Showing 45001 words to 48000 words out of 52049 words

Chapter 16 - GIDAN AUNTY

26 Jul 2025

2915

gidan ganin haka yasa motoci biyu na sojoji bin bayansu, suma sauran yan gidan shiga mota sukai da bin bayansu sojoji ne take musu, aunty kawai aka bari datace ta zata taso amrah sai su taho tare, ba Wanda yace mata kala har suka taho asibitin.

Koda su dada suka shigo asibitin da gudu sojojin nan suka zagayesu kowa duk Wanda yazo wucewa sai ya kallesu, kara dialing number king abey yayi akaro na ba adadi, yanxu ma kara kiran yayi not rechable Daidai lokacin da wasu manyan likitocin asibitin suka karaso da gadon daukar mara lapiya , inda take abeey ya nuna musu, daya daga cikin doctor dinne ya bude motar da niyar dakko ta, Daidai lokacin da motar king ta sharo da gudun gaske,Kai tsaye inda su abey suke zaki ya nufa, suna ganinsa suka sauke a jiyar zuciya yau da kanshi ya bude kofar ya fito tare da nufarsu,ganin su gabaki d’aya a wajan ne yasa ya maida hankali kan abeey” what happen “ ya fada a kasalance, kasa yi masa magana sukai sai bayan Botar da suke nuna masa , a hankali ya bude kofar wacce ya ganine yasa shi dan ja baya kafun cikin azama ya shige cikin kotar, ganin yadda jikinta ya baci da jinine yasashi rintse ido kafin ya dauke ka kamar yar baby a jikinsa , ko gadon da aka dakko be kalla ba ya nufa da ita ciki cikin sassafa, kowa na wajan binsa da kallo yayi amma ba bakin magana hatta ma’aikatan wajan kowa sai satar kallonsa suke, sau daya ya kalli doctor din gefansa , “doctor halima” yana gama fadar Hakan ya shige lifter tare da barin yan gidan , direct office dinsa ya nufa da ita duk jikinsa shima ya baci, cikin few minutes sai ga wata doctor mace tazo lokacin da yake mata dressing din ciwon kan nata, sau daya ya kalleta be ce mata komai ba ya dauki tahee yanxun ma cikin sassarfa ya nufi wani door da ita, itama ma doctor haliman cikin Sauri tabi bayansa bayan ta kirawo wasu nurse, duk ragowar likitoci tsayawa sukai suna tsoran shiga theatre din ganin be nemesu ba kowa ya koma gaban aikinshi, kusan hour daya da rabi ya fito daga cikin theater din, kallansa abeey yayi cikin damuwa “ yaya jikin nata “ duk zuba masa ido yan gidan sukai suna jiran amsarta sa “ sai ta farka tukunna” ya karashe zancan nasa da kallon ammi da yake jin kukanta har zuciya, muryar abeey ce ta Katse masa tunaninsa” zamu iya shiga” jin jina masa kai king Kawai yayi sabida ciwon kan da yake ji, wani baban daki aka kaisu inda aka kwantar da ita, sosai Wajan yake da girma kamar ba asibiti ba, kwance take kan gadon sanye da kayan marasa lapiya , kanta nannade da bandage sai drip din da aka sa mata, sosai fuskarta tayi fiyau da ita ga wani kyau data kara jikin ta kamar babu Jini a jiki, ko wannansu kallanta yake cikin tausaya wa hatta summy da bata santa saida ta zubar mata da hawaye, sun dade zaune a asibitin har wjan 2 na rana kafun abeey ya bada umarnin su koma gida yayi saura daga dada sai ummey saishi ,uncle Saleem da uncle musaddiq kuma suka tafi tare dasu, shima abeey office din king ya nufa cikin rashin sa’a ya tarar da office din a kulle, ganin ana kiraye Kirayen sallane Ysa abeey ya nufi masallaci koda aka idar da sallan be koma ciki ba sai da yayi la’asar. Koda ya koma cikin tashin hankali ya samesu ganin yadda tahee ta cire drip din hannunta sai kuka take , duk Wanda yayi yun kurin tabata sai ta buga masa wani abu, gabaki d’aya doctor din tsaya wa sukai suka su ammi kuka suka saka ganin halin da take ciki, zuyawa yayi da niyar kiran king sai gashi yashigo cikin wata shigar daban,bin dakin yayi da kallo ganin yadda ya baci, daya daga cikin nurse dince ta nufi tahee da niyar rigeta bayan ta ga Shigowar king , bata Ankara ba tahee ta buga mata abu ka , kara ta saki tana ja da baya , kuka tahee ta saka “karku tabani, su wanane ku, kumaini wajan dady na” sukenan kalaman da take, umarni king ya bawa doctors din su fice da ido kafun a hankali cikin takunsa ya nufi wajan gadon, cikin rufewar ido tahee ta dauki abu daniyar kwala masa sai kuma ta tsaya da kukan da take ta fara dariya kamar wata zautacciya, be ankara ba sai ji yayi ta rungumesa “daddy na “ shine kadai abunda tace tare da kudun dune king da ko motsi yakasa bayan rungumesan da tayi.

Comment and share 😌✍️
Mss Lee 💖

‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

💖💖GIDAN AUNTY💖💖
(a heart touching love story)

Story & written
By
Mss Lee 💖


PAID BOOK

MESAN COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YAYI MUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581.

BOOK 1

LAST FREE PAGE

Free Page 26 and 27 🦋

“Dady na “ ta kara kira sunansa idanuwanta na zubar da hawaye, salati dada ta saki “ Innalillahi wa inna ilaihi raji’una, Allahumma a jirni fi musu bati , tahura wanene kuma dady”, dada ta fada da nufar inda tahee take , wani kukan tahee ta saka “karku tabani bana so, ku dena ta bani su wanene ku”, gabaki d’aya su abeey kasa motsi sukai sai Innalillahi da suke maimaitawa tun dasu , ammi ko tsayuwa ta kasa sai waje ta samu ta zauna ta cigaba da kukan da yazo mata.nunfashi king ya saki yana kara hade rai tare da kokarin banbareta daga jikinsa, kamar wacce ake karawa karfi haka ta kara kudun duneshi tana sakin kuka, nunfashi king ya saki me zafi , besan lokacin da ya data mata tsawa ba, sosai ta razana da tsawar da ya daka mata, hatta abeey sai da suka kallesa, kuka tahee ta fashe dashi, cikin futar hayyaci tayi kofa da niyar fita,ko karin riketa abeey yake ,wata karar tasaki “banaso banaso banaso, shima dady bayasona ,Nima banasan kowa” ta kara fashewa da kuka , cikin ta da ya murya ne yasata sakin kara tana durkushewa, a wajan tare da sakin wani saban marayan kuka tana dafe cikinta,taki bari kowa ya ta’bata sai kuka take, lumshe idanuwansa king yayi kafun a hankali ya tako inda take, jada baya ta soma tana girgiza masa kai tare da sakin wani saban kukan, be dena bin nata ba har ta jin gida da jikin bangon, tsayawa dada tayi zani a hannu tana kallan ikon Allah ,tun bayan kuka data sa mata ta buya bayan ummey dake tsaye itama , a hankali ya tsugunna a wajan kansa har ya fara sara masa, gefe tayi da kanta tana cigaba da kukanta ga ciwon cikin dake nukur kusarta sai faman rike ciki take, “kalle ni” ya furta a hankali yana binta da idanuwa,dan mitsitsin bakinta ta tabule kamar me shirin yin kuka “shhhhhh” yace mata , shirun kuwa tayi har yanxu taki dago da kanta sai hawayen dake biyo fuskarta,” me akai miki kike kuka “ ya furta a fusge kamar bashi ba, bakin ta bude daniyar kuka ya kara dakatar da ita “bana san kuka” kukai kuwa gaya dena “basu ne ba suna ta bani nace kuma sudena banaso, Kai ma bakasona ka koreni” ta karasa maganar tata tana turo dan karamin bakin ta kamar wata yar yarinya “ Wannan yarinyar Anya ba aljana bace “ ya fada a zuciyarsa, amma sabida buguwar datayi aka yasa bece mata komai ba, “toh shikenan mun dena , suma bazasu ta baki ba”, da sauri ta kallesa tana share hawayen fuskar tata, “dady da gaske kake”,girgiza mata kai yayi kawai ba tare da yace mata komai ba, da sauri ta fada jikinsa tana kara dukun kune shi” dady banasan su na tabani kaji”,be ce komai ba sai lips dinsa da ya datse “ dady ! You killed me “ ya fada a zuciyar sa , ganin ta fara kuka kasa kasa ne yasa ya kalleta, be auneba ta fashe masa da kuka, “dady cikina, cikina” ta fada tana rike cikin nata, kasan cewar yasan dalilin ciwon cikin nata yasa be ce komai ba , ya dauketa tare da barin dakin a hannunsa kamar wata yar baby, bin bayansu da kallo su dada sukai, kafun ta sauke a jiyar zuciya, kallan su ummey tayi” mude mun shiga uku, yanxu kenan sadauki yazama Baban ta, ku kalla fa , wai bata san muba “ babu Wanda ya kulata harta gama surutun ta kowa da abunda yake sa’kawa a ransa.

🫧🫧🫧🫧🫧

Tunda aunty ta koma part din ta tsabar murna bata bata sanar wa da amrah da bata falon komai va, yayarta da ta haifi amrah ta kirawo, “yar uwa rabun jiki, Al bishirinki “ banji amsar da aka bata ba sai dariyar da aunty ta saka “uhmmm tsinanniyar can ai ta mutu, yanxu aikin mu zaizo cikin sauki daman “ gabaki d’aya yadda ta ga taheen sai da ta sanar wa yar uwar tata suna yi suna dariyar farin ciki , tana gama wayar tata takirawo aminiyarta, bata jira komai ba ta nufi dakinta cikin kasa kasa da murya ta sanar da ita Abunda ke faruwa,banji me akace mata ba Amma sosai ta nutsu tana saurarar kawar tata , wata dariyar mugunta aunty ta Saki “ bar shashashu , a tunaninsa ina yin duk wannan abun sabida su, Kema kinsan wacece ni , ina gama an fani dasu zan zubar dasu”, kara kyalkyalewa tayi da dariya, sun dan jima suna wayan kafun ta kashe kiran.

******* wayace kare a kunnan amrah , sosai ta nutsu tana sauraran abunda ake ce mata, fuskarta dauke da yalwataccen murmushi, ta dauki dogon lokaci taba wayan kafun ta kashe , dariya ta saki sosai saida tayi me Isarta sannan ta tsaya “ Lalle yarinya da dani zakice zaki taka, cikin sauki na gama dake saura aunty inma in ta kammala mun aikin” ta karashe zan can nata tana sakin dariyar mugunta harda rike ciki, ta dade a hakan sai ga aunty ta shigo itama dakin, duk abunda ya farun saida auntyn ta sanar da ita, nunawa tayi kamar batasan anyi ba, ta kara shiga cikin murna dan tabbatar da zancan mahaifiyarta, tsabar murna har wata kwarya kwaryan liyafa suka hadawa kansu ko tunanin su duba a asibiti ba sayi , duk a tunaninsu ta mutu.

🫧🫧🫧🫧

Direct office dinsa ya nufa da ita sai faman kuka take masa, baice komai ba sai ajjeta da yayi cikin wani bedroom me kamar daki komai nacikin daki akwai a ciki ga wasu na urori dake dakin kamar ba cikin asibiti ba, murkususun ta cigaba dayi tana kiran “dady !! Dady”, kallanta yayi yana lumshe idanuwansa da suka fara gajiya sabida ciwon kan da yake ,kafun ya karaso a hankali inda take, wasu injection ya hada tare da nufar inda take, tana ganin injection dinnan ta kara sakin wani saban kukan, tana girgiza masa kai “banaso , banaso” be kulata ba har ya karaso wajan , a guje ta mike duk da ciwon dake cinta ta saka kafa zata gudu, taku daya yayi ya rike damtsen hannunta, kuka ta saka masa tana kokarin kwace hannunta da ya rike , ganin allurar hannunsa yasa taci gaba da kokarin guduwan, sosai tasaka iya karfinta tana san kwace wa , kwakkwaran riko daya yayi mata tare da zaunar da ita kan gadon har lokacin kuka take, alkuran ya ajje abayansa tare da kallonta “na fasa to, yimun shiru”, kallan hannunsa tayi ganin babu alluran yasa lokaci d’aya kukan nata ya tafi, jingina tayi da jikinsa tana dan turo baki , be ce mata komai ba har kusan minti daya tana wasa da abun rigarta, allurar da taji ya tsira matane yasata sakin kara da niyar mikewa, sosai ya riketa kwakkwaran motsi ta kasa harsaida ya kammala allurar tasa, hade rai yayi sosai kamar bashi ba , cikin kausashshiyar murya ya firta “yi mun shiru” tsit kuwa kukan nata ya dauke sai karamin lips dinta da take turo masa , tsawan lokaci suna a haka lokaci zuwa lokaci yakan dago da idanuwansa , jim kadan ya kara dago da idanuwan nasa yaga ta fara bacci, ajiyar zuciya ya sauke kadan” am dead “ ya furta kawai kafun ya dakko wasu na ura, sosai yayi bincike akan ta bayan Wanda yayi mata lokacin dressing , nunfashi ya fesar ganin kiran abeey, be dau dogon lokaci ba ya dauki kiran ,”kana ina “shine kadai abunda abeey yace masa, “office “ king ya furta tare da lumshe idanuwansa kamar abeey na kallonsa, ko minti biyar cikakkiya abeey beyi ba ya shigo office din, inda tahee take kwance ya kalla tare da girgiza kansa, “me ya sameta” ya kara tanbayar king din” she lost her memory abeey” da sauri abeey ya kallesa tare da furta Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ganin hakan yasa king ya mike daga inda yake tare da nufar abeey din,” please abeey karka tayar min da hankali , kasan ba lapiya Kake dashi ba please abeey “, zuciyarsa abeey ya dafa tare da dafe kan sa, rikosa sosai king yayi duk da yanayin tashin hankalin da ya shiga amma a fuska ba alamun hakan, dago da idanuwansa abeey yayi da suka fara jaa alamun ciwon sa zai tashi,”kayi mun alkawari guda daya” kallansa king yayi da lumsassun idanuwansa, sosai abeey ya kara dafe zuciyarsa “KAMUN ALKAWARI ZAKA AURETA YAU DINNAN “.


Comment and share ✍️
Mss Lee 💖

Alhamdulillah yau na kawo karshen free pages dina , mea san cigaba da gidan aunty zai turo kudin sa fa wnn asusun 7041879581 palm pay Ayshatou galadima , sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.

Masu comment ina Godiya 💖🫶.

💖💖GIDAN AUNTY💖💖
( a heart touching love story)

Story & written
By
Mss Lee 💖


PAID BOOK

MAISAN COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YAYI MUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581

BOOK 1

BONUS

PAGE 28 and 29🦋
2 page ne na hade muku🫶.

“IMPOSSIBLE “cewar king da idanuwansa suka fara canza launi,cikin bacin rai, be bari abeey ya kara magana ba cikin sarkewa,” how on earth abeey zakace na auri wannan yarinyar, as small as she is, yarinyar da in da Auran wuri nayi zan haifeta, please abeey mana I can’t marry her,never”, cikin sauri abeey ya kallesa ganin yadda idanuwansa suka fara canza kala ,yasan ransa ba karamun baci yayi ba Amma shima ba yadda zayyi tunda babu Wanda yake wucewa kaddarar sa,”bazaka iya aurantaba kake fadamun” abeey ya fada azafafe, “yes I can’t marry her ,and I will never “cikin bacin rai abeey ya mike tsaye, “shikenan kaje Kayi duk yadda kaga yayi maka tunda ban isa da Kai ba,yau ni ka kewa musu akan abunda na umarceka dashi, nagode sosai, Allah yajikan dan uwanka Muhammad nasan da yana raye da shine zaimun wannan alfarmar ya aureta”ya karasa a raunane , cikin sauri king ya dago da idanuwansa jin sunan da abeey yakira,”abeey” yakirawo sunansa a sanyaye, daga masa hannu abeey yayi “bana bukatar jin komai daga bakinka, kaje kayi duk yadda kakeso”, yana gama fadar hakan ya kama hanyar fita, jiri ne ya d’ebesa zai fadi cikin zafin nama king ya riko hannunsa tare da zaunar dashi, kara tashi abeey yayi wani jirin na kokarin ka yadda shi,”bana bukatar temakonka “, rintse idanuwansa king yayi, cikin sanyin murya ya furta “am sorry abeey, please ka zauna”be kulashiba sai ma kokarin tafiya da yayi “ Dan Allah “ king ya kara fada kamar Wanda nunfashinsa zai fita daga gangan jikinsa, kallansa abeey yayi duk da tsananin tausayinsa da yakeji a kasan zuciyarsa, azahiri kuwa hade ransa yayi shima, waje ya samu ya zauna , “am sorry abeey” king ya kara fada har yanxu idanuwansa na kasa,”ba fushi nake da kai ba,amma inaso ka tuna halin da amminka zata shiga, da me kake so taji da rashin ganeta da yarinyar bata yiba ko da rashin temakonta da zakayi,karka manta kai me temakon Al’umma ne, meyasa bazaka tausayawa rayuwar yarinyar nan ba ,sanadiyyar rashin mahaifiyarta da d’an uwanta tashiga wannan halin, kayi tunani inda nine..” be bari abeey ya karasa zancan nasa ba king ya soma magana” zan aureta amma da sharadi” da sauri abeey ya kallesa murmushi na kokarin su’buce masa,abunda bai taba tsanmanin jiba daga garesaba, bai kalli abeey ba yaci gaba”maganar yan uwanta zan sa a bincika,I will marry her just for her condition, idan memory dinta ya dawo zan saketa “ kallansa abeey yayi jin ya anbaci saki, amma be ce masa komai ba,yanxun ma be kalli abeey ba,”and it has to be a secret marriage,wannan ba aure bane temakone kawai data warke zan sauwake mata” yana gama fadar hakan ya kalli abeey, shima har yanxu abeey din shi yake kallo” na amince” abeey ya furta yana sauke ajiyar zuciya. Be kuma kallan abeey ba ya mike tare da shigewa toilet , da kallo abeey ya bishi yana girgixa kai, kafun ya mike tare da fita daga dakin, tunda ya shiga toilet ba abunda yayi sai jin gina kansa da yayi da kofar toilet din, sosai kansa yake sara masa,sink ya kunna,a hankali yake watsawa fuskarsa ruwa, ya dau godon lokaci a haka kafun ya fara sauke a jiyar zuciya, karar da ya Jine yasa shi bude idanuwansa da Sauri tare da barin toilet din, kwance take a inda ya barta , jikinta sai faman karkarwa yake, kara sakin wani karan tayi,”ze tura ta, ze turata “ shine abunda bakinta yake faman furtawa,a hankali ya karasa wajan tare da dora hannunsa kan goshinta, a matukar razane ta farka ,”Zee.. turata…. Zeee turata ,mugune shi” ta furta tana kokarin barin gadon, ganin yadda ta fita a hayyacin tane yasashi rike dan tsan hannunta, ture hannusan ta shiga kokarin yi, ganin ta kasa kwacewa ne yasata fashe cewa da kuka, “ze tureta “ ta kara furtawa, “shhhh” ya furta mata, bata kulawa ba sai kokarin kwacewa da take , tsawar da ya daka matane yasata hadiye kukan nata tana girgiza masa kai hawaye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login