hassan beyiba akan yazauna yace aiba zama zeyi acanba sedai ze ɗan jima domin akwai abinda zekaishi sa'annan tare da Basam zeje..ba yadda Sarki ya iya doli yabarshi yatafi..sam wannan tafiyar batayiwa kursum da mahaifiyarta daɗi ba domin su ƙullah wani ma kirci dasukeso ai watarwa akan Sheikh sudais ɗin wanda zesaka doli ya amince da auren kursum kobaya so sadai sun makaro yau kam Sheikh sudais yaɗaga zuwa ƙasarshi ta haihuwa sedai sujira dawowarshi...agefen gimbiya zaitun kuwa baƙaramin daɗi tajiba domin koba komai Basam zetsira daga tarkonsu domin muddin Sheikh sudais yabar gidan to sesun ƙullah mishi wani makircin.

Nigeria

Yau rana ta ukku kuma yau ne jirgin daya ɗauko fawan yasauka agarin Abuja. Anan airport yasamu zugar sojojin shi da ƙanen shi fadeel suna jiran isowarshi, rungume juna sukayi shida fadeel cikin farin ciki da ɗaukin juna domin dai wannan ahalin kam akwai son ƴan uwa sam basason wani abun yasamu ƴan uwansu musamman najini... sojojin shi kuwa sara mishi sukeyi cikin girmamawa haryashiga mota, kana suka ɗauki hanyar gidansu, cikin azababben gudu kamar yadda suka saba....suna isa gida sukayi Perking yafito cikin sassarfa yaƙara cikin gidan fadeel na biye dashi abaya..azaune suka samu mama da Abba a perlor suna fira se A'isha dake kwance kamar me Bacci amma kuma azahiri ba bacci takeyiba. "Oyoyo my son soja mazan fama y to yagajiyar tafiya? Cewar Abba tunkamin fawan ya gaidashi. Ƙarasawa yayi yana mannawa mahaifin nashi kiss agoshi kana yace "lpy qalau alhmdllh abbana ya gidan ? "Lpy qalau son. Good, mama barkada rana. "Yawwa barka fawan andawo lafiya? Tafaɗa tana Murmushi domin Hajiya Bintu akwai sanyin hali da Dattako. "Lpy qalau mama. Ɗan shiru babiyo baya can Abba yace "son miyake damunka ne naga duk kazama wani iri? Please gayamin idan akwai matsala? Ajiyar zuciya yasauke kana yace "akwai damuwa Abba, "last time abbey yayimun zancen aure kuma wlh lokacinda yabamu yakusa nikuwa gaskiya ƙanwata Nakeso bansaniba ko zaku bani, yafaɗa ashagwaɓe. "Tofa Masha Allah ai wannan abun farin cikine mizesa muhanaka kuwa wannan wacece? "Maisoon ɗin Dady, yafaɗa kanshi tsaye domin yayi alwashin seyayiwa muhseen baƙin ciki.. "kai Masha Allah amma gaskiya wannan zancen yayimun daɗi yanzu sabida kanason maisoon shine kake wani cin magani kana ɓata rai? Humm to shakuruminka Indai maisoon ce tazama taka anjima in sha Allah zansamu yaya Ishaq dazancen ayi komai aƙare..yawwa my sweet Abba haka nakesonji wlh, fawan yafaɗa yana rungume abban nashi...wani irin faɗuwa gaban A'isha yayi domin jitayi kamar itace za'ayiwa wanan kutsen yah fawan da sweetheart ɗin kuma batareda saninta ba inaa sam bazata bari hakan takasanceba, tanacan duniyar tunanin taji muryar mama tana faɗar....!



SAWUN GIWA paid book ne akan nera 1k kacal 👌 free page yakusa ƙarewa kuhanzarta biyan naku domin kusamu damar karanta shi har karshe domin bazan lamunci akaranta min wani abuna batareda anbiyani hakkinaba, please akiyaye🙏 idan kinshirya biya saki iya tura kuɗinki a wannan account ɗin 👉 2276776261 sha'awanatu ƙasim UBA Bank kana kitura shaidar biyanki awannan nomber 👉 07037092176. 🙏











Autar alheri ✍️
🐘🐘🐘 *SAWUN GIWA*🐘🐘🐘


🐘
🐘🐘
🐘🐘🐘
🐘🐘🐘🐘
🐘🐘🐘🐘🐘


Romantic love story 💋💓💞


Daga alkalamin✍️👇

Dr Yasmeen Ahmad

(Autar alheri ✍️)



Marubuciyar 👇


SIRRI

SOLDIER'S FAMILY

INGARMAM NAMUJI

MEJO NAJEEB

WAYE MIJINA

TANTIRANCI SABON SALO

IZZAR MULKI

BIG LADY'S

MY LITTLE SISTER

JEJI GIRL

JIKAR IYA DELU

SHUGER DADY

And NOW 👇

SAWUN GIWA LABARIN GIRMA AKAN GIRMA SOYAYYA MULKI ISA FINƘARFI RIKICI BAN MAMAKI DADAI SAURANSU DUK ACIKIN BOOK ƊIN *SAWUN GIWA*


Free

Book 1

Page 21 & 22

Last free page 🙏

Duk wadda ke buƙatar karatun SAWUN GIWA har complete tayi hanzarin biyan nata kuɗin domin samun damar karatu cikin aminci, ban yadda kowa yakaranta min abuna batareda yabiyani hakkinaba dan Allah akiyaye🙏

*Masu yimun document ɗin book bansaka kowaba kuma wlh duk wanda yayi banyafeba idan kuma nakama mutun dayimun hakan wlh ko aina yake senayi shari'a dashi domin besan wahalar danayiba kafin nayi abuna* 😥

"Tana faɗar "ko kusa Alhaji wannan ba Dede bane kafara tambayarshi shin maisoon ɗin tasanda zancen shi kuwa? Idan tasani shikenan babu damuwa amma idan batasaniba to kaje kafara neman soyayyarta tukkunna daga baya se ayi zancen aure dukkanmu zamuyi farin ciki da hakan, kuma kaida nahaifa umurnine ba shawaraba tabbas idan maisoon bata amince dakaiba to kaje kafara neman yaddar ta tukkunna. Tanakainan azancenta tamiƙe domin tasan yanzu Abba zega laifinta kuma tayi hakanne dan tasan tabbas maganar taje gun Abbey ko maisoon bataso se anyi acutarda ƴar mutane sabida son zuciya...ajiyar zuciya A'isha tasauke domin baƙaramin daɗi maganar mama tayi mataba.....shikuwa fawan wani mugun takaici yaji domin yasan zesha wahala kafin maisoon ta amince dashi dubada rashin tsoron yarinyar dakuma tsiwarta gaya besan abinda muhseen yakitsa mataba. Ajiyar zuciya Abba yasauke ganin yadda yaron nashi yayi kici kicin da fuska yace "kabarta my son kayi haƙuri ai bawani abin damuwa bane nasan ƙanwarka bazata ƙikaba domin Kanada duk wata nagarta daya dace ace namiji nada ita doline kowacce mace tayi alfaharin samunka amatsayin mijinta, sabida hakan kaje kawai kanemi soyayyar Tata kamar wadda mahaifiyarka tabaka umurni, nikuwa daga ranarda ta amsa aranar zan cimma yaya Ishaq asaka muku ranar aure, yaƙarasa zancen yana dafa shoulder ɗin shi sabida ya ƙarfafa mishi guywa. Ɗan shiru yabiyo baya nadan lokaci kana fawan ɗin yace "shikenan Abba in sha Allah zan yi hakan acikin satinnan zandawoma dazancen soyayyar maisoon. "Yawwa jarimin namiji ai nasan zaka iya domin soja da jarumta akasanshi, tashi kaje Allah yayima albarka.."Ameen Ameen Abba daga hakan yamiƙe yanufi bedroom ɗinshi.


A yau kusan kwanan maisoon 12 da dawowa daga saudia kuma suna waya da yaseer jefi jefi kala bata sake mishi harta dawo tana sake mishi, sabida fakewa dayakeyi da hajiyarshi yana samun doguwar magana da ita....daga gefe ɗaya kuma shirye shiryen bikin ƙasarsu maimoun sukeyi sosai domin ansaka amarya lalle kuma yau ne ranar kamu tun safe suna wurin ƙunshi, se yanzu suka fito yamma liss, kowacce anyi mata baƙin zane makyau itada A'isha, gidan suka nufa inda A'isha ke driving maisoon na gefenta. "Sweetheart Inaso zanyi wata magana dake please, cewar A'isha. "Okay inajinki wani abun yafarune? "A'a kawai dai zefarune to Inaso nagaya Miki ne dan kikwanta da shiri. "Okay inajinki minene? "Humm wai kinsan abinda yah fawan yaje yagayawa Abba kuwa? "A'a sekin faɗa minene? "Kedai bari sweetheart wai cewa Abba yayi ai yanasonki keze aura Ni wlh yabani mamaki, shine Abba shikuwa zeje yagayawa Abbey, amma mama tace sam bata yadda ba seya fara neman yardar ki tukkunnah nana ɗauka ma yazo Miki dazancen, taƙarasa zancen tana kallon maisoon da ko ajikinta, bakiji minaceba sweetheart naga babu inda kika damu? "Murmushi maisoon tayi kana tace "to mize damar dani sweetheart nadesan ba yadda za'ayimin auren dole kuma dan yah fawan yace yana sona ba abun mamaki bane domin mazan ayanzu ba kunyace dasuba duk abinda yazo musu arai zasu iyayi sabida Karki wani damu muyi sha'ani kawai. "Ajiyar zuciya A'isha tasauke kana tace "tabbas hakene zancenki sweetheart amma kinsan koda bakiso muddin zancennan yaje gun Abbey wlh se anyi kokin manta waye abbey kuma kinmanta yadda akayi auren anty Zainab ne? Damm gaban maisoon yafaɗi jin kalaman A'isha tabbas maganarta gaskiya ce domin bata manta yadda akayi auren anty zee ba a lokacin ita yah jawwal takeso amma beyi saurin yin maganaba har abokin Abba yazo nemawa ɗan aurenta kuma Abbey yabashi, daga baya dataji tace ita yah jawwal takeso akace sedai tayi haƙuri basataɓa canja magana idan sukayi, tofa hakan anty zee tahaƙura itada yah jawwal bayan sunci kuka har sun gode Allah amma ba wanda ya tausaya musu daga karshe ma dady yasaka yah jawwal yabar ƙasar shiyasa har yanzu beyi aureba, haka akayi auren anty zee kamar takashe kanta...taɓo maisoon A'isha tayi ganin tanata magana tayi shiru domin ita talulu duniyar tunani. "Yadai sweetheart? "Humm ina tuna yadda akayi auren anty zee ne wlh banmanta ba sweetheart shine gabaki ɗaya yarikitani. "To kingani sabida hakan wlh tunwuri idan akwai wanda kikeso kiyi gaggawar kaishi gun Abbey kar ayimiki yadda akayiwa anty zee domin kinganni anan wlh inada wanda Nakeso kawai bazanyi magana bane sabida bansan shi wayakeso ba dudda cewar ina fatar nice domin tabbas idan ban sameshiba wlh zanshiga tashin hankali sweetheart. "Tofa waye wannan yayi Miki mugun kamu hakan sweetheart? Maisoon ta tambaya cikin mamaki..."Humm kinyi mamaki ko? Aibazama kiyi mamaki ba sekinji kowaye?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login