Showing 66001 words to 69000 words out of 77938 words

Chapter 23 - KURUCIYAR MINAL COMPLETE

11 Jul 2025

3850

nifa banason kina Karin gashi ba dole kanji yayi kaikayi ba. Dago da kanta tayi ta kalleshi
sannan tace Allah ya kiyaye in saka izgan doki ko gashin roba a kaina, wannan gashi nane.

Tabawa yazeed yayi yaji laushi ga kamshin sun flower shampoo dake tashi, lumshe ido yayi
sannan yace kina kudin gashinki ne wannan? Ta gyada kai hancinshi yakai yana shinshinan
gashin sannan yayi pecking yace kamshi. Murmushi tayi tace kanaso ne?yace sosai ma ki
daina saka hula kinji ki barmin ina gani. Gyada kai tayi sannan ta kara kwanciya ya fara Sosa
mata kan a hankali sai lullumshe ido takeyi.
Can yazeed yace ina rigannan na jiya tace yanakasan wannan yace tashi ki cire wannan din.
Mikewa tayi ta core dukda tanajin kunya amma tadan fara sabawa da nuna jikinta wa yazeed.

In ka ganta sai kace yar India irin model dinnan sanda yazeed ya kare mata kallo iya son ransa
itako sai kokarin gyara Rican rake Dan ko guiwa bai karasa mata ba tashi ana ganin Komai.

Kwanciya ta sake yi yaci gaba da Sosa mata kai yana mai shara bayanta a hankali a haka har
bacci ya dauketa bata sani ba.
Daukanta yazeed yayi yakaita kan gado sannan shima ya hau ya kwanta a gefenta sannan ya
janyota ya rufe musu kafarsu da bargo bayan ya cire jallabiyarsa.

Shidai a Gaskiya akwai wani special Abu da yakeji a zuciyarsa game da minal kuma Idan dai
abinda yakeyi wa zakiyya shine so to ba son minal ya keyi ba wani Abu ne na daban shima....


*Irin wannan murmushi haka ai sai bakinki yayi ciwo. Ko duk jin dadin chaptern nanne?*

Anyway don't forget to comment and tell a friend to tell a friend

1 to tell 10 sukuma 10 to tell others.
Idan kika karanta ke daya kinyi son kai�

Miss untichlobanty💕

10 December, 2019
[1/11, 2:29 AM] Mzz_Untichlobanty💞: *🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆*

*🌹by miss untichlobanty🌹*

*Wattpad:* mzz_untichlobanty

*Instagram:* miss_untichlobanty

*CHAPTER 54*

Koda ya Abubakar ya dawo daukan Laila yayi direct sai gidan aunty fauziyya sannan yace kar
ta Fadawa kowa abinda ya faru Dan bayaso su fuskanci matsala Idan yace zai aureta sannan
abin zai iya shafan yaransu sannan next week zai kaita asibiti domin a tabbatar babu shigan
ciki.
Itakam kuka take tayi Dan abin ya fara daura mata kai Dan har yanzu bata dena bleeding ba ga
irin azaba da takeji amma dai tayi deciding zata Fadawa aunty fauziyyan matsalanta tunda ita
daya ne tasan abinda ya faru da ita.

Koda suka iso sallama ya Abubakar yayi. Aunty fauziyya ta fito da Sauri domin dams su take
jira ta riko Laila tana mata sannu da kai kawai take amsawa. Fiki ta Shiga da ita yayinda akabar
ya Abubakar a parlour.

Direct toilet ta nufa da ita sannan tace ta fara core kayanta tana zuwa bata ta sallami ya

Abubakar.
Parlour ta sameshi sannan ta tambayeshi Karin bayani tunda bayani kadan ya mata a waya.
Nan ya fada mata duk abinda ya sani da abinda Laila ta fada masa. Lokacin da ya gama bayani
mamaki ya cikata tana kasa magana can ta sauke ajiyan zuviya tace Allah ya rabamu da
azzaluman Yan uwa da dangi ya Abubakar yace Ameen. Aunty ni zan wuce tace tsaya kasha
ruwa mana yace a ah babu Komai ai ina godiya amma aunty ki tabbatar babu Wanda yaji Dan
Allah tace karma damu Insha Allah babu Wanda zai sani yace na gode Allah ya saka Idan kuna
bukatan wani Abu sai Ku kirani tace Toh ba matsala sannan ta rakashi koda ta dawo ta sani
Laila yanda ta barta babu wani kayanta da tacire.

Aunty fauziyya ta riko kafadan ta tace hakuri zakiyi acikin gama ya gama Koma gode Allah kin
zamu mai sonki tsakani da Allah Idan ba haka ba ai Anan zaki fuskanci tashin hankali.
Acikin sheshekan kuka tace ni babu abinda ke damuna illa yadda jinin yaji ya tsaya kuma
marata azaba takemin.
Shiru aunty fauziyya tayi tana nazari kamin can ta girgiza kai domin kawar da tunanin da take
Dan ba Abu mai yuwuwa bane.

Ruwan zafi ta hada mata sannan tace ta Shiga ciki kuma ta tsaya akanta Dan tasan Yan Mayan
yanzu ba sason ruwan zafi(Cesar tsofi)
Fire kayanta tayi amma tabar vest sannan ta Shiga ga mamakin aunty fauziyya batayi ihu ko
nuna wani alamu na Cewa taji ciwo ba Kamar yadda take zubda mini. Don't ita a tunanin ta idai
har taji ciwo da yake zubda wannan jinin to ko tafiya bazata iyayi ba. Kai akwai alamar tambaya
Anan wurin.
Matsowa tayi kusa da ita ta zauna sannan tace Laila tana mai riko hannunta dago da rinnanun
idanunta tayi ta kalleta. Auntyn taci gaba da Cewa zan miki wani tambaya bawai Dan inaso in
banbaro miki tsohon ciwo ba sai Dan in gano wani abu. Gyada kai tayi alamun tanaji.

Tace kin tabbata Cewa wani abu ya Shiga tsakaninku?gyada kai tayi har lokacin hawaye basu
bar sintiri a fuskanta ba tace Kiyi min bayanin yadda Komai ya faru Dan kinsan Abubakar bazai
iya min bayani a faiyace ba.

Nan Laila ta fada mata yadda goje ya mata karya har ya kaita dakinsa da irin kokuwar da sukayi
har izuwa sanda ta suma sannan ko da ta farfado ga yananyin data tsinci kanta.
Jinjina kai aunty fauziyya tayi sannan tace wato kina nufin bakiji sanda ya Shiga jikinki ba har
kika suma kawai dai kinji maranki ya murda? Ta gyada kai.

Sake kallonta aunty fauziyya tayi tace yaushe ki kayi al'adar ki ?shiru tayi kamin tace kwana 28
da suka wuce.
Aunty fauziyya tace bayan kwana bawa yake kewayowa? Tace hakan kewayo min bayan kwana
27 ko 29 tace kina nufin jiya ya kamata ki fara. Ta Daga kai tana mai nazari domin itama ta fara
hada possibilities da aunty fauziyya ke hadawa.
Tace Idan kina al'ada kina ciwon Mara ne?ta girgiza kai alamun a ah

Aunty fauziyya tace tambaya na karshe shin kinajin wani zafi hakannan Kamar ciwo Daga ciki
banda na maranki? Ta sake girgiza kai.

Murmushi aunty fauziyya tayi tace ina tunanin bayi raping dinki ba. Kallon neman Karin bayani
Laila ta bita dashi tace ban tabbatar ba amma alamun sun nuna bai miki Komai ba ni a ganina
kafin ya miki wani abu al'adarki tazo Dan haka dole ya rabu dake.

Atake Laila ta fito Daga ruwan daya Koma jaa Dan basu ma lura da launin ruwan yana canjawa
ba.
Kusa da aunty fauziyya tazo tace toh amma me yasa Mara ta kemin ciwo? Ta fadi hakan tana
mai daina zubda kwallah Dan hope ya samu.

Aunty fauziyya tace abu biyu nake tunani ko stress yakawo miki cramps din ko kuma sauyin
jikinki Dan wasu Idan suka fara baya musu ciwo da sunyi shekara 18 sai ya fara cramps wasu
kuma da ciwo zasu fara da sunkai 18 sai ya dena wasu kuma kwata kwata baya musu ciwo
wasu kuma da ciwon zasu fara kuma ko sunkai 18 baya dainawa sai sunyi aure yake ragewa.
Jinjina kai Laila tayi tace aiko 18th birthday na is few months Away. Aunty fauziyya tace bari na
kira wata kawata likita ce ta dubaki.
Dakinta yaje ta dauko wayanta sannan ta kira kawarta ta mata bayani a takaice. Nan likitan tazo
ta dubata tace babu wani abu daya sameta mensuration ne kawai. Dadi kashe laila. Painkillers
ta bata sannan tace ta rage damuwa Dan shi yayi causing zuban jinin dayawa. Murmushi tayi
tace Insha Allah Dan farin acikin daya lullubeta a wannan lokacin tama manta da Cewa an mata
rasuwa kuma mahaifiyarta na asibiti.
Kiran ya Abubakar aunty fauziyya tayi tace yazo da gaggawa akwai abinda zata fada mishi
shiko duk ya tsure karfa aje cikine da ita dukda ko da wuya a gane cikin kwana daya inba Anyi
test ba.

🌹........

Itakam auntyn Laila da ta dawo bata ganta ba bata wani damu ba ta dauka gida ta tafi. Itace ma
me Dan kokarin da take zuwa tana Dan zama akan ummin nasu Dan wasu Daga cikin dangi
Cewa sukema Wai bata lokacin ne su zauna akanta Dan babu abinda zai hanata mutuwa. Sai
kace su suke kashewa.
Koda taga har safiya shiru babu Laila babu alamarta kawai sai ta kirawo nurse tace ta kula da
ummin zataje gida tayi wanka.

Allah sarki umminsu lailai!duk abunnan da take fuskanta saboda ita daya mamanta ta Haifa
kamin ta rasu wanda ake zargin tsafi akayi mata. Shiyasa kaf Yan uban babu mai sonta saboda
irin kaunar da babansu ke nuna mata.
Auntyn nan ce ma suke dan Fadawa kaf gidan.

Gida ta wuce abina ta Shirya sannan ta dawo asibitin wayan lailan ta kira taji a rife kawai sai
tace bari zata sake gwadawa anjima maybe network ne sannan ta zauna taci gaba da taryan
kawayen Ummi Yan gaisuwa da dubiya.

🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹

Abangaren su minal kuwa ita ta fara tashi jinta kwance jikin yazeed yasata yin murmushi
sannan tadan kamo sajen dake kwance a fuskansa luf luf tana wasa dashi........

*Gaskiya na gode sosai da supporting dina da kuke yi Allah ya biyaku.*

*Sainaji comments dinku, yau bakuga yanda na dinta murmushi da ina karantawane ba Kamar
wata shashasha.*

*Insha Allah zanyi kokari ina yi muku reply*

*Ya kukaga yadda na warware matsala Laila?yayi ko?*

Karamarsu babbarsu ce fa�

Miss untichlobanty💕

11 December, 2019.
[1/11, 2:29 AM] Mzz_Untichlobanty💞: *🏆🏆KURUCIYAR MINAL 🏆🏆*

🌹by miss untichlobanty🌹

*CHAPTER 55*

Yazeed jin Kamar ana Jan gemunsa yasa yadan bude ido ya kafawa minal wacce Keta jajjan
sajen nasa Dan batama lura da Cewa ya bude idonsa Ba.

Hannunsa yasa ya riko hannunta da take ja masa gemu yace kazame yau kuma da gemuna
za'ayi wasa? murmushi tayi tana kifa fuskanta a faffadan kirjinsa mai dumi da sanyin kamshi.

Murmushi yayi mai Sauti yace humm ! Yar kazame taga handsome. Dago da fuskanta tayi tana
mai kicin da ido tace Allah yazzy baby Idan ka Kara cemin kazame zanyi fada dakai.

Rife ido yayi yace oooo not this name again please ki daina cemin yazzy baby Wai bazaki
manta bane?tace har abada kuwa. Yace haba kazame na please ki dena cemin Yazzy baby
tace saide Idan zaka daina cemin kazame yace to me kikeso in dinga ce miki?kinaso in dinga
ce miki beauty?kindy? Sweet? Cup cake?cutie pie? Bl..........

Datseshi tayi tace ni banaso kawai ka dinga kirana da abinda kake kiran..... Um..... Ka gane ai
ta fada tana kara sa dayan hannunta dake free Wanda bai rike Ba.

Yace ah ah ni ban ganeba,tace yadda kake kiran aunty uwar gida. Dan zaro ido yayi yace kina
nufin zakiyya?Daga kai tayi yaja hancin ta yace na ganoki wato kishi kikeyi.

Bata rai tayi tace ni Ba kishi nake Ba yace haba my baby Nasan fa kishina kikeyi turo baki tayi
tace ni Ba kishi nakeyi Ba. Yace Toh me yasa bakya kishina ? Tace saboda me yasa zanyi
kishin ka?

Yazeed's POV

Shiru Nayi jin tambayan data aiko min don bansan yanda zan amsa mata Ba.
Bansan lokacin da bakina yace saboda kinaso.
Murmushi taci gaba dayi da alamu bata dauki abinda na fada da muhimmanci Ba. Girgiza kanta
tayi sannan tace ni bana sonka kawai kai aboki nane.

Sanda zuciyata tayi tsalle dukda Cewa nuna ban tabbatar da Cewa songs nake Ba amma da
tace bata sona take zuciyana ta fara suya. Da alamu ta lura da yanayin Dana Shiga domin
atake naga damuwa dauke a fuskanta saide abinda ya bani mamaki sakan gemuna da tayi
saijin lallausan hannunta nayi akan kumatuna tana goge wani Abu mai ruwa. Innalillahi wa'inna
ilaihi raji'un kuka nakeyi.

Minal's POV

Ni ban dauki abinda yake fada da muhimmanci Ba Dan gani nake wasa yakemin. Ya za'a yi
mutum Kamar ya yazeed ga kudi, ga kyau, ga Suna,ga daukaka yace Wai sonshi nake?
A Gaskiya na kamu da dinshi Ba tare Dana Shirya Ba domin bansani ina sonsa Ba,sai ranan
Dana sameshi da zakiyya a parlour Suna hadiye fuskan kuna ji Nayi Kamar na mutu boyewa
kawai Nayi.

Ganin yana jiran na bashi amsa yasa na girgiza kaina cikin shiririta na nace bana Sonka kawai
kai aboki nane. Mamaki tare da tashin hankaline suka kamani ganin hawaye na saukowa Daga
idanunsa bansan sanda nasa hannuna na goge masa ba. Me yake shirin faruwa ? Me hakan ke
nufi? Me yasa yake kuka Dan nace bana sonshi? Yana sonane?
MY POV

Yazeed ne ya rasa yanda zaiyi Wai kuka yakeyi?kardai dagaske Sonta yakeyi to amma yaushe
ya fara sonta? Ganin shirun yayi yawa yasa ya hade bakinsu Ba tareda yayi Komai Ba abinda
ya basa mamaki shine mayar masa da tayi Dan haka baisan lokacin daya kara zafafa lamarin
Ba. Sanda yaji zasu mutu saboda rashin numfashi ya sake mata baki.

A Dan kunyace ta tashi ta fice Ba tareda suncewa juna komai Ba.
Dunkule Hannu yazeed yayi sannan ya naushi iska. He ruined everything! What if da haske
take bata sonshi?yayi gaggawa wajen nuna mata abinda ke ransa even though it was not
intentional. Shima bai Shirya ba, yanzu ya zaiyi ya gyara abinda ya bata.

🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹

Zaliha kam though time take bawa Yan Maiduguri Dan Cewa tayi dole a miyar da ita Kaduna.
Duk masifar inna sanda ta hakura ta bada gari.
Nan aka lallaba zaliha akace tayi hakuri gobe gobe zasu dawo Kaduna amma sai ta yarda
tasha tsuminta.

🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹

Ya Abubakar yana shigowa Laila ta danno da gudu ta rungumesa. Shidai baisan me ya faru ba
amma ganin yadda take farin ciki kuma ta wartsake yasa yasan Cewa alkhairi ne ya faru.

Janyota yayi har suka zauna yana dariya yace aunty fadamin abinda yasa Laila na irin wannan
farin ciki.

Dariyan manya aunty fauziyya tayi kamin tace kafin wannan yanzu dai ka saketa tunda ba'a
daura auren ba sai a lokacin ya lura da yadda suka kankame juna cikin jin kunya Laila ta gudu
ciki yayinda ya cire hula yana sosa keya.

Aunty fauziyya tace ja'irin yaro ina ganinka Kamar salihi murmushin borin kunya yafi yace ba
haka bane aunty.
Tace to Nide albishirinka yace goro kuma fari kamin ma ki tambaya.
Dariya tayi tace todai in fada maka babu abinda ya Shiga tsakanin Laila da Dan iskan yaronnan.
Nan ta fada masa yadda ta gano da yadda suakyi da likita.
Godiya ya dinga yiwa Allah harda sujjada baisan sanda hawaye ya zubo masa ba. Zaunar dashi
tayi akan kujera sannan ta Dafa kafadan sa tace ba kuka zakayi ba hamdalan da kayi shine
dai-dai addu'a zaka cigaba dayi allah ya kareku Daga sharrin makiya yace ameen.

Kicewa lailan ta samoni a mota zamuje gidansu yazeed tace Toh sannan ta Shiga ciki.
Fita yayi ya kirawo almajirai. Nan ya dinga daba musu kudi sanda ya raba sama da 10k.

Laila da ta fito sai murmushi take har tayi wani Dan kyau hakannan. Kai kwanciyar hankali dadi
gareshi.
Gaba ta Shiga ta kwame ya Abubakar ma ya Shiga driver's sit. Belt yasa sannan ya kunna
motan hannunta ya kamo ya sumbata ta warce tana turo baki yace ya akayine gimbiyata? Tace
ba'afa daura auren ba kake rikeni yace astagfirullah wallahi duk cikin dadin ne ni na manta ma
Allah ya yafemin tace Ameen.

Motar su suka fita Suna masu jin dadi sai gidan oga yazeed.

🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹

Abangaren su yazeed kuwa minal cikin yar iskar rigannan ta nufi kitchen kuma bilhakki da
Gaskiya yunwa takeji Dan 10am ma ya wuce ko time din canja Riga batada shi.
Hamdala tayiwa Allah Dayasa akwai sauran Mara 3 a tuwonsu na jiya Dan da babu da idomie
zata dafa.
Aiko nan ta daura dumame ziciyarta na wurin yazeed da yanayinda ta barshi yayinda takejinsa
a jikinta.
Yazeed ko shiru yayi kawai Dan bai Masan me ya dace yayi a halin yanzu ba kawai sai ya mike
ya fada wanka bai wani bata lokaci ba ya fito dai dai lokacin wayarsa ta dauki ruri dubawa yayi
yaga mom ne hakan yasashi yin murmushi Dan yayi kewarta Rabon dayaji muryanta tun sanda
tayi masa fada.
Dauka yayi tare da fadin my sweetheart kaif asbahati? Murmushi tayi Dan itama tayi kewan Dan
nata tace lallai Abu yayi dadi tunda har ka fara manta lokaci nida nake India ne yanzu safiyata?
Yace sorry sweetheart kinsan Nayi missing dinki fah.
Murmushi tayi tace abinda yasa na kiraka kenan Dan gobe ina tafe. Murmushi yayi amma
saboda shekiyanci irin na yazeed yace noo!sweetheart karki dawo zaki batamin honeymoon
dina.

Kama ha'ba tayi Kamar yana kallonta tace dannan kace Abun naka ya girmama ! Lokacin Dana
aurama ba iskanci zaka min ba? Ta fadi hakan sounding like a drama old lady.

Dariya yazeed yayi yace Allah ya kawomin ke lafiya my sweetheart kinsan fa you are my first
and last love. Mom tace first dindai amma last din kam....

Yace tunda kince haka to hakan ne. Kinji abinda ya faru da zakiyya kuwa?tace me ya faru?
Yace ai.............
Nan yazeed ya kwararo mata bayani tace subhanallahi Allah ya Kare na gaba toh, yasa kuma
haka shine mafi alkhairi yace Ameen. Muryan Jamal ya jiyo yana Cewa my man zan biyo mom
fa Dan wallahi inaso inzo in kalli love show kyauta Ba tare da na yanki ticket ba. Mom ne ta
make keyarsa yace ouch da zafi fa. Mom tace araftu(na sani).
Nan su kayi sallama yazeed nata dariya yayinda mom Keta surfawa Jamal masifa Wai a
gabanta zaina mata zancen soyaiya tsabar bashida kunya.

Anyway, don't forget to menene ma?yauwa comment andddd share�

Takuce karamarsu babbarsu

Miss untichlobanty

12 december,2019.
[1/11, 5:13 PM] Mzz_Untichlobanty💞: *🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆*

*🌹by miss untichlobanty🌹*


*CHAPTER 56*

Bayan Kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login