Showing 39001 words to 42000 words out of 52049 words
hagu, a tsorace ta dago da idanuwanta a tunaninta aunty ce ta mare ta ganin ba kowa a dakin ta fara zazzare idanuwa, mafarkan da ta dungayi jiya da daddare ne ya fado mata a zuciya ,da kyar take iya hadiye abunda ke makoshinta, taku ta fara a hankali da niyar barin dakin,talewar da kafarta tayi ne yasa ba shiri ta bige kafar take da sakin azababban kuka, wani saukan marin da ta kuma jine yasa ba shiri ta mike tsaye ga azaba da kafarta kemata kamar wacce tayi targade.”ke “ taji wata razananniyar murya ta kirata,cikin rawar murya ta soma amsawa “naa…am, dan.. Allah kuyi… hakuri innayi muku lefi…”bata karasa maganar taba taji saukar bulala a bayanta,ihu ta soma “nashiga ukuna na lalace,dan Allah kuyi hakuri na tuba bazan sake ba “, kamar wayanda ake zugawa haka suka shiga laftarta saida suka ga ta daku sannan aka daka mata tsawa cikin muryar mata ,”ke, mike tsaye”azabure amrah ta mike fuskarta duk ta baci da majina ga kukan da Tasha “rufe mana baki”aka kara daka mata tsawa, hannayenta biyu tai saurin daurawa abakin mata sai faman waige waige take ga hawayen da ke zuba a fuskarta,”rawa zaki mana yanxun nan , duk rawar da muka saki,kuka kuskura kika fadi zaki gane kuranki, kinajina”, da sauri ta shiga daga kai har ynxu hannunta na kulle a bakinta,dariya muryoyin mace da na mijin suka saka kafun lokaci daya wajan yayi shiru,”maza yi mana rawar dan biri”ana gama fada mata haka aka jefo mata ayaba kuda d’aya, da sauri ta dauki ayabar ta fara tsalle kamar yadda dan biri keyi, fuskarta duk ta baci da hawaye ga guntun gashin ta da ya barbaje sai ta dawo kamar dan birin kuwa, tanayi tana kwantawa alokaci daya kuma tana kuka, sosai taji muryoyin nan guda biyu suna dariya kafin ta karajin wani sautin,”yi mana yadda mage take kuka”, kara fashewa da kuka amrah tayi kafun ta fara “meowwww meowww meowwww moewwww” ta nayi tana share fuskarta da ta baci, sosai suka wahalar da ita, iya rawan dabbobin kam har Wanda bata sansuva tayi rawarsu,ga kafarta dake tsananin yi mata ciwo kamar wacce ta goce a kashi.
********** kwance take kan lafiyanyan gadon dakin nata, hannu daya wayane a ciki yayin da Dayan hannun take rike da apple, waya take sai faman murmushi take saki ita kadai, turo kofar dakin da akai ne yasata dagowa,wacce ta ganine yasata mikewa zaune tare da kashe wayar, Momy kice kuma yau adakina, karasa shigowa wacce aka kira da momy tayi kafun ta samu waje ta zauna daga bakin gadon, “ko na komane”ta fada tana zubawa firdausi idanuwa, dan jinjina mata kai firdausi tayi tare da dage kafadun ta kadan,”akan wana dalili zan hanaki shigowa momy, naga yanxu bakya shigowane tun bayan tafiyar yaya haroon,ta bile baki kawai momy tayi kafun su canza hirar tasu zuwa wata,kallan ta firdausi tayi “amma momy ba kya tunanin waccan yarinyar da Gangan ta bige dan taga mutanan gidan suka tarai rayarta, kalli fa wai yau yaya king ne ya taba wata, ni ko hannunsa aka ce ya dora akan wata ai bazan yadda ba balantana wayancan shashashan da suke wahalar dakansu”,murmushi kawai momyn ta saki ba tare da tace komai ba dan Akan idanta amrah ta tura taheen, ganin momyn tata bata biye mata ba yasa share zancen suka fara zancan dan uwanta.
💖💖💖💖💖
Tunda ya bar gidan a guje zaki ya fara tuka Motan ganin yadda lokaci daya king din ya canza masa kamar wani zaki,a dake ya furta “my house “ya karasa maganar tasa tare lumshe idanuwansa, tafiya akai sosai me dan ta Zara daga banana island kafun suzo kofar wani hadadden building me shegen kyau, tundaga wajan gidan da glass akayi shi komai na cikin sa glass ne , cikin sauri sojojin dake bakin gate din suka wangale baban gate ganin me gayyane da kanshi ya zo, a Daidai parking lot zaki yayi parking inda sauran manyan motocin suke, yau be jira an bude mishi kofarba, yana fito wa ciki ya shiga cikin sassarfa, kofar dake kasa kawai ya bude ya shiga, sosai dakin da yashiga ya hadu, kayataccen falo ne a wajan babban gaske da yafi Wanda yashigo haduwa, Komai na cikinsa whites ne tunda ga kan labulayen dakin har kan lallausan carfet din dake shinfide fari tass dashi, ko ina nawajan tashin kamshi yake kamar ana anfani da shi kullum, kan daya daga cikin white sofa din ya zauna ko takalman kafarsa be cire ba, idanuwansa ya lumshe a hankali ,jijiyoyin kansa ne suka mike sosai , kyakkyawar farar fuskarsa tayi ja sosai, kara rintse idanuwansa yayi da karfin gaske ganin har yanxu yanajin tsayayyun breast dinta a jikinsa, sosai gashin jikinsa ya mike ,a zamube ya fara bal da duk abunda yaci karo dashi, zafi yake ji sosai a cikin Jikinsa,sosai gashin jikinsa ya kara tashi ji yake kamar tana jikin sa haryanzu, adduar ya fara cikin zuciyarsa, tsawan lokaci kafun wata nutsuwa ta fara saukar masa, sosai ya ke ajiyar zuciya ganin lokaci daya azababban zafin dake ratsashi ya tafi sai ma sanyi da yake danji a haka wani daddadan bacci ya dauke sa.
*****har yanxu tana zaune a kasa tun lokacin da ya tunku data, kafarta hannunta rike da kafar tata, shigowar da akai ne yasata saurin dago da kanta?ganin su dada ne yasata sakin ajiyar zuciya, da sauri dada ta karaso inda take “me nake gani haka , tahura ya naganki a kasa duk zafin ciwon ne”, rasa me zatace mata tayi kawai sai ta gyada mata kai alamar a’ah, murmushi ta sakar mata a hankali kafun ta gaishe ta “ina kwana dada” girgiza kai dada tashiga yi “Allah sarki tahura,lapiya ta Lou, jiya da kyar nayi bacci sabida halin da kika shiga “wani murmushin ta kara saki kafun ta gaishe dasu abeey, shima cikin kulawa ya amsa mata tare da tanbayarta ya jikinta, sosai ta dan saki dasu Bayan ta gaisa da su uncle musaddiq da suka shigo daga baya, ganin sauran yan gidan ma suna zuwa yasa duk suka koma falon ammi,sosai kafarta tayi sauki dan tana dan takawa kadan kadan , afalon suka cigaba da hira har ummey ta shigo part din yau batare da zoya Suke ba sabida makarantar da tafi,a haka kowa na gidan ya shigo sabanin amrah , wunin ranar a part din ammi sukayi shi sosai suka nuna mata kulawa musamman ummey dake gefenta.
🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧
🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧
BUNKURE
Da sassafe kaka ta bawa ta tashi yau kai tsaye dakin su oumma ta nufa , bubbuga kofar dakin ta shiga yi, jin shiru ba abude ba yasata kara bubbugawa “maryama kina ji ina kiranki shine zakimun uwarshegu ko, zaki nunamun ba’kin halin naku kenan ko, bazaki fito bane kina jina”, ganin yadda take faman buga kofar dakin su oumma ne yasa mutanan gidan fara taruwa,Dije dake labe tun lokacin da kaka tabawa ta fito yasata karasowa wajan,kallan kaka tabawa tayi tana kumshe dariyar dake cint kafun ta soma magana”inna ai maryama yanxu ta zama abinda ta zama “kallanta kaka tabawa tayi kamar ya bangane ba,”oh ai inna komai a filine , jiya agaban idanunmu tafita daga gidan nan , har kokarin zagin mu tai da muka yi kokarin tsayar da ita” sosai kaka taba ta kalleta “kina nufin tana yawan dare kenan”, tabe baki Dije tayi”ai kowa nanan sheda ne inna ki tanbayesu”, nan da nan yan gidan kowa ya fara tashi gulmar,babu me fadar alkairi akan oumma su taheer ganin yadda tafita tun jiya bata dawo ba, girgiza kai kawai kaka tabawa tayi rai a bace ta bar wajan” za tazo ta sameni ne duk gidan karuwanci da take zuwa”, da dad d’aya kowa ya fara watse wa ganin hakan yasa cikin sauri Dije ta shige dakin harda taka rawa, kallan ta bintalo tayi,”ya naga sai faman washe baki kike kamar wata tababbiya”a maimakon ta tsawa tar mata akan kalaman ta sai ta kuma kyalkyalewa da dariya, nan da nan ta kwashe duk abunda ya faru ta sanar wa bintalo, itama bintalon sosai tayi farinciki ganin burinta na Auran babban mutum zai cika ,wani shegen murmushi ta saki a zuciyar ta kuwa fadi take “lallai ma Dije baki da hankali,ai wallahi kafin nayi Auran nan sai na ci duniyata da tsinke yanda na fara jin dadin abinnan da boka Yayi mun ,wallahi yanxu na fara anjima ma sai na koma wajan sa dan ya mallake mun duk Wanda yace zai takuramun, ciki kuwa har dake dan ke kika koyamun”,duk wannan maganganun nata cikin zuciyar ta take kafun lokaci daya ta saki wata yar iskar dariya da ita kadai ta san ma’anarta.
Comment and share
LITTAFIN GIDAN AUNTY NA KUDINE AKAN 300 kacal
zaku biya kudin ku ta wannan asusun 7041879581 palm pay ayshatou galadima , sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.
Saura few pages na gama sakin free pages dina .
MASU COMMENT INA GODIYA SOSAI DA SOSAI , I HEART ❤️ YOU ALL ✍️.
MSS LEE 💖✍️
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA
💖💖GIDAN AUNTY 💖💖
(a heart touching love story)
Story & written
By
Mss Lee 💖
PAID BOOK
NA KUSA KAMMALA FREE PAGES DINA
Mesan KARANTA GIDAN AUNTY DAGA FARKO ZUWA KARSHE ZAI IYA BIYAN KUDINSA TA WANNAN ASUSUN 7041879581 palm pay ayshatou galadima sai a turo shaidar biya ta wanna number 07041879581
BOOK 1
Free page 22 and 23 🦋
A kwana a tashi ba wuya wajan Allah SWT, yau kusan sati biyu kenan da batan su oumma , Tsawan wannan lokaci babu Wanda ya damu da yasan inda suke ,hatta kaka ta bawa da ta share zancen, cikin wannan lokacin sosai bintalo ta fara bin maza ,ganin hankalin yan gidan su nasan komawa kanta ta koma wajan bokannan da mahaifiyarta Ke zuwa, gaba daya ta mallakesu ko dare zatayi babu me tanbayarta dalili, sosai ta baci da kazamin rayuwarnan, Dije kuwa kullum cikin farin ciki take idan bintalo ta Kawo mata kudi ko damuwa da inda ta ke samo kudin batayi,burinta ya cika tun lokacin da oumma tabar gidan,yanxu burinta ta kai bintalo can birni wajan da tahee take sannan itama tasa taheen ta shiga duniya.
🫧🫧🫧🫧🫧
A tsawan kwana kinnan sosai wata shakuwa me karfi tashiga tsakanin zoya da tahee, kullum in ta dawo daga makaranta zaki ganta wajan tahee tana fada mata abunda aka koya musu, yawancin lokuta suna part din ummey ko part din dada da yanxu take kulawa da ita sosai, ta bangaran yan gidan ma haka, momy tana sake mata sosai sabanin mamy da aunty,musamman aunty da ke nuna mata kyautata mata agaban yan gidan , abayansu kuma taita zaginta, ihsan da firdausi ma sosai suka sake mata a yan kwanakin nan, amrah da sumayya ne ko kallo basu isheta ba,ganin hakan yasa itama bata sake musu fuska. Cikin yan kwanakin nan sosai tayi kewar su oumma tanaso tacewa aunty ta kira mata su amma bata san ta yadda zata tanbaye taba.
Yau ma tunda ta tashi da kewar su oumma ta tashi,so take kawai taji muryarsu sabida mummunan mafarkin da tayi a kansu, sai faman zagaye take a daki tana tunanin ta yadda zata tanbaye ammi , ganin bata da wata mafitane yasa ta mikewa tare da fitowa falo a hankali kamar Mara gaskiya, Daidai tana fito wa shi kuma yana shigowa ciki, kamewa tahee tayi wajan tare da rintse idanuwanta,yau sati biyu kenan rabanta da ta gansa, sosai ya kara yi mata kyau kamar kullum kara masa shi ake , a hankali tayi kokarin bude idanuwanta jin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri sauri ga kamshin turaransa da ya cika mata hanci, da gyar ta karasa bude idanuwannanta, Ganin baya wajan kamar yadda tayi tunani yasata sakin ajiyar zuciya, ta juya daniyar komawa kenan idanuwanta suka sauka a kansa, kyawawan fararan idanuwanta ta zuba masa duk da yadda zuciyarta ke faman bugawa, sosai shigarsa tayi mata kyau musamman gyaran gashinsa da ya tubke sai faman kyalli yake ,sak ya fito a balaraben sa dan Inba Hausa yayi baza ka taba tunanin yasan Menene kalmar ba, wayace a hannunsa sai faman dannawa yake cikin kwanciyar hankali,fuskarsa kwata kwata ba annuri kamar Wanda yayi rashin lapiya ga kafar sa da yayi crossing lokaci zuwa lokaci yana motsata, a hankali ya motsa pink lips dinsa kamar me sanyin magana sai kuma ya fasa tare da datse lips din nasa,tunda ta Kafe shi da ido ko motsi batayi sam ta manta ma agaban watake, a hankali ya dago da idanuwansa karaf suka hade da nata,bata janye idanuwan ba sai ma sarkewa da idanuwansu sukai cikin na junansu , bata farga da shirmen da take ba sai jin saukar tsawar sa tayi, sosai ta razana juyawa tayi daniyar guduwa ta ji saukar muryarsa “if you dare “ya karasa kamar be san yin magana , cak tahee ta Tsaya kamar me shirin sakin kuka , ahankali take juyo da fuskarta da ta dukar sosai take jin kunyar abunda tayi ,zuciyarta sai faman bugawa take da sauri da sauri kamar wacce tayi gudu. Lokaci zuwa lokaci take dago da idanta ganin hankalinsa baya kanta cikin rawar murya ta soma magana “ ina wu..ni”, be amsa mata ba haryanxu idanuwansa na kan wayarsa, kara dukar dakai tayi tana wasa da kasan hijabin jikinta,”ina wuni” ta kara gaishesa cikin rawar murya, yanxun ma be amsa mata , ganin hakan itama ta shareshi tana dan turo dan mitsitsin bakinta, dauke gansa yayi daka kallan dan mitsitsin bakin da ta motsa kafin cikin kasa kasa da murya ya furta “coffee”,kara turo dan mitsitsin bakin nata tayi gaba kafin ta nufi hanyar kitchen din , cikin kan kanin lokaci ta kammala hada coffee din azuciyarta sai faman mitar Shan coffee din nasa take ,”coffee ,coffee”, kafun kuma ta sassaita nutsuwarta ta fito falon, a yadda ta barsa a haka tazo ta samesan yana zaune da kafarsa da yayi crossing, duk da yadda zuciyarta ke rawa hakan be sa nutsuwarta fito wa ba” gashi” ta mika masa tana dan russunawa, be fi sakon biyu ba yasaka hannunsa kan dan karamin tray din da ta miko masa, sipping ya fara a hankali,ta kasan ido tahee take satar kallansa “shi wannan kullum cikin Shan coffee ko abincin arziki be ci,nan gaba inaji sai coffee dinnan ya fito masa a jiki”, ita kadai take hirar ta a zuciya,kamar yasan me take tattaunawa ya dago da idanuwansa ,saurin sunkuyar dakanta kasa tayi, dan ta bile bakinsa yayi kafin ya soma magana” get me something to eat “,da sauri ta dago idanuwanta jin abinda yace , bata ce komai ba sai kitchen da ta nufa, a ba’kin gas ta tsaya tana karewa kitchen din kallo,tu nani ta fara me zata dora masa Mara sauki , ganin tana bata lokaci ne yasa ta nufar babbar freezer din kitchen, manyan tilapia fish ta dakko guda biyu , cikin kwarewa ta gyara kifin kafun ta feraye Irish potatoes dinta, bata dau dogon lokaci ba ta kammala hada grilled fish dinta ,da yaji sauce din Dankali sai faman tashin kamshi yake, kunun ayan da ta ga ammi ta jera a fridge ta dakko tare da zubawa cikin madaidai cin jug, cikin lokaci kankanin ta kammala hada abincin , kafin ta fito falo zuciyarta sai bugawa take, hanyanxun yana zaune a falon sabanin dazu yanzu ya dan jingida da jikin kujeran, sunkuyar da Kai tayi kasa,”ga abincin”, be ce mata komai ma sai gyara zamansa da yayi kafun ya bude plate din, sosai yadda aka kawata abincin ya burgeshi amma a zahiri sai ma tabe bakinsa da yayi, be kulata ba ya faraci a hankali , 3 spoon yayi kawai tare da Shan kunun ayar Daidai lokacin da ake shigowa part din da sallama , ammi ce ta fara shigowa bayanta kuma su amrah ne , duk tsayawa sukai cirko cirko a tsaye kafun ammi ta karaso falon cikin mamaki,”son Yaushe ka shigo”kamar bazea ce komai ba sai kuma ya bude baki “am looking for u”, murmushi ta sakar masa “sorry son ina tare da su ummey ne”, lumshe mata idanuwansa yayi, cikin rawar murya su amrah suka bude baki tare da gaishesa, ba Wanda ya amsawa a cikin su saima cigaba da tsakurar abincin da yayi kamar Wanda aka saka dole , kallan tahee dake tsaye ammi tayi, “daughter yanaganki a tsaye ke kuma , kisa mu waje ki zauna mana “ dan dago da kanta tayi kadan tare da satar kallansa ,be dena abunda yake ba hakan yasata sauke a jiyar zuciya kadan ,cikin rarrabewar murya ta furta “daman ina gyara dakine “, jinjina mata kai ammi tayi ba tare da tace komai ba ganin hakan tai saurin nufar dakin ta, da kallo su amrah suka bita dashi ko wannansu na mamakin ganinta a falon.
🫧🫧🫧🫧
KANO
UMC ZHAHIR HOSPITAL
Wata kyakkyawar yarinyace me matsakaicin kyau zaune kan daya daga cikin kujerun da aka ajje a cikin dakin asibitin, sosai ta zubawa Wanda ke kwance akan gadon ido, kafun ta fara share hawa yan da suka tarar mata a ido, cikin sanyin murya ta soma magana “Allah sarki ummu na ,Allah ya jikanki da rahma”, bata kammala zancan nata ba ta fashe da kuma me cikin rai, tana cikin kukan ne tashi alamun taba kofa , cikin sauri ta goge hawayen da suke zubo mata kafun ta kakalo murmushi a fuskarta, sallama nurse din tayi mata kafin maza wani matashin saurayi ya shigo dakin bayan sa kuma wani kamilllan dattijo ne , drip din da ya kare nurse din ta cire ,cikin girmamawa ta kalli dattijon nan, “insha Allahu ta kusa farkawa a ko Wana irin lokaci “,jinjina mata kai dattijon yayi kafun matashin saurayin gefensa yayi mata godiya, murmushi ta sakar masa tare da barin dakin bayan ta kwashe abin drip din data cire, kujerar da budurwarnan take Kai ta mike tare da sakar wa dattijon nan murmushi “Daddy ga waje ka zauna”, binta yayi da kallo kafun ya sakar mata murmushi shima “nagode daughter” cikin takun dattakon ya karasa tare da zama kan kujerar, kallanta matashin saurayin nayi tare da hararar ta cikin tsokana yace “daman nasan