Showing 30001 words to 33000 words out of 52049 words
tace komai ba tabar dakin. Samun waje amrah tayi kan gadonta tare da dakko wayarta dake ajje saman gadan, dogon tsaki ta saki sai a lokacin take tuno abunda tahee tayi mata,azabure ta mike tsaye “ ni amrah , nice yau nake bawa wata yar iska hakuri, ni amrah hmmm” girgiza kai tashigayi “ yau nice na kaskantar dakai na bawa wata shegiya hakuri, wallahi ko zanyi yawo tsirara sai na wulakanta ta sai na musgunawa rayuwarta sai tasan dani take magana “ ta kare zancen tana sakin kwallar bakin ciki…
******* Director part dinsa ya nufa sai faman taunar lips dinsa yake, be bi steps ba ta elevator ya hau , a second floor dinshi ya tsaya ko ina sai faman tashin kamshi yake da sanyin Ac musamman kamshin turaransa da ya kama ko ina na part din, rigar jikinsa ya cire kai tsaye faffadan zurar jikinsa ta fita fari tass dashi,sosai muscles dinsa da 6 spacks dinsa ya fito kallo daya zaka masa kasan ba karamin motsa jiki yake ba,kofar da take facing dinsa ya nufa, ya dau kusan mintuna 30 aciki kafun daddadan kamshi ya karade ko ina , sosai yayi kyau , a maimakon suit yanxu kananan kayane a jikinsa ,tun daga kan bakar jigar jikinsa tare da bakin wanda jikinsa , sosai yayi kyau cikin kayan , sumammiyar gashin kansa ya fito sosai yau ma kadan daga cikin yalwataccen gashin kansa ya fito har wajan idanunsa, sabida tsananin bacin rai pink lips dinsa ba karamin turuwa yayi ba sai faman tsuke fuskar yake, cikin takunsa na kasaita ya hau elevator tare da nufar 3rd floor, a maimakon hanyar da ya saba bi yanxu wata daban yabi,babban waje ne nashakatawa gata iska me dadin gaske dake huro wajan,kayataccen wajan shakatawa ne a wajan sosai wajan ya hadu,ga gefe d’aya dayake abude ko ruwan sama akai yana dan shigowa kadan kadan , akan daya daga cikin kujerun shakatawan yazauna ne kama da sararin samaniya, sosai yanayin wajan yasakashi cikin nutsuwa sai faman lumshe ido yake, daga gefensa ma wani cup ne me shegen kyau cikin sa wani lemone kamana da sararin samaniya shima.sai faman lumshe idanuwansa yake yana budewa, wayarsa dake ringing a hankali ya dauka batare da bata lokaci ba, Ahankali yake magana ko nakusa dashi ba Lalle yaji me yake cewa ba,sai lumshe kyawawan idanuwansa da yake faman yi.
🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧
Futowar da ammi zatayi a kitchen ne taga babu king babu tahee, tsayawa bin falon tayi da kallo kamar anan ne zata gansu,a tunaninta tahee ta koma daki ne shiyasa bata bita ba ta dauki wayar ta da niyar kiran king, tana kara wayan a kunnenta ta haye stair case din din falon..
A dan kwanciyar da tayi batasan lokacin da bacci ya dauketaba, wasu matasan yara tagani da akalla befi su bata shekaru uku ba, kyawawa dasu sai faman kuka suke , daga gefensu wani farin macijine shima tass dashi, kallan tahee dake gefe sukai sai suka kara fashewa da kuka , suna kuka suna biyota , cikin tsorata tahee ta fara jan baya, girgiza mata kai suka shigayi, cikin daddadan muryarsu “sun kashe mana farin cikin mu , sun cutar damu, bamuyi musu komai ba, laifin me mukai musu, nace laifin me mukai musu” suka karasa cikin data tsawa , firgita tahee tayi da yanayinsu, ganin sun tsaye ne yasa itama tsayawa,cikin rawar murya tahee ta fara magana “su..suwane ku, me nayi muku”, dariya suka saki tare da kara sakin wani saban kukan, “SIF,LOLA,”sai kuma farar magan ciki ta shafa can macijin nan” SUSAN”, tana gama fadar haka suka kara sakin kuka tare da bace bat kamar basu taba wanzuwa ba. A firgice tahee ta farka daga baccin da ya dauketa bakin ta dauke da addua , shafa wuyanta da ya dan rike tayi” me yasa nake yawan mafarkin masu sunannan,su wanene su”ganin babu me bata amsa yasata mikewa , kayan jikinta ta cire tare da shiga wanka , mintuna kadan tafito daga nan dakin, daya daga cikin abayoyin da ammi ta bata ta saka , gaban mudubin dake shake da kaya ta nufa,kurawa fuskarta ido tayi ganin irin sahirtaccen kyan da tayi a cikin kwanaki uku da tayi a cikin gidan , sanye take cikin red Egyptian abaya sai faman walwali stone din jiki ke dauka,asalin farin fatarta ta buzaye ta fito tass a jikinta, yayinda cikakken yalwataccen gashin kanta ya sauko har wajan kugunta, sosai bakin kwantaccen gashin goshinta ya kara kwantawa tare da dogon siririn hancinta , ba make up ne a fuskarta ba amma fadin haduwarta bata lokaci ne musamman dan karamin lips dinta da ya fito tass dashi kamar wacce ta saka janbaki,bakin kwalli ta saka da ya fito da farin kyawawan idanuwanta, sosai kwallin ya fito da asalin kwayar idanunta,cikakkiyar gashin girarta da dogayen eye lashes din idanuwanta su suka kara fito da ainahin kyawun fuskarta , ba ma a bociyar lip gloss bace shiyasa tabar dan karamun lebenta a haka, ribbon dinta ta dauka shima red colour tana kichiniyar daurashi, sosai ta jigata kafun ta daureshi sabida cikowarsa,mayafin abayarta ta dauka tare da yafashi saman kanta, red din takalmin ta ta saka , gaban mudubin ta kara komawa tare da karewa kanta kallo , murmushi ta sakar wa kanta tare da rufe fuska , “ ke din me kyau ce “kalmar da kullum taheer ke fada mata, murmushi kawai ta kara saki , tayi kewarsu sosai, hanyar fita daga dakin ta nufa bayan ta gama feshe jikinta da turaruka, Daidai lokacin da yan matan ke shigowa part din,amrah sai faman dingishi take haryanxu jikinta be dena tsami ba, sakin baki tayi ganin irin kyawun da tahee tayi, bama ita kadai ba hatta su ihsan duk sakin baki sukai suna binta da kallo, gaishe da su tayi babu Wanda ya amsa mata sai ihsan dake faman sakin murmushi, “tubarkallah Masha Allah , gaskiya ke kyakkyawa ce tahee”,sun kuyar da kai kawai tahee tayi tana wasa da yan yatsun hannunta, binta da kallo su sumayya sukai kowa yana hadiye abunda ke ransa, dogon tsaki amrah taja tare da karasa kan daya daga cikin kujerun falon, sosai take bakinci, dama ace Itace take da wannan kyawun, wani dogon tsaki ta kuma ja tare da daukar wayarta suma duk yan matan waje suka samu tare da zama ,ihsan ce ke kokarin magana ,jin sallamar zoya ne ya katse mata zancenta, inda Ihsan take ta nufa “aunty ihsan” rungumeta ihsan tayi “na’am my baby”kallan yarinyar da aka kira da baby tahee tayi , Itace dai yarinyar da ta gani tana bacci,”aunty ihsan wai ina da wata aunty tana ina “murmushi ihsan ta saki, “toh daman bazuwan kowa kikai ba sai na auntyn taki ko”dariya zoya tayi tana rufe fuskarta , itama murmushi ihsan din ta saki “oya kinganta” juya wa zoya tayi tare da kallan Wanda aka nuna mata, zaro fararan idanuwanta irin na king tayi, “aunty ihsan tana kyau, harta fini ma, amma yaya king dina ya fita” dariya ihsan ta saki kawai , sai alokacin tahee taga tsananin kamanninta da Wanda yake zuwa part Dinsu,murmushi kawai tahee ta sakar mata, itama murmushi zoyan ta saki “Aunt ya sunanki” taheera shine kadai abinda tahee tace,kara zaro ido zoya tayi “sunanki me dadi , ni kuma zoya yanxu Kema kinzama aunt dina kinji”girgiza mata kai tahee tayi sosai yarinyar tashiga ranta, duk wannan abun su sumayya na zaune suna kallan ikon Allah musamman amrah dake jin kamar ta samu wuka ta caccakawa tahee..shigowar ammi ne ya katsemata tunanin da ta shiga,”yaude yan mata na sai yanxu nake ganinku” ko wannansu murmushi ya saki sabanin sumayya da amrah da suka saki na yake “Aah ammi kinsan akwai school shiyasa “gyada musu kai ammi alamun gamsuwa kafin ta mike ,”yanxu dai ku Tashi ku kaiwa son abinci sai a dawo a yi hirar”, cikin firgita kowannansu ya zaro idanuwansa tare da furta YAYA KING…..
Comment and share .
💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖
Duk karfin izzata
Gidan Aunty
Ya fita zakka
Jini daya
Sarki sameer
Baby .
MSS LEE💖..
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/JyvVuOvzYyF19np8UmFKV4
💖💖GIDAN AUNTY 💖💖
(a heart touching love story)
Story & written
By
Mss Lee 💖
PAID BOOK
littafin gidan aunty na kudine akan 300 kacal ne so har karshe zai biya ta wannan bank din 7041879581 opay Ayshatou Galadima , sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.
Masu bukatar a tallata musu kasuwancin su , su tuntubeni cikin wannan number 07041879581.
BOOK 1 📕
Free page 17🦋
Duk binsu da kallo ammi tayi ganin lokaci daya duk sun tsorata,suma duk sai sukai shiru ganin irin kallan da ammi ta bisu dashi, tahee da zoya ma duk tsayawa kallansu sukai, kamar daga sama cikin sauri amrah tace “zani ammi”jinjina mata kai ammi tayi tana sauke ajiyar zuciya, kafun ta karasa kitchen taji saukar muryar sumayya” Ammi nasan kayan sunyi yawa bari na temaka mata”ta karasa tare da dallawa amrah harara batare da ta bari ammi ta ganiba, ita tahee dariya suka bata ma, ko za a yankata aibazata je inda za a ballataba,jinjina mata kai ammi tayi tare da karasa shigewa cikin kitchen din, cikin sauri amrah ta jiyo tana kallanta,”mtswww na tsani shishshigi Wallahi “, kallan rainin wayo sumayya ta bita dashi, “zaki hanani taka ko ina na gidan mune”, dogon tsakin da firdausi taja ne ya katsesu “malamai kunbi kun ishemu inda gaske sansa kuke kuje kuce a aura muku shi mana kinbi kun cika mana kunne” tana gama fadar hakan ta mayar da headphone din kunnenta, ba Wanda ya kara cewa komai sai kallan banzan da suke bin junansu dashi , ihsan kam sharesu tayi tacigaba da game din da zoya ta sa musu , zuwa zaune kusan yan mintuna su asabe suka fito da kayan da za akai masa, har yan rigen rigen tashi ake tsakanin amrah da sumayya,amrah ce ta fara karasa tare da amsa kayan hannun asabe tana yatsina fuska,itama sumayya ragowar kayan ta dauka tana hararar amrah, Tashi tahee tayi da niyar komawa daki ammi ta tsayar da ita, “Kema daughter jirani na aikeki part din dada da na ummey”tana gama fadar hakan ta shige wani daki, mintuna kadan tafito dauke da wasu designers bag guda biyu, lokacin har su amrah sun bar part din, purple din ta nuna mata na dada ,red din kuma na ummey, mikewa zoya tayi “ammi zan bita”murmushi ammi ta sakar mata “toh daughter “kama hannun tahee zoya tayi, kowa na mamakin ganin lokaci daya ta sake da tahee, Kai tsaye part din dada suka fara zuwa Tun a hanya zoya Kezuba mata surutu falon yayi saura daga ihsan sai firdausi dake jin waka.
Zaune dada take kasan lallausan carfet din falon ta, kamshin farfesun kayan cikin da akai mata sai faman tashin kamshi yake, cikin sallah tahee ta shigo falon tare da zoya,amsa sallamar dada tayi tana sakar masu murmushi” sai yanxu kika tuna dani tahura, ai nayi fushi “,sun kuyar da Kai tahee tayi cikin jin kunya” kiyi hakuri dada ba haka bane”, dan ta bile baki dada tayi “ gaskiya kam ki gyara, ko d’an hirar nan ki dunga zuwa kina tayani tunda su wadancan bankadaddun ba zuwa suke ba, sarakine kawai shima kullum cikin fada muke”, kallan ta zoya tayi”dada nifa , kinsan dai ina zuwa ko”,sakin baki dada tayi tana kallanta” kiji tsoran Allah, ni nayi mamakin ganin ki ma yau, ba dai kyau karya kinsani”, dariya zoya tayi tana rufe dan karamin bakinta, sakon da Ammi tabayar abata tahee ta mika mata “Allah sarki,kilishi ba dai mutunci ba ,duk gidan nan ita da hajiya suhaima ne masu kaunata sai sadauki”ta karasa zan Canta tana Shan farfesun ta, kallan tahee dake wasa da hannunta tayi”kinga zamu bata sai wani jin kunyata kike kamar wacce akace miki na zama sirikarki”, sosai dada da zoya suke janta hira tun bata sake ba har ta sake da su, sun dad’e suna hira kafin tahee tace zata kaiwa ummey sakonta,’kin barin ta dada tayi har saida taci farfesun da ta zuba musu zoya sai faman dariya take musu, da zata tafi ma sai da tayi wa dada alkawarin dawowa anjima sannan ta barta,tsakanin part din dada dana ummey ba nisa shiyasa basu dade ba suka karaso, sai bin ko ina tahee take da kallo ganin irin kyan da wajan yake dashi, zoya na gaba tahee na bayanta har suka shiga hadaddan kayataccen falon, sosai falon yake da girma da tsaruwa,ta ko ina kamshi ne ke tashi da sanyin Ac, ganin babu kowa a falon yasa tahee zama kan lallausan carfet din falon me shegen laushi da daukan ido, a guje zoya tashiga wata kofa kusan minti 5 sai gasu sunfi to ita da ummey dake sanye da black abaya sosai kyawun ta na larabawa ya bude shekarunta, wacce ta ganine yasata dan sakin murmushi, tare da zama kan daya daga cikin lallausan kujerun falon, gaishe da ita tahee tayi , yayinda ummey ta amsa mata cikin kulawa, haka kawai taji yarinyar ta kwanta mata arai sabida nutsuwarta, sakon ammi tahee na mika mata, wani murmushin ummey ta saki,”kice mata nagode sosai kuwa, bata gajiya “yadda ummey ta yabi ammin sai kaunar auntyn tata yakara shigarta sosai take santa,mikewa tayi daniyar tafiya ummey ta zaunar da ita “ ina kuma zaki, yanxu zamuyi lunch “ komawa tahee tayi ta zauna bazata iya yi Mata musuba sabida kunyarta da takeji, kallan ummey zoya tayi” ummey kingama a part din dada guduwa tasoyi “,girgiza mata kai ummey tayi cikin yaren larabci “bana hanaki surutu ba”, sun kuyar da Kai tayi”ana asf”ummey bata kulataba sai kallan tahee datayi “daughter taso muje muci abinci”ba yadda tahee ta iya dole ta mike ,tare suka nufa hadadden dining din dake falon,sosai wajan dinning ya hadu kasancewar wajanshi daban a cikin falon bayan antaka 3stairs, dakanta ummey tayi serving Dinsu , sosai kamshi girkin ya cika ko ina , nut spicy herb rice da Greek chicken kebab ummey ta zuba mata ,sai wani yan bowl masu shegen kyau da ta zuba mata salad da sauran dishes din, cikin glass cup kuwa strawberry milkshake ne aciki me shegen sanyi, sosai abincin ya birge tahee amma ta kasa moshi ,sai godiyar da tayi wa ummey kawai, itama ummey serving din su tayi ita da zoya, har sun fara cin abinci ganin sai wasa tahee take da spoon din hannunta ummey ta kalleta” daughter ya naga ba kyaci, ko abincin be miki bane”saurin girgiza mata kai tahee tayi “a’ah ummey yanxu zan faraci” ta fada tare da soma cin abincin a hankali , ummey batace komai dan Sarai ta gane kunyarta tahee takeji,suna cikin cin abincin kuwa daddad’an kamshin turaren da basuyi tsammani bane ya cika dodan hancinsu,da ma duk wani kamshi dake tashi a falon,kasa cigaba da cin abincin tahee tayi zuciyar ta sai faman bugu yake, naman da yake bakinta ma ta kasa taunawa sai faman tsotsanshin take, a hankali cikin daddadar muryashi yayi sallama , amsawa sukai baki daya banda tahee da ta kasa mosi, zoya sai kallansa take tanaso taje wajan sa amma ya Hana ta intanacin abinci,kan daya daga cikin kujerun falon ya zauna tare da crossing legs dinsa , binsa da Kallo ummey tayi , tayi kewarsa sosai da sosai amma a zahiri sai dauka hankalinta be kansa, cikin kasa kasa da murya zoya ta kalli ummey” ummey please ki cewa akhii yazo muci abinci , this once only please “kallan ta ummey tayi tare da dauke kanta,ganin hakan yasa zoya kara marairaicewa “please ummey”, girgiza Kai kawai ummey tayi har lokacin kuma tahee ta kasa ko kwakkwaran motsine, duk maganganin zoya yanajinta Sarai amma a zahiri sai ka dauka bayacikin falon,cikin larabci yaji saukar muryarta” taso muci abinci”,kamar bazai motsaba sai kuma ya tashi a hankali tare da nufar dining din ba tare da yace komai ba, Daidai inda yake shigowa tahee tana facing din sa, sarkewar da idanuwansu yayi te yasata shakewa da abincin da ke bakinta, sosai take tari dan ba hakaramun Shakewa tayi ba…
*********Tun lokacin da suka baro part din ammi suke wa juna kallan kaskanci, daman ba shiri suke da junansu ba musamman da ya kasance suna san mutum d’aya , har suka karasa part dinsa ba Wanda yace wa kowa kala,duk da fargabar dake tattare dasu haka ko waccen su ta shiga falon dan bakantawa yar uwarta, bakowa a falon kasa ganin hakan yasa amrah nufar center kujerun tare da ajiye tray din hannunta, itama summy cikin gadara tanufi inda amrah ta ajje nata inama ta dora natan, ganin hakan yasa amrah saukar da na sumayya, itama sumayya sai abun ya bata haushi ta dan kwalar da na amrah, cikin kankanin lokacin suka fara ture turen abinci,a lokaci daya suka sa hannu tare da ture abinci junansu, take a wajan komai ya fadi kasa ya fashe Daidai lokacin da king ya fito daga wata kofa,bin ku waccen su yayi da rinannun idanuwansa , a part dinsa zasuyi masa wannan iskancin,kwata kwata basu ankara da shi a falon ba, amrah da tafi tsiwa ta tunkari sumayya , lokaci d’aya suka fara danbe da junansu, bece musu komai ba sai koma daki dayayi , cikin kankanin lokaci yafito hannunsa goye a bayansa sosai ransa ya baci, basu ankara ba sai saukar belt da sukaji, cikin bacin rai yake jibgarsu,”how dare you”, sosai suka firgita, sai faman hakuri suke bashi, sai da yasan sun daku sannan ya kyalesu, cikin nutsuwarsa ya zauna kan kujerar dake zaman mutum daya tare da crossing legs dinsa, ko wannansu zubewa yayi a kasa tare da yin kneeling, kowannansu na nadamar zuwa part din, kara had’e ransa yayi tare da kallan tulum abincin da suka bata,”it them all”, daga nan be kara cewa komai ba, sosai sumayya taji wani kukan na zuwan mata dan bata dade da cin abinci ba, amrah ma sai faman zare ido take hawaye na zubomata, belt din dake gefe ya dauka cikin sauri ko wannansu ya karasa inda suka zubar da amincin har da Wanda suka tattake, suna kuka suna tusa abiinci da suka zubar, ko wannansu ba yunwa sukejiba,sai