Showing 45001 words to 48000 words out of 62695 words

Chapter 16 - YAR HANNU BOOK COMPLETE NA ZEE MD

Zee Md   

13 Jul 2025

4576

cikin d'akin
tana jin wani abu me zafi a k'irjin ta , tabbas Khalid ya cuceta da ya dasa mata son shi aranta ,
tasan kafin fitarsa dole sai tasha wuya ,....

Alhaji Ashir ya nufi kan dirowar gado ya d'auki mukullin motar sa ya fice daga d'akin ,
dama Mumy tunda Ruma ta fita itama tabi bayan ta suka fice dukan su daga d'akin.......

Khalid kallon sa ya maido kan Leeemah yace " dan Ubanki wace ce ke ? tuni ya fito daga
cikin bargo yana neman abinda zai doki Leeemah dashi , da sauri Aysha ta fito daga toilet tana
fad'in " dakata Khalid karka kuskura kadake ta , jiyowa yayi yana duban Aysha sai sannan
yafara tunanin duk makircin tane itace ta had'a masa wannan shirin , kallon ta yashiga yi tare
dajin wata tsanar ta aransa , Cikin kakkausar murya ya furta " menayi miki kika sakamin da irin
wannan abun ? kin tozartani a idanun sirikaina sannan kin zubarmin da mutunci , inaso ki
fad'amin dalilin ki nayi min wannan tozarcin haka , wani shu'umin Murmushi Aysha tayi
sannan ta zauna a gefen hannun kujera tace " Khalid kenan Manyan gari , Inaso kasani Nice
Ayshar Gogal wacce ka lalatani , kaine namijin da yafara ketamin mutuncina , ka Yaudareni ka
wulak'antani sannan daga k'arshe ka gujeni , ta sanadin abinda kamin yasa nazama *'Yar
Hannu*, tundaga lokacin jikina yazama abin hutawa ga Maza masu hali irin naka , sai dai duk
iskancina inayin sane akan taku , na dad'e ina jiran wannan ranar da zatazo ace gashi kazo
hannuna amman ban samu ba sai yau , kad'auka kaci bulus ko ? ka d'auka Ayshar da ka lalata
bata duniya ma ko ? to kasani na rok'i Allah yakawoni wannan ranar da zan d'au fansa akan ka
, kuma daga rana irin ta yau natashi daga sunan *'Yar Hannu* nakoma Asalin sunana Sayyada
Aysha , wata zufa ce ta karyowa Khalid jin Ayshar Gogal ce wacce yayiwa Fyad'e har tasamu
ciki tazo masa da maganar cikin ya koreta , To ya akayi yakasa gane itace ? taya tazama wata
hamshak'iyar mace haka ? wannan gidan datake to gidan waye sanin da yayi musu basu da
kowa kuma basu da komai , to gidan waye wannan d'in datake a cikin sa ? kuma ina Gogal
tabbas yasan ya aikata wa Aysha ba dai dai ba dole hakkin ta ya bibiyesa......
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU*
🤒🤒


_NA_
*Zee* *MD*



*WOMEN WRITERS ASSOCIATION* 📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/





*Bisimillahir Rahamanir Rahim*

_Page._ 28


Tunda suka fara tafiya Aysha ta kunna karatun Alk'ur'ani me girma , sabanin indai ita
kad'ai zata fita sai dai tasa Music tana ji , a haka har suka k'araso Cikin Asibitin , samun waje
Aysha tayi ta faka motar sannan suka suka fito ita da Gogal suna takawa har cikin harabar
zaman masu ganin likita , wajen bud'e files Aysha taje tagama biyan kud'i sannan tadawo su ka
zauna suna jiran kiran Dr. ....

Ba'afi Minty 5 ba aka kirasu suka shiga ciki , Bayan tambayoyin da Dr yayi wa Gogal akan
yadda takejin jikin nata tashiga bashi bayani yana rubutawa , nan ya shiga baya shawarwari
game da yadda zata kula da jikin ta , ya sheda mata hawan jini gare ta kuma yana neman tab'a
mata kwakwal wa mutukar bata daina saka damuuwa aran ta ba , Aysha ta dubi likita sannan ta
dubi Gogal tace " tunanin me kikeyi haka da har yake neman rikita kwakwal warki ? dan Allah
Gogal kirage saka damuwa aranki duk duniya kinsan bani da kowa in bake ba , kema kina so
narasaki ne ? Gogal tayi murmushi sannan tace " Aysha mutuk'ar bakiyi aure ba to tabbas
bazan daina damuwa ba , Aysha tace " Aure lokaci ne Gogal indai lokacin yi yazo ko nashirya
ko ban shirya ba to tabbas zanyi , nidai kici gaba da yimin addu'a Allah yazab'amin miji nagari ,
Dr yayi murmushi yana duban su dan sun burgeshi sosai , nan yace da gaskiyar Hajiya gaskiya
yakamata ace k'anwata kin yi auren nan dan Hajiya tasamu farin ciki , Aysha tayi murmushi
tana cewa " zanyi lokaci Dr . Nan suka mik'e yabasu kati tare da ce ma Aysha lallai su siyi
magun gunan ta dunga sha , ....

Bayan fitowar su Aysha ta shiga wajen sai da magunguna ta siyo samnan ta fito , tana
fitowa suka nufi wajen da motar su take zasu shiga , kamar daga sama Aysha taji ana k'wala
mata kira " Aysha Uwar ruwa kankana uwar dad'i daga ina zuwa ina ? cak Aysha ta tsaya wata
zufa tana karyo mata , Gogal itama juyowa tayi tana kallon wanda yake kiran Ayshar da wannan
sunan , Jabir ne a tsaye ya hard'e hannun sa a kan k'irjin sa yana zuba mata wani murmushi
tare da shu'umin kallo , Aysha tayi ta maza ta dake tana d'auke kai tamkar bata gansa ba ,
murfin motar ta ta bud'e tare da cewa Gogal " shigo mutafi Gogal kinga ana rana kar ta dameki
da yawa , Gogal tace " waye wannan d'in ? kuma wanne suna naji yana kiranki dashi haka ?
Aysha tace " anya dani yake kuwa dan ni bantab'a ganin saba ma sai yau , sai dai ko nayi masa
kama da wata wacce yasani ne , Jabir yayi wani shu'umin murmushi yace " Hajiya barka da
wannan lokacin ya gida , Gogal tadubesa sannan tace " lafiya lau amman yaro inaso insan kai
waye kuma meye had'in ka da jikata naji ka kirata da wani banzan suna ? Murmushi Jabir yayi
sannan yace " ki tambayeta zakiji komai daga bakin ta nabarku lfy , yana gama kaiwa nan ya
dubi Aysha ya kashe mata ido tare da barin wajen , Aysha jitayi tamkar tabi bayan Jabir ta
rufesa da duka saboda abinda yayi mata , Gogal zubawa Aysha idanu tayi tana mata kallon
tuhuma tabbas akwai abinda Aysha keyi wanda bataso tasani , in ba haka ba taya zai kirata da
irin wannan sunan haka , Aysha duk jikin ta yayi sanyi ganin irin kallon da Gogal keyi mata ,

Gogal xagayawa tayi ta shiga motar yayin da Aysha ta d'an tsaya tana nazarin yadda zata kare
kanta a wajen Gogal , a haka ta shiga motar taja su suka bar harabar asibitin.......


Tunda suka taho har yanzu Gogal batayi magana ba kuma bata kalli inda Aysha ke tuk'i
ba , Aysha cikin ranta sai tsinewa Jabir take da irin abinda yayi mata , a haka suka k'araso cikin
gidan Gogal ta fice daga motar tashige cikin gidan abinta , Habu sai sannu da zuwa yake masu
amman ko kallon sa Gogal batayi ba ta shige , zama Aysha tayi a cikin motar ta tana jin
tamkar kar tashiga cikin gidan , me zata cewa Gogal ta kare kanta ta nuna mata batasan Jabir
d'in ba , ta dad'e a zaune a cikin motar kafin ta fito tashiga cikin gidan gwuwa a sab'ule , ...


Tunda Gogal ta shiga cikin gidan take zagaye palor gidan , tabbas dole akwai abinda
Aysha ke b'oye mata , ita kanta akwai wani abun in Aysha tayi sai tashiga mamakin Ayshar ,
tana tsaye a hakan Ayshar tayi sallama ta shigo cikin palor , k'arasawa Aysha tayi kusa da ita
tana cewa " dan Allah Gogal karki saka abun nan aranki kinajin abinda likita yace miki , wani
kallo Gogal tayi mata sannnan tace " inhar kinaso in yarda dake to lallai inason sanin gaskiyar
komai , Aysha cikin zuciyar ta ta furta " bazan iya gaya miki gaskiyar komai yanzu ba , amman
nasan wata rana sai kinsani duk b'oye b'oye na , a fili kuma ta furta " iya gaskiya ta nafad'a miki
wallahi bansan shi ba ban kuma tab'a ganin sa ba , ranar nan ma dana dawo daga makaranta
akwai wasu mata da nahad'u dasu a hanya suma sunkirani da irin sunan da wannan d'in ya
kirani dashi , dana tsaya a wajen su nace bani bace suna kallona suka yarda , sai dai sunce min
akwai wata 'Yar uwar su wai muna kama da ita sosai in dai aka gan mu to tabbas za'ace 'yan
biyu ne , kuma suka tambayeni suna na na sheda musu nan ma sukace sunan mu d'aya da ita
, Aysha data kalli Gogal ta gefen ido ta ga yadda maganar ta shigeta tuni tayi k'asa da
gwuwowin ta taci gaba da magana muryar ta na rawa tace " bana b'oye miki komai Gogal
kinsani , dan Allah kar zuciyar ki tafara rawa akaina ki yarda da Ayshar ki bazata tab'a aikata
wani abu wanda zai saka zuciyar ki tayi rawa akanta , tuni jikin Gogal yayi sanyi tasamu waje ta
zauna tana kallon Ayshar , sai dai har yanzu zuciyar ta takasa yardar mata abinda Ayshar tace
, nisawa tayi sannan tace " shikenan na yarda Allah ya kyauta , cikin zuciyar ta ta k'udurce lallai
yanzu dole tasa ido sosai akan Aysha shine kawai zai tabbatar mata da gaskiyar abinda Ayshar
tace , Aysha ta d'auko jakar ta ta zuge tare da d'auko magungunan Gogal tana fad'in " bari na
d'auko miki ruwa kisha magungunan yanzu saboda yanayin jikin naki , Gogal tace " barshi
kawai zan shiga d'aki na kwanta zansha kafin na kwanta d'in , tana fad'in haka ta mik'e tashige
d'akinta.......

Aysha tabi bayan ta da kallo har ta shige , mik'ewa tayi tashiga cikin d'akin ta da sauri tana
rufo k'ofah sannan ta d'auko wayar ta tashiga laluben number Jabir , dama ita tana da number
sa shine dai bashi da ta ta , aikuwa tana kira number tashiga sai da ta kusa katsewa sannan
ya d'aga , Aysha cike da jin zafin sa tace " me kake nema dani ne mai nayi maka da kake bibiya
ta kakeso kasa Kaka ta cikin tashin hankali ? Jabir tunda tafara magana yagane wace yafara
wani shu'umin murmushi , sai data gama sannan yace " Hajiya Aysha kenan ashe kina gari
daman , aini na d'auka ko kina wata k'asar saboda yadda kika samu duniya , wata tsawa ta

daka masa sannan tace " ina so kafad'amin meye damuwar ka dani da kake bibiyar rayuwata ?
Jabir yace " Aysha ina bibiyar ki ne dan inasonki kuma inaso ki shiryu kidaina abinda kike , sai
dai kashh kinkasa bani dama ko sau d'aya inyi magana dake , kuma koda yaushe cikin shigar
dani kike saboda kin maidani wani wawa , Abinda yasa nayi miki haka kuma saboda ta hakan
ne kawai nasan zaki nemeni muyi magana , kuma gashi hasashena ya gayamin gaskiya ,
Aysha meyasa kika zab'i ki ringa shiga rigar mutunci kina aikata fasik'an ci ? kuma abin haushin
duk abinda kike har yanzu kakar ki takasa ganewa , nikuma abinda nakeso shine ki tagane
wace ke ko zaisa ki gyara halinki , Aysha a fusace tace " meye damuwar ka da shiryuwata da
rashin ta ? kai uba nane ko wani nawa da zaka shiga rayuwa ta ? inaso kasani wallahi mutuk'ar
baka rabh dani ba indai na juyo kanka bazaka ji da dad'i ba , Jabir yace zakimin yadda
kikayiwa Farouq ne da Mahaifinsa ko ? take k'irjin Aysha ya buga cikin zuciyar ta tace "
wannan kodai ba mutum bane taya yake sanin komai nawa ? katse mata tunani yayi da cewa "
kina mamaki da yadda nasan komai naki ko ? to kamar yadda kika iya taku nima haka nake
nawa , nabarki lfy ki k'ara shiri My Aysha naki Jabir d'an sa idon ki , tuni yakashe wayar yabar
Aysha da waya rik'e a hannu tayi tsaye cak.......




*Comment* plss🥰🌹
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU*
🤒🤒


_NA_
*Zee MD*



*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/





*Bisimillahir Rahamanir Rahim*



_Page._ 32

A b'angaren Hameed kuwa duk wata damuwar sa yanzu ta ragu , farga bar sa guda
d'ayace Akan Aysha Ko zata amince masa ? ranar duk wani iri yake jin sa Allah Allah yake
dare yayi yaje yaji me zata ce masa , Hajiyar sa sai tambayar sa take meke damun sa amman
sai yace mata bakomai , ko abinci kasa ci yayi ranar haka ya yini cikin d'akin sa , sai wajen
magriba yayi wanka ya shirya sannan ya fito.......

Ana idar da sallar Magriba Hameed yanufi gidan su Aysha , sai dai me yana zuwa
yasamu gidan a rufe da kwad'o, wata fad'uwar gaba yaji ta ziyarce sa cikin zuciyar sa yashiga
cewa " haba Aysha meyasa zaki yimin haka ? nasan saboda ni kika kuma tashi daga wannan
gidan , da kin san baki da amsar da zaki bani da kin cemin inyi hak'uri bakya sona , tuni idanun
Hameed sukayi jawur saboda takaicin ganin gidan a rufe , ya dad'e a tsaye a k'ofar gidan yana
kai kawo har yagaji ya juya ya nufi gida , sai dai yana zuwa k'ofar gida ya tsaya ya kasa shiga
yana nazari , wata zuciyar tace masa " kodai kaje tsohuwar unguwar su ko nan sukaje ? tunda
yasan dai ba tashi sukayi ba , haka ya shiga gida ya fito da motar ya nufi unguwar su Aysha ta
da......


Aysha tana zaune cikin motar har aka idar da sallar Magriba , tuni tagama yankewa kanta
zata shiga cikin gidan tayiwa Gogal bayanai koda zata kashe ta , tasan duk duniya bata da
kamar ta kuma bazata iya guduwa tabar ta ba , haka ta fito daga cikin motar tanufi cikin
gidan.....
Gogal tun sanda taje Makarantar su Aysha ta buk'aci son ganin Shugaban Makaranta ,
koda suka shiga office suka gaisa dan yasan Gogal sosai , nan take tambayar sa Ya k'ok'ari da
hidima sannan ta fara masa godiyar irin Kyautar da Aysha tasamu , shuru yayi yana nazari
kafin yace " ban fahimci abinda kike nufi ba , nan tashiga ce masa kyautar gida da Aysha
tasamu da kuma motar har ana shirin bata kujerar saudiya , nan Shugaban Makaran ta yashiga
jimami da jinjina maganar ta , andad'e ana kawo masa zancen Aysha tana yawon banza kwata
kwata bai mai da hankalin sa akan hakan ba , yasan Aysha ta dad'e bata zuwa makaran ta
amman inda yayi kuskure shine bai je yasamu Gogal da maganar ba , nan ya shedawa Gogal
komai nagame da halayen Aysha , kuma yace baisan zancen gida da motar ba , dan yafi
shekara d'aya da rabi rabon da yaga Aysha tazo makaranta , koda Gogal taji maganar
shugaban Makaranta tuni jikin ta ya d'auki rawa , take ta yi masa sallama suka nufo gida ita da
Habu........

Bayan ta kwaso kayan ta ta sheda wa Habu shima ya kwaso nasa kayan , nan suka nufo
tsohon gida suka bud'e tare da taimakon Habu suka gyara gidan , tunda Gogal ta shiga cikin
gida tashiga d'akin ta na da ta kwanta saboda zazzab'in da ke barazanar rufe ta , hawaye ne
yashiga zubowa ta idanun Gogal cikin zuciyar ta tashiga cewa " tabbas Aysha kin cuceni kin
cuci rayuwar mu , menene wanda kika nema kika rasa da kika zab'i irin wannan Rayuwar ?
tamkar wacce Aysha ke gaban ta tadunga fad'in " wanne irin fad'i tashine banyi ba dan ganin

rayuwar ki tasamu nagarta , wata zuciyar tace " kina da laifi kema taya zaki dunga ganin ta
tana kashe kud'i amman kiyi shuru , haka dai Gogal ta shiga zancen zuci tare da ambaton
istigifari dan neman tuba akan sakaci datayi har Aysha tazama haka , jira take taga Ayshar zata
biyota nan gidan ko kuma bazata biyota ba ? kuma in tazo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login