Showing 12001 words to 15000 words out of 30200 words

Chapter 5 - Dubai Part 2

Unknown   

04 Sep 2025

2183

ajiyeta a matsayin kyautar da zan bata duk ranar data zama mallakina Abba ka fada mata da hannunta nakeson ta karba don Allah"



Ba Abba da ciwon yar tasa yakecin zuciyarsa ba hatta likitar dake kula da ita kuka takeyi cike da tausayin Taheer din tunda take bata taba ganin kojin lbrn irin wannan soyayyar ba, Tasha ganin irin wannan usue din da zarar namiji ya fuskanci mace batada amfani a gurinsa zubar da ita yakeyi Amma shi yanzune ma ya fara sonta itakam zataso jin mafarin wannan sarqaqqiyar qaunar.
Da wannan tunanin ta dafashi tace “kayi hqr zata warke insha Allahu saita haifa maka yan biyu munzo Bauchi munsha suna yallabai" miqewa yayi yace “na gode Dr amma ya kamata kema kiyi wani taimakon wata goma yayi yawa inajin tausayin matata ni banida matsala wlh ko a haka zata dawwama zan zauna da ita zan sallama lkcna wajen kula da matata"




Dafashi Dad yayi yace “dama jiran warkewarka mukeyi zaku tafi Germany na tanadar muku gdan da zaku zauna da likitan da zaike kula da ita gdan kusa da Royal hospital Germany yake daganan likitocin zasuke zuwa dubata ga kuma abbanku kusa daku"
Granny ce tayi saurin cewa “anya Aliyu wannan tsarin babu wauta a cikinsa jinyar mace sai mace kuma yaushe ma zakace zaka bawa Taheer wannan yarinya ya tafi da ita shi kadai nidai wannan shiri bai kwantamin ba"
Shigowa Mom tayi itada Zahrah tayi saurin cewa “wannan tsarin kwata² baiyi ba shima Taheer din ai zai iya kula da matarsa gsky bazasuje ko inaba kabarta anan yake kula da matarsa ga qanwarta nan saita zauna tare da ita"




Saurin kallonta Saudat tayi ta qifta Mata ido ta juya ta kalli Taheer ya zabga mata wata uwar harara yace “amma dai sainaji kamar baa sanyaki cikin maganar nan ba ko" daga masa hannu Dad yayi yace “hakan zaayi Taheer kawai a hqr da tafiyar nan tunda zatazo da matsala ko ya kagani Salahu?"
Jinjina kai yayi yace “duk yanda kukayi ma daidaine amma Saudat bazata gidan Habbatullah ta zauna ba kamar yanda na datse duk wata alaqa ta kusanci tsakanin Habbatullah da mahaifiyarta Hajar haka na datseta tsakanin Saudat da Habeey harsai zuwa lkcn data samu sauqi dakanta ta nemeki kinji ko?"
Daga Kai tayi cikin qunar zuciya tace “naji Abba Amma..." Daga mata hannu yayi yace “kune musabbabin faruwar koma saboda haka banson jin komai daga gareki Taheer ka kula da matarka Allah ya taimaka maka zan nemo muku yan aiki biyu da zasuke tayaka jinyarta"




Murmushi yayi yace “na gde Abba amma bana buqatar tallafin kowa wajen kula da matata zan iya komai nasani idan nine a irin wannan halin Habeey bazata taba yarda wani ya kula dani ba ita zatayimin komai saidai idan fin qarfinta akayi"
Sosai zuciyar Abba tayi sanyi yaji dadin kalaman Taheer duk da yasan hana tafiya da Habeey din wani salon makirci ne saboda sarai yana hango qiyayyarta a idanun Mom da matarsa Zahrah.
Itakuwa Saudat a duk lkcn da taga yanda Taheer yaketa jagwalgwala Habeey sai taji wani shauqi yana shigarta duk da tasan cewa yayi Mata nisa amma ta kasa daina kallonsa da fuskar qauna inda shi Kuma bata hangen komai a idonsa sai qiyayyarta.




Ran Mom baiso hakaba taso aja maganar har rai ya baci amma sai taga akasin haka suka fice zuciyar kowa babu dadi suka nufi gida Mom ta daki sitiyari tace “wannan abin yana firgitani anya kuwa Taheer mutum ne"
Tabe baki Saudat tayi tace “to wai Mom meye yasa kika tsani Aunty Habbatullah ne nifa indai danni kike wannan abin kima daina nariga na sallamawa yar'uwata mijinta dama tun farko rashin sanine yasa nayi yunqurin shiga tsakaninsu, Mom abin yayi yawa da wanne zasuji ne sunason juna kuka cusa musu tsanar juna lkcn da muke tunanin haqanmu zai cimma ruwa lkcn ne kuma Allah ya zartar da nasa hukuncin ya qullah auren da bakwaso...."




Wani bugu Zahrah takaiwa yar tata tace “shashasha mara kishin kai dama ashe kema haka kike inata kashe kudina don ginaki ke kina qoqarin rusani to wlh kika sake tausayin wannan makirar yarinyar ya ratsa zuciyarki sai ta rabaki da duk wata fada da kike taqama da ita uban naki ma saiya daina kallonki"
Shiru tayi batace komai ba qasan zuciyarta yana tunano mata yanda taga Taheer yana shigewa jikin Habeey tayi saurin kawar da tunanin ta dauki wayarta tana wasa da ita har sukazo gdan.
Kwanaki biyu Habeey ta qara a asibitin aka sallameta zuwa gda Taheer yaso su tare a gdan da Dad ya mallaka musu amma fir Dad yace saidai ya bari idan matarsa ta warke saisu tare, hakanan badon ransa yasoba saidon nasihar da Abba sahabi ya rinqa yi masa, shine dalilin da yasa ya hqr ya zauna a cikin government house din bangare guda aka ware musu aka zuba musu yan aiki sosai....
# *UMMUH HAIRAN*
[8/9, 4:08 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *HABEEYTAH*
*_DUBAI PART 2_*


*12*


Ranar da suka tare kwana yayi yana kallonta yana hawaye yau ga Habeey dinsa yar uwarsa jininsa matsayin matarsa amma saidai ya kalleta.
Miqewa yayi ya dauro alwala ya tayar da sallah yana kuka yana nemawa rayuwarsa lafiya gurin Wanda yake da ikon canza al'amura sai asuba ya kwanta bacci ya dan daukeshi yana rungume da ita yanajin dumin jikinta na ratsashi.



Takwas ya tashi ya zuba Mata ido yana murmushi ko yaushe a kowanne hali fuskarta bata rabo da annuri ya share hawayensa ya sunkiyo daidai bakinta yace “kinaso nayi miki wanka?" Zuba mata ido yayi kawai sai yaji kukansa yana qara qarfi ya kwantar da kansa a jikinta yana lasar jajayen lips dinta da suke kullum kamar tasanya musu jambaki.
Dagata yayi a hankali ya cire mata komai dake jikinta yanajin faduwar gabansa na tsananta, ya dade yana kallonta daqyar a galabaice ya dauketa ya shiga da ita bathroom ya sanyata a ruwan wankan daya hada Mata ya diba ya watsa Mata a fuskarta duk ta rame yayi murmushi yace “nasan zakiso ramawa ko?" Diba yayi ya watsawa kansa yayi dariya yace “komai kikeso sh izanyi miki ko kaya zansa sai wanda nasan zakiso HABEEYTAH"



Yanayi mata wankan yana wasa da jikinta yanajin feel dinsa na qaruwa daqyar ya gama yimata wankan hakanan yaji yana sha'awar ya daura Mata alwala yayi Mata alwala ya daukota ya bude cikin wardrobe ya zubawa wardrobe din ido kayansa ne da nata a jere komai sabone yayi ajiyar zuciya wannan yasan aikin Abba Sahabi ne.
Wata baqar doguwar riga ya dauko ya juyo ya wareta ya kalleta yace “kinasonta baby?" Zuba Mata ido yayi sai kuma ya ninketa ya mayar yace “nasan bakison baqin kaya bari na dauko miki ja" wata jar doguwar riga ya dauko ya bude wata wardrobe din ya dauko jajayen band da dankunne fashion shima ja ya dawo ya ajiye ya dauko wasu mayuka masu masifar kyau da tsada ya matsa ya shafa mata ya taje Mata kanta a hankali sannan ya sanya band din ya daure mata ya kama jelar gashinta ya tufke kamar yanda yaga tanayi masa.




Kayan ya saka mata ya fesa mata turare ya koma gefe yana kallonta yana ajiyar zuciya tare da murmushi yace “Rayuwata inasonki" shima wanka yayi ya dauko wani blue din jeans yasa ya dauko jar riga yasaka ya kalleta yace “nayi miki kyau My life?" Murmushi yayi ya matsa ya lakace mata hanci ya fita yana cewa jirani na dauko alluranki..."
Turus yaja ya tsaya ganin Mom dinsa a tsaye a parlourn ita da Saudat ya kallesu a wulaqance, a zahiri kallonsa ne a haka indai ba saninsa kayi ba zakace tsabar iskanci ne, jikin Saudat rawa ya fara yasa hannu ya karbi Safnah dake hannunta yace “lafiya da safen nan?" Yanda Mom taga yanayinsa babu damuwa da Kuma kalaman da taji yana furtawa ya fadar Mata da gaba amma saita dake tace “dama munzo ganin jikin matar takane" murmushi yayi daya bayyanar da kyawawan haqoransa yace da sauqi fa sosai shiga ki ganta Mom har kwalliya nayi Mata".......
# *UMMUH HAIRAN*
[8/9, 4:09 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA:      HABEEYTAH
*_DUBAI PART 2_*



*13*



Zaro ido Mom tayi tace “kwalliya kuma gawar kayiwa kwalliya?" Tsuke fuskarsa yayi yace “aa Mom banason ki qara cewa matata gawa qila saima ki mutu ki barta waike meye yasa kullum bakinki baya taba fadin alkhairi akan matata ne nifa banson irin haka wlh rai zai iya baci"
Sakin baki tayi tana kallonsa har ya gama fadansa ya juya ya koma dakin ya kwantar da Safnah kusa da mahaifiyarta ya miqe domin fitowa suka hada ido da Mom ya sake tsuke fuskarsa yace “banason a dameta muje parlour" murmushin takaici tayi tace “indai wannan hoton hotiho dince da kanka zata isheka Taheer tunda ta zama Liability komai sai kayi mata"



Ko sauraronta baiyi ba ya dauko feedar Safnah ya zauna ya daukota yana Mata wasa ya hada mata madara ya jorner mata ganin bashi da niyyar basu guri yasata cewa da Saudat “ki zauna ki tayashi aiki"
Dagowa yayi ya watsa mata wata uwar harara ya mayar da kansa wa yarsa har saida Mom ta kusa ficewa daga dakin yace “dallah malama ki bacemin da gani anan banza mayya uwarki zaki tsaya kiyimin nida matata sai ansamin ido idan wani abin nayi niyyar yimata jiya da ubanwa muka kwana"
Tsorone ya kama Saudat tasan tana cewa wani abu jibgarta zaiyi ita ta rasa Ina Taheer ya kwaso wannan baqar zuciyar tasa, bin Mom tayi da sauri har ta fita ta dawo tace “am Yaya Safnan fa?"




Wata uwar tsawa ya daka Mata yace “uwarki ce ta haifamin ita da yazama dole na baki ita?" Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata tace “amma dai Yaya kasani yar yar'uwata ce nima inada haqqi akanta..."
Wani kallo da yayi matane yasata ficewa da gudu ta nufi bangaren Mom din tana zuwa tayi kicibis da Mahfuz ya daka Mata tsawa yace “ubanme kike yiwa wannan uban gudun ballagaza kawai kizo ki shirya ni bazan iyada da zafin 9ja ba komawa inda na fito zanyi bandama su Dad da abinsu wani ni zaace na tafi dake ke wlh bama zan tafi dakeba kawai kice musu na tafi"
Yana gama fada Mata haka ya juya ya fice da sauri ta tabe baki tace “banza a banza duk izzarka baka kama qafar Hussain dinka ba, batakai nakeyi ba"




Shiga ciki tayi ta fara hada kayanta tare da cin alwashin ba zata qara kwana uku a 9ja ba ko su Abba bazasu koma ba ita zata tafi,
Itakuwa Mom tana shiga dakinta ta dokawa Hajiya Ummah waya tace “gsky Ummah banga alamun nasaraba shegen yaron nan bazai sare ba wlh bakiga yanda yake rawar qafa akan yarinyar nan ba abin haushin iyayensa sun daure masa gindi duk wasu shagunansa Dad ya sanya yaransa a ciki zasuke juya masa dukiyarsa sannan har wani albashi ya yanka masa hatta mara lfyr saida ya yanka Mata salary"




Dariya Ummah tayi tace “shine me da har zai sanya ki sare Safinah yau da gobe fah sai Allah wlh dole sai Taheer ya gaji da jinyar yarinyar nan Kuma duk ke kika bata abin aida kin bari sun tafi wajen inda babu wanda zai taimakeshi da komai"
Shiru tayi tana tunani kafin tace “Germany fah zasu tafi nafiso su tafi inda basuda kowa..." Katseta tayi da cewa “ki aiwatar da aikin da aka baki kawai kice da Excellency ya kadasu su tafi acen din komai zaifi tafiya daidai kuma kada ki yarda a bar miki yarinyar nan ya tafi da kayarsa kinga itama qarin wahala ce"




Dake lusara ce haka ta yarda cikin farin ciki ta rinqa gudanar da al'amuranta cikin dare ta tashi batare da kowa ya ganta ba ko tsoron girman gdan bataji ta shiga bangaren nasu Taheer tayi saa ko lkcn daya fito zai raka likitan Safnah ta fara kuka ya koma da sauri bai dawo ya rufe ba bayan yayi Mata wanka ya hada Mata madararta ya bata ya dorata a kafadarsa tayi bacci ya kwantar da ita a gadonta ya koma ya daga Habeey ya gyarata yayi mata wanka ya dawo dawo da ita ya kwantar da ita.
Shima ya gaji saboda haka yana kwanciya bacci ya daukeshi har cikin ransa yafi tausayin Abba Sahabi fiye dashi kansa saboda yanda duk ya susuce akan ciwon na Habeey yau sun dade dashi suna tattaunawa akan ciwon yana cewa dashi yana shirya musu tafiya Saudia Wani Islamic Hospital akwai abokinsa acan yace yawanci irin wannan ciwon biyu ce take haduwa kodai tanada junnu a tare da ita ko kuma an jefeta dasu abin ya tadda ciwon, saboda haka Dr Manzir ya bashi shawarar a kawota nan a dorata akan magungunan Islamic.




Yaji dadin shawarar ta Abba Amma yace da abban yayi Shiru harsai komai ya kammala na tafiyar, nan Abba yake fada masa cewa mahaifiyar Habeey dinma batada lfy cikin dare aka jita tana ihu kamar mahaukaciya tun daga lkcn itama ta daina magana saidai kallo kawai ta kwatance Kuma bama kowanne mutum take ganewa ba yanzu haka tana Ɓillire gidan mahaifinta anata sauke mata qur'ani.
Jinjina kai Taheer yayi yace “amma lamarin da daure kai kuma Ina mijinta da yayanta maza da sukayi saura?" Girgiza kai Abba yayi yace da Taheer “tun ranar data tashi da ciwon da safe kafin kowa yazo kanta akace yazo ya tattare yayansa maza ya tafi dasu har jiya baa qarajin duriyarsu ba" da wannan tunanin bacci ya dauke Taheer nasararsa daya shi ko bazaiyi nafila ba baya kwanciya babu alwala Kuma ko iskancinsa yayi daya gama yake wanka wannan dalilin yasa hatta Habeey da batasan waye a kanta ba sai ya daura Mata alwala duk lkcn da zaiyi sallah.




___________Itakuwa Mom tana shigowa ta kunna turaren tsafinta ta banka a parlourn ta tsaya idanunta a rufe hayaqin yabi ta qasan qofar dakin ya shiga daidai lkcn Taheer yana saman sallaya yayi sujjadah yana nemawa matarsa sauqi gurin me duk.
Bajewa hayaqin yayi sannan ya nufi jikin Habeey dake kwance kamar gawa ya rinqa kewayeta abin mamaki hikima ta ubangiji Taheer yana cikin sujjadar nan kawai sai yaji motsi a saman gadon ya dago da sauri yayi tahiya yayi sallama yanajin Motsin na qaruwa baidai juya ba tunaninsa Safnah ce ta tashi.
Ji yayi anyi attishawa hakanne ya basa damar dago idanunsa da sauri ya saukesu akan gadon kawai sai yaga Habeey ce take motsawa bakinta yana furta “ LA'ILAHA ILLALLAH MUHAMMADUR RASULULLAH SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM, ASHHADU ALLA'ILAHA ILALLAH WA'ASHHADU ANNA MUHAMMADUN ABDUHU WARASULIHI".........
# *UMMUH HAIRAN*
[8/9, 4:09 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA:   *HABEEYTAH*
*_DUBAI PART 2_*



*14*



Da sauri ya miqe ya Isa inda take ya durqushe ya kama hannunta cikin matsanancin mamaki da murna yace “Habeeytah! Kece kin tashi? Da gaske kece kika tashi wayyohh Allah na Habeey alhmdllh ya Allah"
Duk wannan surutun da yakeyi bata bude idonta ba sai yanzu taketa qoqarin bude idon tare da son tuno wani abu game da ita, muryar data janyo mata faduwar itace ta rinqa dawo mata.
Ta yunqura da azama zata miqe sai taji gabobinta kamar baa jikinta suke ba ta bude idonta a hankali ta zubasu akan Taheer da yake tsugunne gabanta yanata kallonta hawayen farin ciki suna zubo masa.




Ganin tanata kokawar tashine yasashi miqewa da nufin taimaka mata ta tashin amma ga mamakinsa sai yaga ta girgiza masa kai, ya saki baki yana kallonta har ta samu ta motsa daqyar ta dan muskuta daga inda take.
Zama yayi a kusa da ita yace yace “ki bari in tasheki inkira likita ya dubaki idan babu matsala saina nema miki abinda zakici" sake Kai hannu yayi zai tabata tayi saurin rintse idonta tare da girgiza masa kai, tsayawa yayi sororo yana kallonta daidai lkcn da Mom ta gama siddabarunta ta fice.




Safnah ce ta farka ta fara mitar neman abinci ya miqe da sauri ya daukota ya kwantar da ita a gefen Habeey yace “yi hqr daughter bari na hada miki abincinki kinji" kallon Safnan ne ya rinqa mayar Mata da tunaninta baya kalamansa na batanci da tozarci gareta suna dawo Mata kazalika mgnr da taji wannan mutumin daya rungumeta dazu yana fasa cewa an daura auren Taheer da Saudat Kuma Saudat qanwarta ce.
Cikin wata murya tace “ina Addah waye ya kawoni nan kai me kakeyi anan qarfe nawa yanzu?"
Cikin mamakin tambayoyin nata yace “kiyi hqr gobe zan baki amsa yanzu darene Kuma kina buqatar hutu kin kallah 2:33am fah" bata qarayi masa mgn ba har ya gama hadawa safnah madarar yazo ya dauketa ya rinqa bata tanasha tana bangale masa baki shima yanata yimata waqoqinsa itadai Habeey kallonsu kawai takeyi tana hawaye tunaninta saceta Taheer yayi ya sakeyi camping dinta a wani gurin.



A hankali tace “Taheer Ina ne nan meye ya kawoni nan Ina matarka da kazo gurina a wannen daren yaushe? Yaushene zaka gane Annabi ya faku ka qyaleni ka fita daga rayuwata ne, meye yasa kullum burinka ka quntatawa rayuwata ne Taheer kai kace na barka bakaso na bazaka iya rayuwa da karuwa ba na hqr na barka to Kai meye ya dawo dakai cikin tawa rayuwa..."
Maimakon yabata amsa kawai sai taga yayi wani dogon murmushi ya daga yarsa sama ya cillata ya cafe yace “beautiful daughter ta qoshi sai bacci ki qyale Dad da Mom Suma suyi bacci ko?" Yayi mgnr yana sauke idonsa akan Habeey ya kwantar da yarinyar yace “aini mayene akanki banida zuciya Kuma bana fushi bazan taba barinki ba ke idanma tunanin na saceki kikeyi naji na amince ni barawonki ne amma wannan karon ban saceki nayi camping dinki don na aikata fasadi dake ba aa kawomin ke akayi matssyin matata ta sunnah"




Yana fadin haka ya dagota gaba dayanta ya miqar da ita tsaye qafafunta na rawa saboda rashin qarfi yaja numfashi lkcn daya sauke idanunsa a saman boobs dinta komai ya ragu a jikinta amma banda nononta da mazaunanta.
Numfashi ya fuzgo da qarfi yanajin wani yanayi na ratsashi amma komai rashin imaninsa dole dai ya dagawa Habibatullah qafa a wannan taqin, jinginata yayi a jikinsa ya kaita bathroom ya sake mata wanka bataso amma batada ikon hanawa saboda babu kowacce gaba da take aiki yanda ya kamata a jikinta tanajin yanda yamai da hankalinsa wajen wasa da nononta yana wani shaqar numfashi yana kallon qwayar idonta.




Shassheqar kukanta yasashi saurin dakatar da abinda yakeyi ya dagata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login