Showing 102001 words to 105000 words out of 118398 words
kwanaki ta yi ɓarin shi, har tausayi take ba ma Ummu Salma, ga wahalan rayuwa tana tunanin in dai ta buɗe foundation ɗin ta, Shamsiya za ta shiga cikin waɗanda za ta fara tallafamawa, sannan ta roƙeta yan ajinsu na makaranta suna ta tambayan lambarta tana neman izinin ta tura musu? Ummu Salma kuma ta ce ta ba su ba komai ikon Allah kenan yanzu tunda ta zama matar Sarki kowa neman ta yake yi an mayar da ita group na makaranta girmamata suke yi ranki ya daɗe sama da ƙasa ba mai kiran sunanta ko kuma su ce Sarauniyar Daurama.
Ita dai sama sama, duk wanda ya kira ta za su gaisa amma tun daga kan Shamsiya ta daina aminci da yarda da ko wata ƙawa.
Received at 19:42
8 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Tana da Baɗɗo ba ta neman kowa a halin yanzu, amma in abu ya faru na buƙatar taimako tana taimakawa iya ƙarfinta ko kwanaki wata class mate ɗinsu ta samu hatsari za a yi mata aiki a kugu ana neman dubu ɗari takwas, mijin ba shi da karfi ana neman taimako ta yi ma Mai martaba mgana ya ba ta kuɗi ta tura musu dubu 1M mazan su da matansu haka suke yi mata godiya. Sannan sun ce suna so su shirya haɗuwa na mates ɗin su, ta ce su shirya ba sai sun jira ta ba, ƙarshen shekara aka ce ta ce lokacin suna Abuja bikin Saleem amma daga can za ta zo Adamawa.
Saleem zai auri ƴar sarkin zazzau ne kuma a garin Abuja za a yi duka bikin angon ma a can za su zauna tunda anan yake aiki.
Sagir ne ma ya dawo garin amma ya koma ya ce sai ya haɗo Phd ɗinsa Yazeed kuma yana masters ne. Mai martaba mai murabus kuma ya samu lafiya da kwanciyar hankali ya dawo yana gida yana hutawa.
Ummu Salma su ta riƙe a matsayin iyayen ɗakinta duk sati tana hanyar zuwa, da abinci domin Mai martaba mai murabus har jiran girkinta yake yi Lamiɗo ya faɗa masa abin da take so kenan harkan girke girke Mai martaba ya ce za a buɗe mata har gidan abincin in dai tana so tana ta godiya. Burinta ya kusa cika ta kai in da take so ta shahara, ta samu ƙwarewa daga mabambamta makarantu na online sun fi biyar sannan ta zo ta yi online class na mutane ɗari sannan bayan an gama ta raba musu dubu hamsin hamsin ta ce su je su ja jari ko wacce ta je ta kafa abin da ta iya.
Wannan dalilin ya sa ta yi suna sosai kaf arewa a cikin masu girke girke za ka ji ana zencen Sarauniyar Dauramas Kitchen, cikin ƙanƙanin lokacin sunanta da komai na ta ya tafi viral tuni mutane sun fara yarda matar Sarkin Daura ce wasu har sun lalubo hotunanta ana yawo da shi, yanzu social medi ba tsaro in suka taso ka gaba sai Allah.
In da ta gode ma Allah ba ta samu ciki ba ga shi har Banafsha na shirin shekara har ta fara tafiya ba in da ba ta zuwa. Shi yasa sai komai ya zo mata da sauki Baɗɗo ce kamar P.A ɗinta Mami kuma mai ba ta shawarwari ita da Hamma Saddam kuma tana jin daɗin haka sosai.
Har sun fara maganar foundation da Hamma Abdulrahaman ya ce zai haɗa ta da wata Barrister Salamatu Doma, a nan Abuja take tana aiki da suprime court Abuja, itama suna da wata foundation da take jagoranta za ta taimaka mata sosai. Yanzu sun ajiye mganar in suka je Abuja bikin Saleem za ta je har gida ta samu Barrister Salamatu Doman su yi magana.
A karshen watan november Baɗɗo ta haifi ɗa Namiji ya ci sunan Baffa, suna kiran shi Junior.
Ummu Salma ta zo suna, Bilkisu lokacin ba ta nan ta je Canada hallatar wani Seminar na su na likitoci. Da za ta koma da Islam ta koma ta gama jarabawar fita babban sakandiri kafin sabuwar shekara za ta fara jami'ar a Kasu dake Kaduna in da Mami ke aiki.
Tana komawa Daura ta fara zazzabin dare sai amai ana duba ta sai ga ciki har ya yi wattani uku ma ba ta san da shi ba. Duk da tana jin canje-canje a jikinta.
Ta ji daɗi amma ba ta ji ba saboda cikin zai yi mata cikas da shagalin biki, sannan ga shi Mai martaba ya yi mata alƙawarin zuwa Saudiya, yanzu kuma ciki na ɓulla ya ce sai ta haihu yaro ya yi ƙwari, sai da ta yi kuka ta so ta je Saudiya ta yi ta ibadu tana roƙa ma Baffa gafara a harami.
Allah ya sa ma cikin bai ba ta wahala kamar na Banafsha ba. Shi ya sa har ta samu daman shiga ciki ana ta shirin biki da ita.
Gimbiya Shahida da ya'yanta suna girmamata shi yasa itama ba ta sanya a duk abin da ya shafe su. Islam sun haɗe da Amira da su Hafsat, da yaran Sakeena, Amiran ma wannan shekaran za ta yi candy Hajiya Zaliha suke da biki a zaria ƙanwar mijinta ne Saleem zai aura.
Tun a satin biki suka tafi Abuja, akwai gidan Mai martaba acan suka sauka ana ta shirin biki.
Ango kuma yana Daura sai sun ɗaura aure a zaria za a taho da Amarya Abuja a yi dinner. Saddam na cikin abokan ango shi da Hamma Abdulrahim sun saje da yaran manya nan ma tare da Adda Nauwara ake yin komai tunda suna gari.
Received at 19:42Reactions: ❤ 7, 👎 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Kowa ya ga Ummu Salma ko ba ta faɗa ba sai a ce tana da ciki, ta yi kiba kamar ba ita ba. Gimbiya Shahida na Daura nan za ta yi taron ta sai ranar Dinner za ta taho.
Ammah da Ummin ikki Daura suka fara sauka.
Daga can ne ranar ɗaurin aure suka taho Abuja a jirgi suna isowa ba daɗewa ango da tawagarsa tare da amarya da danginta suka sauka.
An sauketa a ƙayattacen gidanta mai kama da aljannar duniya A daran aka yi wata lafiyayyiyar Dinner a ɗaya daga cikin manyan hall na garin Abuja, an barar da dukiya kamar ba san zafinta ba an ƙure adaka ankon leshi ne amma kowa ya saka kalan na shi Ummu Salma ta yi makeup, duk da ba ta ji daɗi ba Baɗɗo ba ta zo ba saboda jego, Hamma Abdulrahim ƙiri kiri ya ce ba za ta zo ba ga shi ta saka rai.
Bilkisu ma ta zo, yaran ma duk tare da su suka zo suma sun kure adaka, Hanan da Beena sun girma in ka gansu kamar wasu yan biyu, yanzu Mahma suke kiran Ummu Salma tunda suka ji Hanan na faɗa Bilkisu kuma Momi, Lamiɗo kuma Papa, Sultan an girma shekaransa sha biyu yanzu amma yana da girman jiki da tsawo kamar ɗan shekara sha biyar.
Mawaƙa sun zo sun baje kolinsu sun kwashi kuɗi.
Anan ne Ummu Salma ta haɗu da Hajiya Hauwa Inuwa Aminu(Anty Hairi) daga haɗuwarsu suka gaisawa shikenan suka yi ta hira da Ummu Salma, Anty Hairi sune tawagan amarya daga masarautar Zazzau, sai ga shi har suna sharing contanct. Anty Hairi akwai kirki sosai mace ce mai karamci Allah ya kara wadata ya kuma raya mata zuru'a Amin.
Ummu Salma ta tura ma Lamiɗo hoton ta ita da yaran da ta ɗauke su, sai dare ya duba ya tura mata emojin harara. Cewa ya yi sun tafi sun bar shi, ta ce ya zo shima ya ce in ya tafi wa zai bar ma Daura, ta yi ta masa dariya.
Amma ya ce ta yi kyau sosai ya yi kewarta. Ummu Salma ma har videon Bilkisu ta ɗauka a wajen ta tura masa, ita ba ta da wannan Ummu Salma ce komai da ruwan ka, kuma a hakan Lamiɗo ke son kayansa ba Bilkisu kaɗai ba har video ta dinga masa tana tura masa wai kar ya ji kewa shi bai zo ba, gwara ya ji kamar yana wajen shi dai ta saka shi mirmishi kamar wani yaro ƙarami.
Shi dai na shi karɓo aure ne kuma sun je Zaria sun karɓo aure sun dawo Daura.
A garin Abuja suka ci bikinsu suka suɗe, daman ita Ummu Salma Jimeta za su wuce tare da su Ammah, amma kafin tafiyarsu sai da ta je ta gana da Barrister Salamatu Doma.
Hamma Abdulrrahaman ya tura mata lambarta ta kira ta, adireshinta ta tura mata direba ya kaita sai da suka haɗu a a fili sannan ta ga kirkinta da Hamma Abdulrrahaman ke faɗa, sum yi batutuwa sosai ta ba ta shawarwarin yadda za ta tafiyar da ƙudirinta, kuma ta ji daɗin magana da ita sun rabu da cewa za su dinga tattaunawa ta waya in sha Allahu.
Sun bar Abuja 28 ga wata ne, tunda bikin 25 ne aka yi, ta je Jimeta saboda talatin ga wata za su yi class reunion ɗin su kuma yadda suke kiran ta ana buƙatarta a wajen da ta faɗa ma Mai martaba ya ce ta je ba matsala dalilin wucewarta Adamawa kenan amma Bilkisu Daura ta koma, ita kuma Ummu Salma ta taho da yaran Adamawa tare da Harira yar amanarta da duk in da za ta je tana tare da ita Islam na Abuja tare da su Hafsat Daura za su koma ta ce ba za ta je Jimeta ba.
Baɗɗo ta sha takaicin rashin zuwa bikin nan haushin ma ya ragu tunda shi Hamma Abdulrahim bai je Abuja ba daga Zaria gida ya dawo saboda Baɗɗo tunda Ammah bata nan. Ranar reunion ɗin su shigar alfarma Umma Salma ta yi na super wax sai ta naɗa lafaya jakarta da takalminta ma abin kallo ne kama daga kyawawan ya'yanta Hanan da Banafsha ga su Sultan, Harira ce ke rike jaka da Banafsha ga matashin cikinta ya fara fitowa da ya ƙara mata kyau da ƙwarjini.
A toyota ɗin Lamiɗo ta tuka su, zuwa makarantar a can aka shirya taron a babban hall ɗin makarantarsu ta Ahmadu ribaɗu Collage
Kowa a wajen nan Ummu Salma kawai yake kallo da ya'yanta da motar da ta tuƙo, Shamsiya ko duk ta bushe gaisawa kawai suka yi da Ummu Salma, ta ɗauki Hanan tana yi ma Banafsha wasa, wasu sun samu labarin matsalan da aka samu tsakanin Ummu Salma da Shamsiya tunda abin duniya ba ya ɓoyuwa, ana ta kuskus ganin Shamsiyar gefe ko Harira Hadimar Ummu Salma ta fita kyan gani.
Received at 19:42Reactions: ❤ 11, 👍 1, 👏 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ummu Salma ta haɗu da Madeena Jaafar lokacin lokacin suna makaranta sun yi mutumci sosai ta yi aure da yaranta uku tana koyarwa.
An ci an sha an yi hotuna tunda sun haɗa kuɗi Ummu Salma 2M ta ba su, su Hanan sun sha ɗauka kamar yaran turawa. An yi jawabai sosai tare da cewa za a kafa asusu domin tallafawa in wani abu ya taso na biki ko suna ko ciwo a cikin su, an naɗa shugabanin rikon kwarya sai ga shi sun ba ma Ummu Salma matamakiyar shugaba, ta ce ba za ta karɓa ba suka ce sai dai in ba ta so ne shi yasa ta yi shuru. Yanzu duniya in kana da shi kai Sarki ne ta karɓi mic ta yi jawabai anan ta yi maganar za ta buɗe foundation domin tallafawa ma mata da ƙananun yara ana ta mata fatan alheri sun gayyaci wasu malamansu wasu ma duk sun rasu, a jin na su ma an rasa wasu, an fara saka kuɗi a asusun nan take ta saka kuɗaɗe masu kauri hall ya ɗau ihu ana faɗin Allah ya taimaki Sarauniyar Daurama.
Shamsiya na gefe tana hawaye tana mai nadamar biye ma zuciya da sheɗan ba domin soyayyar Habib da ta zama kaddaranta ba, da yanzu ita ce a gefen Ummu Salma tana shawara da ita, amma ga Ummu Salma can a sama an zagayeta ta yi mata nisa, ita ko tana gefe in da take ma in ta ce za ta je ita ce za ta muzanta.
An yi taro lafiya an ta shi lafiya Ummu Salma ba daliɓai ba har malamai sun karɓi lambarta suna mata magana cikin girmamawa, balle mates ɗin su, an karɓi lambarta kamar ba gobe kowa ya na so ya shige mata.
Da za tafi ne ta nemi shamsiya ta ba ta dubu Hamsin tana da canji a cikin jakarta ta tausaya mata ne amma ba domin Habib ta yi ba. Shamsiya har tana hawaye.
"Na gode sosai Ummu Salama."
Kamar ta san suna cikin wani hali, ga kuɗin hayar in da Habiba take, ita ma ba ta lafiya tunda ta yi ɓarin nan lokaci bayan lokaci tana fama da zubar jini tana bukatar zuwa asibiti. Ga rashin abinci, komai dai ya kwaɓe albashinsu ita da Habib ba shi da yawa ba zai iya rike su ba sai ga tallafin Ummu Salma, kuma ta yi mata alkawarin za ta tallafa mata da zaran gidauniyarta ta fara aiki.
Haka Ummu Salma ta shiga mota ita da ya'yanta ta bar makarantar ana ta ɗaga mata hannu. Kowa sha'awa take ba shi, rayuwa kenan wasu a cikin sun yi karatun amma babu aiki yi wasu kuma an yi aure an haɗu da gwagwarmayan gidan miji ga ƴaya a lokacin duk wanda ya ji Ummu Salma ba ta cigaba da karatu ba sai ya ce ita ko me ya sa. ? Suna ganin kamar rashin ilmin da ba ta yi ba zai katangeta da samun alheri cikin su har da Shamsiya domin a baya tana ganin boko shi ne matakin arziki. A wajen suna ta cewa suna bibiyar girke girkenta ba su san ita ba ce sai yau da ta faɗa Shamsiya ta ce itama tana bibiyan Ummu Salma amma ba ta taɓa sanin ita ba ce duk da ranar da fara jin muryan sai da ta ji kamar ta san me muryan.
Yau ga shi Ummu Salma da iya sakandirin tana auren ɗan Sarki ta samu dukkan cigaban rayuwa. Su kuma ga kwalin degree ɗin amma suna cikin kalubalen rayuwa Rayuwar nan ka bi ta a sannu kawai abin da kake tunanin ba zai yuyu ba shi yake faruwa. Ilimi na da amfani amma kar ka dogara da shi, mu tashi mu nema mu dogara da kanmu, in karatun ya yi mana amfani muna da plan B ba za mu zauna jiran Gwamnati ba, yanzu Nigeria ta yi yawa ba zai yuyu kowa ya samu yadda yake so ba. A yi ilimi amma a nemi abin da za a dogara kar a sakankance da boko ce ƙarshen tsira.
*Janafty*
Received at 19:42
15 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ummu Salma ta so su koma Daura first week of January ne saboda yara za su koma makaranta, har sun fara shiri sai kuma Adda Suwaiba ta haihu, Ummu Salma ta san tana da ciki amma ba ta taɓa tunanin cikin ya isa haihuwa ba tunda ba ta da girman ciki sai ko ga shi ta haihu da ta faɗa ma Mai martaba Lamiɗo ta nuna masa tana so ta zauna sai an yi suna ya ce ta yi yadda take so ba zai hana ta ba.
Dalilin tsaikon tafiyarta kenan amma ita Bilkisu ta koma Daura bayan an shiga sabuwar shekara. Islam na can tunda tare da su Hafsart suka koma Daura daga Abuja tana gidan Sarki mai murabus, tare da su Amira da Hafsat tunda Ummu Salma ba ta dawo ba.
Da suka yi magana ta waya Ummu Salma ta ce me ya sa ba ta zauna a masarauta ba tunda Bilkisu ta dawo
"Ya Umma ni fa ban wani saba da Anty Bilkisu ba gwara na zauna anan ga su Amira da Hafsat."
Haka ta faɗa, kuma gaskiya ta faɗa Bilkisu ba ta sakin jiki da kowa, matar nan rayuwarta ma na dabam ne, ba irin na sauran mutane ba ne shi yasa ba ta damun Ummu Salma domin ta fahimci har danginta ba da kowa take shiri ba sai wanda Allah ya haɗa jininsu, ballatana ita kishiya da zuwan ka zo na zo ne. Suna haɗa sati ba su haɗu da juna ba, ba ta shigowa bangarenta itama Ummu Salma ba ta shiga, amma yaran suna zuwa wajenta haka ma Banafsha, su Debora dai suna shigowa barin ma Hidaya, Sabuwa ce sai jifa jifa. Sun fi haɗuwa wani lokacin a bangaren Mai martaba ko kuma in ta je can gidan Sarki gaishe shi ta ganta, tana gaisheta duk in da ta ganta ta amsa a tsume, amma bayan gaisuwa wata mgana mai tsawo bai ta taɓa shiga tsakaninsu ba, miji ɗaya dai suke aure amma rayuwar kowa tsarin shi yake yi, shi kuma Hamma Lamiɗo bai damu ba, ba shi da yawan saka ido, kuma ya san haka suke tsarin su ya yi masa daidai muddin ba a zaman gaba kuma ba a faɗa.
Da niyyar zama ta yi sunan Adda Suwaiba ta tsaya amma kuma kana naka Allah ya gama na shi, mura ta yi mata mugun kamu da ta saka mata zazzaɓi mai zafi, kuma wannan cikin ma ba ta sha ruwan sanyi ba, ba ta yi laulayi mai zafi ba, amai ma sau uku ta taɓa yi ta dai san tana cin abinci sosai shi yasa ta fara kiba da naman wuya.
Ta yi tunanin sanyin December ne ya kamata a garin Adamawa. Har Banafsha ma sai da ta kwanta zazzaɓin nan sai da suka je suka ga likita aka ba su magunguna.
Sunan da ba ta samu ba kenan tana gida a kwance, muryanta har ta dishe ta yi ƙatuwa saboda mura, in suka yi waya da Mai martaba sai ya ce muryansu iri ɗaya yanzu ba maraba ta yi ta masa shagwaɓa tana masa kuka shi kuma yana jin daɗin tsokanarta.
Mami ta zo suna an yi suna lafiya mace ta haifa yarinya ta ci sunan mahaifiyar Adda Suwaiba Zainab, bayan sunan ne Ummu Salma ta yi ma su Mami bayanin haɗuwarta da Barrister Salamatu da shawarwarin da ta ba ta, da cewa sai ta koma Daura in sun sake yin magana da Hamma sai su ga ta yadda za su fara kudirinta kafin