Showing 81001 words to 84000 words out of 84332 words

Chapter 28 - BA SONTA NAKE BA Complete Hausa Novel

08 Aug 2026

150

ta naji salkamar ta, cikin ihun murna na fito na rungume ta zan iya cewa bayan yinin bakwai da akayi sai yau wani nawa yazo min dan haka cike da farincikin na tarbe ta ina tambayan ta Inna ta da mutanen gida tace min duk suna lafiya.


Bayan gama gaishe-gaishe na gabatar mata da sauran abincin da na rage ta fara ci muna hira cikin tsananin farincikin da kewar juna.


Shi kuwa Zafar tunda ya tafi gidan su hankalin shi na kaina dan ya kasa sakin jiki suyi hira kaman yanda suka saba, bini-bini sai kallon agogo yake har Abban shi ya gano shi yace" ya kamata ka tashi ka koma gida son dan my daughter tana bukatan kulawar ka musamman a halin da take ciki yanzu".


"Wani hali take ciki kuma?" Mom da tundazu taki saka baki a hiran nasu ta tambaya a d'an rikice.


"Ke kuwa ai zaki fimu sanin halin da take ciki tunda ke macece, yau ta tashi bata da lafiya wai tana fama da jiri da ciwon kai kinga alamun ciki sun bayyana a tare da ita amma fa a nawa hasasshen kenan ko kunje asibiti?" Abba ya amsa mata da wadatattacen murmushi saman fuskar shi yana kallon Zafar daya duke kai shima yana murmushin tare da girgizawa Abba kan shi.

"Ja'iri ji wani murmushi dan Allah Hajiya yaran yanzu da shegen son 'ya'ya suke" ya karasa yana dungure mishi Kai.

Mom da tayi suman zaune ko jin abinda yake fad'a ba tayi ba har yayi musu sallama ya fita ya bar ta baki bud'e.

Anan Kuma nida 'yar uwata sai hira muke zubawa yanda tun daga kofar shigowa zaka ji hayaniyar mu ba dan komai ba sai na labarin sabon saurayi da tayi na gidan mu take tana yayi mata amma tana gudun kada yaji ta tab'a aure da haihuwa ya guje ta...


Ni kuwa ina kara karfafa mata giwan cewa babu wanda zai kalle ta yace ta tab'a aure balle har ace ta haihu, muna cikin haka Zafar ya dawo gidan jiki a sanyaye amma tunda ya fara jiyo murya ta cike da nishadi muna hira yasa ya shigo da karfin shi, sallama yayi ya tsaya daga bakin kofa fuskar shi d'auke da tsantsan farincikin samu na a haka da yayi, bude min hannuwa yayi alamun inzo gare shi har zan watsa masa harara na tuna cewa ashe fa in a gaban mutane ne drama muke yi hakan yasa banyi musu ba na taso cikin wani yauki da ban san na iya shi ba na nufe shi tare da kashe da wani sexy smile.


Kafe ni yayi da ido ko kiftawa ba yayi yi har na iso gaban shi kaman zan shiga jikin shi sai na zille ina dariya nace" ga Yaya ta nan ku gaisa"

Shafa suman kan shi yayi da hannnu daya dayan hannun kuma yasa ya rike min hannu sannan ya kai duban shi ga Hajara da duk kunyan abinda ke faruwa ya rufe ta yace " babbar Yaya barka da zuwa" har da d'an risinawa kaman da gaske, cikin jin nauyi Hajara ta amsa suka gaisa duk yana rike da hannu na.

"Zo muje ki had'a min ruwan wanka wifey" yace yana kokarin jan hannu na zuwa parlor, tirjewa na fara kokarin yi tare da nuna mishi nayi bakuwa zan zauna wajan ta ya tafi kawai banyi aune ba naji ya d'aga ni cak in a bridal style yayi waje dani.

" Naji dadi sosai da nazo na same ki cikin koshin lafiya" yace yana bin ko ina na jiki na da kallo ,muna karasa fitowa parlorn na watsa mishi harara tare da kokarin sauka a jikin shi nace " Mallam kana over acting fa sauke ni dan Allah sai kace da wanda yake ganin mu a nan".

Cikin wani yanayi na sanyin jiki ya sauke ni kamin yace min wani abu na bar shi nan tsaye na shige kitchen nemawa Yaya ta abinda zata ci da rana , jiki a mace ya koma ya zauna tare da dafa kan shi tsakanin jiya da yau din nan bai san me yake damun shi he feels a different person.
[6/16, 9:22 PM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._



_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_


_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*


*_BA SONTA NAKE BA_*




✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*wΜΆΜΆΡ” Ξ±rΜΆΜΆΡ” Π²Ρ”Ξ±rΜΆΜΆΡ”rΜΆΜΆ'sΜΆΜΆ ΟƒfΜΆΜΆ sΜΆΜΆΟƒ gΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ*
*wΜΆΜΆΡ” wΜΆΜΆrΜΆΜΆΓ­tΜΆΜΆΡ” Ξ±sΜΆΜΆsΜΆΜΆΓ­dΜΆΜΆΓ­ΟƒuΜΆΜΆsΜΆΜΆlΜΆΜΆΡ‡ pΜΆΜΆΡ”rΜΆΜΆcΜΆΜΆΡ”Γ­vΜΆΜΆΡ” nΜΆΜΆΟƒ pΜΆΜΆΞ±Γ­nΜΆΜΆ,*
*sΜΆΜΆΟƒ mΜΆΜΆΞ±gΜΆΜΆΓ­cΜΆΜΆΞ±lΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ cΜΆΜΆrΜΆΜΆΡ”Ξ±tΜΆΜΆΓ­vΜΆΜΆΡ” gΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ* ✍ *,Π²Ρ”hΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ wΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆdΜΆΜΆsΜΆΜΆ.Ξ± pΜΆΜΆrΜΆΜΆΟƒdΜΆΜΆuΜΆΜΆcΜΆΜΆtΜΆΜΆ ΟƒfΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆ*ΜΆ *,sΜΆΜΆΞ±vΜΆΜΆΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ wΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆdΜΆΜΆsΜΆΜΆ, fΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆ Γ­tΜΆΜΆ wΜΆΜΆΓ­lΜΆΜΆlΜΆΜΆ* *cΜΆΜΆΞ±uΜΆΜΆsΜΆΜΆΡ” Ρ‡ΟƒuΜΆΜΆ nΜΆΜΆΟƒ pΜΆΜΆΞ±Γ­nΜΆΜΆ.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buΖ™ata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana Ζ™ara mana Ζ™arfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*



*43&44*



A wannan rana a nan parlourn ya yini kaman an dasa shi yana zaune sai kurb'an ruwa yake duk inda zan wuce kuwa sai yayi ta bina da ido kaman ya samu tv, ni dai ko kallo bai ishe ni ba dan yau wani tashen rashin mutunci nake ji dashi.


Sallah azahar kad'ai naga ya fita yayi a masallaci ya dawo a lokacin ni Kuma fitowa ta kenan daga kitchen hannu na d'auke da wani tray mai d'an girma da na d'aura kayan dad'i dana girkawa 'yar uwata, wuce shi nayi zuwa parlona inda na bar Hajara zaune tana kallo,nan tsakiyar parlour na ajiye na fita na had'o drinks masu sanyi a fridge na kara wucewa ta.

Ya d'an jima zaune wai ko zan dawo in kawo mishi rabon shi yaji shiru, murmushi yayi kawai tare da kad'a kai ya d'auki makullin mota ya fita ba jimawa sai gashi nan ya dawo da kaya niki-niki a hannu leda d'aya tak ya ajiye a parlorn ya wuce da sauran parlona ya same mu mun fara cin abincin muna hiran mu, ajiye kayan hannun sa yayi ya d'an kalle ni yace " pls ga kada ki manta da drugs d'in ki in kin gama cin abincin ki sha sannan ga fruits suma ki sha zaki ji dad'in bakin ki" gyad'a mishi kai kawai nayi ya juya ya fita yana waiwaye na.


"Zareefa gaskiya kinyi dacen miji nagari a wannan zamani da maza ba abinda suka iya sai wulakanta matan auren su, amma ki ga yanda yake tarairayen ki" cewar Hajara kenan, murmushi kawai nayi mata ba tere da na bata amsa ba na fara bud'e ledan fruits d'in a raina ina baki san waye shi bane har kike yabon sa.

A can main parlour kuwa Zafar zaune ya saka fried rice nd chicken daya sayo dan yaci amma ya kasa kwata-kwata bai fi spoon 3 yayi ba yaji abincin ya fita ran shi, tsaki yaja yana hararan inda muke bai san ya akayi haka ta faru ba daya saba da cin abinci na har baya iya cin wani abincin wani.

Kara kallon abincin yayi gashi dai so color full ya sha veggies amma sam bai ji wani taste ba a bakin shi,tattre su yayi ya ajiye a gefe ya sha fruits d'in daga baya duk ya kwashe su ya mikawa Baba mai gadi.


Har kusan la'asar muna tare da Hajara sannan tace zata koma amma zatayi kwana 2 a jere tana zuwa saboda akwai wani waje da Gwaggo Aisha take Aiken ta ita kuma bata son zuwa shiyasa zata rinka zuwa nan as ta tafi inda ta aike ta, ni kuwa cikin murna da jin dad'in zan samu mai taya ni hira har na kwana 2 na amsa mata da ina jiranta tazo da wuri.


Duk sauran kayan ciye-ciye da Zafar ya kawo ita na tarawa nace ta kaiwa su Ibrahim, ta amsa tana ta godiya na rako ta har bakin kofan main parlorn ta tafi.


Tana zuwa gida ta tarar da Gwaggo Aisha a tsakar gida tana jiran ta, ganin ta da manyan ledoji yasa ta fara washe baki domin taga alamun nasara a aikin bokan ta.

"Ya kika dad'e haka Hajara, kin gan ni nan tun d'azu nake zaman jiran ki" ta fad'a cikin d'aga murya yanda sauran 'yan gidan zasu ji.

Cikin kara fad'ad'a farar ta ta karaso gaban ta tare da ajiye kayan hannun ta murya kasa-kasa tace" gashi nan yace in kawo gida yana gaishe ki".

Wani irin shewa Gwaggo Aisha ta saka tana dariya tace" wannan duka yace ki kawo min lalle sirkin nawa ba wasa" murmushi kawai Hajara tayi ta shige ciki ta bar ta a nan sai bud'e su take d'aya bayan d'aya tana kara bud'a murya tana yabon kayan tare da yad'a habaici.

Dare nayi suna zaune suna hira da Gwaggo Aishan wayan ta ya fara ringing ganin number sabon saurayin ta ne yasa ta d'aga tana murmushi bayan sun gaisa yake ce mata bata ma tambayi sunan shi ba, nan itama tace ai ba sai ta tambaya ba shi ya kamata ya fad'a mata nan yace mata sunan shi Amadu.


Tashi tayi zuwa bedroom d'in su ganin Gwaggo Aisha ta ishe ta da waye ya kira ko Zafar ne? Da kai kawai ta amsa mata ta karasa shigewa daki ta barta tana ta murna.

*****************************

Da daddarem ma kin girkin girka komai nayi na kwanta Ina kallon wani series da nake matukar so a zee world ya shigo min da sallama na amsa mishi ciki-ciki kaman yanda shima ya min, tsaye yayi kaman me son cewa wani abu ko me neman wani abu ni dai bance mishi kala ba na mayar da hankali na kan tv.


"Ya jikin naki?" Naji muryan sa kaman daga sama.

" Na warke" na bashi amsa ba tare da na kalli inda yake ba.

Bai kara cewa komai ba ya fita nabi bayan shi da harara, a raina ina wa zai kara kula ka kaci zalin shi ko ka mishi mugunta da ka saba.

Shirin bacci na nayi bayan na gama kallon, na sha bacci cikin kwanciyar hankali sab'anin Zafar daya kwana cikin wani yanayi da shi kan shi ba zai ce ga inda ya dosa ba shi dai kawai so yake ya zauna kusa da ni ko kuma inda zai samu yayi ta kallo na, tun yana d'aukan abin da sauki har ya fara jin haushin kanshi wai me yasa ya damu da wani lamura nane? in ya kalle ni uban me zan bashi illa ma in b'ata mishi rai da sabon rashin kunya da na samo, bayan wannan ma tun lokacin da ya d'auke ni ya fito dani parlor jiki na da nashi da ya had'u yake kewar d'umin jiki na tare da kamshin jikina mai sanyi da tsayawa a rai sai dai dole ya matse gudun kada raini ya shiga tsakanin mu.

Ya san bakomai yasa ya damu da lamurana ba maybe tausayi na da ya fara jine kawai dan yaji bani da lafiya, " hakane ma" ya furta a sarari yana mai kara bawa kanshi karfin guiwa da kyar dai ya samu bacci yayi nasaran sace shi a wannan daren.


Da washe gari na tashi da sauki dan wannan nauyin da zuciya ta yayi jiya yayi sauki hakan ne ya bani daman fara aiyuka na kaman yanda na saba, bayan na gama share ko ina tass na gyara sannan na shiga wanka ban dad'e ba na fito light make-up nayiwa fuskata na shirya kaina cikin English wears riga da skirt pink color anyi mishi ado da flowers blue hakan yasa na yane kai na da blue vail, kayan bai wani matse ni ba amma ya zauna das a jikina ya min kyau sosai.


Zagewa nayi ina girki sanin cewa Hajara zata iya zuwa at any moment,kayan dad'i nake dafawa dan haka gidan ya cika da kamshi masu dad'in shaka,kamshin nan shi ya fito da Zafar daga d'akin shi sai bud'e hanci yake yana lumshe ido tsohon yunwar shi ta jiya na dawowa sabo fil.


Kofar kitchen d'in yazo ya tsaya yana kallon yanda nake aiki gaba daya hankalina yana kan aiki ban san ma da zuwan shi ba,shi kuma controlling d'in kan shi yake akan abinda zuciyar shi take ingiza shi ya aikata dan ji yake kaman yaje ya rungume ni yaji wannan d'umin jikin nawa da wannan daddadan kamshin mai sanyaya zuciya amma ya daure yayi gyaran murya Wanda ya d'an firgitani na juyo a d'an razane na ganshi tsaye cikin kayan baccin sa farare kal da alamu tashin sa kenan ko wanka baiyi ba.


Kaman ana min dole nace mishi" Ina kwana" saboda ganin babu wasa a fuskar shi, maimakon ya amsa min sai cewa yayi " ki tabbata kinyi da rabon masu aiki tunda kin samu lafiya" sai da na turo baki sannan na bashi amsa da cewa " ni bada su nayi ba dan Hajara zata zone shiyasa nayi girkin".


Kara had'a fuska yayi yace" try anything stupid and see"Yana gama fada ya juya ya fita ba tare da ya jira amsa ta ba, " zaka gani kuwa ai ka daina cin abinci na a gidan nan tunda kai d'an wulakanci ne"nace ina cigaba da aiki na.


Bayan kaman 30 minutes na kammala komai na jera su kan try na fito na wuce parlour na ba tare da nabi ta kan shi da na gan shi zaune a main parlour ba, shirya su nayi anan tsakiyar parlour na tare da kara saka turaren wuta na dawo inda na shirya kayan abincin kenan sai gashi nan ya shigo da fuska kaman an aiko mishi da sakon mutuwa.


"Ina na masu aikin da na gaya miki?"
"Banyi dasu ba na amsa mishi ina kara gyara zamana a gaban warmers d'in, bai saurare ni ba direct kai tsaye ya karasa shigowa da niyyan zai d'auke warmer d'aya, cikin azama na kai hannaye na duka biyu na rungume su a kirjina tare da turo baki ina " ni wallahi ka bar min kayana".

Bai saurare ni ba yana zuwa yasa hannu ya d'agani cid'ak kaman wata karamar yarinya zai ajiye ni a gefe na rike shi gam ina "wallahi ba zaka d'auka min ba ni banyi da rabon ka ai na san cewa kai kake cinyewa ba wasu masu aiki da kake bawa".


Yanayin yanda na cukuikuye shi na rike sai ya haifar mishi da kasala kuma dama abinda tun jiya zuciyar shi ta kwad'aitu da shi kenan,da gangan yayi fara kiciniyan kwace kan shi ni kuma ina kara rike shi akan ba zai d'auka ba kan kace me kokuwa ya kaure tsakanin mu anan yayi amfani da wannan daman hannayen sa babu inda basu je ba a jiki na, ni kuma a hauka na ban kawo komai a raina ba na zata duk cikin kokarin kwace kan shi yake a hannu na.

Sallaman Hajara ne yasaka shi saki na cikin sauri ya tashi itama Hajara cikin sauri tayi hanyan parlour dan tunanin ta wani abu daban ya bata, murmushin mugunta shimfid'e a fuskar shi yace " ga tsaraba nan kin tari yayar ki dashi,sai ki san bayanin da zaki mata "sai a lokacin na fahimci abinda ya faru duk sai naji kunya ya rufe ni me ko zan cewa Hajara ai babu abinda zan fada in wanke kaina,dafe kaina nayi cike da takaicin abinda ya faru tare da dana sanin me yasa na biye shi dana sani da barin shi nayi ya d'auki abinda yake so.

Plate ya d'auka ya bud'e warmers d'in ya d'ebi abinda yake so ya fita abin shi ba tare da na sani ba domin nayi nisa cikin tunani,ita kuma Hajara bata tsaya a main parlour ba direct fita tayi ta zauna a inda ta zauna jiya tare da dafe kai duk Gwaggo Aisha taja mata wannan abin kunyan asuban fari ta taso ta kan ta shirya tazo kada ya fita aikin su ya koma baya.


Hankalin shi kwance yaci abincin sa yana ta sakin murmushi shi kad'ai kaman wani sabon kamu,he really enjoys what happened between us now, fitowa nayi main parlour ganin zaman ba zai fice ni ba .


Wani tukikin bakin ciki ne naji ya tokare min wuya ganin yana ci min abinci,duddubawa nayi ko zanga Hajara amma ko alamarta ban gani ba.

Komawa nayi cikin Ina ta kumbura saboda haushi na san kila ta koma gida shikenan ya rusa mana budget ina ta murna yau ma zamu yini muna shan hiran mu sai gashi ko gaisawa bamuyi ba ya kore ta.


Zaman ta kaman da 15 minutes sai ga Amadu yazo yin aikin sa, maimakon yayi aikin suka bige da hirar su cike da son junan su har Zafar yazo ya wuce da mota bai gama aikin ba ganin sa ne yasa ya maida hankali kan aikin sa,tana zaune ya kammala itama ta mike tace zata koma gida tare suka fito ya rako ta har gida sannan suka rabu cike da kewan juna.


Baba Yana zaune

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login