Showing 3001 words to 6000 words out of 30200 words

Chapter 2 - Dubai Part 2

Unknown   

04 Sep 2025

2179

lkcn Mom ta sace jikinta tabar asibitin ta wucce gidan yayarta tana kuka take zayyane mata komai har auren Saudat yar qanin Dad Sahabi data nema masa tasa Saudat ta dawo daga England kawai saboda ta hadata da Taheer amma abin yana neman gagara.



Yanda take kuka yasa Hajiya Ummah yayarta dariya tace “kece uwa kece kike da wuqa kike da nama fah yanzu dai shawara daya itace tunda ya kafe saiya auri yarinyar nan ki qyaleshi ya aureta din kodan rufuwar asirinku game da wannan yar kafin fatiha din ayi auren cikin sirri ta tare ta yanda babu Wanda zaisan ba aure aka haifeta"
Girgiza kai tayi tace “aikin gama ya riga ya gama Ummah sirrin dan siyasa baya buya ni kaina baa gurin Taheer naji haihuwar ba kirana akayi da baquwar number aka fadamin karuwar dana ta haihu a asibiti kaza har lambar dakin aka turomin"




Shiru sukayi na wani dogon lkc sannan Ummah ta magantu da cewa “shawara ta biyu kije ki hada baki da likitan ayiwa jaririyar allurar guba ta mutu kowa ya huta..." Da sauri Mom ta kalli Ummah tace “kuma nayi kisa Ummah aa bazan iya ba nikam inajin tsoro na lura daga Granny har Dad hankalinsu yana kan wannan jaririyar"
Murmushin takaici Ummah tayi tace “shikenan kije zanyi tunanin mafita kafin a sallamesu daga asibiti cikin wata biyun da kukasa na bikinsa da Saudat dole ne a mantar dashi tunanin wannan karuwar yarinyar idan ba hakaba tabbas da matsala don zama ku iya daura masa auren ya saki matar" miqewa Mom tayi tace “dakuwa na tsine masa ya qarasa lalacewa"





Da haka ta fice a gdan driventa yajata suka fice suka nufi government house suna tsayawa ta fito ta shiga gdan bangaren yammatan nata ta shiga ta tarar dasu sun rufu akan Saudat sunata rarrashinta itakuma sai kuka takeyi, salati Mom tayi ta shiga cikin dakin tana tambayarsu menene.
Kuka bai bari Saudat tayi bayani ba sai shassheqa da takeyi Bushirah tabe baki tayi ta shige bathroom Kubrah ta dago tace “Yaya Taheer ne ya dawo ya shiga dakinsa yana neman wani abu kawai ita kuma sai tabisa dakin munyi qoqarin hanata taqi hanuwa, bamusan me tace masa ba kawai sai gani mukayi ya fito da ita a hannunsa ya jefar da ita a parlour yana jibgarta kamar Allah ya aikosa yana gama dukanta ya fice ya hau motarsa yabar gdan itakuma munyi munyi da ita ta fada mana me tace masa taqi"



Zama Mom tayi zuciyarta na tafasa tace “ke me kikace masa da yaja miki wannan dukan sa'ar haka?" Cikin shassheqar kuka tace “wai...wai don na shiga ya fito daga wanka shine na matsi mai zan shafa masa ya juyo ya dakamin tsawa wai na fice masa daga part shi...shine nace karuwa ma ta samu lkcnsa balleni da zanzama matar sunnah shine ya juyo yacemin wai karna qara cewa da uwar yarsa karuwa domin tabashi abinda a duniya babu wanda ya amince ya bashi sai itadin kuma Koda zaa bashi to bayan wadda tabashi zasu biyo, nikuma sai nace ai ko a shari'a shege bashida gado saboda haka matsayin dan halak yana sama qololuwa dana dan zina, wlh Mom ban qaraba ban rageba kawai naji ya shaqeni ya hadani da bango ya gwaramin kaina da gini ni bansan ya akayi ba kawai saiji nayi ya zubar dani a parlour yasa belt ya rinqa dukana kamar jaka daqyar su Solomon suka qwaceni...."



Ta qarashe mgnr cikin gunjin kuka ta zame bayanta Mom tayi saurin rintse idonta saboda yanda ya farfasa Mata jiki da belt tace “yanzu Mom haka zan rayu da Yaya Taheer babu tausayi babu soyayya ace karuwa ma tafika matsayi a gurin mijinka, gsky Mom da sake duk da inason Taheer Allah ya jarrabi zuciyata da qaunarsa tun bangansa a zahiri ba Mom zan iya jure kowanne wulaqanci a gurinsa indai zai rayu dani matsayin matarsa saboda nasan yanda ciwon so yake nasan abinda yakeji Mom amma bazan dauki duka akan karuwa ba Mom waini meye Habeeytan nan da yake yawan ambata take dashi dani bani dashi? Meye tafini don Allah ki fadamin meye aibina da Yaya Taheer yaqi naam da soyayyata duk da kasancewata yar uwarsa ta jini wacce na yarda da naqasunsa da komai na aminta zan rayu dashi a haka"




Shafa kanta Mom tayi ta share mata hawayenta tace “na rasa meye yasa Taheer ya zama me taurin kai akan yarinyar nan wlh a baya duk abinda na nuna masa bana raayinsa duk son da yakewa abinnan ya hqr dashi amma nakasa juya zuciyarsa akan yarinyar nan wai harni Taheer yake kallo yacemin indai ban janye auresa dake ba nabarsa ya auri Habeey ba to shakka babu zakiyi nadamar zuwanki duniya kuma zina yanzu yafara saboda zuciyar Habeey a hannunsa take duk yanda yayi da ita haka takebi, Saudat zanji tsananin kunyar Sahabi da Zahrah qanwata idan har nakasa tanqwara zuciyar Taheer ya aureki bari kiji wani Abu" kunnenta ta kama ta rada Mata wata mgn sukayi dariya tare da rungumeta tace “shiyasa nake sonki Mom har mafarkin first night dina a gidan Yaya Taheer nakeyi yauma saida nayi mafarki ganinan a kwance a qirjinsa yanata shafa sumata"




Rufe mata baki tayi tana dariya tace “saudat bakida dama wai yaushe Abbanki zaizo 9ja ne?" Lumshe idonta tayi tace “yacemin tunda ya rasa “Matarsa ta fari Hajar lkcn da cikinsa watanni uku a jikinta ya fara wannan ciwon zuciyar yakejin idan an ambaci 9ja gabansa na faduwa yacemin kullum mafarkinsa shine yazo 9ja amma gani yake kamar idan ya dawo abinda ya faru shekaru ashirin da daya baya shine zai qara faruwa"
Girgiza kai Mom tayi tace “har yanzu Sahabi yana mafarkin ganin wannan Dan nasa ko yarsa don ko jiya da mukayi waya da Mamanki take cemin wai yanzu firgita yakeyi yana yawan Kiran sunan Hajar yana ambaton Ina dansa ko yarsa? Kuma fah bayan rabuwarsu ance nemanta akayi aka rasa wasu ma suna cewa ta mutu"
Share hawayen tausayin abbanta Saudat tayi tace “nima kullum Ina addu'ar indai dan uwana ko yar uwata tana raye tazo gareni ko yazo gareni Mom kadaici ya isheni Mom banida abokin kuka banida na dariya banida shaqiqin da zanyi hira dashi naji dadi nasan yanzu da dan'uwana ko yar'uwata tana kusa gareni da zata rinqa tausata da tayani addu'a akan wannan mugun son da nake yiwa Yaya Taheer shikuma baya sona dama tun Ina qarama Yaya Taheer ya tsaneni" ta qarashe maganar cikin kuka me narkar da zuciya.



_Gareku masoya garabasa gareku saboda murnar bikin babbar sallah daga yau 3/8/2020 zuwa_ _10/8/2020 na rage kudin da ake biya domin samun wannan_ _rikitaccen labari me cike da turka turka single Zaki biya 150 VIP 400 idan ta account ne._
_Account 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB, saiki tura evidence_ _of payment ta wannan number 09013718241_
_Idan katine kuma Zaki biya 200 VIP 400 ta wannan number_ _09013718241 kada ki manta lambobin katin ake buqata ko hotonsa._
# *UMMUH HAIRAN*
[8/9, 4:07 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *HABEEYTAH*
*_DUBAI PART 2_*


*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
*UMMUH HAIRAN*


_Qarshen free page na Happy sallah_


_Please ki biya kafin ki karanta nidai bazanyi Allah ya isaba Amma ban yafeba, da masu fitarmin da masu karantawa basu biya ba kuda Allah_



*5*



Shafa kanta tayi tana tausarta saboda tasani iyayenta basason bacin ranta shiyasa take lallabata saboda a gudun abinda kaje yazo amma taci alwashin duk yanda Taheer zaiyi saidai ya mutu aure tsakaninsa da Saudat babu fashi.
Yini sukayi tanata rarrashinta hardai ta samu ta ware Bushirah da Kubrah suka fito cikin shigarsu ta alfarma suka tarar dasu a parlour Mom ta dubesu tace “Ina zakuje?" Cikin yauqi Kubrah tace “zamuje mugano yarmu ne kada Yaya yasamu a blacklist" wata uwar harara ta watsa musu tare da jan tsaki ita kuwa Saudat mutuwar zaune tayi saboda mamaki wai zasuje su gano yarsu yar zinar?




Bushirah ce ta dubi Saudat tace “dama kin tashi munje kya ragewa kanki damuwar son maso wani ko banza kyaganshi acan gurin gudaliyar yarsa da matarsa da yakejin amutu ko a rayu a kanta"
Wasu hawaye ne suka zubo mata ta miqe ta shige daki ta fada gado ta rushe da kuka ta fahimci a gidan daga Mom sai Dad sune suke sonta yaran gidan gabadaya yan partyn abinda Taheer keso ne hatta da Mahfuz da baya qasar da aka kirashi aka fada masa cewa yayi kema dai Mom shirme kikeyi kinsan dai blood bazai taba yi miki biyayya ba indai akan baben nan ne wlh Mom ni kaina don dai blood ya rigani afkawa ne badon hakaba da tafi haka zaayi, Mom ki share kawai irin wannan auren fah dadine dashi tasanshi yasanta awonsu daidai ne Zaki wani zo ki hadashi da wata qyailar yarinya...."




Kalaman na dawowa Saudat tanajin bugun zuciyarta na qaruwa ta miqe zumbur ta fita ta tarar dasu suna shirin tashin mota ta qarasa da sauri ta bude ta shiga suka kalleta sukayi dariya Kubrah tace “iska tana wahalar dame kayan kara nifa banga abinda zaisa na rinqa bata lkc na akan namijin da baya sona ba musamman Yaya Taheer me masifar tsaurin raayi kinaji fah a gabanki Jabir yake fadawa Mom ita kanta Habeeytah bata tsira daga wulaqancinsa ba idan ya tashi itama da yake iqirarin yanaso kenan balle ke yar karere"
Itadai Shiru tayi batace qala ba har suka dauki hanya suka fara tafiya sunata hirar samarinsu Saudat dai bata cewa komai sai tsiyayyar hawaye.




Sai magrib suka isa suna zuwa sukayi parking suka fito daidai lkcn yana fitowa da waya a kare a kunnensa yana cewa “wlh blood bakaga babyn ba kamar kai itama da Mom take kama nayi Mata huduba da Safeenatul Najah....."
Katse maganar yayi lkcn da sukayi karo da Saudat yayi baya da sauri tare da tsartar da yawu yace “ke wacce irin banza ce bakya ganine" cikin rawar jiki tace “ban...ban kula ba Yaya Taheer kayi hqr" tsaki yayi ya matsa gurin yan uwansa suka rungume juna dama gaisuwarsu kenan yace “ashe zakuzo na dauka Mom bazata barku ba" dariya Bushirah tayi tace “ai dole abu namu maganin a kwabemu"




Dariya sukayi dukkansu banda Saudat data zubawa sarautar Allah ido ya kama hannunsu suka shiga dakin Granny tana sallah itakuwa Habeey tana kwance kamar gawa saboda shaqar da Mom tayi Mata ta mayar da ciwonta farko, ya saki hannunsu ya matsa ya sanya hannunsa ya tattare Mata gashinta daya rufe Mata fuskarta yayi kissing lips dinta yace “a kowanne hali kyaune dake Habeeytah"
Gyaran muryar Granny yasashi saurin janyewa kunya kamar ya nutse ya juyo tare da sosa kansa ta sakar masa ranqwashi tace “kaikam kwai fitinannen namiji a jinyacen ma bazaka qyale yar mutane ba anya kuwa Taheer ba Mata hudu zan aura maka ba?"




Murmushi yayi yace “bazasu mayemin gurbin Habeeytah ba ita kadai gayyace Granny a duk matan duniya babu wacce zata iya dani sama da Habeeytah" wani mashine ya caki zuciyar Saudat tayi saurin juyawa zata fita Kubrah ta riqo hannunta tace “bakiga yar taki ba don nasan a hannunki qila zata rayu" sake hadiye wata kibiyar baqin ciki tayi ta caki qahon zuciyarta ta nemi guri dabar ta zauna.
Shikam yama manta da an halicceta a gurin surutu kawai yakeyi yana fasaltawa Granny irin son da yakeyiwa Habbatullah tare da zubawa Safnah ido yana murmushi yace “wlh Granny ji nakeyi kamar na hadiye my daughter saboda nakasa fasalta irin son da nakeyi mata nifa yanzu ko ke kikace bakison yata Allah idan muka rabu har abada bare wani banza da rayuwata batayi kama da tasaba dan karere"




Sarai duk wanda yake gurin ya fahimci da wadda yake amma shi har cikin ransa bada itan yakeba, Bushirah ce ta karbi Safnah ta zuba Mata ido tace “wow! Yaya wannan babyn kamar jinin larabawa Masha Allah amma Yaya kamar ba bakwaini ba"
Granny ce “nima da aka haifeta nace ba bakwaini bace saida likitan ya aunata yace kawai dai me girmance amma watanta bakwai da kwana daya a cikin mahaifa yanzu ma ance a daina jagwalgwalata amma wannan dan rawar kan yaqi barinta ta huta" murmushi yayi yace “aini dama komai zanyi ban iyaba indai a gurinki ne tsohuwa dake"
A kasalance Saudat ta taso ta leqa fuskar yarinyar ta zuba mata ido tanajin faduwar gabanta na tsananta a ranta tana raya dama itace ta haifa masa ita qila da soyayyar yarinyar zatasa yasota itama.




Miqo hannu tayi zata karbeta yayi saurin dauke abarsa yaje ya kwantar da ita a kusa da uwarta sai yanzu Saudat ta samu damar kallon Have dake kwance matsayin gawa tayi saurin matsawa gabanta tana furta “lahaula wala quwwata illah billahil aliyul'azeem" hannunta takai zata taba fuskar Habeey yayi saurin riqe hannunta cikin tsawa yace.
“Idan kika kuskura kika tabamin mata wani abu ya sameta wlh sai nayi shari'a dake gabadayanki na tsaneki Saudat...."
Rufe masa baki tayi jikinta na rawa tace “nikuma inasonka a haka Yaya kuma saina aureka Koda kuwa zaka kasheni don qiyayya, Taheer ba takai nakeyi ba yanzu na gama dakai domin ko kanaso ko bakaso saika aureni dole"..........


_Gareku masoya garabasa gareku saboda murnar bikin babbar sallah daga yau 3/8/2020 zuwa_ _10/8/2020 na rage kudin da ake biya domin samun wannan_ _rikitaccen labari me cike da turka turka single Zaki biya 150 VIP 400 idan ta account ne._
_Account 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB, saiki tura evidence_ _of payment ta wannan number 09013718241_
_Idan katine kuma Zaki biya 200 VIP 400 ta wannan number_ _09013718241 kada ki manta lambobin katin ake buqata ko hotonsa._
# *UMMUH HAIRAN*
[8/9, 4:07 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *HABEEYTAH*
*_DUBAI PART 2_*


*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
*UMMUH HAIRAN*


*6*



Tsayawa tayi sake da baki yana kallon ikon lillahi wai saita aurets dole ko a Ina aka taba yiwa namiji auren dole? Murmushin tausayinta yayi shi gabadaya ya gama raina hankalinta hakanan yakejin amai yana taso masa idan ya kalleta.
Juyawa yayi ya fice daidai lkcn wayarsa tayi qara ya daga da sauri tare da kasheta ya mayar aljihunsa kusan ko yaushe a tsakanin jiya da yau sai an kirashi da number qanin na habeey Ibrahim shikuma haushin abinda Addah tayiwa Habeey akan cikinsa yasa yaji ya tsani duk wani wanda ya rabeta basu da adalci dangin Habeey ko kadan basusan darajar dan Adam ba, basu da damu da itaba itace ta damu dasu take sadaukar da komai domin danginta.




Da wannan tunanin ya shiga mota yana Shirin tashinta qannen nasa suka fito Bushirah ta matso gabansa tace “sati biyar akasa aurenka da Saudat Yaya a halin da aka ciki Habeey da Safnah sunfi kowa buqatarka don Allah kada kayi sakacin da baiwarka Allan nan zata qara shigs gararin rayuwa Yaya Taheer jin Habeey nakeyi kamar yar uwata ta jini"
Riqe hannunta yayi yace “karki damu qanwata babu Wanda ya isa yayimin auren dole auren ma da wannan tsakuwar yarinyar haba suma su Dad wasa sukeyi wlh Idan suka suka matsa zan iya farke shegiya ta mutu kowa ya huta"




Yana gama fadin haka ya figi motar a guje ya nufi gidan Granny ya shiga bangarensa na gidan yayi wanka ya kwanta ya fara aikin sanar da abokansa cewa anyi masa haihuwa mamaki sukeyi sosai yaushe yayi aure da har matarsa ta haihu.
Shikam ko a jikinsa gani yakeyi ai shima aiki yayi ya samu abarsa sabida haka ya cancanci a tayasa murna, daya gama buge bugen wayar tasa sai ya budo hoton sahibar tasa da yar tasa ya rinqa kallo yana murmushi har bacci ya daukesa.
Cikin sati biyun da habeey tayi a asibiti abubuwa da dama sun faru ciki harda qarfafuwar mgnr auren Taheer da Saudat tabbas Saudat tana cikin matsananciyar damuwa saboda Wanda takeyi dominsa din baisan tanayi ba tana kallon yanda Khamal da Sudess samarin su Kubrah suketa rawar qafar bikin amma banda nata angon dako kallon tsiya bata samu a gurinsa balle na arziqi.




Da taimakon Hajiya Ummah yayar Mom da Zahrah mahaifiyar Saudat aka shiga aka fita aka cusawa Taheer jin tsanar Habeey a ransa sunyi duk me yuwuwa su cusa masa qiyayyar Safnansa amma abin ya faskara saima kamar qara masa qaunar yarinyar da akeyi.
Cikin sati biyun jikinta ya fara kyau sosai ta fara sanin waye yake a kanta, farkon fari kullum a asibitin yake yini amma yanzu sai ya yini sur baizoba saidai ya kira a waya yaji ya babensa, wannan canji ya tashi hankalin Granny da Bushirah dake jinyar Habeey da farko sun dauka mgnr auren nasa ce tasashi a busy amma sai Bushirah ta lura shima auren ba wani murna yakeyi dashi ba kullum ka nemeshi zaka sameshi a garden ya hade kai da gwiwa yanata karatun wasiqar jaki"




Yau ta kama asabarce wadda tayi daidai da satin Habbatullah hudu a asibiti misalin qarfe biyu na rana ta fara motsa qafafunta tare dayin attishawa daga Kubrah har Bushirah da Granny dama Addah da ciwon yar tata yasata saukowa shima Bushirah ce tayi tattaki taje ta sanar da ita.
Dukkansu kanta sukayo ta muqar da hannunta tare da amsa kalmar shahadar da Addah take laqaba mata ta riqe qam tanayi tana girgiza kanta, fita Bushirah tayi da gudu ta fadawa likitan abinda yake faruwa daidai lkcn da likitan ya iso daidai lkcn Taheer suka shigo shida Saudat a zahirin gaskiya shi kansa baisan Saudat ta biyosa ba saboda kaca² suka rabu dutsi a hannun riga amma sai gashi sun shigo tare kafadarsu na gugan juna.




A lkcn ne Habbatullah ta fara bude idonta a hankali tana kallon kowa dake dakin da fuskar rashin sani har takai ga sauke idonta akan Addah ta zabura zara miqe likitan yayi saurin riqeta tare da cewa.
“Kibi a hankali Hajiya zaki tashi insha Allahu" a sanyaye da murya ta alamun jin jiki tace “Ad...Addah ashe zakizo gurina ashe har yanzu kina sona Addah ina qannena Aysha da Fatima ina Taheer Addah ki kiramin shi don Allah" juyawa Kubrah da Bushirah dama kowa dake gurin sukayi inda yake tsaye yana danna wayarsa.
Wani mugun kallo Addah takeyi masa a cikin kwana ukun da tayi a asibitin yaune ta fara ganinsa taja ajiyar zuciya hakanan takejin tsanar Taheer a ranta kuma ta qudurce a ranta indai yarta zataji mgnrta to zata rabata dashi rabuwa ta har abada.



Matsawa Bushirah tayi kusa dashi ta warcr wayar hannunsa tace “haba Yaya kanaji sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login