Showing 24001 words to 27000 words out of 62695 words

Chapter 9 - YAR HANNU BOOK COMPLETE NA ZEE MD

Zee Md   

13 Jul 2025

4686

Aysha ta kira Alhaji Na Lamma akan aturo mata Farouq zai fara koya mata motar , basu fi
minty Ashirin da waya ba saiga Farouq yazo , koda aka sheda mata zuwan sa sai da ta b'ata
lokaci kafin tafito , ta sanar da Gogal zata fara koyan motar gashinan anturo me koya mata ,
dayake Gogal tasan Farouq shiyasa Aysha tace dole sai dai yasaka face mark da glass kar
Gogal tagane sa , haka kuwa akayi suka fice koyan motar tana rainawa Farouq hankali.......


Lokacin da suka fita a motar daga layin shi kuma Hameed lokacin ya shigo , dan shima a
cikin unguwar gidan su yake haka ya shiga gida duk jiki a sanyaye ......

Aysha kuwa Farouq ko kanzil yak'i yace mata , kawai jan motar yake baya nuna mata yadda
zatayi ta koya , tuni ta kira Alhaji ta sheda masa yadda suke , kiran sa yayi ya shiga masa fad'a
sosai ala dole yafara nuna mata yadda zata iya motar.........


*Insha Allah gobe zanyi muku 'Yar kishiya*
_Rik'on Me Hak'uri_

*Comment* plss


*'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU*



_NA_
*Zee* *MD*



*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046

✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨


*Bisimillahir Rahamanir Rahim*



_page._ 17


Kwata kwata Aysha bata kula da Hameed ba , wayar ta ta zaro a cikin jaka tana danna
kiran number wani Alhaji da sukayi promise zasu had'u , tana kara wayar a kunnen ta shikuma
Hameed yana k'arasowa d'auke da sallama a bakinsa , da sauri Aysha ta juyo tana duban
wajen da akayi sallamar , gaban ta ne ya fad'i ganin Hameed cikin zuciyar ta tashiga tambayar "
taya wannan mutum yasan gidan nan ? kuma dama har yanzu yana nan kenan ita har ta
manta dashi ma , katseta yayi da cewa " baiwar Allah ko bakya amsa sallama ne ? tattaro
nutsuwar ta tayi sannan tace " wa'alaikas salam , Hameed take ya gasgata lallai Aysha ce
wannan , wannan muryar ta ta ko a mafarki bazai tab'a mantawa da ita ba , cike da nishad'i
yace " malama Aysha dama kina nan ? Aysha tunani tafara akan tace masa ba ita bace ko
kuma tace masa tayi aure yayi hak'uri , a hankali ta furta " kayi hak'uri ina da aure yanzu kar
mu sab'awa Allah , wani abu Hameed yaji ya soke shi a zuciya ya mai maita kalmar " aure
yaushe kikayi aure Aysha ? da sauri tace " banfi wata d'aya ba dan Allah kayi hak'uri Allah
yabaka wacce tafini , tana gama maganar bata jira cewar sa ba tashige abinta , dan bata so ko
kad'an yaja ta da wata maganar gudun kar yaganeta , da idanu Hameed yabi bayan Aysha da
kallo cikin zuciyar sa yana nazarin kalmar ta wai tayi aure , tabbas zai koma unguwar su yayi
bincike sosai akan maganar ta tunda su dai sunce tashi sukayi , kuma dole yasa ido a cikin
unguwar nan dan tabbatar da maganar tata.........


Kamar kullum yau ma Aysha ba makaranta taje ba , hotel d'in Green palace taje gun
Alhajin ta da sukayi alk'awarin had'uwa , tana zuwa tasamesa yana jiranta daga shi sai gajeran
wando , yana ganin ta yashiga yasar baki yana mata kirari " wani far Aysha tayi da ido tana
neman guri ta zauna a gefen gadon , Alhaji Bashir ya dubi Aysha yace " 'Yar Hannu meye
kuma na sakomin wannan k'aton Hijab d'in ? Murmushi Aysha tayi sannan ta mik'e ta cire Hijab
d'in nata , daga ita sai wata rigar bacci ce a jikinta wacce da ita wanda babu , Alhaji Bashir
naganin haka ya susuce yafara k'ok'arin janyo ta jikinsa , turesa tayi tana wani irin kashe masa
idanu , da sauri yafara surutai yana fad'in " haba babyna so kike ki kasheni da sonki kitaho
jikina mana inji d'umin jikin naki , hannu ta mik'a masa tana fad'in " banji alart d'ina ba ai ,
Alhaji Bashir a rud'e yace mata " kifad'i komai kikeso zan mallaka miki mutuk'ar zaki bani jikin ki
, murmushin k'eta Aysha tayi sannan tafara masa wasu salo wanda ya fitar dashi daga
hayyacin sa , wayar sa ta d'auka ta shiga number account d'in sa , take tayiwa kanta transfer ta
1 million , sannan ta goge komai takuma shiga yi masa video yana tub'e , kwata kwata Alhaji
Bashir baya hayyacin sa baisan tanayi ba , a haka suka fara aikata iya shegen su......

Jabir sosai yake yawon neman Aysha Hotel Hotel , duk inda yaje sai ya tsaya a k'ofar
Hotel d'in yana ganin shige da ficen mutane , kamar kullum yau ma a Hotel d'in Green palace
yaja yasamu guri ya zauna , yana zaune yana ganin masu shige da fice kala kala tamkar wani
d'an jarida, dai dai lokacin Aysha tagama komai sunyi sallama da Alhaji Bashir ta fito , tana
fitowa kamar ance ta hangi k'ofar shigowa ta hango Jabir zaune suna hira da security , da sauri
ta lab'e a wani guri tana maida numfashi , cikin Zuciyar ta tace " wai wannan mutumin shikuma
me yakawo sa nan ? tana tsaye a wajen tana lek'awa har ta shafe minty Sha biyar bai tashi ya
tafi ba , duba a gogo tayi taga yamma tayi sosai lokacin komawar ta gida yayi , dabara ce ta
fad'o mata ta kiran Farouq akan yaje ya d'auko mata motar ta yazo ya d'auke ta , aikuwa hakan
tayi Farouq yana d'aga wayar bai musa mata ba ya amsa da to kawai ya kashe wayar......


Kamar yadda ta buk'ata haka Farouq yayi yazo ya d'auketa suka fice daga Hotel d'in , sai
dai me ? suna fita ya kulle glass d'in motar ya d'auke hanya yashiga gudu da ita tamkar zasu
tashi sama ........

Hameed tuni ya bayyana a unguwar su Aysha yana tambayar ko Ayshan tayi aure ? sai
dai duk wanda ya tambaya sai yace masa ba aure tayi ba tashi sukayi , sai da ya tambayi
mutun uku sannan ya gasgata ya d'auko hanyar dawowa gida........
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU*



_NA_
*Zee* *MD*



*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A)✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*Bisimillahir Rahamanir Rahim*

_Page._ 19


Har Aysha ta shigo cikin gida tashige d'akin ta Habu a tsorace yake , dan yagama
tsorata sosai duk da yaga babu abinda yafaru da Ayshar , mamaki yashiga yi cikin zuciyar sa
yana tunanin wanda yazo gun Aysha a tsohon daren nan haka , haka dai yaja jikin sa ya nufi
d'akin sa tare da rufo k'ofar........

Washe gari sai wajen shabiyu sannan Farouq ya kawo wa Aysha motar ta , sosai yanayin
Farouq ya canza duk jikinsa yayi sanyi , Harya juya zai tafi sai kuma yadawo , Aysha ta dubesa
tace " lafiya kuwa ko akwai maganar da zaka fad'a ? Farouq ya nisa sannan yace " Dan Allah
Aysha kiyi hak'uri ki yafemin Abinda nayi miki , nasan saboda hakan kike ramawa akan
Mahaifina , Murmushi Aysha tayi sannan tace " Farouq ina yafewa duk wanda ya zalunceni ,
sai dai gaskiya bazan tab'a yafewa wanda yayi sanadin lalata rayuwa ta ba , kafi kowa sanin
wacece ni farkon had'uwar mu , amman a yanzu kunriga da kun canzamin rayuwa zuwa wani
bagiren daban , batare da takuma magana ba ta shige cikin gidan idanun ta cike da k'wallah ,
Farouq da ido yabi Aysha sannan ya shiga jin haushin kansa , tabbas yana da Babban laifi akan
komawar Ayshar haka , duk da yajita ba dai dai ba amman tana da kyawawan halaye , dana
sani yashiga yi tare da tsanar duk wani namiji me hali irin nasa......

Tunda Aysha ta shige gida d'akin ta ta nufa kai tsaye , tana zuwa tafad'a kan gado tana
zubda hawaye , duk duniya babu wanda ya cuceta sama da Khalid , duk randa Allah ya had'ata
da Khalid to tabbas sai tashiga rayuwar sa ta ruguza komai , abinda yasa ta ma sauran mazan
datake bi take musu haka saboda ai suma duk amanar Matan su suke ci , kuma da sannu saita
gyara musu zama mutuk'ar sun shigo gonar ta , da zarar ta kammala duk wani abubuwan ta to
zata nutsu waje d'aya sannan ta tuba , da wannan tunane tunanen bacci yayi awon gaba da
ita....

Ruma tunda tadawo gida take ta murnar tayi k'awa , Sai bawa Hajiyar su labarin irin kyan
da Aysha k'awar ta take dashi , Hajiya Shafa tace " kefa Ruma Allah yayiki da k'aunar mutum
me kyau tuntuni , daga had'uwa da yarinya sai kifara d'oki kina lissafe lissafe , dariya Ruma
tasa tana fad'in " Allah Hajiya dan dai baki ganta bane wlh tayi kyau sosai , Hajiya Shafa tace "
Allah yabarku tare keda ita , yanzu kitashi kije kiyi wanka dan Khalid nasan yana hanya ,
Murmushi Ruma tayi tana fad'in " Nifa nagaji da yawa banajin zanyi tad'i yaud'in nan , Hararta
Hajiya tayi tana fad'in " magulmaciya anaso ana kaiwa kasuwa , tund'azu yazo shine Daddyn ki
ya aikesa super market ......

wacece Ruma ?
'Ya d'aya tilo a gurin Alhaji Kabeer da Hajiya Shafa , ita kad'ai Allah yabawa iyayenta shiyasa
suka d'auki son duniya suka d'ora mata , duk abinda Ruma keso shi suke so koda kuwa abin
yakasance badai dai ba , Khalid yaron Alhaji Kabeer ne yakasan ce yabashi yadda sosai a
kasuwan cin su , tunda Khalid ya k'yallah ido akan ruma yaji duk duniya inba da itaba bazai iya

soyayya da kowa ba , sun shak'u sosai tsakanin su kuma kowa yasan da wannan soyayyar
tasu , wannan kenan......


Bayan Aysha ta tashi daga bacci wanka tashiga tayi sannan ta fito , shiryawa tayi da irin
shigar ta tafito ko abinci bata tsaya ta ci ba tace wa Gogal " zataje asibiti duba Baban k'awar ,
Gogal bata hana ta fita ba sai fatan Allah yadawo da ita lafiya......


Motar ta ta nufa ta bud'e ta shige tare da kunnah ta ta fice abinta hankali kwance , tana
tafe tana direving hankali kwance taji wayar ta na ruri , dubawa tayi taga nunber bata santa ba
kwata kwata , da har zata k'i d'agawa sai kuma ta d'aga tana fad'in " waye bangane number ba
? Ruma da murnar ta tace " Ruma ce wacce muka rage miki hanya , Aysha tad'an saki fuska
tamkar suna ganin juna tace " haka zakice Kawata , barka ki da wannan lokaci , yagajiyar ku
dafatan kunje gida lafiya ina godiya sosai da kulawa , Ruma cike da fara'a tace " haba sai kace
wani Abu dama kiranki nayi nafad'a miki anjima zamu kawo miki ziyara nida Wanda zan aura ,
Aysha cike da jin dad'i tace masha Allah to indai nadawo zantab'oki a waya , yanzu ina hanya
zani dubiyar Baban k'awata , Ruma tace " ayya babu komai kiyi masa sannu sai kindawo ,
sukayi sallama ko wacce ta kashe wayar , ......

Dai dai Danger aka tsayar dasu Aysha ta tsaya tana duba wayar ta , to dayake batasa
Nik'af ba shiyasa bazatayi wuyar ganewa ba ga wanda yasanta , hankalin ta kwata kwata yatafi
kan wayar ta dayake taga kafin a sake su sutafi za'a d'an jima , Dai dai lokacin Jabir shida
Abokinsa suna kan Lifan suka tsaya dai dai jikin motar ta , aikuwa Jabir kamar ance masa kalli
cikin motar aikuwa ya hango Aysha zaune akan sit d'in Direba , wata zabura yayi yana fad'in "
Aysha dama nasan mutuk'ar kina garin nan wata rana saina ganki , da sauri ya dira daga kan
Lifan d'in abokin nasa yana nufar motar , Kamalu yashiga k'walawa Jabir kira yana fad'in " Jabir
ina zaka haka kuma ? ina kwata kwata Jabir bai ma san Kamalu na kiran saba , Jabir na
k'arasowa jikin motar ya furta Aysha , aikuwa Aysha ta juyo tana kollon wajen da ake kiran ta ,
ido suka had'a da Jabir take gabanta yafad'i , da sauri ta d'age glass d'in duk ta rufesu , tamkar
mahaukaci Jabir haka yashiga jijjiga mata murfin mota , adai dai nan kuma aka saki hannu
alamar su wuce , aikuwa da gudu Aysha taja motar ta tamkar zata take Jabir ta wuce abinta ,
da sauri Jabir ya koma ya haye Lifan d'in Kamalu yana fad'in " dan Allah Kamalu ka bimun
bayan waccan motar , duk inda tayi inaso kabita dan Allah kayi gudu sosai ...........



Tofah✍
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR* *HANNU*



_NA_

*Zee* *MD*



*WOMEN* *WRITERS* *ASSOCIATION*
(Domin Marubuta Mata)
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*




_Page_. 18


Gudu sosai Farouq yake da Aysha a cikin motar , Aysha kallon sa kawai take taga iya
gudun ruwan sa , dan da alama har yanzu bai san wace ce ita ba , sai da suka fara fita daga
cikin gari sannan yaja ya tsaya yana huci tamkar wani kububuwa , duban ta yayi yace " me kike
tak'ama dashi da har kike raina mana hankali nida Mahaifina ? shuru Aysha tayi tana kallon sa
kafin tasa hannu ta zuge jakar ta ta d'auko cingum ta jefa a baki , wani haushine ya kuma kama
Farouq yaji tamkar ya shak'eta ta mutu kowa ya huta , wata tsawa ya daka mata yana fad'in "
ba magana nake miki ba ne ? murmushi Aysha tayi sannan tace " inaso kasani ko Na Lamma
wato Uban ka bai isa ya titsiyeni a gaba ba yanamin tambayoyi , wani Mari Farouq ya sakar
mata tare da fad'in " ki iya bakin ki dan kinsan sarai ubana ba sa'anki bane , Aysha rik'e kuncin
ta tayi tana duban Farouq sosai tare da mamakin irin k'arfin halin sa , duban ta yayi yana huci
sannan yace " inaso wannan yazama last wornig da zan miki akai na da kuma Mahaifina ,
nabaki nan da kwana biyu ki had'a kayanki kibar wannan gidan , sannan kuma komai da
kikasan na Mahaifina ne to inaso ki ajiyeshi a cikin gidan kar ki fita dashi , in kuma kika k'i ji to
tabbas bazaki k'i gani ba , banza shasha sha 'yar tasha wacce batasan kanta ba , Aysha
tamkar mutum mutumi haka ta koma sai idanu kawai da ta zubawa Farouq , fitowa yayi daga
motar ya zagayo b'angaren da take ya bud'e tare da finciko ta waje , fad'uwa tayi a gefen titi
har kanta sai da ya bugu , tana kallo ya bud'e motar ya shiga ya fige ta da gudun tsiya yabar ta
a wajen ......

Aysha ta dad'e a haka a wajen kafin tayi yunk'urin mik'ewa , duban dare yafarayi gashi
kuma tafiyar da nisa yasa ta fara k'ok'arin tsaida abin hawa , dayake amfara fita daga cikin gari
sosai yasa ta kasa samun abin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login