Showing 39001 words to 42000 words out of 45109 words

Chapter 14 - KATANGA COMPLETE

27 Oct 2026

91

zama dole. “

Shukhur

a da Nusrat suka d'ago suka kalli mahaifiyarsu bayan sun gama kallon kayan suka had'a baki gurin fad'in.

"Mama kayan waye to?“

"Naki ne Shukhura. “

"Nawa kuma Mama?“

Ta fad'a ta na kallon fuskar Nusrat kafin ta mayar dubanta kan Maman, ita kuma tai mus

u bayani kamar yadda Baba ya yi mata ta d'ora daa.

"Ba dole za'a miki ba Shukhura, ba kuma za'a tab'a musu kaya ba har sai kun fahimci juna kin kuma aminta da shi, sunzo sun nemi izini ne sun kuma kawo kayan na gani ina so.

Ki tsayar da zuciyarki guri d'

aya, kada dukiyarsu ta rud'e ki ko wani abu na k'yale² idan har bai kwanta miki a rai ba, ki same ni ki gaya mini ni kuma zan gayawa Babanku sai a mayar musu da kayansu a basu hak'uri.“

D'aga kai kawai Shukhura ta yi ta na sunkui da kai k'asa, Mama ta ma

yar da kallonta ga Nusrat tace.

"Yayarsu babu wani wanda ya tab'a tunkararki da zancen soyayya ne?“

Kai tsaye tace.

"Eh babu Mama. “

Shukhura ce tai saurin d'ago kai ta kalli Nusrat d'in yayin da Nusrat d'in ta galla mata harara, ganin hakan da Mama ta

yi ne yasa tace.

"Gaya mini Shukhura waye? In ita kunya ta hana ta fad'a. “

"Babu kowa Mamanmu. “

Shukhura ta bata amsa.

"To shikenan tun da ba za ku gaya mini ba, idan Babanku ya dawo kwa gaya masa, Allah dai ya had'aku da mazaje na gari.“

Suka amsa

da. "Amin." A tare.

Da yamma Hajiya Suwaiba tazo gidan su Shukhura, Mama tai mata tarb'a ta mutumci da girmamawa dai² da k'arfinsu, yayin da Hajiya Suwaiba take ta yabawa da karamcinsu, ta kuma samu sirikartata

💯

.

Kayan kwalliya ta

kawo mata tace ita da 'yar uwarta, don Mustafa yace mata ya na jin fa 'yan biyu ne, Inna kuwa daga jin haka har ta fara murnar za'a haifo musu tagwaye.

Tun daga kan mayuka na gyaran fata babu abinda babu a ciki, godiya sosai Mama tai mata, ta rakata guri

n Iya suka gaisa, Iya yadda kuka san ta gurfana a gabanta tai mata sujjada aikwa da ta tashi tafiya ta ajiye mata then thauthand, murna gurin Iya ba'a magana ta taho filin tsakar gidansu ta na ta rangad'a gud'a ta na shiwa Mama albarka don ta iya haihuwa t

unda ta haifo Shukhura jinin arzik'i.

Umma na d'aki takaicin duniya ya bi ya isheta, wani malulun bak'in ciki ne ke damunta, yanzu ta na gani su Maimuna zasu fandama cikin daula, don had'a zuri'a da Familyn Fanda kamar ka tako arzik'i ne, haka za'a ma

shaheta bora a cikin gidan nan da ita da 'yarta, don Shukhura ba kunya ce da ita, idan ta auri jinin Fanda kanta zai k'ara girma ta kuma taka wanda taga dama, tazo ta na d'agawa k'arshe ma komai na gidan ya dawo hannunta, da ace Nusrat ce ta san ba ta da m

atsala za ta dubeta tamkar mahaifiyarta, Shukhura kuwa babu abinda take hanga cikin idanuwanta banda tsantsar taya mahaifiyarta kishi, idan kwa ta samu wannan power ta riga ta zama sorry a cikin gidan nan daga ita har 'yarta, don haka dole ne ta nemi mafit

a tun lokaci bai nemi k'ure mata ba.

"Wai meyasa kika cewa Mama ba ki da saurayi? Bayan ga Malam Tajo nan kamar zaiyi hauka a kanki kin kuma k'i ki bashi damar da zaizo ya fallasa asirin zuciyarsa. “

"Bazan tab'a bashi damar hakan ba

Shukhura. “

"Saboda me? “

"Saboda girman alk'awari. “

"Hmmm Yayarmu kenan, na tambayeki.“

"Tom Allah yasa na sani.“

"Wai Yaya Rj yace yana sonki ne? “

"A'a baice ba, amman na san ya na dawowa zai gaya mini.“

"Baice ya na sonki ba, amman kike wahala

r da kanki gurin zaman jiranshi, baki da tabbas d'in soyayyarki a zuciyarsa, bacin haka Aunty Maryam ba za ta tab'a bari ki auresa ba, domin Hidaya take da burin ya aura.

Dan Allah Yayarmu kiyi watsi da lamarin Yaa RJ, ki tsayar da zuciyarki guri guda,

kina da samarin nan ki basu dama har ki samu gwani a cikinsu, don ni a ganina Yaa RJ b'ata miki lokaci kawai yake yana kuma wasa da hankalinki, tun da shekara uku yace miki zaiyi ya dawo, yanzu a k'aida saura shekara d'aya kenan amman me Hidaya tace, cewa

tai saura shekaru biyu ya dawo, ke a tunaninki Baba zai barki har nan da shekaru biyu a cikin gidan nan, ko kuma za ki cigaba da nuna babu wanda ke zuwa yace ya na sonki?

Ta yaya kike tunanin zan karb'i lamarin aurena da muhimmanci bayan ke ba kiyi aure b

a, har ga Allah ba na son na yi aure na tafi na barki.“

Hannuwan Shukhura Nusrat ta kama ta rik'e da hannu biyu kana tace.

"Ni yanzu ba lamarin Yaa RJ ne ke damuna ba, akwai abinda ke damuna, kuma shi yake hanani karb'ar soyayyar kowa.

Kada ki damu

da lamarin aurena Shukhura, shi aure lokaci ne, kowa da akwai lokacin da Allah ya rubuta mata, babu ruwansa da wannan yaa ce ko k'anwa duk wacce lokacinta ya yi shikenan, haihuwa, aure da mutuwa duk tafiyarsu d'aya ne suna zuwar maka ne a sanda ba kai zat

o ba ba kai tsammani ba, don haka kada ma ki sake ki saka a ranki don banyi aure ba kema ba za ki ba, kin san Baba ba zai d'auki hakan ba, kar kuma ki amfani da hakan kice Mustapha bai miki ba, za ki cuci kanki ne don ni ba na hango aurena a nan kusa, ina

ji a jikina akwai wasu abubuwa da zasu faru, amman bansan meye su ba.“

"Wani lamari ne ya hana ki karb'ar soyayyar kowa a zuciyarki. “

Wayar Mama ce tai k'ara alamun an kira Nusrat tace.

"Kinga har ya k'araso ba ki gama shiryawa ba, maza kiyi² ki k'aras

a shirin in kin dawo ma k'arasa maganar, kuma ina fatan k'anin nan nawa ya dagargazo miki zuciyarki kafin ki dawo, kizo kiy tai mini hirarsa ina saurare don naga alamun hakan ma tun a waya. “

Murmushi kawai Shukhura ta yi, don har ga Allah muryar Mustapha

ta tafi da ita, sakamakon wayar da suka dunga yi, Maryam k'anwarsa ya turo ta anshi number Mama shine yake kiranta suna gaisawa, burinta kawai ta ganshi a fili don ta na fatan ganinsa ya fi jinsa shikwa ya dinga ja mata aji har sai yau da aka kusa cin sat

i suna wayar sannan yace mata zai zo.

Shi d'inne kuwa yazo, don haka a gaggauce ta k'arasa shiryawa ta fita, Nusrat na ta zolayarta, don sun zamo tamkar wasu k'awaye aminai, don dukansu babu wacce za ta daki k'irji tace ta na da k'awa aminiya sai dai k'a

war da za'a gaisa a

wuce, sune k'awayen kansu, kuma hakan baisa Shukhura ta raina Nusrat d'in ba........

300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.

NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK

In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki tu

ro cikinta.

09037093702

In katin wayane 400 zaku biya.



Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a l

ayina muyi magana.

Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin.

#Team KTG

#N.W.A

[10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH*

Wattpad@Rashuna

https://my.w.tt/Cjpv9nxoJ9?utm_

*KATANGA*





____________

*NINE*



Shukhura ta rasa yadda za ta yi da Iya, don abin nata kullum k'ara gaba yake, don idan taje su gaisa bai bata ko ficika ba samun guri take ta zauna, ranar da tai mata haka kuwa mantawa

ya yi ya fito babu kud'i a jikinsa, ba ta tashi ba har sai da yace.

"Iya a mini afuwa ban fito da kud'i ba yau, amma gobe insha Allah za kiga sak'o. “

Takaicin duniya ya ishi Shukhura ji tayi kamar ta nitse a gurin da take a zaune don tsabar kunya yayin

da Iya kuwa ta wangale baki tace.

"Tom shi kenan jikana babu komi, da yau da gobe duk d'ayane.“

Kunji sai kace ajiya ta bashi, wani d'an iskan kallo Shukhura ta bita da shi a ranta kuwa tace.

'Zanyi maganinki wallahi, yadda ko shi kansa Fandan aka ce

gashi a soro ba za ki fito ba, ke ko govnor garinnan El Rufa'i akace gashi yazo zance gurina ba za kiyi gigin fitowa ba.'

Fuska taje ta siyo me mugun abun tsoro, sai dagurintaa ruwa bayan an idar da sallar asham, dama lokacin ne dai² zuwansa, tun ya

mma da tai wanka ta saka riga da wando dama, don haka sai ta d'auko hijabinta har k'asa ta sanya, Mama dama ta na d'akin Baba don haka sai ta cewa Nusrat.

"Yayarmu bari na fita soro.“

Tace mata.

"Tom. “

Iya na ganin giftawar Shukhura ta fasa tayar da

sallar da za tai, don yau ta makara ba ta samu bin jam'in asham ba wani bacci ne ya kwasheta ta na zaune.

Murmushi ta yi ta ziro silifas d'inta ta biyo bayan Shukhura ta na k'iyasta yau sallamar da za'ai mata me matuk'ar nauyi ce, don ta na bin bashin wa

ncen zuwan.

Shukhura na fita soro ta cire hijabinta ta sak'ala shi jikin k'ofa sannan tai saurin d'aura fuskar ta juya baya.

Bakin Iya ya k'asa rufuwa har ta doso soron, dama soron gidan gashi da mugun duhun tsiya, ko hucewa za kai sai ka haska saboda gu

dun masu lab'ewa, zance ma in zasui sai sun kunna fitila.

"A'a yau kuma ba ku kunna fitilar ba ne? “

Cewar Iya ta na tsayawa a dai-dai tsakiyar soron gidan don ba ta hangar komai kar taje ta taka wani daga cikinsu shiyasa tai maganar don su kunna fitil

a, wani irin dank'a Shukhura taiwa kanta ta had'a fuskokinsu guri d'aya ta sauya magana zuwa me abun tsoro.

"Ke wata iriyar nanatacciyar tshowa ce, mu ba ma son mutum me son abun Duniya, daga yau idan Mustapha ya k'ara zuwa kika fito sai mun karya tsila

tsilan k'afafuwan nan naki masu kama da Babyn roba, kuma mu shanyar miki da b'arin jikinki gaba d'aya. “

Kar kar kar kawai jikin Iya ke yi uwa mazari ihun da taso ta yi ma ta k'asa wani mugun tsoro ne ya shigeta wanda ba ta tab'a jin irinsa ba.

Allahumma

inni auzu bika minal kubsi wal kaba isi, kawai take karantawa a ranta kafin Shukhura ta buga mata razananniyar tsawa had'e da fad'in.

"B'ace mana da gani tun kafin mu mayar miki da k'afafuwanki a sama kanki a k'asa.“

Fitsari ne zirrrr ya fara bin k'afa

fuwan Iya kafin ta juya a guje sai ji kake k'um ta bugu da bango ta dawo baya, wata wahalalliyar k'ara ta saki, ta na so ta rarrafa ta bar soron ma ta k'asa anan ta zube a sume tsabar tsoro da rikirkicewa.

Umma ce ta jiyo k'arar, don haka ta nufo soro

da 'yar fitilarta, ta na haskawa taga Iya a sheme cikin fitsari.

"Subhanallahi.“

Shine abinda tace kafin ta juya taje ta kirawo su Baba, ruwa aka watsa mata ta farka a mugun tsorace ganin su Baba kawai ta fashe da mugun kuka, Baba na tambayarta abinda ya

faru, kawai cewa take su kamata su kai ta gurinta.

Babu yadda Baba baiyi da Iya ba akan ta fad'i abinda ya faru da ita tak'i, k'arshe tace ina ruwansa ya rabu da ita don dole ya k'yaleta

Mama ta dubi Nusrat tace.

"Kika ce Shukhura na soro, ya kuma ba

n ganta ba?“

"To nidai Mama haka na ji tace mini, to ina kyauta zaton ban jita dai² ba tun da banga ta d'auki tabarma ba ma.“

Ta na rufe bakinta Shukhura na sallama Nusrat tace.

"Yauwa ga ma ta nan.“

Kafin su amsa mata sallamar.

"Ina kika je? “

Shin

e tambayar da Mama ta jefeta da ita, sosa kai tai kafin tace.

"Mustapha ne ya kirani gashi a k'ofar gidanmu na fito na anshi sak'o, kuma da na fito ban ganshi ba ina jin zolayata yake, shine muka had'u da 'yar ajinmu muka tsaya muna d'an tattaunawa. “

"Y

a yi miki kyau."

Mama tace mata, Nusrat kuwa ta kafe ta da idanuwa, ita ta san dalilin kallon da take mata akan abinda ya samu Iya ne ta na zargin Shukhuran ce tai mata wani abu, murmushi kawai Shukhura ta yi, don ta san in ta ritsa ta dole ta gaya mata g

askiya.

Tun daga wannan ranar Iya ba ta k'ara gigin fita in Mustapha yazo ba, saboda ita kad'ai ta san azabar da ta sha na jinyar goshinta, shi kuwa da yaga kwana biyu ba ta fitowa shine ya cewa Shukhura zai shiga su gaisa da Iya taje ta gayo mata,

ko da Shukhura taje kuwa, iya tace ba ta san zance ba, ta yiwa Allah ta yiwa Annabinsa tace masa yasha zamansa ta yafe duniya da lahira, Shukhura kuwa tace ai kuwa sai ya zo ta fita ta na dariya Iya ta banko k'ofarta ta saka sakata tace sai dai yazo ya gai

sar da k'ofa alk'ur'an.

Kayan toshi ma da aka kawowa Shukhura k'arara Umma ta nuna bak'in cikinta a gurin, duk da Saminu ma ya yi dai² k'ok'arinsa amman ta raina ta na ta tsine masa albarka, ta na kiransa me kantar talauci, azu

mi kawai take jira ya k'are ayi sallah ta dugunzuma neman mafita, cikin k'udurar Ubangiji akai sallah lafiya aka gama lafiya, aikuwa ta shiga can cikin k'auyen zariya acan ta samo wani malami, ya shaida mata kud'in aikinta dubu ashirin idan har ta kawo du

bu ashirin d'innan to tabbas wannan aure bazai tabbata ba, jiki na rawa ta dawo gida ta sayar da kayan gadonta gaba d'aya ta koma ta kai masa yace to yanzu ta

koma taje ta kawo masa k'asar da Mustapha ya taka, idan ta kawota to tabbas da kansa zai zo yace

ya fasa wannan aure, shi kuma Saminu za mu juyar masa da ra'ayi da kansa zaice ya fasa auran Nimha, kinga daga nan sai mu juyo da hankalin Mustapha kan Nimha.

Farin ciki sosai Umma tai da jin jawabin Malamin, aikuwa ranar da Mustapha yazo ta k'asa ta tsar

e ta na jiran shigowar Shukhura ta yi sauri ta fice ta d'ebo k'asar da Mustapha zai taka, aikuwa ta na ganin shigowar Shukhuran ta yi saurin ficewa ta 'yebo washe gari taje ta kaiwa malamin aikuwa yace ta na kwance za ta ji kyakkyawan labari...

300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.

NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK

In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta.

09037093702

In katin wayane 400 zaku biya.



Garab'asa gareku maso

yana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana.

Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin.

#Team KTG

#N.W.A

[10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *KTG*

Wattpad@Rashuna

https://my.w.tt/Cjpv9nxoJ9?utm_



____________

*TEN*

KWANCI TASHI

Gurin Ubangiji ba wuya, su Shuk

hura har sun yi candy, sati d'aya da yin candynsu aka kawo lefen su.

Akwatina 6 haka Saminu yaiwa Nimha, kuma ya yi iya k'arfinsa kayanta babu kushe ko d'aya, Shukhura kuwa akwatina goma sha biyu dank'are da kaya na alfarma, sark'ok'in daham kuwa zasu k

ai 6 a ciki, nan da nan hankalin Umma ya k'ara tashi, ta fuskanci wannan malamin kawai kud'inta yake ci dole ta canja shik'a.

Wani k'ungurmun boka ta kuma samowa shi ya sanar mata.

"Duk wanda yace miki wannan aure bazai tabbata ba to tabbas yai miki

k'arya, kud'inki kawai yake ci, wannan aure muk'addari ne daga Ubangiji kuma babu makawa sai ya faru, don haka kije ki rungumi k'addarar da tazo miki da hannu bibbiyu.“

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yanzu babu wata mafita? “

" Babu wata mafita i

ndai akan hana auran nan ne, sai dai wani da ban kuma, don wannan ba makawa sai ya tabbata. “

Shiru Umma tai hankalinta in yai dubu ya tashi, yanzu dole ta koma ta d'ebi cin kashi gurin kishiyarta, haka za ta zauna ta na kallon Shukhura na d'agawa da fari

ya ta na auren me kud'i, komai ta yayibo ta kaiwa uwarta ta na zaune kamar jaka, 'yarta kuwa sai dai ta yayibo kantar talaucinsu ta juye mata, ina bazai yuyu ba da sake, to kuma ta ya ya?

Koma ta yaya ne ta bawa zuciyarta amsa daga bisani ta kalli bokon z

a tai magana ya dakatar da ita da hannu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login