Showing 18001 words to 21000 words out of 52049 words
biyu ne yasashi kara ware mummunar fuskarsa “ kutumar ubancan , ya na fara ganin garin yana juyawa ko an fara hazo ne “be kammala maganar tasaba tahee da idanuwanta suka juye ta kara tsinka masa mari” saurin dafe fuskar tasa yayi har yanxu bakin nashi be mutu ba” auzubillahi, ko an fara tafiya lahira ne ban sani ba” saukar marin da yaki a fuskarsa ne ya sashi zabura da fita “shikenan a fara sha hada , an fara mutuwa “, sai da ya bace wa ganin ta sannan idanuwan ta suka dawo Daidai ganin ba kowa a wajan yasata dage kafada da komawa cikin gida . Koda ta kowa cikin gidan oumma bata ce mata komai ma , itama tahee batace komai ba sai hirarsu da suka cigaba .
➰➰➰➰➰➰➰➰➰
LAGOS
Tun d’azu ta kasa zama sai faman zirga zirga take , Aunty kawai take jira ta shigo, ta dade a tsaye kafun hajiya Amina ta shigo falon duk rai a bace , kallanta amrah tayi kafun ta sauke a jiyar zuciya, “Anda ce aunty!?” Ta tanbayeta da sigar tanbaya , bata kulataba sai da ta samu waje ta zauna “ amrah ban taba sanin matar nan makira bace sai yau, wai harni tsohuwar matar nan zata karya ta”, tass ta bawa amrah labarin abunda ya faru ta dora da cewa” wai ni amrah kina shafa kwallin tayar masa da sha’awan da Malam ya baki “ cikin kun burin fuska Amrah ta amsa mata “ ina shafawa aunty, gasky ya kamata a koma wajan Malamin dan bazan taba yadda wata ta same shi in ba ni ba, ni ko baze aureni ba inaso mujiyar da juna dan inasan na d’ad’and’ana zumarsa kona kashe sha’awar dake tasomun”jin jina mata kai kawai hajiya Amina tayi, itama amrah bata kuma cewa komai ba ta shige daki, da kallo aunty Amina ta bita “ ba ke ba ai amrah ko ninan da zan samu damar d’and’anasa so nake , musamman yadda yake da kakkarfar jikinta, ni kadai nasan dad’in da zansha “ duk cikin zuciyarta take wannan sa’ke sa’ken kafun ta nufi haryan dakin ta itama .
***********
Ya dan Jima a hospital yau sabida wasu Mara lapiya a dake dake cikin wani mayuwacin hali, successfully kuwa akayi musu aiki, bayan ya dawo ne zaki ya kawo masa files din company, ba karamun barnan kudi akai ba, makudan millions sun ‘bata, batare da kwakkwaran daliliba,duk account din da kudin ke fita ta wajansu anne mesu anrasa, Wanda hakan ya bashi alamar tanbaya , tabbas ana fitar da kudi sannan dasa hannun wasu daga cikin companyn , amma tanbayar su wanene suke fitar dashi, daya daga cikin secret agent din companyn king yasa a nemo masa, tare da bashi Umarnin binciko masa komai daya danganci file din companyn,suna gama aikin da zasuyi sukai futar gaggawa shida zaki yau ko masu tsaro be fita dasu ba.
➰➰➰➰➰tunda ta tashi yau da fargaba ta tashi, ganin kullum mutanan gidan sai sunyi maganar aura mata dan iskan da suka ce, komai cikin sanyi take yinsa, “tahee”oumma ta kira sunanta “naam oumma”sosai oumma ke kallanta”meke damunkine yau”murmushin ya’ke tahee ta saki “babu komai oumma kawai yau da fargaba na tashi”, murmushin manya oumma ta saki” in Auran nan kikesa wa aranki kicireshi, ki dunga yawaita addua in alkairi ne, in kuma sharrine Allah ya nisan taki dashi”jin jina mata kai tahee tayi “insha Allahu oumma”.
Bin bayan ta da kallo oumma tayi , abun na damunta sosai amma tana boye rauninta ne sabida kar tahee ta karaya, kullum adduar ta Allah ya zaba mata mafi alkairi.
Shigowar tahee dakin ne yasa taheer sakin murmushi dan duk yaji zancensu,kara sakin wani murmushin yayi yana kamo hannun tahee din, be bari tayi magana ba ya dora da “nayi mafarki, nayi mafarki kinyi aure ,kin auri babban mutum da kowa yake san mallakarsa ba wancan dan iskanba, zakiyi rayuwa dasu sosai wasu zasu soki, wasu kuma zaki nuna miki ki”binsa da kallo kawai tayi duk da bata yadda da magan ganun saba amma hakan ya sanyaya mata zuciya .
Karfe biyu na rana wasu manyan motocine suka shigo garin, kowa sai bin motar yake da kallo ana d’aga musu hannu, Daidai kofar gidansu tahee motocin nan sukai parking yara da manya kowa ya cika wajan , cikin gida kuwa har an kawo musu labari, da sauri kaka ta bawa ta shige daki tare da dakko wata farar Leda data cukurkude, bude ledar tayi tare da dakko tsinken turaran wuta, bayan ta kunna turaren wutarne ta koma ta dauko sabuwar tabarmarta ta shinfida a tsakar gidan , komai cikin sauri take yinsa .
A hankali ta fito daga cikin bayan wata tinted prado,bayan uban damin kudin data bawa security su rabawa mutane , ba kowa bace face hajiya kilishi, a hankali cikin takun manyan mutane ta nufi cikin gidan fuskarta dauke da murmushi, yayinda biyu daga cikin security din suka fara fito da kayan motar suna shigar dasu cikin gidan . Tun daga kan matasan gidan har manya kowa tsugunnawa yake yana gaisheta, cikin sakin fuska take amsawa kowa harta karasa zama akan tabarmar da aka shinfida mata batare da ‘kyan ‘kyanin komai ba. Sosai sukai hirar Yaushe gamo ta bawa kowa tsarabarsa , duk wannan abun da ake su tahee basu sai me ke faruwa ba , sai hayaniyar da suke ji tana tashi sama sama,anan ne suke mata gulmar dawowar oumma da Sanar da tahee, sosai hajiya kilishi ranta ya baci akan rashin sanar da ita da basuyi ba , da Auran da suke san yiwa tahee, ranta ba karamun baci yayi har suka fara dana sanin fada mata , bata nuna musu komai ba sai fadan da tayi musu da Nasiha me ratsa jiki , sun dade suna tattaunawa kafin ta mike ta nufi dakin su tahee, kwankwasa kofa tayi , TAHEE dake tsaye rike da tsintsiya ta bude kofar , cikin waro ido da tsananin farin ciki ta furta “AUNTY” itama aunty tata murmushi ne kwance a fuskarta, budewa tahee hannuwa tayi da sauri kuwa tahee ta nufe ta , ta rungumeta sosai tayi farin ciki da ganin auntyn Tata har hakan ya kasa boyuwa, kallanta hajiya kilishi tayi ganin yadda ta kara ramewa ga bakin da tayi, batace mata komai ba sai girgiza kai kawai da tayi bayan tahee ta bata hanyar wucewa, sallar da hajiya kilishi tayi ne yasa ko wannansu kallan kofa, take ko wannansu ya saki murmushi, TAHEER ne ya tashi daga inda yake ya bawa aunty ta su waje , bayan sun gaisa sun dade suna hira kafun hajiya kilishi tayi wa oumma jajan abin da ya faru , kallan tahee hajiya kilishi tayi kafin ta kira sunanta” taheera “ tagowa tahee tayi tana amsa mata “na’am aunty” cikin dan hade rai hajiya kilishi ta soma magana” naji labarin kince kinaso kiyi aure har ankawo kudin ki , hakane “, fashewa da kuka tahee tayi tana girgiza kanta ni bana san shi aunty”ganin yadda take kuka ne yasa aunty tausaya mata itama tayi mata hakan ne sabida ta san asalin gaskiyar “shikenan share hawayen to” kamar yadda ta satan kuwa share hawayen tayi” yanxu zan baki za’bi zaki bini ko zaki auri tanimu” saurin dago da idanuwan ta tayi da zubawa auntyn tata, murmushi hajiya kilishi tayi tana mikewa “ kuyi shawara toh “, ganin yadda ta mike din zata basu waje oumma ta dakatar da ita “itama yar kice ai wata shawara zatayi , duk yadda kikayi ai Daidai ne”,Murmushin farin ciki hajiya kilishi tayi “nagode sosai yaya, Allah ya bar zumunci, nan da munti 30 zamu tafi “ tana gama fadar hakan ta bar dakin.
Dan kallan oumma tahee tayi cikin damuwa tace “oumma kin yadda na tafi ya barku” yar harara oumma tayi mata kafun ta mike “ idan ba kyaso ki bita sai kitsaya ayi miki auren inyaso sai ki tare” tana gama fadar hakan ta shige dakin. Kallanta TAHEER yayi “ shawarar da oumma tayi miki shine alkairi a gareki dan mutanan nan bazasu kyaleki ba sai sun aura miki shegen mutumin can , me kama da biri “jinjina masa kai tayi cikin damuwar dake fuskar nan, ganin yadda ta damu yasashi fara janta da hira har ta sake. Suna zaune oumma tafi to tare da kallansu, sosai tayi wa tahee fada da nasiha akan ta rike mutuncin ta, ta zama me hakuri da kawaici a duk yadda ta sameta, sosai oumma tayi mata nasiha da nuna mata illar rashin yin azkar, har kuka tahee tayi ganin yadda oumma take Mata nasihan me ratsa jiki, ko wannansu dauriya yake, shima taheer ji yake kamar ya saki kuka amma ya dake tare da sakin murmushi, suna zaune a hakan hajiya kilishi ta dawo , kasan cewar tahee tayi wanka hijabinta kawai tasa tana sharar kwalla, TAHEER ya dauki jakar kayanta tare da fita dasu, oumma bata biyota rakiya ba gudun abinda ze je ya dawo . Cikin sanyin jiki tahee ta fito waje , tsatstsaye ta same mutanan yan gidan kowa sai faman harare Harare suke ba bakin magana , musamman Dije da har kwallar bakin ciki se datayi, bintalo ba sai faman zaginta take ganin ba a tafi da ita . Saida hajiya kilishi ta gama sallamarsu kafun ta kama hannun tahee ta shigar da ita mota, a haka motocin suka fara tafiya, tunda aka fara tafiya tahee tunani take , har aka karaso airport din bata sani ba sai da hajiya kilishi tayi mata magana , wata Hanya sukabi a cikin airport din da ya kaisu wani babban fili, wasu manyan jiragene awajan kusan guda uku, ko wanne da tanbarin AL_NAHYAN a jiki , daya daga cikin jiragen suka nufa jikin tahee sai faman rawa yake,Daidai bakin step din jirgin ta tsaya ta fara rarraba idanu, ruko hannunta hajiya kilishi tayi “karki damu ba abunda zai miki” saurin gyada mata kai tahee tayi zuciyarta sai faman bugawa take , ga hannun hajiya kilishi da ta rike gagam a haka suka shiga cikin jirgin, duk sauran bodyguard din Sara mata sukai tare da tsayawa a wajan jirgin….
Comment and share ✍️.
💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖
💖LITTAFAN SUNE KAMAR HAKA 💖
👇👇👇👇👇
💖DUK KARFIN IZZATA( star lady)💖
💖GIDAN AUNTY (mss Lee )💖
💖SARKI SAMEER (xeenat love )💖
💖YA FITA ZAKKA (maman sayyid)💖
💖JINI DAYA (mrs bbk)💖
Comment and share ✍️.
Mss Lee 💖
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA
💖💖GIDAN AUNTY💖💖
(A heart touching love story )
Story & written
By
Mss Lee 💖
💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖
PAID BOOK
MAISO AYI MISHI TALLAN KAYANSA YAMUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581
BOOK 1📕
Free page 11 🦋
Karfe 9:10 na dare jirginsu ya sauka a murtala muhammad international Airport (MMIA) dake Garin lagos, wasu dankara dan karan motocine sukazo daukarsu,da kyar tahee take daga kafarta jin yadda kanta ke sara mata, mintuna 35 ne suka kaisu AL_NAHYAN EATATE dake banana island ,tundaga kan Layin gidan kan tahee ke matukar sarawa ga wani irin tsananin bugu da zuciyarta kema ta,ko ina da yalwataccen haske kamar ba dare ba , ta ko ina sojojine ke Sara musu, sosai tahee ta rike hannun hijabinta gagam ganin irin sojojin dake gidan , sabida ydda zuciyarta ke bugawa sosai ta kulle idanuwanta , direct motocin part din hajiya kilishi suka nufa,sau biyu hajiya kilishi na kiran tahee amma bata masa ba , ana ukunne ta tabata sosai tahee ta ware idanuwanta, kallan ta hajiya kilishi tayi na yan sakanni kafun ta soma magana “ lapiyan ki kuwa “ gyada mata kai taheera tayi sai kuma ta bude bakinta” Kai na ne ke dan ciwo aunty “, cikin damuwa hajiya kilishi ta kamo hannunta ta futo da ita daga cikin motar”sannu kinji, nasan gajiya ce muje ciki kisha magani sai ki kwanta”nan ma gyada kanta tahee tayi batare da cewa komai ba,kafarta ta taka da soma tayifa sosai wani azababban zafi ke ratsa kafarta , kamar wacce ta dora kafarta a garwashi, ko wacce addua tazo bakinta yi take , nan da nan taji zafin ya tafi, haka suka karasa ciki tana bun hajiya kilishi a baya, dakin dake gefen star case ammi ta bude , “Bismillah tahee”, shiga ciki tahee tayi bakin dauke da Bismillah kamar ydda hajiya kilishi ta umarceta,”ga ban daki nan , zansa a kawo miki abinci da magani sai kishi ki kwanta”cewar hajiya kilishi,”na gode sosai aunty ,Allah ya saka da Alkairi”bata bari ta karasa ba ta katseta”Godiyar ta isa haka kisa mu ki huta”tana gama fadar haka ta bar dakin.itama toilet ta nufa tare da kama ruwa sannan tayo Alwala , tana fitowa ta tarar da jakar kayanta, hijab ta dauka tare da nufar inda dadduma take shinfide,sallolin da ake binta ta rama tana cikin addua ne aka kwankwasa kofar, Tashi tayi tare da budewa , wata budurwace ta shigo sanye da blue din Riga da dark blue din skeat ,”good day ma”cewar ta, murmushi kawai tahee tayi batare da ta amsa ba, abincin dake hannunta ta ajiye cikin center table din dake kusa da ita , cikin gurbatacciyar hausarta tace” madam tace na kawo miki abinci sannan kisha magani ki kwanta,”toh na gode”, jinjina mata kai budurwar tayi tare da furo mata kofa , abincin da aka kawo mata ta bude lafiyayyan abincine me rai da lapiya a ciki,sai kunun aya da aka sa mata cikin wani mini glass jug, daga gefen tray din wasu Kayan mar marine aciki, kadan ta tsakuri abincin “da oumma da taheer sunanan tare za muci abincin , nasan yanxu Suna can su kadai”, cewar tahee harta kammala cin abincin, kuskure bakinta tayi tare da watsa ruwa , sannan ta hau kan lapiyayyan gadon dakin ,lilliba tayi jin sanyi na ratsata ta ko ina , bata dade da kwanciya ba bacci ya dauke ta .
➰➰➰➰
A gajiye ya dawo gidan bayan zaki ya ajjesa, ko part din ammi be Jeba, Wanka kawai yayi tare da nufar down stairs , Kai tsaye kitchen din dake falon ya nufa, banban kitchen ne da ya gaji da haduwa komai na anfanin kitchen akwai shi a ciki,kitchen din sai faman daukan kyalli yake, coffee ya hada cikin coffee maker din kitchen din, kan daya daga cikin kujerun dining din kitchen din ya zauna, a hankali yake sipping coffee din dake hannunsa,bayan ya shanyene ya kara hada wani tare da barin kitchen din, stair case ya dau tare da nufar kofar hagunsa, taku kadan ya kai shi wasu kofofi guda uku, kofar tsakiya ya shiga , ya dau dogon lokaci a ciki kafun ya fito, stair case din da zai kaishi second floor ya hau, a hankali yake taka stairs din har ya karasa hawa saman, kan daya daga cikin kujerun falon ya zauna tare da fara operating din system dinsa, ya dade yana anfani da ita kafun ya kashe ta gaba daya , toilet ya nufa be dade ba ya fito tare da nufar faffadan gadonshi, remotes din fitulun part din ya kashe kafun ya kwanta cikin lallausan gadonsa, be dade da kwanciya ba bacci ya daukesa.
Wutace sosai take ci, da anzuba mata ruwa Sai ta kara tashi kamar wacce ake hurata , ga hayaki da ya gauraye ko ina, daga cikin wutar kuwa hannu ake miko masa cikin azaba “Akhee habeeby!!Akhee habeeby!!”hannunsa ya Mika da niyar ya kamo Wanda yake cikin wutar… farkawa king yayi sai faman hada gumi yake bayan sanyin Acn da ya cika dakin, adduoi ya fara karantawa a hankali wata nutsuwa tazo masa ,wayarsa dake side din gadan sa ya kunna,4:30shine abunda agogon ya nuna masa, mikewa yayi tare da nufar toilet, wanka ya fara yi kafun yayo Alwala, ya dade yana nafila kafun ai kirin sallah, direct kasa ya nufa bayan ya idar da sallahn , sanye yake cikin white jallabiya , sosai farar jallabiyar tayiwa surar jikinsa kyau,gashin kansa sanye yke cikin bakin rawanin larabawa, sosai kyawun fuskarsa ya fito, musamman idanuwansa da suka kara haske sai kyalli suke duk da kasancewar fuskarsa a hade yake,a hanyar zuwa Masallaci suka hadu da abeey shima zasu tafi masallacin,a haka motocin su suk fita , a dawo wa ma tare suka dawo gidan,Kai tsaye part din dada suka nufa dukansu, ganin babu kowa a falon yasa su samun waje ko wannan su ya zauna. Mintuna kadan sai gashi ta fita sanye da hijabi a jikinta , ko wannansu gaishe da ita yayi , yayinda take amsawa fuskarta washe da fara’a, kankance ido king yayi” dada yau naga sai fara a kike ko an miki albishir da zuwa umarace”a hankali yayi maganar amma duk da haka sai da ta jisa, hararar sa dada tayi”A’ah gorin daurin aurenka aka kawomun”kara hade fuska king yayi tare da dauke idanuwansa daga kanta,tabule baki dada tayi “Kai dai Kasani mutum kullum cikin daure fuska ,kamar audiga ina dalili”, be tanka mata ba sai ma lumshe ida nuwansa da yayi, abeey kam murmushi kawai yayi, hira suka dada ta fara tare da su uncle musaddiq , abeey na sa musu baki lokaci zuwa lokaci na yana kallan king, ganin hirar tasu bame karewa bace yayi musu sallama tare da nufar part dinsa. Gym room dinsa ya nufa , tare da sa kayn motsa jiki , ya dade yana motsa jiki kafun ya futo duk ya hada zufa ,kwantaccen gashin kansa ya zubo masa har wajan idanuwansa,Wanka yayi tare da shirya cikin wani hadadden suit red colour, daddadan kamshin turaransa ya cika ko ina , gashin kansa ya sha gyada yayin da gefe guda na fuskar sa gashin ya futo harwajan idanuwansa,pink lips dinsa ya turo sosai , yayinda fuskarsa take a daure,sosai yayi kyau cikin shigarsa , sai ta kara futo da ainahin kalarsa ta larabawa,cikin takun sa ya bar part din , direct part din ummey ya