Showing 21001 words to 24000 words out of 77938 words
inkika gansu
Kamar masu cutan ehmm......kwa..?!kwash....
Mom tace kwashoko
Minal ta gyada kai kamin tace kwarai shi cutan tamowa Ba
Sai tace ganan gidan mun iso
Tsayawa sukayi suka sauko daga motan almajirai da masu tuyar kosai da samarin anguwa Yan
zaman kashe wando Suna bawa idonsu abinci
Acikin Land cruiser fara kal suka zo
ko minal ma tasha mamaki lokacin da akace Anan zasu tafi dan San da akayi cakwakiya da ita
tukun tahau domin tala Cewa akayi in bata hau Ba za'akira oga sir
Saukowa minal tayi zata antaya da gudu mom tace daughter tafiya zakiyi ki barni ?
minal tace Ahe tare tare zamu higa
(tofa minal wannan phonetics din Yan kauye ko daga ina?)
Shiga sukayi yayi da akabar malam bala awaje domin jira
ASSALAMU ALAIKUM INNATA !INNA!!INNAROS!
Hazbiyallahu la'ilaha illahuwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem wa nakeji Kamar
aminatu na
Inna ke fadin haka cikin murya mai alamun zatayi kukan dadi
Fitowa tayi yayinda baba yake biye da ita rike da hotan minal a hannunsa domin kaiwa gidajen
talabijin
Let me take a nap,hmm da fatan kunyi enjoying long chapter nan mude je zuwa
Ina team zakiyya ne ?are you happy da suka dinke da yazeed?
Team minal kada kusami damuwa everything happens for the best a gaba zaku gane dalilin
dinkewar
Team yazeed how far mutumin naku fa zai danyi chilling inji Yan birni
Masoya Ina jiran comments dinku
Your comment determine the longness and sweetness of next chapter
Love you all takuce
Miss untichlobanty
23th August, 2019
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty: KURUCIYAR MINAL
by @mzz_untichlobanty
*CHAPTER 20 HIGHLIGHT*
Am so sorry, dear readers! wattpad Suna bani headache,my chapter 20 is missing and I don't
plan on rewriting it saina gama novel din duka so here is a summary of what it contain:
Emotional moment akayi sharing tsakanin minal da iyayenta yayinda mom tace musu ai bige
minal sukayi Allah dai ya kare bataji ciwo sosai ba saboda gudun kar hankalinsu ya tashi yasa
bata dawo da minal dinba.
Minal tayi 'kiw da ido mom ta mata alamun karta damu nan su inna suka yiwa mom godiya tana
kara nasu hakuri.
Suna zaune cikin parlour minal tace zata gidansu zaliha akace yaje amma ta kula.
Mom tace tanson yin magana mai mahimmanci dasu daidai nan ya abubakar ya dawo daga
zariya yana tambayan ko an sami minal akace aiko ba gaisuwa yayi sallama ko? Hakuri ya
hada sannan yace shima ayi maganan dashi.
Nan aka gaggaisa sannan akayi masa bayanin Wacece mom. Nandai mom tayiwa su baban
kalamai masu kashe jiki sannan ta nemi auren minal kuma tana fata insun yarda ta turo uncles
din yazeed next week.
Miss untichlobanty
3 - CHAPTER 21-30
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty: KURUCIYAR MINAL
By @mzz_untichlobanty
*CHAPTER 21*
Shiru parlourn yayi yayinda kowa ke nazari aransa
mom tana fata Allah yasa su yarda
Yayinda baba ke nazarin me Yan anguwa zasuce ai Dan abin duniya ya aurarta
Yayinda inna ke Mazarin anya minal zata iya zaman gidan miji kuwa?
Yayinda ya abubakar ke farinciki finally dirty sister dinshi ta samu miji nagarcacce Duba da
mutuncin mahaifiyarsa kuma dai ruwa da kankara Abu daya ne samfuri ne kawai ya banbanta
Baba ne ya dago ya kalli mom kamin yace agaskiya hajiya.........
Minal koda ta fito hanyan gidansu zaliha tayi malam bala ne yayi saurin kunna mota tare dayi
mata horn sannan ya zuge glass yace hajiya kihau nakaiki Inda zaki mana
Allah ya gani malam bala naaon yarinyan saboda babu ruwanta gashi batada girman kai irin na
madam zakiyya
washe baki tayi kamin tace malam bala da ka barhi kawai
yace a ah dai kizo muje
shiru tayi tana Neman hujjan da zata bayar da taji medulla oblongata dinta bai harbo mata Ba
kawai sai tahau baya
Owners kwana ta Shiga sai tayi wani das da ita kamar hajiyar gaske
Kwatanta mai ta fara yi.........
Zaliha's POV
Hm
Swthrt Wai me ya samekine duk kin canja min gashi na kosa na ganki amatsayin matata
Dagaske?
Eh dagaske nake, kina gida ne?
Eh ina gida Kasan tunda aminiyata ta bata jiya....hhhh....na dawo..daga....gid......
Sai kawai ta fashe da kuka
swthrt me kike Cewa kina nufin Amina jagwal ta bata?
Tace eh,yace
Kiyi hakuri ganinan zuwa kinji ki yi shiru kinsan kukanki yana tada min hankali.
Toh kawai tace kamin suka datse kiran taci gaba da kukanta
After 10 minutes
Karan mota zaliha taji a kofar gidansu ana horn
Mamaki take Dan Ba haka karan motan Suleiman yake Ba
To kodai yasai wani mota ne?
Hakadai ta dinga sake sake yayinda take saka hijabi da takalmi Dan yau Ba kwalliya aminiya ta
bata
Kofar dakin iya taleka tace mata Suleiman yazo
Iya tace to tamai iso mana tace Toh sannan ta fita
MINAL kuwa tun ahanya take sake sake yanda zatayi surprising zally Suna isowa tace baba
kayi mata horn Dan Allah
Yace toh yata sannan yayi horn Kamar bayan minti biyu saiga zaliha ta fito
Tsayawa tayi sakoko tana kallon motar kawai sai ta basar tahau waige waige tana Neman
motan future hubby dinta da taga dai babu alamarsa kawai sai ta juya zata koma ciki tana mai
yana kyau irin na motar
Daidai lokacin minal tace wa bala ya sauke mata window ta control din wajensa akwai Abu a
hannunta
agaskiya dai babu Komai a hannuta tana tsoran kar yaje ta taba abinda Ba daidai bane ta
lalatawa mutane mota wannen azzalumin oga sir din ya kasheta Dan bayida imani
(Kaji fa minal Wai bayida imani hmm Allah dai ya kyauta)
Yana saukewa kuwa tace "Yan mata ki mana" tana dariyan shekiyanci
Zaliha dai inba kuskure take Ba to lallai muryan minal taji may be depression na batan minal din
yasan ta fara imagining things
Juyowa tayi aiki karaf suka hada ido murza idonta tayi yayinda bakinta ya budu mamaki da
tambayoyi fal ranta
Da sauri ta karaso tana mai saka hannu domin taba fiskan minal Dan ta tabbatar da kokontonta
Aiko minal dince Ba gizo gizo Ba
Cikin dashasshiyar murya tace minal
Smiling minal tayi tana gyada kai
Zaliha tace Kece ?minal tace nice
Bude kofan motan tayi ta sauko kamin suka daka tsalle atare suka rungume juna suna ihu tare
da juyi
Smiling kawai baba bala keyi
Nanfa minal ta juya tacewa baba bala zai iya tafiya
Yace hajiya kin tabbata Ba matsala? murmushi ta masa alaman eh kamin sukayi jikin gida aguje
sai dakin iya bakinnan nasu har kunne
Aiko iya taji dadin ganinta sosai bayan ta mata jaje ne suka fito suka koma dakin zaliha
Zaliha tace kawas wayar dani, Wai yankan kai kika fara ne?ko sata?ko kidnapping?
Minal ta kyalkyale da dariya tace Kamar kinsan yanxu haka kanki nazo cira kuwa
Ai bashiri zaliha ta rufe kanta
Wannan karan minal dariya take harda buga cinya tace ke dallah wasa nikeyi matsoraciya
Zaliha tace anji ai tsoran ma da dalili nakeyi nidai yi mini bayanin yadda akayi kika samu mota
irin wannan kuma harda driver
Minal tace "jiya........
Nan ta labarta mata abinda ya faru Kamar yadda mom ta tsara har izuwa yanzu zaliha ko sai
gyada kai take Kamar kadangaruwa alamar gamsuwa
Minal ko taki fada mata Gaskiya ne saboda tasanta da karadi yanxu sai tayi subul da baka ta
fada Ba tare da tasani Ba
Aiko hira suka kafa minal na bata labarin yadda gidan su yazeed din yake wani abin ma Zaliha
sai tace "kai minal arage na tomorrow"
minal tayita rantsewa amma zaliha bata yadda ba
Wayan zalihanne yayi ringing ta Duba Suleiman ne dauka tayi yace mata ya iso tace to gatanan
zuwa kamin suka fito ita da minal
Jingine yake ajikin motarsa kin 406 Yace lallai ma swthrt dama kawai so kike kiga fiskana shine
kika wani cemin minal ta bata minal tace eh hakane na bata amma yanxu na dawo
nan zaliha ta labarta masa abinda ya faru yace Allah dai ya kiyaye na gaba tace Ameen
Hira suka ci gaba dayi abinsu sai wajen azahar tukunna minal tace zata tafi Suleiman yace bari
ya rage mata hanya
.........agaskiya hajiya Duba da irin mutunci da karamci da kika nuna mana dukda Cewa kin fimu
arziki zamuso kuma zamuyi farin ciki ace Mun hada jini dake saide wani hanzari Ba gudu ita
yarinyan bamusan ra'ayinta Ba
Dan! Dan!! Dan!!!
Gaban mom ne ya fara lugude lallai dakyar minal zata yarda da wannan batu Duba da irin
abinda yazeed din ya mata saide ikon Allah
Tace to shikenan ga card dina duk shawaran da kukayi sai kusanar dani ko?sukace Insha Allah
Sannan ya Abubakar ya amsa card din
Yayi waje shida baba yayinda inna ta bisu da Karin kumallo sannan ta dawo ta sami mom bata
fara Ciba
Tace hajiya kick mana mom tace aike make jira muci tare sannan ki dena ce min hajiya kicemin
yar uwa
Toh kawai inna tace sannan ta zauna suka fara ci tana mai kara jin mom har cikin ranta
Wajajen azahar saiga minal ta Shigo alokacin mom ta Dade da tafiya
Baba da ya Abubakar ta gani zaune suna dan hiransu yayin da inna ke dafa abinci
Tsalle minal ta daka taje ta fada jikin sa
Baba yace yi ahankali kada ki karya Mani d'a
/\/\inal tace ai Nayi kewansa ne nan ta jona aka ci gaba da labari da ita can inna ta leko tace a
ah har kin dawo kenan? Tace eh
Inna tace ya kika tadda kawar taki minal tace lahiyatta lau kawai de tayi kuka ne baba yace
Allah sarki
Inna ce tayi ma baba Alama da ido Cewa ya fada mata
Gyara zama yayi yace AMINATU
Tace na'am baba yace ki saurareni da kyau sannan Kiyi tunani
Tace Toh
Yace nasama maki miji sunansa YAZEED........
Tofa fans kuna ganin minal zata amince da wannan batu?
Ya ake cikine tsakanin yazeed da
Zakiyya
Ina jiran comments dinku kada ku manta da offer na.
NAGODE
takuce karamarsu babbarsu
24 August, 2019
Miss untichlobanty
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty: KURUCIYAR MINAL
by @mzz_untichlobanty
*CHAPTER 22*
Sunansa YAZEED Dan gidan w.......
Bai karashe maganarsa Ba sakamakon ihun da minal tayi
Alhamdulillah! Baba da gaske ka saman miji ?ai Ba sai Nayi tunani Ba indai gidan akwai abinci
shikenan anwuce gurin
Murmushi kawai baba Dan ya fahimci kuruciya na dawainiya da minal fatansa de Allah yasa
mijin Ba Yaro bane inba haka Ba to Akwai matsala
Ya Abubakar ne yace iye iye 'yar kazamar kanwata zatayi aure an girma. Turo baki tayi "ni Ba
kazama bace" yace ai na sani nan dai suka ci gaba da sabgogin gabansu
Salati yazeed yayi lokacin daya bude idonshi
Ganinsa a dakin da Ba nashi Ba yasa ya tuna da abubuwan da suka wakana awanni kadan da
suka wuce Wai yau shine matarsa kwance jikinshi batare da tashin hankali Ba balle ace ta tafi
office.
Smiling yayi sannan yayi pecking dinta ya tashi ya fada toilet ya sakeyin wanka sannan yayi
alwala ya fita domin yin sallh
Koda zakiyya ta tashi wanka tayi taci abinci sannan ta dauko laptop dasu tablet dinta ta fara
Duba business
Yazeed ne ya shigo yace babyyyyyy!har kintashi?
Smiling kawai tayi sannan tace afternoon yace afternoon daga nan ya zauna yana shan green
tea dinshi while tana aikinta
After ya gama sha yahau gefenta ya zauna suna Dan taba hiransu
___________________________________
/\/\om tana zaune a dakin ta wayanta ya fara ringing unknown number ne hakan yasa bata
dauka Ba sanda aka kara kira sannan ta daga
Salamu alaikum
Wa alaik assalam mom ta fada zaka rantse bata iya hausaba
Mama ina wuni?Abubakar ne yayan Amina
Allah sarki Abubakar ykuke
Lafiya kalau,em........dama akan wannan magananne Toh ta amince
Alhamdulillah, to ai shikenan next week Insha Allah uncles dinshi zasuzo
To shikenan zan Fadawa baba,ina gaida brother Inlaw
Kacewa su baban Muna godiya kuma yazeed dinma zaiji
Bakomai mune da godiya
Da haka sukayi sallama mom na mamakin yadda akayi minal ta yadda Allah dai yasa Ba'a boye
mata wani Abu Ba,emm Allah dai ya kyauta
Minal kam fita tayi zata koma gidansu zaliha bakinnan har kunne
Ahanya ta hadu da su haruna(Yan shaye shayen nan from chapter 2) dauke da wani ghana
must go cikeda atamfofi
Ah ah hajiya minal dama kina duniyar nan ?
Eh inanan sai akayi yaya ?
Allah baki hakuri mu Ba masifa muke so Ba
Ghana must go din suka dauka sai nishi suke zasu cigaba da tafiya.
Minal tace amma kude Anyi ragwaye wallahi anji kunya yanzu duk girman kunnan bazaku iya
daga Ghana must go 1 Ba ? Sai Anyi magana kuhau cika baki Wai June karfafan anguwa.
Suka ce wa? aimu bazamu hada kanmu dake Ba ina babu ma hadi, saboda cin fiskane
agaremu ace an kwatantamu da mace.
Minal tace wannan kanku akeji sannan taci gaba da tafiyarta Dan taga alamun zasu bata mata
rai
Murtala ne yace ma ta "inkincika ke yar malam yusufa baban kowa ne ki daga wannan jakar
ance miki kayan wasa ne aciki
?
Basu ankare Ba kawai sukaga Ghana must go a sama ta daura aka.
Haruna yace na Shiga uku ni dan mutum 2 jikan mutum 4,murtala munji kunya ta d'aga!
Ajiyewa tayi ta juya zata tafi murtala yace
"Nide ina baki shawara inkinyi aure a gaba karki nunawa mijinki kinada karfinnan Dan wallahi
sakoki zaiyi Dan mu maza akwaimu da son mace me nuna rauni ko zata iya Abu ta nuna bazata
iya Ba,macen da take nuna Cewa mu muka cika mata kuma muka gyara rayuwarta
kai haruna kama muje"
Jakarsu suka dauka simi simi suka tari Napep dama mamar murtalan ce ta aikesu
Minal ko tahiyatta tayi tana Cewa har Dan shaye shaye zai iya bada shawarar arzikine?yo jakar
mafa Ba wani Nauyi gareta ba kawai de tsabar shaye shayensu har garkuwar jikinsu ta zamo
batada karfi. Aikin banza!
Gidansu zaliha ta fada ta labarta mata abinda ta riska bayan ta koma gida nanko ta dinga
tsokanarta sunata raha abinsu.
BAYAN SATI DAYA
Mom tayi magana da uncles din yazeed Kamar yadda tayi alkawari kuma sun sanarda ita
zasuzo
Shirye Shirye ake agidansu minal makota da abokan arziki hardasu aunty fauxy da iya maman
zaliha sun shishshigo ana ta aikace aikace domin taran baki
Minal kam Cewa akayi su Shirya itada zally su tafi gidansu zally
Suna cikin daki zaliha ke Cewa ke kawalliya na kasa yarda wai zakiyi aure
Minal ta daga hannu ta zuba mata duka acinya tare da Cewa da fatan kin fahimci Ba mafarki
kike.....
Maganarce ta Koma sanda zaliha ta yarfa mata tafi abaya tare da fadin saura daya.
Bankarewa minal tayi saboda dukan ya shigeta kuma bazata akamata
Nan fa suka fara duke duke zaliha ce tayi surrender tace
Ke shegiya ni matsa hanunki saikace wuka
Minal tace zama Kiyi bayani
Suna cikin haka sukaji hayaniya ya karu
Lekowa sukayi sai suka ga luba Maman bilkisu tsaye tana fadin:Kamar da gaske ai dama
wannan yar taku kazama ,ballagaza babu Wanda zai kalli ko Inda take balle ya
shinshinata,yanxu haka Nasan sadakanta za'a bayar,wallahi kowaye ya karba ancucesa
Aunty fauziyya ne tace ke dakata inhar kinsan......
Minal ne tayi carab yayinda suke fitowa adaki rike da hijab dinsu tana mai Cewa "ko Ba Komai
ai nafi su o'o tunda dai ankarbi sadakan nawa kuma zani da mutunci na wasu da ko a sadakan
bazasu sadaku Ba fah?sai yawo a gari an zama shaddar kasuwa kowa zai iya tsuguna
duwaunsa akai "
Daganan ta fizgo hannun zaliha sukayi waje yayin da ta balla mata harara
Sauran matanne da basufi goma Ba sukayi mata chaaa aka kowa da irin nasa comments din
daganan akayi waje da ita
Bayan minti talatin saiga Yaro yayi sallama Wai inji baban kowa
Akawo abincin baki parlourn zaurensu.
Nan inna tace ya nemo yara biyu sai sukai. Haka ko akayi bayan sun gama cin abinci tare da
santi suka sha zobo da kunun aya sannan aka tsaida aure nan da wata 3
Uncles din yazeed sunji dadi sosai da irin karamcin da akayi musu hakan yasa sukasan yazeed
yayi dace domin lokacin da sukaje gidan su zakiyya ruwa da lemo kawai aka basu ko snacks
basu samuba balle abinci gaisuwan ma sama sama .
Mom suka kira suka fada mata abinda yadda akayi aiko taji dadi daganan aka dinga Sanya
alkhairi ana watsewa.
Minal sai 5pm ta dawo aka fada mata yadda akayi bakinta har kunne ya abubakar nata
tsokananta.
AT NIGHT
mom,Jamal,yazeed and zakiyya zaune a parlour zakiyya na latsa waya while YAZEED and
Jamal are watching football, mom kuma na rubuce rubuce
Mom tace yazeed,kowa juyowa yayi ya kalleta tace akwai aabinda nakeson in fada maka......
Dan! Dan!! Dan!!
Cabdi anxo gurin. Me mom zata Fadawa YAZEED kuma yaya zaiyi ko ince