Showing 18001 words to 21000 words out of 118398 words

Chapter 7 - Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel

07 Aug 2026

206

za su gina mata jiki sannan ta dinga motsa jikinta sannan wannan haihuwar ta ɗan ajiye tumbi ba kamar na Hanan ba.

Ita ba ta wannan take ba, jikinta ko wani gayun duniya ba ya gabanta yanzu
Received at 10:01Reactions: ❤ 6, 👍 3
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
In ta tuna yau Baffa a duniyar nan sai ta ji ta rasa meke yi mata daɗi, sai da ta dawo gida aka ba ta wayarta.
A status ta ga Hamma Saddam ya saka hoton jaririnta ta yi saving a ɓoye ta ɗauka tana kallo tana kuka haka ma hoton Baffa gani take yi kamar zai dawo gani take yi kamar a mafarki.
Kwata kwata ba ta cikin natsuwarta amma dai tana bin shawaran likita tana kokarin yaki da abin da ke damunta amma dafin da radaɗin rashin Baffa wani abu ne da har ta koma ga Allah ba zai taɓa gushewa ba.

Baffa mutum ne na gari ba domin yana matsayin uba gare ta, ta tuna ranar da ya rasu Hamma Jibo na tambayan ko ana bin shi bashi, tunda ana so kafin akai mamaci makawancinsa a biya masa bashi ko ya yi kwanciyar kabari cikin salama nan take Hamma Abdullahi ya ce Baffa ba ya cin bashi, tunda tare suke kasuwanci ya ce sai dai shi Baffan ne ke bin mutane bashi.

*

Ranar da Baffa yake da kwana da ashirin da biyu da rasuwa Umma A'i da Baffa Umaru suka koma Mubi, aka bar Umma Balki tare da Ammah sai Mami da matan su Hamma Jibo.
Suna nan ba su koma ba, kowa ba ya son tafiya duk da duk sun koma bakin aiki amma suna tunanin acikin satin nan duk za su koma suna ma ta shiri ne.

Lamiɗo ne kawai bai koma aiki ba yana ma shirin tafiya Daura ne. Mai martaba zai koma London ganin likita cikin satin nan.
Mami ma tana nan ba ta ma saka rana ba, itama ba ta son tafiya duk dare haka suke taruwa suna tunawa da Baffa suna kuka, wato mutuwar Baffa rami ne a zukatansu da ba zai taɓa cikewa ba.
Ga Ummin ikki da itama koda yaushe a gidan take yini. Baɗɗo kuma nan wajen Umma Salma ta tare saboda ta ɗebe mata kewa
Duk ba wani hira suke yi ba.
Amma mutum rahama ne.

Ammah ko har yau ba wanda ya ga kukanta kuma ta na nan tsaye kan kafafunta.
Daman Umma Balki ta sha cewa Ammah jaruma ce sai da rasuwar Baffa kowa ya ga tabbaci ko kuka ake yi yanzu za ta fara faɗa da cewa su daina yi ma Baffa kuka addu'a kawai take roƙo su yi masa kodayaushe tana cikin hijabi da casbaha tana cikin ibada da nema ma Baffa gafaran Ubangijinsa kowa jinjina ma dauriyarta yake yi ta yi jarumta matuƙa.

Washegari kuma aka ce za a je maƙabarta ayi ma Baffa addu'a. Baffa Kabiru da Baffa Mustpaha gobe za su koma gidajen su.
Hamma Lamiɗo ma a goben zai bi jirgi zuwa Katsina.
Mami kuma ta ce sai sati na sama Daddy zai zo sai su koma. Hamma Jibo kuma ya ce sai karshen sati za su koma Abuja.

Za a tafi gabaɗaya ne har da Mami da Ummu Salma duka gidan ma gabaɗaya.
Bayan la'asar suka tafi Ummu Salma ma motar Hamma Jibo ta shiga Hamma Lamido kuma motar Amininsa.
Sauran kuma suka shisshiga ta su Hamma Abdullahi.
Harira kawai aka bari a gida sai Islam da yara. Har da su Adda Nauwara aka je maƙabartan.

Maƙabatar ba nisa shi yasa suka isa da wuri.
Sun yi magana da maigadin wajen tunda ana ziyara addini ya hallata amma ba wai mutum ya samu wajen zuwa a kodayaushe ba.
Sunna ta yarje ma iyalan wanda ya rasu su ziyarce su domin su yi musu addu'a amma ba wai a mayar da abin kamar ibada ba.

Alaman da suka sanya yana nan amma zuwa lokacin nan Baffa sun yi nisa a makabarta. Kafin shigarsu Hamma Jibo ya ce kowa ya yi addu'an da muka sani a cikin azkar na shiga makabarta.
Kowa ya yi sannan daman suka shiga, a gaban kabarin Baffa Ammah ta dafa kasar tana yi ma Baffa addua'a.
Sai a lokacin ta yi kuka hawayenta na ɗiga a saman hannunta da kasar kabarin Baffa.

"Allah ya jiƙan ka Baffa. Haƙurin da ka ba ni kafin rasuwarka na yi, ban yi kuka ba. Na gode Baffa Ubangiji ya sanya kabarinka cikin salama Allah ya yalwata maka hasken shi. Mun yi kewarka Allah ya sada ka da rahamarsa."

Sai a lokacin ta fashe da kuka Ummin ikki ta rumgumeta gefe tana lallashinta. Amma da Ummu Salma da su Mami suka fara kuka sai ta fara musu faɗan ba ta so. Hamma Abdullahi kuka Saddam kuka haka ma Abdulrahim
Ummu Salma kam sai da Lamiɗo ya rumgumeta yana ta lallashi kuka har yana sauti.
Received at 10:01Reactions: ❤ 11, 👍 2
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Sai da kowa ya yi masa addu'a sannan suka bar wajen kamar kar su tafi kamar su ga Baffa ya fito daga kabarin sun tafi gida tare da shi. In da aka binne jaririn Ummu Salma ne ya ɓace ba su gane wajen ba.
Shi ya sa ba su daɗe ba suka bar makabarta.
Suka duba hagu da dama, gabas da yamma maƙabarta babba ce amma ta yi rabi da mutane.

Jama'a mu dinga ziyartan maƙabararta za mu kara imani da tsoron Allah, za ka ga fa cewa kai ma wata rana nan ɗin ne gidan ka na gaskiya. Duk tarin arzikinka nan ne karshen ka, Sarki ma anan za a san ya shi haka ma Gwamna haka ma attajiri , haka ma talaka nan ɗin ne dai shine ƙarshe, za mu ƙara imani za mu ƙara jin cewa mu shirya ma muttuwa ko yau ko gobe ko anjuma tana tare damu.

Ubangiji ya sa mu yi kyakyawan ƙarshe. Allah ya sa mu mutu cikin imani.
Amin.

Sun koma gida kuma sai mutuwa ta dawo sabuwa
Suka haɗu suna ta kuka.
Ammah tana ta faɗan ita ba ta son kukan nan.

"Abdulrahim har da kai? Kai da za ka zama namiji mai lallashi "

Umma Balki ke magana ganin har da shi cikin masu kuka. Mami kuma ɗakin Ammah ta shige tana ta kukanta.
Haka ma Ummu Salma Baɗɗo na tare da ita.
Mazan ne ke zaune a falo masu dauriyan daman su Hamma Kabiru ne da Hamma Lamiɗo da su Hamma Abdulrrahaman.
Ammah dai yau ta yi kukan hawaye shaɓe shaɓe amma a hakan take ce ma wasu su daina kuka.

Hamma Jibo na maganar bayan sallar isha'i za su zauna gabaɗaya su tattauna kafin tafiyar su.
Suna cikin wannan maganar
Sai ga sallaman baki mata.
Mata huɗu ne, ɗaya tsohuwa ce ɗaya kuma ba yarinya ba ce sai yaran mata biyu.
Suna shigowa mazan suka tashi suka fita kuma daman bakin sun ce suna da tare da maza ne a waje.

Har baƙin suka zazzauna ana gaisawa Ammah ko su Ummin ikki dake falon ba su gane su ba.

"Hajiya ba ki gane ni ba?

Gwaggo ta faɗa tana kallon Ammah ganin ba ta gane ta ba. Ammah ta kalleta domin ga shi ta san kamar fuskar amma ba za ta iya tunawa ba. Duk da sun haɗu da Gwaggo lokacin da Umma Salma ta yi ɓarin cikinta na farko.

"Ayya Ban gane ki ba wallahi ki yi hakuri ki yi mini bayani."

Ammah ta faɗa murya a sanyaye.

"Daman na yi tunanin haka, duka duka bai fi sau biyu muka ga juna ba"
Gwaggo ta faɗa tana kallon Shamsiya da kanta ke kasa ta kasa ɗago kanta.
Habiba kuma sai kalle kalle take yi tana taɓe baki daga ganinsu dai masu ragwamen gata ne

"Ɗago kan ki Shamsiya."

Gwaggo ta faɗa tana kallon Shamsiya.

"Na san in ni ba ki gane ni ba wataƙila ki gane Shamsiya."

Daidai lokacin Ummin ikki ta ƙura ma Gwaggo idanuwana sai a lokacin ta ganeta.
Ita ta yi jinyar Ummu Salma asibitin a lokacin da ta yi ɓarin cikin Habib sannan wacce ke kusa da Gwaggo ma ta gane ta matar kanin baban Habibu ne, Hajiya Sahura.

Da ɗago kan Shamsiya tare da maganar Ummin ikki da Ammah duk a lokaci ɗaya ne.

"Shamsiya."

Ammah ta kira sunanta cikin mamaki.

"Wa nake gani kamar dangin Habibu."

In ji Ummin ikki.

"Mu ne ashe kin gane mu"

Gwaggo ta faɗa cikin ɗan yake.
Sai aka fara kallon kallo.
Ammah mamaki ya kama ta.
Ummin ikki kuma ta ma kasa magana.

"Wai wani Habibun na ji kuna magana?

"Ba dai wanman yaron tsohon mijin Auta ba? Mara mutumci mara albarka ba, ba dai dangin shi ba ne nan zaune a gaban mu?

Umma Balki ta faɗa tana kallon su Ammah.

"Su ne."

Ummin ikki ta faɗa cikin gatse.

"Me kuma ya kawo su ni Balki?

"Shi muke son sani Umma Balki."

Ummi ikki ta amsa tana kallon Gwaggo da suka kasa magana.

"Lafiya me ke tafe da ku?  Naga tun bayan sakin wulakancin da ɗanku ya yi ma ɗiyarmu alaqar dake tsakanimmu ta yanke me kuma ya kawo ku?

Ummin ikki ta tsare su da tambaya.

"Alheri muka zo da shi Hajiya."

Gwaggo ta faɗa, tana gyara zama.

"Ku tashi ku koma da alherin ku, duk alherin da zai fito daga ɓarayin ku bama so."

Ummin ikki ta faɗa a fusace.

"Aa Hajiya ba za a yi haka. Ku tsaya dai ku saurare mu ku ji da abin da muke tafe."

Hajiya Sahura ta faɗa cikin kwantar da kai daman ta san haka zai faru.
Shi ya sa Alhaji Sheriff ya da ke ba zai zo ba, darajan Gwaggo ne da ita da ta sanya baki ya sa ya amince ya zo Shamsiya kuwa tana ta sharan hawayen kanta a ƙasa.

"Wallahi ba da sharri muka zo ba alheri ne ya kawo mu"
Received at 10:01Reactions: ❤ 12, 👍 2
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta sake faɗa cikin lalama.

"Gaskiya ba za mu saurare ku ba. Ku tashi ku tafi kawai."

Ummin ikki ce ke magana Ammah ta yi shuru kanta na kasa. Gwaggo da Hajiya Sahura na ta rokon a bar su su yi magana.
Dai dai lokacin Baɗɗo ta fito falon daga ɗakin Umma ta zo ɗaukan ruwa.

Ta ga mata a falo a cikin matan ta ga Shamsiya.
Ta razana ta ja baya ta kwalalo idanuwana ta kira sunanta da karfi.

"Shamsiya"

"Baɗɗo."

Ta amsa mata cikin hawaye

"Ke ce?

Baɗɗo ta tambaya saboda ganin kamar ba Shamsiya ba. Fuska duk kuraje ta yi baki ta rame ga wani hijabi a jikinta mai kama da tsumma.
Mami ma maganar Baɗɗo ya fito da ita ganin Baɗɗo tsaye cirko cirko ya sa ta tsaya tana tambaya.

Nan take faɗa mata Shamsiya ce da dangin Habibu domin ta gane har Gwaggo sauran ne ba ta san su ba.

"Wani Habib ɗin?

Mami ta tambaya tana yi musu kallon wulaƙanci.

"Kuma suke zaune anan ba ku fatattake su ba."

Ta gama rufe baki kenan Ummu Salma ta fito daga cikin ɗakin ita ce daman za ta sha ruwan Baɗɗo ta fito ta ɗauko mata sai ta ji shuru, daga baya sai ta ji kamar tashin maganganu a falo.

Lokacin da ta fito ba ta ma lura da mutanen dake falon ba Jikinta da hijabin da suka fita da shi ba ta cire ba kafarta akwai safa.

"Me ya fa.."

Sai ƙarshen maganar ya maƙale daga bakinta.
Lokacin da ta ga waɗanda ke zaune a kasan cafet a falo.
Tana wurga idanuwanta tsakanin Gwaggo da Shamsiya.

Ta ji gabanta ya yanke ya faɗi, wani irin ɗaci da raɗaɗi ya dawo mata sabo.

"Bestie"

Shamsiya ta miƙe tsaye tana kiran Ummu Salma.

"Ummu Salma."

Gwaggo ma ta kira ta a muryanta akwai tausayi.
Har idanuwanta na cikowa da kwalla.
Ummu Salma ta kasa amsawa domin sai ta ji kanta ya sara ƙafafunta na rawa tare da jikinta.

Ta damƙe hannun Baɗɗo kawai ta juya za ta koma ciki
Ba za ta iya ganin su ba, ba ta kaunar ta sake ganin wani abu da ya dangancin Habib har abada.

A lokacin kuma sai ga Hanan ta rugo da gudu Faruk ya biyo ta suna guje guje.
Uwarta ta nufa sai jin ta kawai Umma Salma ta yi akan kafafunta ta rumgumeta.

"Mahma Faruk zai kama ni."

Take faɗa da muryanta na yara shi kuma Faruk na faɗin sai ya rama tsungilinshi ta yi Mami ce ta janye shi gefe.
Jikin Ummu Salma ya fara rawa ba ta san ta juyo ba, sai kuma idanuwam su Gwaggo na kan Hanan suna kallonta itama ganin baki sai ta kura musu idanuwanta na yara har tana dariya.

Tsoron Ummu Salma a yanzu rasa Hanan ba za ta iya jure wannan rashin ba.
Ko ba a faɗa ba duk wanda ya ga Hanan ya ga Habib domin tun a jaririyarta kamar shi ta ɗauko bayan ta fara wayau sai kamanin ma suka sake bayyana.

Da Shamsiya da Gwaggo zuciyarsu na bugawa a lokaci ɗaya suna ƙura ma Hanan ido. Haka ma Habiba da Hajiya Sahura.
Wannan yarinyar jinin Habib ne tabbas Hajiya Sahura ta furta a zuciyarta Habiba kuma haushi ta ji me ya sa Maganar Habib ta tattaba ta?

Jwalla suka ziraro ma Gwaggo ashe da rabon Habib zai ga gudan jininsa.
Hannu ta miƙa ma Hanan tana faɗin" Zo nan y'an mata"
Hanan dake tsaye da jan riga yar kanti a jikinta kanta ba ɗankwali an yi mata kitson shuko.

Kamar ba za ta je ba haka ta nufe Gwaggo tana zuwa ta kamata ta rumgume.
Kowa kuma a falon ya kasa magana ballatan motsi saboda mamaki.

Gwaggo da tsufanta amma hawaye take yi.
Ta ɗago Hanan tana kallonta.

"Ya sunan ki."

"My Name is Hanan."

"Hanan Habib Jimeta"

Gwaggo ta ce magana ta ƙare a zuciyarta
Hannatu Habib wannan jinin Habibu ne.
Shamsiya ta duƙa a gaban Hanan tana kuka tana riƙeta sai Hanan ta turje ganin ba ta san su ba kawai sai ta fara kuka kamar an buga ma Ummu Salma guduma a saman kanta ta dawo hayyacinta ta saki hannun Baɗɗo ta nufe su ta ture shamsiya sai da ta faɗi zaune ta janye Hanan.

"Bestie"

Shamsiya ta kirata cikin kuka.

"Kar ki ƙara kirana da wannan sunan"

Ummu Salma ta faɗa a fusace cikin ƙaraji.
Sanman ta ja Hanan za su koma ciki.

"To ki bar ni na rumgume Hanan"

"Kar ki kuskura, kar ki kuskura ki matso kusa da yata."

"A'a ba su da kunya ne "

Mami ta faɗa tana tafa hannu mamaki duk ya ishe ta.

"Ku fita kawai tun kafin rayukanmu su ɓaci."

A lokacin Hamma Abdullahi ya shigo falon Ammah kamar an jeho shi.
Received at 10:01Reactions: ❤ 12, 👍 2
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Ammah ki ji mini marasa kunyar mutane wai dangin wannan shegen yaron da shi kan shi ne da ya tozarta Ummu Salma sun zo suna mana maganar wai sun zo ba da hakuri duk abin da ɗansu ya yi a lokacin ba su san su ba da haƙuri ba sai yanzu."

Ya faɗa yana huci idanuwansa sun rufe ko ta kan su Gwaggo bai bi ba.

"Na ce a kore su kawai Hamma Jibo ya ce a'a, Ammah wallahi tallahi zan kira musu hukuma."

"Shi Habibun ne ya zo don ba shi da kunya?

Ummin ikki ta tambaya.

"To ai daman an ce in ba ka da kunya ka yi abin da kake so, yana can zaune a koɗe mara mutumcin ba."

"Ku kore su, ga ma sauran nan ku tarkata su bar mana gida."

In ji Mami tana sake tafa hannuwa.
Ummu Salma kuma tun da ta ji an ce har da Habib sai da ta tsaya cak ta kasa gaba ta kasa baya.

"Nima dai ban ga amfanin zuwan su ba, tun a lokacin ba su zo ba sai yanzu."

Umma Balki ta faɗa.

"A'a ku ƙyale su."

Sai a lokacin Ammah ta yi magana gabaɗaya suka kalleta

"Ku ƙyale su. Ku shigo da su nan a yi maganar."

"Su shigo fa kika ce Ammah?

Hamma Abdullahi ya tambaya.

Ta gyaɗa kanta cikin tabbatarwa.

"Haka na ce, kuma ko Baffa na raye shima haka zai ce"

Jin sunan Baffa ya sa kowa jikinsa ya yi sanyi.

"Wasiyar Baffa ne, a daran da zai rasu tare da ni da su Saddam ya faɗa mana in sun zo mu saurare su in sun nemi gafara mu yi musu afuwa."

Tunda ta ce wasiyar Baffa ne ba wanda ya kara magana
Ummu Salma ta ja Hanan suka shige ciki Baɗɗo ta bi bayanta.
Haushi take ji, me ya sa Ammah za ta ta ce a saurare su ta sha roƙon Allah kar ya sake haɗa ta da Habib ko Shamsiya.

Ba ta ƙaunar su san ma abin da ta haifa balle ya zama yana da alaƙaa da su.
Sai ga shi komai ya kwaɓe mata. Ba ta jin za ta iya yafe ma Habib da Shamsiya sun cutar da ita.

Kulle ɗaki ta yi saboda Hanan na so ta fita.
Ummu Salma kuka kawai take yi komai ya dawo mata sabo. Baɗɗo kuma mamaki kawai take yi na ganin Shamsiya a haka.

"Tab rayuwa Sisna kin ga yadda Shamsiya ta koma?"

Tana jin ta ba ta yi magana ba. Ba wannan ba ne a gabanta ita haɗuwa da su ne ba ta so.
Fargabanta ma Hanan ne, za ta iya yin komai domin Hanan ba ta kasance tare da su ba har abada.



*Janafty*
Received at 10:01Reactions: ❤ 16, 👍 2, 🥰 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
*FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.*
08032773332
09069067488.

Tunda har Ammah ta ce su shigo a ba su dama sannan a saurare su ba wanda zai yi musu da ita. Ko lokacin Baffa na raye ba ya musa ma umarnin Ammah balle kuma yau da ba ya raye maganar Ammah tana saman na kowa duk abin da ta ce shi za a yi. Balle kuma ta ce wasiyar Baffa ne.

Hamma Abdullahi ya mayar da fusatar shi ya fita can haraba in da su Hamma Jibo ke tare da su Alhaji Sharif ya ɗan duka ta wajen kunnensa yana faɗa masa saƙon Ammah.
Shi daman Hamma Jibo ɗan sauki ne ya ce a saurare su.

Hamma Abdullahi ne da Hamma Abdulrahaman sune ke ta bala'i Allah ya sa ma tun a farko ba su gane su ba da ko gaisuwan da suka yi musu ba za su amsa ba.
Su uku ne daga Alhaji Sherif sai Baba Usman sai Habib ɗin da yake ta raɓe raɓe yadda rayuwa ta mayar da shi ne da kuma daman ba wani sanin shi suka yi ba shi ya sa ba su gane shi ba gwara ma Saddam shi ya je gidan Ummu Salma ba adadi sun sha haɗuwa da Habib ɗin amma shi da farko bai gane shi ba sai daga baya ya fara masa kallon sani.

Hamma Jibo kuma ya so ya gane Alhaji Sherif tunda sun taɓa zuwa da Baffa a wancan lokacin amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login