Showing 51001 words to 54000 words out of 118398 words
shinshina ƙasar har tana sauke ajiyar Zuciya.
Nan ta ce Harira ta ɗauko mata leda ta ɗiba ta jika mata shi da ruwa.
"Ba ki dai shiga gida ba ko?
"Ai kin ce kar na shiga ranki ya daɗe. Mutane ne dai na ta kallona sun ga ina ta ɗiban ƙasa."
Ummu Salma ta yi dariya kafin ta ce.
"Ai sai ki ce lalura ce ba da gangan ba ne."
Harira ta amsa da ba su mini magana ba amma mamaki suke yi na me zan yi da ƙasa haka, mai adaidaitan da yakai ni ma ya jirani sai da ya tambaya na ce masa na mai ciki ne ya ce wallahi shima matarsa ƙamshin yashi take so.
"Gwara da kika faɗa masa kar ya ce na asiri ne."
Dukkansu suka yi dariya. Sannan Harira ta tafi kitchen ta ɗauko mata roban gwangwanin madara da ya ƙare ta ce bari kawai a zuba a ciki ta huta da leda
"Kuma fa hakane, to zuba da sauri ki jiƙa mini, wannan kuma ki ɓoye mini a cikin kitchen"
Harira ta aiwatar da duka umarninta.
Lokacin da ta kai hancinta tana shaƙan kamshin har jikinta sai da ta ji ya samu natsuwa cikinta kuma ta ji kamar ya juya.
Shike nan ta samu zaman lafiya Hamma Saddam kuma sai wajen sha biyu da rabi ya kira ta haushi ya sa ba ta ɗaga wayarsa ba. Ba amfanin da zai yi mata kuma a yanzu ga ƙasarta a hannunta tana shinshina kamar wata mage.
Sallar azahar ya sa ta bar falo ta koma ciki ta yi salla. Ta kwanta tana ta barci saboda likita ya ce ta dinga samun barci sosai wajen uku na rana yunwa ya tashe ta, ta je kitchen ta nemo sauran tuwonta tun na shekaranjiya da Harira ta yi mata da miyar kuka ta ciro a firiza ta kunna gas ta ɗumama miyar ba manja ba maggi dunƙule sai gishiri shima kaɗan sai farin maggi, ba ta son ko wani ƙamshi.
Kodayaushe ta zo kunna gas sai ta tuna da wani abu ya faru farkon dawowarsu kawai ta shigo kitchen ta rasa abin da za ta yi, kawai sai ta kunna gas ta ɗora tukunya ta manta kawai ta koma ɗaki ta kwanta, Allah ya taimaka Harira ta zo kitchen ɗin ta ji ƙauri, da sauri ta kashe gas ɗin ta sauke tukunyar har ta fara ƙonewa da Harira ke faɗa mata shuru kawai ta yi ba ta san ta yi ba
Received at 07:54Reactions: ❤ 15, 👍 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
abubuwa suna yi mata wani irin tun bayan abin da ya same ta na rasa jarirnta, sannan tana zaune kawai sai ta dinga jin wani ƙara a cikin kanta, ƙaran mai yawa yana barazanar fasa kunnuwanta, chanje-chanje da dama take fuskata da ta koma asibiti ta yi musu bayanin likitan ya ba ta tabbacin alamomin cutar Eclampsia da ta yi fama da shi ne lokacin da ta haihu, amma ta gode ma Allah ta fita daga haɗari suma canje canje a hankali za ta daina fuskartarsu. Kullum ta yi salla sai ta yi ma Allah godiya da ya tsare ta da wannan cutar, domin tana da haɗari itama za ta iya ba da labarin haɗarin ta.
A kitchen ɗin ta ci tuwon nan ta wanke hannunta sannan ta koma ɗaki Harira na cikin ɗakinta wataƙila ta kwanta ne. Da ta koma ɗaki ba ta kwanta ba sai ta fara gyara kayanta wajen kwana huɗu kenan mai wanki ya kawo su da sauran ƙananun da Harira ta wanke mata ita kuma ta ce ta bar mata za ta gyara su amma ta kasa.
Sai da ta gama tas ta jera a wardrope sannan ta shiga tiolet ta yi wanka ta ɗauro alwala ta fito ba shafa mai take yi ba doguwar rigarta kawai ta material ta saka akwai tattara ta ƙasa sai aka sake ta. Akwai zanen baƙi a cikin material ɗin sai ta saka hula baka ta rufe kitsonta da ya tsufa.
Falo ta fito ta zauna a saman kujera tana canza tasha zuwa Saira movies ta ga suna maimaicin shirin gidan Sarauta.
Ba daɗewa sai ga Harira ta fito, tana tambayan abin da za a dafa.
"Harira ni fa ba cin abincin nan zan yi ba kullum sai kin tambaya ne?
Harira ta sunkuyar da kai ba ta yi magana ba.
"Ki je ki dafa duk abin da kike so Harira nan fa gidanmu ne."
"To ranki ya dade"
Har ta wuce sai ta dawo.
"Ba za a yi miki wani abu ba?
"Tuwo ne kuma ina ɗan da sauran shi, bari da safe sai ki yi mini wani"
Harira ta wuce kitchen tana faɗin Allah ya kaimu.
Ta bar Ummu Salma na kallo. Ta mayar da hankalinta kan kallo amma ba ta jin nishaɗin da take ji a da in tana kallo gata nan dai zaune kawai.
Adaidai lokacin da agogon bangon dake falo ya harba 4:30pm na yamma daidai ta ji ana buga ƙofa an yi knooking na farko ba ta tashi ba, ta ɗauka ma Saddam ne har tana tura baki.
To tun ɗazu ta so zuwansa bai zo ba sai yanzu.
Ta ji daɗin zaman kamar kar ta tashi sannan ga Harira na kitchen akwai ba da wahala ta ce ta baro kitchen ta zo ta buɗe ƙofa.
Sai biyu aka yi knooking sannan ta iya miƙewa ta isa ga ƙofar ta buɗe
Tana buɗe ƙofar ta juya ko kallon wanda ke tsaye ma ba ta yi ba.
"Sai yanzu? Ai Sai ɗan cikina ya bare da na tsaya jiran ka."
Ta faɗa tana komawa ta zauna a in da ta tashi.
Abin da ya ba ta mamaki jin shuru ba ta ji motsi ko surutun Hamma Saddam ba, shi da tun kafin ya shigo ake fara jin karaɗinsa.
Sai ta juya a hankali wanda ta yi arba da shi ne ya sa gudun zuciyarta tsayawa na wani lokaci.
Kasala da wani irin sanyi ya lulluɓeta a lokaci ɗaya nauyin jikinta sai ya ƙaru.
Ya shigo falon sannan ya saka hannu rufe ƙofar falon
Lokacin da ya fara takowa a tsakiyar falon ƙirjinta ya fara bugawa fat! Fat!
Ta kafe shi da idanuwana ba kiftawa shima ita yake kallo da yanayin kallon nan na shi mai sanyata kasala.
*Janafty*
Received at 07:54Reactions: ❤ 19, 🥰 1, 😁 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Duk takun zai yi domin matsowa zuwa gareta, tare yake da tsinkewar zuciyarta. Ita ta fara ɗauke idanuwanta a kan shi domin ba za ta iya juran kallon shi ba tana jin wani iri kaifaffun idanuwansa da kuma ƙwarjinsa sun cika falon ga ƙofofin hancinta na shaƙo mata sanyayyan ƙamshin shi wanda a baya yake sanyata cikin shauƙi da soyayya amma yau zuciyarta ne ta fara tsinkewa tana jin kamar za ta yi amai tunda ya shigo falon ƙamshin gabaɗaya ya gauraye falon.
Kanta na ƙasa tana wasa da zoben azurfan da Mai martaba ya yi mata kyautar shi tana jin a jikinta da zuciyanta Hamma Lamiɗo bai daina kallonta ba sannan yana ƙara kusantowa zuwa gare ta ne.
Jikinta har rawa ya fara saboda fargaba, duk da ta daɗe tana shirya maganganun da za ta kare kanta duk ranar da Hamma ya waiwayota amma kuma ganin shi a gabanta bagatatan ya wargaje duka shirinta, ta kasa ko iya kallon shi ta kasa miƙewa saboda yadda jikinta ya yi mata nauyi.
"Ummu Salama."
Ta ji ya kira sunanta a hankali da wannan muryan na shi cikin amo.
Sai idanuwanta suka cika da ƙwalla ta yi kewar kiran sunanta da yake yi shi kaɗai ne ke kiranta da Ummu Salama. Ta ɗago suka sake haɗa idanuwana wannan karon har ya ƙariso gabda yana tsaye hannunsa guda ɗaya a cikin aljihun bakin yadin dake jikinsa ɗinkin riga da wando har da babban riga. Amma babban rigan tana hannun shi na dama, kafafuna sanye da budaɗɗen takalmi na fata baƙi kansa kuma ya saka baƙar hula gashin sa ya fito ta gefe da gefen hulan sannan fuskarsa ta yi fayau tunda ya rage gashin gemu sa da sajensa gabaɗaya.
Kallon shi take yi tana ji kamar ba Hamma Lamiɗon da ta sani a shekara ɗaya da wani abu baya ba. Kamar Hamma Lamiɗo da ta sani dai a shekarun baya ne. Ta kasa iya motsi ballatana ta iya amsa kiran sunanta da ya yi ko ta yi masa sannu da zuwa ba komai ya ƙwace mata kanta ta mayar ƙasa tana jin tafin kafafunta na ɗaukan ɗumi sosai. Wattani biyu ta yi ba ta gan shi ba amma ji take yi kamar shekara ce.
Shi ko kallonta yake yi da dukkan zuciyarsa. Me ya same ta? Ya ga ta rame wuyanta sun faɗa idanuwanta sun ƙanƙance komai na ta ya sauya ba kamar yadda ya tafi ya barta ba.
Wani abu ne ya faru da ita ne?
"What wrong with you?
"Are you sick?
Tambayoyin duk a tare ya jera mata su, ita kuma lokacin zuciyarta ne ke cigaba da tsinkewa tana jin kamar za ta yi amai shi ya sa ta miƙe dakyar tana jin kamar jikinta ya yi ma kafafunta nauyi.
"Sannu da zuwa."
Ta faɗa cikin sanyin murya amma ta ki bari su sake haɗa ido.
Ya amsa da yauwa a iya fatar bakinsa.
"Na ce ba ki da lafiya ne?
Ya sake tambaya yana mai ƙureta da idanuwansa.
Yana jin wani irin zafi a cikin zuciyarsa? Me ya sa ba a faɗa masa ba? Kuma dalilin da ya sa ya ke turo Abdullahi kenan amma sai ya ba shi tabbacin lafiyanta lau, me ya sa ta rame? Gabaɗaya ta sauya masa ta yi baƙi kamar ba Ummu Salama ba.
"I'm asking you. Ba ki da lafiya ne?
Ya sake maimata tambayar wannan karon muryansa ta ɗan buɗe.
Ba ta so hawayen da suka kawo mata su zubo, hancinta kuma ya gaji da shaƙar iskar ƙamshin turarensa zuciyanta na yunƙurin amai kawai sai ta juya baya daidai lokacin da hawayen suka taho mata.
"Lafiya ta ƙalau Hamma."
Ta amsa shi da raunin murya kafin ta kwashi sauri tana mai rufe baki zuwa ɗakinta amai ne ya taho mata take saurin isa tiolet kafin ta sake shi anan shi kuma tunanin shi ko ta gudu ne sai ya taka ya bi bayanta. Yau ba gudu ba duk wani rashin fahimta dake tsakaninsu za su warware shi.
Yana shiga ɗakinta ya ji ƙakarin amai a tiolet da sauri ya ajiye rigar hannun shi a saman gado ya buɗe ƙofar tiolet ya shiga tana durjushe a tiolet ɗin tana ta kwarara amai duk tuwon da ta ci ne shi ne take amayarwa daman ya sani ba ta da lafiya yana ganinta ya fahimci haka kamar ba jini a jikinta.
Bai damu da kar ta ɓata shi ba, bai damu da warin amai ba, haka ya shiga tiolet ɗin ya riƙeta lokaci ɗaya yana rankwafawa yana yi mata sannu.
Received at 17:28
8 people reacted with ❤
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta ba shi tausayi yadda take amai, kamar hanjin cikinta zai zazzage daga ƙarshe ma sai ruwa kawai ke fitowa, shi bai san shi ne ciwon ta ba ƙamshin jikinsa da take shaƙa shi ke ƙara saka mata hararwa ta rasa kuma yadda za ta yi masa bayani ya fahimta.
Jikinta sai rawa yake yi, tana mayar da numfashi sama sama in ta yunƙura ta yi aman ba ya zuwa sai wahala take sha, shi kuma yana ta faman yi mata sannu.
Ta jingina da bango tana mayar da numfashi.
"Sannu."
Ya faɗa yanan mikewa tsaye.
"Ki tashi ki wanke jikin ki, mu je asibiti."
Ta kalleshi hawaye suka kece mata a saman fuskarta.
"Hamma."
Ta kira shi cikin raunin murya.
"Na'am."
Ya amsa yana kiran nata na ratsa duka jikinsa da zuciyarsa
"Ciwo na yanzu ba shi da magani."
Ta faɗa tana yi masa mirmishi. Ji take yi kamar za ta yi amai amma ba komai a cikinta ba ta son ƙamshin nan tana so ta ce ya fita ta kasa.
"What? Akwai ciwon da ba shi da magani ne?
"Akwai."
Sai kawai ya zura mata idanuwana yana kallonta kirjinsa na duka, ta ga fargaba da tsoro a kallon da yake yi mata.
"Hamma."
Ta sauke numfashi.
"Ka je waje, zan yi wanka ne."
Ta gama faɗa tana yunƙurawa kamar wani aman zai fito amma kuma babu komai.
Ya kalleta sai ta gyaɗa masa kai shi kuma sai ya fara nannaɗe hannun rigan shi wai zai taimaka mata ta gyara jikinta.
"Aa."
"Zan iya da kaina."
Ganin kamar ba ta so sai ya ƙyaleta ya fito ya janyo mata kofa, yana fita ta rarrafa ta yi floshing ɗin aman da ta yi ya wuce rigar jikinta ma duk ta ɓaci da amai cire kayan da ta yi ta watsa ma jikinta ruwan sanyi.
Ta fito ɗaure da towel har lokacin yana ɗakin zaune bakin gado yana jiranta. Bedroom din na ta ma ya gauraye da ƙamshin sa
Da hanzari ya taso ya nufe ta, sai ta yi baya da sauri tana toshe hanci wallahi kamar za ta mutu haka take ji shi kuma mamaki ya sa kawai ya tsaya yana kallonta ya kasa magana.
Dube-dube take yi ina ta baro ƙasanta shi kawai za ta shaka ta zauna lafiya. Sai ta tuna yana falo da gudu ta fita shima sai ya bi bayanta yana tunanin ko bayan baya nan aljanu sun shafeta ne
Ya tsaya kawai yana kallonta ganin ta ɗauko gwangwanin madara ta buɗe ta kafa kai tana shaƙa har wani lumshe idanuwa take yi. Ya ɗauka ma madaran ne a ciki take so ta sha har hankalinsa ya kwanta amma sai ya lura koma mene shaƙan shi take yi ba sha za ta yi ba
Ita ba ma ta shi take yi ba shakan ƙamshin ƙasan take yi kamar da zuciyarta. Har wani daɗi daɗi take ji.
Harira ce ta fito daga kitchen sai ta yi kiciɓis da Yarima ta yi ƙasa da sauri tana yi masa sannu da zuwa
Ya juya ya kalleta sau ɗaya ya amsa.
Ya koma ya kalli Ummu Salama ya fara tunanin akwai abin da ke faruwa da ita wanda shi bai sani ba.
Kamar zai tambayi Harira sai kuma ya fasa itama ta tashi ta koma kitchen ƙarisawa ya yi kusa da Ummu Salma ba ta ma sani sai ganin kan shi kawai ta yi ya leka gwangwanin hannun ta.
"Ƙasa.?
Ya faɗa a saman leɓen shi cikin mamaki. Ita kuma matsowan shi kusa da ita yasa ta yi tsalle ta koma gefe har towel ɗin jikinta na neman faɗuwa ta tare shi da hannu ɗaya.
"Hamma."
"Ka tsaya anan"
Idanuwansa a kanta innalillahi tabbas wani abu ya same ta wanda bai sani ba. Me ta ke yi da ƙasa kuma? Ko Depression ne ya kamata ko wani cuta a ƙwakwalwarta amma in ba haka ba me ya sa za ta yi ta shinshinar ƙasa sannan ta hana shi ya matso kusa da ita.
Tausayin ta ya lulluɓeta koma mene ne ya faru duk shi ne sila da ace tana tare da shi da ba ta samu wannan laluran ba.
Ya yi tsaye kawai yana ganin ta tana ta shinshinar ƙasa.
"Me kike yi haka?
"Kasa ne fa"
Ya faɗa muryansa na yin ƙasa.
"Ina so ne."
Ta amsa mishi, sannan ta kalle shi tana yi masa mirmishi.
"Come here."
Ya faɗa yana ya fito ta da hannunsa guda ɗaya.
"Hamma."
"Ƙamshin turarankaa ne ke saka ni amai da tashin zuciya."
Ya sake yin sakayau kawai yana kallonta.
Ya kasa gane abin da ke faruwa.
"Meke damun ki?
"Ciki gare ni."
Ta ba shi amsa kai tsaye sannan ta bi ta bayan kujera ta wuce.
"Ka jira ni anan."
Received at 17:28
15 people reacted with ❤
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ba ta so ya biyo ta ɗakin, kamar daman umarninta yake bi ya yi tsaye yana kallonta har ta shige ɗakin, shi ba ma wannan ba sai ya ji kamar da ya tambayeta abin da ke damunta ta ce ciki gare ta amma sai wata zuciyar ke tunanin bai ji daidai ba ne
Yana nan tsaye ta fito ɗauke da wata farar takarda a ninke ta zo ta ajiye a saman kujera.
"Hamma ka yi hakuri ka duba wannan sai mu yi magana."
Tana gama faɗin haka ta koma ɗaki sai da ta bubbuɗe window amma duk da haka ƙamshin na nan Allah yasa ga kasarta a gefe tana ta shaƙa shi ne ya saukaka mata.
Shi ko takardan ya ƙarisa ya ɗauka tsoro har ya bayyana a saman fuskar shi.
Yana buɗewa ya bi rubutun dake ciki daki daki kafin ya gama karantawa ya ji hannunsa na rawa
Ummu Salama tana da ciki, ashe abin da ya ji ta faɗa gaskiya ne. Date ɗin ya duba tun tafiyar shi ne ba daɗewa. Ko bai yi lissafi ba ya san ranar da suka samu matsalan nan ne ashe akwai rabo mai nauyi a tsakaninsu idanuwansa suka ƙankance da hanzari ya shiga ɗakin nata har ta saka kaya doguwar rigar Abaya.
"Why?
Ta juya tana kallon shi.
"Me ya sa ba ki faɗa mini ba?
"Ba wanda ya faɗa mini kina da ciki Umma Salama."
Ya gama faɗa kamar zai yi kuka. Ba ta yi tsammani ba kawai sai ganin shi ta yi a gabanta tana kallon shi da idanuwanta masu ruwan hawaye.
"A ina zan faɗa maka?
"Ka rufe ni ko na kira ka bana samun ka."
Ta gama faɗa hawayen na kece mata da kuka.
Sai kawai ya rumgumota a cikin jikinsa ƙamƙam tare da takardan a hannunsa kamar tana jira ta saki kukanta mai sauti wannan kukan da kewar wattani biyun da ba ta samu kafaɗan da za ta yi kuka ba, yau shi take yi duk da ƙamshin turaransa na tsinke mata zuciya ba ta damu ba, tana bukatar kafaɗan da za ta yi kuka a lallasheta.
"Hamma.."
"Ka yi hakuri."
"Shii."
Ya faɗa yana ɗan bubbuga bayanta alaman lallashi ita kuma tana ƙara shigewa jikinsa tana rirrikeshi lokaci ɗaya tana kuka.
"Na yi kewarka, na yi kukan rashin ka."
"Wallahi na yi nadaman kalaman da na faɗa maka tun a ranar."
"Na yi nadama."
Take faɗa tana gunjin kuka.
"Is Ok."
"I'm Sorry."
"Na barki ke kaɗai. Am sorry bana tare dake a lokacin da kike buƙata ta."
"I'm Sorry Ummu Salama. I'm sorry."
Shima yake faɗa kamar ya yi kukan haka yake ji, Ummu Salma ta yi ta kuka kukan dake fitowa daga ƙarkashin zuciyanta bai hanata ba ya barta ta yi kukanta har sai kukan ya dawo shessheƙa.
Ya ɗago fuskarta yana share mata hawaye da gefen hannun rigansa.
"I'm sorry."
Ya sake faɗa, ta ƙamƙame hannuwan shi.
"Hamma."
"Yes"
"Ka yafe mini."
"Komai ya wuce Umma Salama."
"Ka yafe mini?
"Na daɗe da yafe miki."
Ya faɗa yana kallon cikin idanuwanta. Wasu hawayen suka sake kece mata.
"Shi ne ba ka nemi ni ba! Ba