Showing 6001 words to 9000 words out of 30200 words

Chapter 3 - Dubai Part 2

Unknown   

04 Sep 2025

2180

kiranka Habbatullah takeyi Amma ka wani basar...." Bata rufe bakinta ba ya sauke Mata wani gigitaccen mari ya sakeyin bal da ita yace.
“Wata banza dake Zaki qwacemin wayata saime to dan wannan banzar ballagazar ta kirani dama jira nakeyi ta warke Kuma alhmdllh ta warke banida haqqinta zata iya komawa inda ta fito Amma karki sake ki daukarmin yata inason abata Saudat zata riqemin ita, yawwa ladan haihuwar kyakkyawar baben nan da kikayimin na mallaka miki gidana dake layin gdan sarkin Bauchi ki duba wayarki nayi miki transfer ta million hamsin nasan ta isheki ki qarashe rayuwarki na bakisu a matsayin fansar budurcinki"




Yana fadin haka ya ajiye Mata want a saman cinyarta ya juya zai fita ta bude bakinta jikinta na rawa tace “na roqeka da girma da matsayin ubangijin daya sanya tausayi da jinqai tsakanin bayinsa kada ka juyamin baya Taheer karka manta kayimin alqawarin duk tsanani bazaka gujeni ba bazaka juyamin bayaba wlh na amince zan aureka Taheer kada ka wofintar dani lkcn da nake tsananin buqatar jin qanka...."
Ta qarasa mgnr cikin sarqewar numfashi baiko qarasa jin abinda zata fadaba ya fice kamar iska yaja motarsa a guje yabar harabar asibitin ta kuwa zabura ta miqe zata bisa Dr Shattima yayi saurin riqeta ya hadata da jikinsa yace “tabbas kina cikin jarabawar ubangiji kamar yanda nake cikinta Habbatullah banyi tunanin wannan lkcn zaizo ba kiyi hqr zuciyarki a kumbure take idan kika mutu bashida asara saboda saura kwanaki biyar ya angwance da sabuwar amaryarsa...........



_Gareku masoya garabasa gareku saboda murnar bikin babbar sallah daga yau 3/8/2020 zuwa_ _10/8/2020 na rage kudin da ake biya domin samun wannan_ _rikitaccen labari me cike da turka turka single Zaki biya 150 VIP 400 idan ta account ne._
_Account 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB, saiki tura evidence_ _of payment ta wannan number 09013718241_
_Idan katine kuma Zaki biya 200 VIP 400 ta wannan number_ _09013718241 kada ki manta lambobin katin ake buqata ko hotonsa._
# *UMMUH HAIRAN*
[8/9, 4:07 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *HABEEYTAH*
*_DUBAI PART 2_*

*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
    *UMMUH HAIRAN*

*7*


Zamewa tayi daga jikinsa ta zube a qasa numfashinta yana sarqewa ta dafe qirjinta jikinta yana rawa Dr Shattima ya matso da sauri ya kamata ya dorata a gadon ya zaro wata allura ya danna nata nandanan jikinta yayi laushi ta suma Granny ta juya ta kalli Saudat data zubawa Habeey ido cike da tsananin tausayawa hawayenta na zuba a qasa tace.
“Meye kuma abin kukan Saudatu kunyi nasara tabbas kuyin nasara Allah ya baku saa kun raba tsakanin Taheer da Habeey, Saudatu badai Taheer kikeso ba gakinan gashi daukar yarinyar dake bacci tayi ta miqa Mata tace “ga yar mijinki nan ki dauka ki riqe kwafi samun nutsuwa amma kafin wannan lkcn inaso kisan wani abu qwaya daya ita duniya juyawa takeyi saboda haka kada kiyi tunanin dawwama cikin farin ciki kin rabashi da farin cikinsa kin yankewa Habiba nata farin cikin shakka babu lkc na zuwa da zakiyi naki kukan babu hawaye"



Kubrah ce ta dubeta tayi “murmushi tace “haqqin rai biyu ne akanku Saudat koma nace uku saboda ke yaya yaci mutuncin Habiba saboda ke ya rabata da yarta saboda ke komai zai iya faruwa dashi kansa yayan, Abu daya nima da zan fada miki shine quncinki sai yafi wanda kika sanya zuqatan masoya sannan babu ubanda ya isa ya raba Safnah da mahaifiyarta harsai idan sune sukace bazasu riqe ba"
Addah ce ta girgiza kai tace ku bashi yarsa kawai bsmu buqata Allah ya rayata a duk inda take wannan qaddarorin na Habbatullah sinyi yawa Allah ka sassautawa baiwarka haka" hawayen saudat ne ya qara tsinkewa tace “wlh tallahi bansan meyene ya kawo wannan sauyin ba Granny yanzu kafin mu taho har zagina Yaya Taheer yayi akan Habeeytah ya rantsemin ya qara kan cewa koya aureni saiya sakeni ni zuwa nayi idan ta farka na roqeta ta nemamin alfarmar ya hadamu ya auremu"



Murmushin takaici Granny tayi ta juya zauna daidai lkcn da Dr shattima ya sake shigowa yace “nan da 30 minutes zata iya farfadowa don Allah a kawar mata da duk wani Abu dazai sanyata damuwa" jinjina kai sukayi ya sake fita, haka kuwa akayi 35 minutes da fitarsa ta farka a firgice tana Kiran Taheer kada kayimin haka don Allah wlh nafi kowa sonka kada ka rabani da yata ita kadai na mallaka duk duniyar nan kada ka sanyama yata maraicin uwa a halin uwarta tana raye kada ka qara tabbatarwa da zuciyata namiji tuwon rezar ne miyar Allura ashe wannan ranar zatazo Taheer Kaine da kanka kayimin gori?"
Kuka takeyi Addah na riqeta tace “da nasan wannan ranar zatazo Dana roqi Allah ya kasheni kafin lkcn, wayyoh Allah qirjina Allah ni yaushe zanyi farib cikine kamar kowa...."



Ta qarashe mgnr tans kakarin amai kamar zata amayar da kayan cikinta amma aman yana qara tsanani sai jini, wani ihu Addah tayi ta qanqame yar tata Saudat ta nufota da gudu itama ta riqeta tana kuka tace “nashiga ukuna Taheer kada kayi kisa don Allah ka dawo ka janye kalamanka Taheer asheni ba sonka nakeyi ba ga wacce take sonka..."
Daqyar cikin taimakon Allah Dr Shattima da Dr Zainab suka samu aman ya tsaya suka daura mata na'urar shaqar iska saboda Athmer dinta data tashi tanata gwama numfashi Dr Shattima cikin tashin hankali yaketa fadan ya akayi aka bari ta tuna abinda ya faru?



Wannan rana sunga ikon Allah dukkansu anan suka kwana akanta Kiran duniya Bushirah tayiwa wayar Taheer amma a kashe saita Dad ya Kira ta fada masa abinda yake faruwa shima ya shiga rudu saboda zuwa yanzu tausayin Habeey ya gama ratsa jikinsa yace su jirashi gashinan zuwa.
Haka kuws akayi jiransa sukayi bai dadeba ya iso.
Granny ce tayi masa bayanin komai ya zauna yana salati tare da tunanin mafita a fili yace “aikuwa saidai ya hada biyun ya aura wannan ma zalumcine ya gama lalata mata rayuwa sannan yace bazai aureta ba" da sauri Addah tace “aa kada ayi haka Alh tunda yace bayaso ku qyaleshi matar mutum kabarinsa qila dama ba matarsa bace" duk yanda Dad yaso yabawa Addah hqr ta tubure qarahema tace itafa indai ta isa da Habeey bazata auri Taheer ba.




Jikin kowa yayi sanyi Dad ya dauki takarda da biro yayi rubutu ya miqawa Addah yace “ku riqe wannan don Allah kafin a daidaita komai ina ganin Taheer ba a cikin hayyacinsa yake ba" girgiza kai tayi tace “bama buqatar komai daga gareku ranka ya dade iya hakama min gde Allah ya qara daukaka"
Daqyar ya roqeta ta karba check din kudin sannan ya debe yayansa suka tafi amma banda Bushirah da takejin ciwon abinda ya faru kamar ita akayiwa, sai dare Habeey ta farka ta bude idonta tana kallon silling din maganganun Taheer sunayi mata yawo a kwanya “ballagaza banza me zanyi da ita karuwar yarinyar nan..."




Wata qara ta saki Dr Shattima daya kasa ya tsare ya miqe da sauri ya isa gurinta ya fara dubata ya cire mata abin taimakawa numfashin da aka maqala mata ya zare mata allurar drip din yana Mata murmushi ita kuma sai kallonsa takeyi hawaye na zuba a idonta.
Zama yayi a gefenta yace “idan baki manta da komai kin fawwalawa Allah ba Zaki kashe kanki Habbatullah akwai darasi me yawa a cikin rayuwarki kuma ita qaddara bata shawara lkcn da zata fadowa mutum wlh a iyakar kwanakinki a asibitin nan bantaba sanin Taheer ba mijinki bane sai kwanaki uku da mahaifiyarki tazo, shima waya naji tanayi tana kuka tana fadawa wata halin da kike ciki"




Shassheqar kuka takeyi ta yunqura zata miqe yayi saurin kamota ya tallafa mata ta zauna yace “kiyi hqr muyi addu'a Allah yayiwa kowa zabi na alkhairi amma ni dama nayi tunanin faruwar hakan ba yanzu bako a gaba"
Itadai batace komai ba har ya zauna ya zuba mata ido zuciyarta suya takeyi sosai qaddarorinta sun fara bijirewa kwayarta a firgice ta dago tace “ina yata?" Dago idanunsa yayi da suka kada sukayi jah tunda yake aiki baitabajin tausayin wata mace kamar yanda yake tausayin Habbatullah ba yace “babanta ya dawo ya dauketa kiyi Mata addu'a duk inda take zata isheta" miqewa yayi da sauri ya fice saboda zuciyarsa ta gama karyewa.




A cikin kwanaki biyun da suka qara sosai Addah da Granny ke qarfafa mata gwiwa tare da kafa Mata misalai da hujjoji da zasu sanya ta manta da Taheer a rayuwarta saboda juyin duniya Dad yayi dashi akan ya koma kodan safnah su daidaita da Habbatullah suyi aure Amma fir yaqi yace shifa baisan meye yasa masa tsanarta ba ko sunanta aka Kira gabansa faduwa yakeyi.
Ganin yanda ran Dad ya baci ne yasashi fadawa jikinsa ya fashe da kuka yana cewa “wlh Dad qasan zuciyata danqare take da qaunar Habeeytah amma jikina da ruhina tsanarta suke qarayi Dad bansan meye ya canzamin qaunar Habeeytah da tausayinta zuwa qiyayyarta ba, alfarma days zakayimin Dad kada ka daura aurena da Saudat wlh idan ka daura mutuwa zanyi kabarni na rayu da yata ta isheni rayuwa nayi maka alqawarin kare kaina nayi maka alqawarin zan rinqayin azumin litinin da alhamis"




Lamarin ya fara girmamewa tunanin Dad duk yanda yake tunanin Taheer ya wucce nan kamashi yayi ya dagashi zuwa yanzu ya daina ganin baqin dannasa tausayinsa yakeji a sanyaye yace “bazan taba takura maka ka auri abinda ranka bayaso ba amma zamanka haka risk ne kayi hqr ka auri yar uwarka Saudat nasan zakaji dadin hakan a gaba Taheer inajin kunyar na kira sahabi na fada masa na fasa aurawa dana yarsa shi tunani yakeyi na isa dakai kayimin wannan alfarmar Taheer"
Miqewa yayi yana hada hanya ya shiga bangarensa ya fada gado yanajin qirjinsa yana zafi ya zubawa qaton hotonsa da Habbatullah ido yana kallon yanda suke cikin nishadi lkcn da sukayisa yana kukan zucci qaunarta tana qwaqular qasan zuciyarsa amma ya kasa gane hakan yanda ya zuba mata ido yana kallonta har wani buda hannunsa yakeyi wai ta shiga qirjinsa.



Kwana biyu suka qara Granny ta rakasu har Gombe har sukaje Habeey na kwance a kafadar Granny zuwa yanzu ta daina kukan rabuwa da Taheer kukan rabata da yarta takeyi a sanyaye tace “don Allah Granny ki kawomin Safnah naganta nayi Mata addu'a Ina roqon Allah kada yakaita lkcn da zata dandani irin abinda ubanta ya dandanamin, Allah kaji qanta ka tausaya Mata kada ka juya sakayyar bataji ba bata gani ba a kanta Allah ka rayamin ita rayuwa me albarka, shikenan yanzu Granny bazan qara ganinta ba?"..…......



_Gareku masoya garabasa gareku saboda murnar bikin babbar sallah daga yau 3/8/2020 zuwa_ _10/8/2020 na rage kudin da ake biya domin samun wannan_ _rikitaccen labari me cike da turka turka single Zaki biya 150 VIP 400 idan ta account ne._
_Account 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB, saiki tura evidence_ _of payment ta wannan number 09013718241_
_Idan katine kuma Zaki biya 200 VIP 400  ta wannan number_ _09013718241 kada ki manta lambobin katin ake buqata ko hotonsa._
# *UMMUH HAIRAN*
[8/9, 4:08 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *HABEEYTAH*
*_DUBAI PART 2_*


*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
*UMMUH HAIRAN*



*8*



Sosai kalamanta suka ratsa zuciyar Granny jin kukan nata takeyi kamar tana dora mata dutsi aqirjinta a hankali taci gaba da rarrashinta har suka isa gidan sukayi sallama da Granny akan cewa idan an gama biki zasu dawo suga yanayin jikin Habeey.
Tunda suka shiga ta qule daki taja bargo ta rufe jikinta sanyin zazzabi yana ratsata tana nunka nadamarta tanajin ninkin tsanar jinsin da namiji a zuciyarta, ashe dama muguntar da Taheer ya shirya mata kenan ya nace saita soshi saida ya koya mata sonsa sannan ya juya Mata baya ya rabu da ita rabuwa mafi ciwo a lkcn da tafi kowa buqatarsa.




Kuka takeyi sosai tana juyi a cikin bargon tana ambaton ya Allah tare da danna qirjinta son Taheer qila ita kuma shine ajalinta, a galabaice ta miqe ta sauko tana dafa bango ta shiga bandaki ta kama ruwa ta dauro alwala tazo ta tayar da sallar azahar tana kuka tana fadawa Allah damuwarta.
Bayan ta idar ta dauki qur'ani data gani a gefe ajiye ta fara karantawa tanajin sassaucin nauyin da qirjinta yayi bayan ta idar ta daga hannunta tana kuka kunyar ubangijinta takeji ta kasa bude baki ta nemi yafiyarsa gani takeyi kamar bazai dubeta da idon rahmaba.



Amma data tuna Allah gafuru al rahim ne sai taji sanyi a ranta ta fara neman yafiyarsa da zuciya me tsarki ta jima tana Istigfari sannan ta rufe qur'anin ta koma ta kwanta tunanin baya yana dawo Mata da irin alqawurran da Taheer ya rinqa yimata lkcn da yana kwadayin jikinta.
Safnah tafi komai tsaya Mata a ranta tunanin kalmar da zata fadawa yarinyar lkcn data girma taji irin hanyar da sukabi suka samar da ita takeyi.
Toshe bakinta tayi da hannunta saboda ita kanta tagaji da kukan da takeyi so take ta saba da wannan rayuwar data samu kanta a ciki saboda tasan itace qaddararta, Addah ce ta shigo da waya a kare a kunnenta ta zauna kusa da ita ta dafata tace “na fada miki banson damuwar nan da kike sanyawa kanki Habbatullah muyi hqr komai yayi farko zaiyi qarshe ga yar uwarki zakuyi mgn"




Kara Mata tayi a kunneta tayi sallama da murya me rauni Fatima tace “Yaya Habeey ya jikinki ince dai kin warke?" Ajiyar numfashi tayi tace “gangar jikina ta warke amma zuciyata zafi takeyi Fatima nafi buqatar mutuwa akan wannan rayuwar da nakeyi mara albarka na rasa farin ciki ta ko ina..." Saurin katseta tayi da cewa “ki daina wannan zancen Yaya wata rana sai lbr don Allah kiyi hqr ki manta da wannan mayaudarin insha Allahu Allah zai saka miki"
Lumshe idonta tayi tace “don Allah Fatima ku dawo gda kada kiyi sha'awar yin rayuwa irin tawa babu komai a cikinta sai tozarci da qasqanci ki fito a kamoki ko ki bawa argent dinki number ta ya kirani na bashi kudinsa ku dawo mu nemawa rayuwarmu makoma, bana fatan rayuwarku ta lalace kamar tawa nikam nasan babuni babu farin ciki a rayuwata"




Jikin Fatima yayi sanyi matuqa sukayi sallama ta Addah ta dubeta ta kawar dakai tasani duk itace ta jefa rayuwar Habeey cikin wannan gararin, miqewa tayi a kasalce ta nufi nata dakin tana kukan zuci dana zahiri yarinyarta me biyayya dason faranta mata yau gata tana kuka saboda wasan da tayi da rayuwarta ta rabata da gatanta ta kawota ts hadata da muguwar rayuwar data zabawa kanta yanzu ta Yaya ma zata tunkari Salahu da mgnr wata ya dake tsakaninsu balle har ya karbeta ya a matsayin jininsa bayan an fada masa cewa cikin ya zube?
Hakanan suka yini a daki kowa zuciyarsa babu dadi sai yamma sannan Habeey ta qarfafa jikinta a qoqarinta na sanyawa kanta dangana da rungumar qaddararta ta fito tsakar gidan ta zauna Addah na gyaran kubewa ita kuma tana gyara Mata ganyen ugo saboda rashin wadataccen jinin da Habeey ke fama dashi shiyasa ta bayar aka siyoshi zatayi mata miya dashi.





Rayuwar Habeey da mahaifiyarta da yan'uwanta gwanin dadi cikin kwanaki ukun gata sosai suke nuna Mata basu barinta da damuwar komai ko yaushe cikin sanyata dariya suke, biye musu takeyi amma qasan zuciyarta ta kasa cire Taheer a cikinta kullum mafarkinta shine ko magana akayi mata wani lkcn shi take ambato.
Lamarin da yake damun Addah itadai da gaske batason ko wani abu daya shafi Taheer so takeyi ya fita cikin qaddarar yarta har cikin ranta dadi taji days karbi yarsa, cikin kwanaki ukun ne Addah tasa aka ciro Mata kudin da governor Waziri ya basu kudine ba kadan ba batare da kowa ya sani ba tasa aka nema mata babban gida na alfarma a cikin birnin gombe ta siya da sunan Habeey ta zuba musu komai na more rayuwa sauran ta dora jari sannan ta biyawa Habeey kudin wata babbar makarantar islamiyya.




Kwana daya suka qara sun gama shirinsu tsaf tace zasu rakata unguwa Habeey tana daki zaune tanata gwada wayar Taheer taqi tafiya sukaji sallamar mutane a tsakar gidan gaban Habeey ne ya fadi saboda tunaninta Dr Shattima ne saboda ya takura musu da ziyara cikin kwanakin nan.
Amsawa Idris da Ibrahim sukayi suka fita da sauri itama ta miqe ta fito sanye da hijjab dinta har qasa saboda dokace Addah ta sanya mata ta tsaya a bakin qofar dakin.
Shigowa sukayi ta dago kanta a dan tsorace saboda jin muryar Governor Waziri ta zuba masa ido gabanta na faduwa itadai kawai governor Waziri kama yake Mata da wani Wanda ta sani, a bayansa wasu mutum biyu ne sai Shattima dake biye dasu.



Janye idonta tayi dagakan governor Waziri ta saukeshi akan wanda yakebin bayansa shima ita yake kallo ga mamakinta sai taga kowa ya tsaya amma shi ya nufota tayi saurin rintse idonta kawai saijinta tayi a jikinsa ya rungumeta tsam ya fashe da kuka yana fadin.
“Itace wlh azeem Habbatullah yatace yayar Saudat ce Innanillahi wa innah ilaihirraji'un dama zanganta ashe mafarkina gaskiyane da yake nunamin zuwan wannan rikitaccen lkcn meyesa Yaya meyasa kuka boyemin bayan kunsan inda take meye yasa baka sanar dani ba Saida aka daura auren Taheer da Saudat"............
# *UMMUH HAIRAN*
[8/9, 4:08 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *HABEEYTAH*
*_DUBAI PART 2_*


*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
*UMMUH HAIRAN*


*9*


Zamewa tayi a jikin Alh Sahabi ta zube a qasa summamiya Taheer dake shigowa ya hankade governor Waziri dake riqeshi ya fada kanta ya dagota yana jijjigata yana Kiran sunanta kawai shima sai ya zame a kanta zuciyarsa na harbawa da sauri, a haka Saudat da Bushirah suka shigo suka samesu.
Saudat ta sulale qasa cikin kuka me gunji tace “ni dama tun ganina na farko da Habibah nasan akwai wani abu tsakanina da ita wlh na hqr da Yaya Taheer koda soyayyarsa zata kasheni Dad dama tun kafin nasan da wannan jumurdar ya sakeni saki uku minti uku bayan daura aurena dashi...."




Salati Dad ya saki cikin sarewa zuciya ya qarasa gabanta ya riqota yace Alh Sahabi ya sunkuya ya janye Taheer daga jikin Habeey yace “hakan yayimin dadi ya burgeni sosai Saudat yayi abinda ya dace dama bansan da cewa bashi ya amince da aurenki ba da tun farko bazaayi sa ba" Addah ce ta shigo daga maqota data shiga sallama ta tarar da gdan cike da mutane da sauri taja baya saboda hada idon da sukayi da Sahabi tace “Salahu!" Da qarfi tayi mgnr ya kawar dakai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login