Showing 84001 words to 84332 words out of 84332 words
a majalisar shi tare da 'yan maula daya samu yana d'an miko musu da na cefane,daga nesa suka hango motocin sojoji har guda 2 sun nufo su, Baba Yana ganin su cikin sa ya murd'a ya mike jiki na b'ari yace "yau kuma me ya kawo wa'yan nan azzaluman cikin anguwan nan" yana magana ne yana nufan hanyan gida amma ko ten step baiyi ba motocin suka karaso tun kamin motan ya tsaya suka fara durowa daga ciki tare d'aga musu tsawa "kada wanda ya motsa daga nan".
Cak Baba ya tsaya yana tsiyayen gumi duk ya firgice.
"Waye Mallam Hassan a cikin ku?" Suka tambaya.
A tare mutanen wajan suka nuna baban mu da yake tsaye yana karkarwa.
"Kai ne Mallam Hassan ?" Kai kawai Baba ya iya gyad'a musu.
" Common my friend oya! oya! shiga mota mu tafi"wani daga cikin motan ya fad'a, wasu guda hud'u nufo shi fuska a murtuke babu alaman sun tab'a koda murmushi balle dariya, hannu Baba ya shimfid'a yana kokarin rokon su tare da basu hakuri , d'ayan ya d'aga katon bindigan hannun shi yace yana musu gardama wallahi zasu harbe shi a wajan su wuce kuma sun harbe banza.
Gudu-gudu Baba ya nufi wata bakar mota da sai yanzu ya lura da ita suka hankad'a shi ciki babu b'ata lokaci suka fice daga anguwan da matukar gudu.
" Allah ya kiyaye mu da basu d'ubi kowa daga cikin mu ba sai shi kad'ai suka nema" inji wani dattajo cikin 'yan zaaman majalisan.
"Ni dama wannan kud'i na Mallam Hassan akwai ayar tambaya ace mutum yayi kud'i lokaci d'aya"? Wani ma ya kara nashi.
" Ai ko yanda suka ciko motoci saboda shi kad'ai kuma kun san abin azimun ne"
" Kunga yanzu ba lokacin wannan bane mu watse kamin su canza ra'ayi su dawo su had'a da mu"
fad'an hakan ke da wuya duk suka watse cikin abinda bai fi kiftawar ido ba, nan da nan labari ya cika anguwa cewa sojoji sun kama Baba sun tafi dashi.