Showing 30001 words to 33000 words out of 118398 words
yadda duniyar ta fita kanta ba za ta taba damuwa don Hamma Lamiɗo ya sake ta ba. Haushin shi da take ji yasa ta ji ba ta son shi yanzu, ko ya sake ta babu abin da za ta rasa domin ita an gama yi mata rashi a duniya. Har jiya da aka zauna zaman meeting din da Hamma Jibo ya haɗa a daran an kira Hamma Kabiru a waya aka saka a amsa kuwwa tana ji yana faɗin ya so Lamiɗo ya sake ta da gaske ya ga yadda za ta ƙare. Cikin izza yake faɗin ba za ta samu wanda yake ƙasa da shi ba kamar ma kuma ya yi mata nisa ta yi kuka sosai hawayenta har da majina kowa ita yake gani a matsayin mai laifi shi da ya fara furta kalaman shi bai yi laifi ba sai ita da ya mayar ma martani, ba zununci ba ko menene sai da ya lalace za ta nuna ma kowa Lamiɗo ba don shi aka haife ta ba, shima ba don ita ya zo duniya ba kowa ma zai iya rayuwa ba ɗan'uwansa kuma ya zauna lafiya.
Hamma Jibo ya yi maganganu sosai barin ma ita ya yi mata nasiha haƙuri sannan daga ƙarshe shima ya ce ta kira Hamma Lamiɗo ta ba shi hakuri haka ma su Hamma Abdullahi duk suka ce har da Mami, su suna ganin ita ce ba akan gaskiya ba jin su kawai take yi ba za ta ba shi hakuri ba domin ba ita ta fara maganar ba shi ya fara.
An yi maganar in Baffa ya yi kwana arba'in da rasuwa Umma Balki za ta koma gida, wa zai zauna da Ammah? Tunda zaman shurun ba daɗi, ita cewa ma take yi za ta iya zama ita kaɗai.
Received at 11:37Reactions: ❤ 4, 👍 1, 🔥 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Umma Balki ta ce bayan arba'in ɗin za ta je ta duba gida sai Umma A'i ta zo, ta yi ko da sati biyu ne ita kuma sai ta dawo su dinga karɓa karba kafin Ammah ta fita takaba, sannan ga Ummin ikki ma da kullum tana zuwa.
Maganar girki kuma Hamma Jibo ya ce za a ɗauki yar aiki Umma Balki ta ce ba sai an ɗauka ba, za ta iya yin komai da kanta.
Hamma Abdullahi ma ya ce matayensu da yaransu za su dinga leƙowa akai akai saboda kar gida ya yi shuru.
Daga karshe aka tsaya da sai Ammah ta fita takaba za a yi maganar raba gado.
Da gaske kenan Baffa ya rasu! Tunda ga shi ana maganar rabon gado. Mutuwar Baffa mutuwa ce mai zafi ga iyalansa amma a wajen Umma Salma ba a taba mata wani abu da ya daketa da zafi irin mutuwar Baffa ba, ko lokacin da Habib ya saketa ashe abin da ta ji a lokacin wasa ne yanzu ne ta ke jin raɗadin abin da hausawa ke faɗin wasa farin girki.
*
Ta yi niyar ba za ta fito ba, ba ta san ma wani ya yi mata magana amma kudirinta bai cika ba twins Hassan da Hussaini da su Ammi suka shigo suna yi mata sallama.
Sai ga Saudat itama ta shigo tana faɗin Anty Ummu za mu tafi.
Ba a son ranta ba, yaran suka sanya ta fitowa sai ga shi sun haɗe da Adda Nauwara a falo tana ganin ta ta hau yi mata tsiyan ta ɗauka har su tafi ba za ta fito su yi sallama ba.
Ummi ikki ta gani ashe ta zo, ta gaisheta ta amsa tana kallonta.
"Kullun fuska a kumbure Ummu Salma, ko uwar taki ba ta gasa ki da ruwan zafin ne?
Ummu Salma ta yi shuru ba ta yi magana ba. Kanta na kasa tana wasa da Hannun Isma'il da ya riƙe ta.
Tana sanye da hijabinta dogo har da safa tunda Mami ta hana ta zama ba safa hijabi kuma tun dawowarta asibiti take yini da shi barci ne kawai ke raba ta da shi.
Ammah da Mami tare da Umma Balki duk suna falo, mazan ne suna tsakar gida.
"Ba dole ki ga fuskarta kullum a sumtume ba, ba ta da aiki sai shigewa ɗaki tana kuka, kin ga ko ai yanzu idanuwana da fuska suka fara kumbura in dai kuka ta mayar abin yin ta."
Umma Balki ta faɗa tana hararanta, ba ta kuma yi magana ba Mami ce ke amsa mata da cewa ta fa daina kuka.
"Kar ma ta daina yarinya daga faɗa mata gaskiya, sai rashin kunya sai fushe fushe. Kin ba ni kunya Ummu Salma ban za ci haka kike da taurin kai ba, to shi Lamiɗon ma ya yi fushi ya yi tafiyarsa gidansu ki ci kan ki."
Umma Balki ke ta faɗa ta in da take shiga ba ta nan take fita ba.
Mami na tare mata aka haɗa da ita.
"Auta ki daina haka kin ji ko? Ba ki kyauta ba, Ki kira shi ki ba shi hakuri, har yar'uwan ta ki ma ta yi fushi dake yau ma na ce ta zo mu je ta ce ba za ta je ba."
Ummu Salma ta kalli Ummin ikki amma ba ta yi magana ba. Wai har da Baɗɗo a masu jin haushinta. Kar ta zo ta je itama ta yi ta fushin tunda itama ta kasa fahimtar yanayinta.
Shi ya sa ba ta son fitowa saboda ba ta son magana, ranta baci ma yake yi.
Sai da su Hamma Jibon za su tafi ne ta fita tsakar gida Harira da Islam sune masu ɗaukan kaya zuwa haraba Hamma Abdullahi ne zai kai su filin jirgi.
Faruk take kallo yana ta bin bayan Islam da gudu yana rigiman sai ta ba shi wata karamar akwatin da ta ɗauka Hanan kawai ke yi mata gizo yau kwana huɗu ba su dawo da ita ba.
Ita abubuwa da dama ma gizo suke yi mata tunda ta dawo daga asibiti, sai ta ga abu kamar wani abu dabam, ranar fulas ɗin ruwa zafi ganin shi ta yi kamar tunkuya abubuwa dai suna sauya mata a idanuwanta tun bayan fardaɗowanta daga asibiti kuma ta kasa faɗama kowa to waye ma zai saurare ta? Kowa na jin haushin ta wanda ta ke zaune domin shi bai damu da ita ba cewa ma ya yi zai sake ta.
Gabanta faɗuwa yake yi in ta tuna cewa wataƙila gidan su Habib su ƙi dawowa da Hannan da ko mai zai faru sai dai ya faru amma sai ta karɓo yarta ba za ta bar musu ita ba har abada.
A tsakar gida ta tsaya da rakiyar ta yi komawarta cikin ɗaki bayan Hamma Jibo ya jadadda mata ta kira Hamma Lamiɗo ta ba shi haƙuri ta amsa da to amma a zuciyan ta ce shi ya kamata ya ba ni hakuri ba ni ce zan kira shi ina ba shi hakuri ba.
Received at 11:37Reactions: ❤ 4, 👍 1, 🔥 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Baɗɗo ma ta daɗe ba ta yi fushin ba itama ba ta ga laifin da ta yi mata ba, akan gaskiyanta take ai ta san fushi ta yi domin tun ranar ba ta dawo kuma ba ta kira ta a waya ba, itama ba ta kira ta ba.
Tunda Baffa ya rasu ta rasa jarrinta taurin zuciyarta ya karu ba ta jin taushi taushi, ta san tana da taurin kai a baya amma yanzu ya yi ƙamari tana ji ko za a yi tashin ƙiyama ne ba ta yarda a ce ita ce ke da laifi ba shi ya sa ko kaɗan zuciyarta ba ta rusuna ba.
Wanda zai yi fushi da ita ya daɗe bai yi ba.
Tafiyar Hamma Jibo da iyalansa sai gida ya yi shuru.
Hamma Abdullahi daga kai su filin jirgi ma bai dawo ba, Saddam kuma ya fita Hamma Abdulrahim ne kawai muka yana bangaren su.
Harira ta shigo ta gaisheta tana tambayanta ko akwai abin da za ta yi mata, yan zannuwanta da take sawa da dogayen riguna ta ce ta kwashe ta ɗan wanke mata. Bayan fitan Hariran ne Mami ta shigo ɗakin ta ba ta waya Daddy ne ya yi mata ya jiki suka gaisa shi yake faɗa mata ba zai samu zuwa ba tafiya ta kama shi zuwa Lagos amma gobe Mami da su Islam za su bi jirgi su koma Kaduna tunda duk sun koma makaranta.
Bayan sun gama wayar ne ta miƙa ma Mami wayarta.
Ta karɓa tana kallon ta kur kamar tana nazarinta, ita kuma tana kwance ne daman lokacin da Mami ta shigo sai ta ɗan zauna a saman gadon ta cire hijabin jikinta doguwar rigar atamfar dake jikinta ta bayyana kanta akwai hula amma ana ganin gashin ta, a tsefe yake ta so ne in suka zo nan a yi mata kitso to ba kwanciyar hankali, ga rasuwar Baffa ga abin da ya same ta, gashin duk ya yi biji biji.
Mami ta faɗa mata cutar da ya kamata, har goggle ta yi na cutar ta yi daga nan ta san tana da sauran kwana a gaba ne, amma cutar tana da hatsari ga mata masu ciki.
"Yaushe ne za ki koma ganin likita?
Mami ta katse shurun da ya gifta a tsakanin su, itama yanzu Ummu Salma ba ta mata hira in ba ita ce ta tsare ta da magana ba.
"Ranar monday ne jibi."
"Kuma ga shi gobe za mu tafi, ke da wa za ku je?
"Ni kaɗai, Harira za ta raka ni."
"Baɗɗo fa ko kuma Umma Balki ta raka ki."
Mami ta faɗa tana kallonta.
"To."
Kawai ta ce tana kauda kanta.
Ba haushin Mami take ji ba kawai itama ta san tana bayan masu cewa ba ta kyauta ba. E ta san maganganun da ta faɗa ma Ammah ba ta kyauta ba, wannan ta yarda ta kuma karɓi kuskuranta amma a kan maganar Lamiɗo tana da ja akan masu cewa ita ce ta yi masa laifi.
"Ummu Salma."
Mami ta kira sunan ta lokaci ɗaya tana matsawa kusa da ita har tana riƙo hannuwanta.
"Ɗago ki kalle ni nan."
Ta ɗago idanuwanta tana mai kallon Mami.
"Ki yi haƙuri ki daina damuwa. Baffa addu'a za mu yi ta masa, maganar Hanan kuma ki kwantar da hankali babu wanda ya isa ya karɓe ta daga hannun ki."
Idanuwan Umma Salma suka kawo ƙwalla suka kece mata a saman kumatunta.
"Mami yau kwana huɗu amma ba su dawo da Hanan ba."
"Za su dawo da ita, in ma ba su dawo da ita za a je a ɗauko ta."
Mami ke share mata hawaye da tafin hannunta.
"Ke da za ku koma Lagos da zaran Muhammadu ya dawo, tare da ɗiyar ku za ku koma in sha Allahu.'"
Hankalinta ya ɗan kwanta ta tabbata koma me zai faru Mami tana tare da ita.
Ba za ta koma Lagos ba sai Hamma Lamiɗo ya janye kalamansa in kuma bai janye ba ta rantse da wanda ranta ke hannun shi ba za ta bi shi ta koma ba.
Mami ta sake lallashinta da cewa ta sake zuwa ta samu Ammah ta sake ba ta haƙuri.
"Ko ɗazu da safe ma na shiga na gaisheta dakyar ta amsa gaisuwa ta Mami."
"Ki sake zuwa ki ba ta haƙuri abin ne ya dame ta."
"Mami nima fa ba a kyauta mini ba."
"An ji ke ma ba a kyauta miki ba, amma ke ce ƙarama ke ce ba ki da gaskiya."
Sai kawai ta yi shuru.
"Uwa ce ita, duk wanda zai so ki da cigaban ki bayan ita ne."
"Haka ne."
"To ki sake zuwa ki same ta daga ke sai ita, ki sake ba ta haƙuri."
Ta amsa da to za ta je.
"Shi Lamiɗon kin kira shi?
"E bai ɗauka ba."
Ta yi ma Mamin ƙarya domin ita dai ba za ta kira ba.
Kawai sai Mami ta ɗau wayarta tana cewa bari ta kira shi.
Received at 11:37Reactions: ❤ 4, 👍 1, 🔥 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ummu Salma na zaune ko fargaba ba ta yi domin ta san halin shi ba zai taɓa cewa ba ta kira shi ba a e ɗin shima zai tafi.
Wayar a amsa kuwwa Mami ta saka tana fara ringing ya danna mata busy har tana tunanin ko yana cikin mutane ne sai ga kiran shi ya shigo ta ɗaga.
Muryan shi tarai, muryan da kan sanya Ummu Salama kasala da shauƙi a baya ban da yanzu.
Suka gaisa da Mami da tambayan mutanen gida.
"Yaushe za ka dawo?
"Da zarar Mai martaba ya ta shi zuwa London'
Ya amsa mata cikin yanayin maganarsa. Mami ta tambaya da cewa daman bai tafi ba? Sai ya ce sun samu tsaikon Visa ne ta yi fatan alheri.
Suka yi shuru dukkansu ba wanda ya yi magana.
Shi da man ba gwanin ɗago magana ba ne ko da akwai maganganun a bakin shi.
"Ɗiyata ta ce ta kira ka, ba ka ɗauka ba?
Sai ya yi shuru kamar bai ji ba sai da Mami ta sake maimaitawa.
"Ban lura da kiran na ta ba Mami."
Ya amsa kai tsaye amma a ƙasan zuciyarsa yana tunanin ko lokacin haihuwar nan Ummu Salama ta samu natsala ne? Shi dai yana ganin she is not okay.
"To ta kira ka ne ta ba ka hakuri kowa a gida ya ce ba ta kyauta ba. Amma kai ma ba zan fasa faɗa maka ba ka kyauta ba koma me ya faru ai ka duba yanayinta lallashi take buƙata ba faɗa ba."
"Mami."
Ya kira sunanta ta amsa.
"Ni cikin ɓacin rai na yi maganar da na yi, amma Mami Ummu Salama ta kyauta mganganun da ta faɗa ma Ammah? Ta kyauta abin da ta yi?
Ya faɗa a jere daga ji yana ƙokarin sarrafa fushinsa ne
"Ba ta kyauta ba, kowa ma ya faɗa mata kuma ta karɓi laifinta kuma har ta ba ta hakuri ma."
Ya yi shuru kawai bai yi magana ba.
"Kai ma sai ka yi haƙuri, kai ne babba. Ka lallasheta domin tana bukatar hakan."
"I will."
"Amma ni ma mganganun da ta faɗa mini ta kyauta?
"Ba ta kyauta ba, za ta ba ka hakuri."
"Better."
Ummu Salma na zaune haushi duk ya isheta har wani better ya ke faɗi tunda an ce za ta ba shi haƙuri to ya cigaba da jira.
Maganar komawarta asibiti Mami ta yi masa ya ce zai kira Ummu Salman za su yi magana ya tambayi ko an dawo da Hanan?
"Ba su dawo da ita ba, in ba su dawo ba za a je a karɓota ai kana dawowa za ku koma Lagos ɗin ko?
Ya amsa da in sha Alllahu ya kara da cewa shima hutunsa ya kare ga yara ma sun koma makaranta.
"Bilkisun fa?
"Tana nan tare da ni."
Ya amsa ma Mami, sannan ya cigaba da faɗa mata daman bayan sun gama biki a garin Abuja Kano ta koma, daga Kanon ne jiya ta zo Daura ta same shi gabaɗayansu tare za su taho nan Adamawa.
Yanzu akwai sakin jiki tsakanin Lamiɗo da Mami, sai su ɗau lokaci suna magana a waya ma ba su sani ba.
Ummu Salma kuma haushi ya turniƙeta, wato ma matarshi na can tare da shi, ita ce ya gasa ma maganganu ya yi tafiyarsa.
Ta ɗauka Mami za ta yanke wayarta ne amma kawai sai ta ga ta miƙa mata tana ce masa ga Ummu Salma ma su yi magana ta karɓa saboda Mami ce, a gabanta ta yi masa sallama ya amsa a ginshiƙe kamar ba zai yi magana ba.
Allah ya taimaketa Mami ta ba su waje, tana fita ko ta yi zaraf ta kashe wayar, saboda ma an ce za ta ba shi hakuri dakyar yake amsa sallamanta.
Ya sake kiran wayar Mami ta ƙi ɗauka baya nan itama ya kirata sau biyu a wayarta ma ba ta ɗauka ba sai hararan wayar take yi tana sakin tsaki ita kaɗai.
Can ba jimawa sai ga saƙon shi.
"Umma Salama."
"Pick the Call."
Ko buɗe sakon ba ta yi ba ta sreen ɗin wayarta ta hango shi kuma ba ta ɗauka ba ko da ya sake kira sau ɗaya daga nan kuma bai ƙara kira ba.
Mami na dawowa ta miƙa mata wayarta ta yi mata ya ce zai kira wayarta su yi magana.
"Yauwa ko ke fa, yanzu maganar kayan gyara za mu yi bari na kira Hajiya Falmata na ji yadda za mu yi"
Da za ta iya da ta ce ma Mami kar ta ba kanta wahala. Ita ta daina yi ma namiji wannan rawan jikin duk ba yan goyo ba ne halin su saya. Nan jaririn Hamma Lamiɗo ne a cikinta wajen haihuwansa ta kusa mutuwa amma bai damu da ita ba har a yanayin yake cewa zai sake ta maza yan kutumar uba ne, ta yadda da maganar hausawa da suke cewa namiji ƙañin ajali. Namiji hankaka gabansa fari bayansa baki, namiji dafin shi ya fi dafin kunama namiji kuma ba ɗan goyo ba ne.
Received at 11:37Reactions: ❤ 7, 👎 1, 👏 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Lokacin da ta auri Habib tana ganin za ta goya namiji, sai ga shi da ta goyasa ga tozarcin da ya biyo baya, a lokacin tana ganin ta gama bama wani namiji yarda amma Hamma Lamiɗo ya mantar da ita wannan har take ganin namiji ɗan goyo ne sai da ya yi mata wannan abin ta fahimci shegu duk halin su ɗaya ta ɗauko ko a cikin maye ba zai iya cewa zai sake ta ba. Kalamansa sun munana a wajenta, tunda kuma ya furta an ce magana zarar buni ce ta fita ba halin ta koma. Tunda maganar nan ta fito daga bakinsa shike nan take ganin baƙin sa.
Tana jin Mami ta kira Hajiya Falmata suka gama magana.
Tana faɗa mata za ta siya mata babban package na maganin sanyi, da na haɗin maijgo a wajen Surayya Halin yau 080322773332
Bojuwa zuwa jibi sako zai iso ta fara amfani da shi kafin su koma Lagos, ta cinye kaza da ciccibinta anan da kayan sanyi, na garin kuma ta tafi da su.
Ta amsa da to kawai, amma a zuciyarta ta ce ba za ta ci ba ko da an kawo. Domin ita a yadda take jin zuciyarta ba za ta iya yin wani abu da sunan wani gyara ba. Lafiyanta take nema da tunanin ma za ta sake ɗaukan cikin? Ko kuma a wannan karon za ta haihuwa lafiya?ga shi dai an yankata sau biyu a waje ɗaya bawa bai isa ya guje ma kaddaransa ba.
Tana tunanin haka sai wata zuciyar ta ce kin manta kin ce ba za ki koma ba? Sai