Showing 9001 words to 12000 words out of 30200 words

Chapter 4 - Dubai Part 2

Unknown   

04 Sep 2025

2181

tare da cije lebansa ya kinkimi Habeey ya fice da ita ya sanyata a mota zuciyarsa na bugawa da qarfi Alh Aminu da governor Waziri sune suka fito da Taheer sai Kubrah da Bushirah da suka kamo Saudat da taketa gursheqen kukan rabuwa da masoyi tasan Koda Taheer bai yanke igiyoyin aurensa da aka daura awa da suka wucce akanta ba to bayyanar Habeey matsayin yayarta shaqiqiya uba daya zaisa ta janye ta sallama Mata Taheer domin tafita buqatarsa tasani Habeey tafita son Taheer kuma sunmafi dacewa da junansu kasantuwar jinin dake gudanawa a jikinsu ma iri dayane.




Wani babban asibiti dakenan cikin garin gombe suka nufa Abba gudu yakeyi kamar zai tashi sama saboda a yanzu ji yakeyi kamar mutuwar Habeey mutuwarsa ce, suna zuwa ya qara sunkutarta ya nufi cikin asibitin da ita ma'aikatan suna ganinsa suka rinqa darewa suna bashi guri kasancewar asibitin kansa mallakinsa ne.
Shiga yayi da ita dakin agajin gaggawa yasa aka kira masa likitocin shima ya cire babbar rigarsa suka baje fasaharsu wajen ceto rayuwar gudan jinin nasa daya dade yana mafarkinta ya dade yana ganin surarta a baccinsa wannan rans daxai tsaya gabanta yana qoqarin dawo Mata da rayuwarta da take qoqarin qwacewa ta dade tana zuwar masa a baccinsa.




Sunfi awa biyar a kanta komai na jikinta saida aka cire Mata ya rage daga ita sai under siket hstta bra saida Abba ya balle Mata saboda kokawa sukeyi da numfashinta da yakeyin sama suna fincikoshi daqyar zuciyarta kuwa bugunta yayi qasa fiye da mizanin da ruhi zai iya rayuwa da harbawarta.
Daqyar da taimakon oxygen suka samu bugun zuciyarta ya rinqa dawowa a hankali cikin abinda bai wucce daqiqa talatin ba ya dawo yanda zata iya rayuwar qila wa qala dashi, amma anyi rashin sa'ar shigarta commar da zata iya shekara guda a cikinta saboda duka jijiyoyin da suke kai saqon tunani qwanyarta sun tafi hutun wuccin gadi idan aka matsa musu dawowa zasu iyayin bombing gabadaya.




Wannan dalili ya tashi hankalin kowa dake cikin asibitin musamman Saudat da taketa kuka tana tsinewa son zuciyarta da yakaisu wannan matakin qiri² saboda rashin tausayinta da son kanta gashi ta jazawa yar uwarta tilo daya tal a duniya fadawa halin rai kwakwai mutu kwakwai wannan abu zai dade yana taba zuciyarta.
Shima bangaren Taheer yana cikin tsaka me wuya Amma shi da dan dama dama akan Habeey shi karo na farkone daya samu heart attack akwai yuwuwar nashi ya lafa da sauri.
Granny bata samu labarin abinda ke faruwa ba sai dare aikuwa a daren tace sai ankaita taga jikokinta, lkcn da tazo Bushirah tana kuka take fada Mata halin da Habeey take ciki ta rinqa salati tana matsar hawaye tace.




“Ni dama tun ganina na farko da yarinyar nan nasa akwai wani boyayyen al'amari game da haduwarta da Taheer Allah shi kadai yasan abinda ya boye tsakaninsu yanzu gashi gaskiya ta bayyana Kuma dole dan baqin ciki yaji kunya wlh Koda Taheer bai saki wannan ja'irar yarinyar ba sai ubansa ya saketa kuma a daren nan ko Habiba zata mutu saita mutu matsayin matar Taheer a wannan daren zaa daura"
Hakan kuwa itace ta faru a wannan dare Granny ta gwada ikonta Hajiya tanacan gaho da baki aka daura auren Taheer da Habeey wannan abu yayiwa kowa dadi duk da daga angon har amaryar basusan abinda ake ciki ba.




Sai sha daya na dare Dad ya koma gda shida su Kubrah da Saudat ta take dauriya saboda wani mugun zazzabi daya rufeta, suna zuwa gda ta shige dakinsu taja bargo ta rufe jikinta tana rera kukanta a zahirin gaskiya ba kukan rashin Taheer takeyi ba saboda a yanzu tanajin so da qaunar Habeey fiye da kanta.
A haka Aunty Zahrah mahaifiyarta tazo ta sameta a kwance cikin halin jinya ta dagota ta bude idonta da suka kumbura saboda kuka tana ganin mahaifiyarta ta fada jikinta ta rungumeta ta sake qarawa kukanta sauti tace “nayi baqin cikin zamowata silar shiga tsakanin yar uwata da bani da tamkarta a duniya da masoyinta haqiqa gsky ne layu'alimul gaibu illallah wlh da ace nasan Habeeytah yar uwatace da banyi sakacin da soyayyar mijinta ta huda zuciyata ta shigaba yanzu gashi gsky ta bayyana nice a qasa"




Tana fadin haka ta sake fadawa jikin Aunty Zahrah tace “shikenan Taheer ya tabbata ba nawaba dama yasha fadamin shi na Habeeytah ne gara nabarshi tun kafin lkc ya sanya nabarshi ta qarfi yanzu gashi ta qarfin zan barshi aunty naga samu naga rashi ya sakeni saki uku minti uku da daura aurens dashi ya turomin text massage a baya na qudurce bazan fadawa kowa ba amma yanzu dole lkc yasa na fada harma an maye masa gurbina da yar uwata Habbatullah...."
Jijjigata Aunty Zahrah tayi tace “keni kin cikani da shirme wace Habbatullah?" Bushirah dake shigowa tayi murmushin jin dadi tace “uwar wannan yarinyar" ta nuna Safnah dake kwance a kafadarta tana baccinta taci gaba da cewa “dama qarya fure take bata yaya rabon gsky ta bayyana mu qara dangi ne yar uwarmu ta dawo garemu yasa har hakan ta faru ni na tabbata Koda ace auren nan ya dade to bazaa zauna lfy ba saboda zuciyarsa tana gurin uwar yarsa" ta juya ta kalli Mom tace “kema yau kaifin harshena bazai tsallakeki ba Mom an dade anayi Ina sanya ido to yau dai gsky ta bayyana Habeey da kike qi har kike shirka saboda ki rabata da danki itama jininki ce dake da Abba Sahabi abokan wasane da babansa da babaki uwa daya uba daya yanzu kije a zuqe jinin Abba Sahabi daga jikinki kinga shikenan kin huta mudai munason yar'uwarmu sannan aure Allah baiyi hadin naki ba nasa ya qullah Yaya Taheer ya angwance da amaryarsa Habibatullah dan baqin ciki saidai ya mutu Safnah zata tashi cikin gatanta ta zama yar gata haihuwar dangi duk wanda ya zagi uwarta kansa ya zaga ka zagi ubanta ka gingimo dutsin dala dabara ta rage take Mom nidai shawara na baki kiyi maza kije a zuqe miki digon jinin Dad da Abba Sahabi a cikin jininki"................
# *UMMUH HAIRAN*
[8/9, 4:08 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *HABEEYTAH*
*_DUBAI PART 2_*

*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
    *UMMUH HAIRAN*


_Please ki biya kafin ki karanta,daganan zuwa 10/8/2020 VIP 400 single 150, account 0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar GTB idan katine ta wannan number 09013718241 hoton katin Zaki tura ko lambobinsa ta wannan number dake sama idan ta account ne Zaki tura evidance of payment dinki ta number dake sama._


*10*


Dafe qirji Mom tayi tace “Nashiga uku ni Safinah Bushirah me kike cewa ne wlh qwanyata ta tafi hutu bana gane komai" tabe baki Bushirah tayi ta dauki Pampers din baby Safnah ta fice tana cewa “kanku dai akeji aure Allah yayi alqawarin Habibah ce matar Yaya Taheer sai ku hadiyi zuciya ku mutu ku huta"
Binta sukayi da kallo har ta fice kalma daya ta kasa fitowa daga bakinsu Mom ta zube a gurin dabar tare da Dora hannunta aka ta zunduma ihun days firgita kowa suka sake yowa dakin da sauri, zare idanu takeyi tana kallon kowa ta cafki hannun Kubrah tace “me...meye yake faruwa Kubrah don Allah fadamin me ake Shirin yimin ne"




Dariya tabawa Kubrah tace “mom kema da abin haushi kike to meyene kuma alqawarin Allah ne ya cika Taheer mijin Habbatullah kinqi Allah yaso ya qulla abinsa yabarki da kunya amma Mom ai kina da wani dan ki hadashi da wannan yarinyar mana, dama ai gadon ari sai fanna"
Miqewa Aunty Zahrah tayi tana sharar hawaye tace “ashe dama wulaqancin da kuka shirya yimin da yayanki kenan Yaya Safinah kuka matsa saida muka baro England mukazo 9ja, tur wlh kin bani kunya ashe isar taki ta banzace baki isa da danki da mijinki ba Yaya kinbani kunya nayi nadamar zama qanwarki tunda kin kasa cikawa tilon yata burinta data rayu dashi tun quruciya har kawo girma"



Fincikar Hannun Saudat tayi tace “duk Dan daya hana uwarsa bacci to yasa a ransa shima bazaiyi ba zan dauki mataki farin ciki dai Taheer bazaiyishi bs kamar yanda ya hanamin yata ta warwasa"
Riqeta Mom tayi tace “kada muyi haka dake Zahrah ki muje dakina mubi komai a sannu fadan ya canza salo halan ke baki fahimci ma abinda suke cewa ba, to bari nayi miki bayani wannan karuwar yarinyar da nake fada miki Lele ya mutu akansa ta tsaface zuciyarsa ba kowa bace face yar Hajar matar Alh Sahabi ma'ana babbar yarsa da muka kashe maqudan kudade dan batar da babinta cikin rayuwar zuri'ar Maje Bauchi"



Wani mugun tsoro ne ya kama Zahrah ta zame qasa cikin tashin hankali tace “nashiga ukuna Yaya ai ban fahimci abinda yake faruwa ba dama ashe bata mutu ba Mal yacemin zai batar da ita a duniya zata lalace sannan daga baya a yawon barikinta ta dauko abin kunya ta jajubo cutar qanjamau ta mutu ashe duk qarya yayimin"
Rufe mata baki tayi lkcn da Dad yake shigowa ya bisu da kallo Mom tayi saurin miqewa tace “dama yanzu nake shirin kiranka Dad kaji abinda yaron nan yayi mana minti uku da daura aurensa da yar'uwarsa Saudat ya rattaba mata saki uku?"



Kallon inda Saudat take nade yayi yace “haka Allah ya tsara muma godewa Allah da abin ya tsaya iyanan da baiyi hakan ba da abin ya rikice mana ashe yarinyar nan Habbatullah yayar Saudat ce ubansu daya kinga kuwa ai da anyi abin kunya duk da kasancewar aure ya halatta tsakanin Saudat da Taheer tunda a baya ba auren Habbatullah yayi ba Amma ai ana barin halak ko don kunya musamman da yake Taheer ba Saudat yakeso ba Habbatullah yakeso"
Girgiza kai Mom tayi tace “Lallai kam da anyi abin kunya to Allah yasa hakan shi yafi alkhairi yanzu Ina suke ance kun dora auren ko?"



Jinjina kai yayi yace “Granny dinsu ta tursasa aka daura auren tace Koda dayansu zai mutu saidai su mutu matsayin ma'aurata" wani mashi ne ya sake sukar maqoshin Mom amma sai tace “hakanma yayi yanzu ina suke?" Cikin jin dadin yarda Mom ta Basu hadinkai governor Waziri yace “a halin da ake ciki ita Habbatullah jin cewa Taheer ya zama mijin qanwarta yasata yanke jiki ta fadi qanwar matacciya a fadar likitoci sunce zata iya daukar watanni goma a wannan halin na doguwar suma shikuwa Lale ya samu heart attack yanzu haka yana samun kulawa daga likitocin asibitin Sahabi dake gombe amma akwai yuwuwar zaa tafi dasu England acan zasufi samun kulawa"



Cikin tashin hankali Mom tace “taheer din yanzu Kuma mutuwa zaiyi don Allah Dad ayi duk abinda ya dace" miqewa yayi yace “insha Allahu zasu tashi suyi rayuwa me tsayi sai sun Haifa mana halattatun jikoki, Ina Safnah yau banganta ba"
Tabe baki tayi tace “tana gurin iyayenta" sai yanzu ya tuna da yayan nasa mata duka matsayin matan wasu suke, yace “Subhanallahi meye ya hanasu tafiya gidajen mazajensu bayan an gama komai"
Itadai bata bashi amsa ba ya juya ya fice yayi niyyar tasosu yakai kowacce gdan mijinta Amma sai yaga har shabiyu na dare kuma Basu gama bidi'arsu ba.



Kallon Mom Zahrah tayi tace “shikenan burinsu ya cika na yata ya wargatse haka kike nufi Yaya?" Dafata tayi tace “har yanzu akwai quruciya a jikinki Zahrah idan rawa ta canza dole kida canzawa yakeyi kuma Shirin zaune yafi na tsaye a yanzu nuna qiyayyarmu ga yarinyar nan baqin jini zaija mana musamman ke, sakin ranmu zamuyi mu nuna komai ya wucce in yaso sai mu koma gefe mu sake shiri, ai wlh tunda na rantse banasonta bazan taba sonta ba sufa maza basu da tunani saboda haka mu bisu da yanda sukeso sai muci galaba akansu"



Haka suka rinqa tattaunawa har Hajiya Ummah yayarsu saida suka taso suka fada mata abinda yake faruwa, tayi dariya tace “kuma tanan suka bullo? Hmmm ku bar yan iska zamu iya dasu badai a kwance take ba to kuwa a haka zata qare rayuwarta saidai suyita asarar kudinsu a banza amma bazata tashi ba"
Dubanta Zahrah tayi tace “amma Yaya Ummah sai naga kamar yayi tsauri jinya tanada cin zuciya da jiki mudai nemi wata mafitar wannan batayi ba" harararta Mom tayi tace “bantaba yin tsafi ba sai akan shegiyar yarinyar nan nifa wlh yanda nakejin tsanarta da zata mutu ma da zanfi kowa farin ciki, Yaya Ummah shi Kuma wannan gardamammen yaron ya zamuyi dashi?"



Shiru tayi tana tunani sannan ta dago tace “kada ki damu dashi a barshi ya samu lfy ya warke qalau ita kuma a qara dora Mata jinya kuma ki tubure kice saidai a bashi ita yaje yayi jinyar matarsa ta hakane kawai zai fara nadamar bijire miki saboda zaiso kusanci da iyalinsa babu dama zaiso shima yaga matarsa a cikin halin lfy daga haka zai fara tunanin mafita zai fara danasanin aurenta zaiji tsanarta zai fara tunanin qara aure to daganan ne zamuyi amfani da wannan damar mu sanyashi sakinta sai mu maye masa gurbi da Saudat kinga shikenan ciki lfy baka lfy idan ta warke saita dauki jaka ta koma bariki lkcn komai ya kankama tsakaninshi da Saudat qila ma ta haihu kinga aure ya haramta tsakaninsu indai ba mutuwa Saudat tayi ba"



Wani ihu Mom tayi tace “shiyasa nake sonki kanki naja Yaya Allah yabar mana ke" murmushi Zahrah tayi itadai har yanzu da sauran imani a ranta amma ya zatayi bata da wata hanyar ceton yarta saita amince da wannan gurguwar shawarar.
Miqewa tayi ta matsa ta taba jikin Saudat da tayi baccin wahala jikinta zum da zazzabi, gyara Mata bargo tayi ta kwanta a kusa da ita tana shafa kanta tana tausayawa tilon yar tata tasan zafin rashin masoyi tun akan Abba Sahabi lkcn daya gujewa aurenta yaje ya auri Hajar, tana tuna irin azabar data rinqaji a heart dinta tana tunz irin wahalar da gangar jikinta ta shiga a lkcn, hawaye ta share tace badan wata kusan tafi wata ba da bazan bari a cutar dake ba Habibah duk da kasancewar harda sanya hanuna a lalacewarki amma bayyanarki da abubuwan da suka faru sun sanyayamin jiki lkcn da Yaya Safinah ta shigemin gaba wajen bata rayuwarki sai ya kasance kuma da gudan jininta kuka lalace ita ta tsarawa boka tanaso kiyi cikin shege yanzu gashi ita zata goya yar da ta assasa zuwanta duniya tabbas akwai matsala gaba bamusan meye zai faru ba, Amma Kuma ni Yaya zanyi da tawa yar idan naqi basu hadin kai".............……
# *UMMUH HAIRAN*


[8/9, 4:08 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *HABEEYTAH*
*_DUBAI PART 2_*

*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
    *UMMUH HAIRAN*


_Please ki biya kafin ki karanta,daganan zuwa 10/8/2020 VIP 400 single 150, account 0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar GTB idan katine ta wannan number 09013718241 hoton katin Zaki tura ko lambobinsa ta wannan number dake sama idan ta account ne Zaki tura evidance of payment dinki ta number dake sama._


*11*


Haka kwanaki suka rinqa turawa kwanan Taheer biyar a kwance ya fara samun sauqi tunda ya farfado habeeytah kawai yake kira wani lkcn har sai an hada masa da Allurar bacci sannan yake samun nutsuwa, cikin kwanakin zuciya da jikin Mom sunqi hutawa duk inda zasu shiga su fito sun sun shiga.
Itadai Zahrah burinta a sake mantar da zuciyar Abba Sahabi Habeey Amma abin ya faskara qarshe bokan nasu da suka bawa amanna ya sanar da ita indai ta cika matsawa zata bata gomanta daya bata gyaruba dole ta hqr sukabar lamarin tsakanin Habeey da Taheer.



Kudi ba qanqana ba Mom ta kashe akan lallai a cusawa Dad aqidar qin bijirewa mgnrta haka kuwa akayi cikin lkc qanqani take juya ragamar governor Waziri.
Kwanaki goma Taheer yayi ya samu sauqi sosai zuciyarsa wasai da kyakkyawan albishir din da Dad yayi masa na musanya masa Habeey a matsayin matarsa farin ciki a gurinsa kamar zai zauce, Saida ya gama murnarsa da kukan dadinsa sannan yace “yanzu Dad tana Ina koma kun gama bikinku ban sani ba ankaimin ita gdana?"
Shafa kansa Dad yayi yace “kayi har an samu matsala lkcn da Habeey taji labarin an daura aurenka da Saudat ta yanke jiki ta fadi har yanzu batasan waye yake kantaba tana tsakankanin mutuwa da rayuwa Taheer likitoci sun tabbatar mana cewa bazata farfado ba sainan da watanni goma...."




Katse Dad yayi da cewa “what Dad! Kuma shine kuka tsaya kuka zuba Mata ido saboda bakusan ciwonta ba so kuke ku kashemin mata haba Dad haba Dad yaushe zaku fara daukan Habeeytah a matsayin da kuke daukar sauran yayanku...."
Shigowar Abba ne yasashi yin shiru Abba ya dafa Taheer yace “kayi hqr Granny ce ta takura Saida aka daura aurenka da Habeey a halin tana cikin jinya, Taheer naso ace sai Habeey ta warke akayi bikinku kukayi farin ciki kamar kowacce amarya da ango"
Girgiza masa kai yayi yasa hannu ya share masa qwallarsa lkcn da tasa take saukowa yace “inason ganinta Abba ka rakani naganta don Allah"




Miqewa yayi ya nufi qofa Abba da Dad suka miqe suka rufa masa baya har dakin da Granny take jinyar jikanyar tata ya tsaya a bakin qofar ya zuba mata ido yana hawaye ya rinqa jan qafarsa a hankali har ya qarasa gadon ya durqushe a gabanta tare da kama hannunta yana kallon na'urorin da aka daddaure qirjinta dasu.
Wasu hawaye masu dumi suka kwaranyo masa suka zuba a saman hanun Habeey ya sake rungume hannunta a qirjinsa cikin kuka me sauti yace “rayuwata dake a haka tafimin dadi fiye da na rayu da matan duniyar nan Habeeytah ko tausayawa masoyinki me qaunarki domin Allah kada ki yankemin farin cikina wlh nayiwa wannan rayuwar tanadin farin ciki me dorewa har abada Habeeytah nayi alqawarin da sanina bazan qara sanyaki zubar da hawaye ba duk ranar da kika zama mallakina, ki tashi Habeeytah don Allah ki tashi kamata yayi ace a daidai wannan lkcn muna kwance a dakinmu ne a gadonmu na sunnah kina kwance a qirjina Ina shafa wannan dogon gashin naki"




Yakai hanunsa ya shafo gashinta dake baje saman pillow wanda kullum sai Granny ta gyara matashi sai sheqi yake baqi sudik dashi, ya shagala sosai da kallonta da shafa sumar tata ya zubawa dan qaramin bakinta da smile face dinta idanu gani yakeyi kamar murmushi takeyi masa ya dago ya kalli Abba yace.
“Zo ka gani Abba murmushi takeyimin don Allah ka fada Mata karta mutu akai gift din da nakeson bata wacce na siyeta tun ranar farko dana fara saninta mace, na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login