Showing 12001 words to 15000 words out of 45109 words

Chapter 5 - KATANGA COMPLETE

27 Oct 2026

110

zuk'ata.

Bayan kammala karatun Shukhura ta taso a hankula ta koma gurin zamansu, tun tasowarta FANDA ke binta da kallo, duk da kasancew

ar ga tsantsar yarinta nan a fuskarta ya na kallo amman kuma ta kama zuciyarsa sosai, tabbas idan ya bari lokaci ya shud'a wani ne zai riga shi mallakarta, don irin su Shukhura ba wanda ake kalla a kau da kai bane, bare nan gaba ta k'ara girma, har ta zaun

a idonsa ya na kanta, a hankali ya sauke idonsa akan wacce ke Kusa da ita, tabbas ya gano

kama a tattare da su ya na kyauta zatan 'yan biyu ne, duk kallon da yake binta da shi mahai finsa Farouq Fanda na lura da shi, ko ma wacce yarinyace wannan tabbas ta

taki sa'a gurin d'an nasa, kallo d'aya idan yaiwa mace to tabbas ta taki babbar sa'a, tun kammala karatunsa yake masa zancen aure amma yake tai masa kwana kwane, amman yau yaga alamun d'an nasa yayi kamu, idan kuwa hakane zai fi kowa farin ciki, bare kuma

mahaifiyarsa ta ji labari da Hajiya Inna, murmushi ya yi ya na gano yadda Inna za ta d'auki zancen.

Kallonsa ya yi har lokacin idonsa na kan Shukhura, wani kyakkyawan murmushi ya saki ya saka bakinsa dai² kunnansa yace.

"Da dukkan alamu dai yau yarona ya

ga matar aure. “

Kunya ce tai mugun kama shi, ashe dai duk abinda yake mahaifinsa na lura da shi, shafa kansa ya yi ya na mai sunkui da kai, shafa kansa Abban nasa ya yi yace.

"Soyayya ta na da kyau yarona, Allah yasa matar arzik'i ce. “

A can k'asan ma

k'oshi ya amsa da

"Amin“

Ya na mai jin muguwar soyayyarta a zuciya wannan shi ake kira love at first sight.

Bayan kammala saukar aka fara kiran d'aliban da sukai na d'aya zuwa na goma don a basu kyauta.

Aysha Abdullahi Ahmad aka fara kira

wacce tai na d'aya sannan aka kira Safiyya Abdullahi Ahmad ita tai ta biyu sai Maryam Farouq Fanda da tai na uku daga haka har aka kai na goma duk aka basu Kyaututtukansu, anan Alhaji Faruoq Fanda ya karb'i speaker yai magana akan ya bawa makaranta kyaut

ar million d'aya, sannan ya bawa Aysha Abdullahi Ahmad da Safiyya Abdullahi Ahmad kyautar million d'aya, saboda yaba k'wazonsu, cikin d'alibai kusan 100 su suka d'au matakin na d'aya da na biyu.

Nan gurin taro ya hautsine kowa na fad'in albarkacin bakins

a, yayin da wasu ke cewa ai kyautar million biyu gurin Alhaji Farouq Fanda ba komi bace kamar biyar haka yake jin ya cire daga aljihunsa.

Iya kuwa sai dashe baki take ta na kuma b'antarar goronta, ta kalli Umma da ranta yai bak'ik'k'irin saboda bak'in cik

in Shukhura da Nusrat, harara Iya ta galla mata tace.

"An dai yi asarar haihuwa, ace duk kyaututtukan nan da ake rabawa babu sunan Nimha ko d'aya, saboda k'wak'walwarta irin ta jaki ce, amma kalli 'ya'yan albarka, gaskiya Maimuna ta iya haihuwa banda kya

ututtukan da suka samo har kyautan million d'aya suka samo mana saboda 'yan arzik'i ne su irin albarka, don ni har ma na fara kasafta nawa kason da za'a bani, na san dai zan samu kamar dubu d'ari biyu, kinga dubu d'ari zan sayi kayan abinci har da su malti

na da madara da su k'wai, da taliyar nan me kanannad'ewa ta gwamnati, d'aya dubu d'arin kuma na ajiye a hankula ina zara ina siyo gasashiyar kaza da youghot ina ci da daddare in tayar da kai, wayyo ai a cikin satin nan ma sai an k'asa gane ni zan canja kal

a saboda cin dad'i, fatar nan tawa da ta fara yamutsewa saboda wahala za ta gyaru, kai Allah dai ya shiwa Maimuna albarka da ta haifo wa'yannan 'yan albarkar, tun da nake ban tab'a rik'e dubu goma ta kaina ba, amman gashi dalilinsu zan rik'e,har dubu d'ari

biyi, ni ban san ma tun tuni me ya hanani nuna musu k'auna ba wallahi, amman duk cikin jikokina Allah na gani na fi son su.“

Duk zubar nan da take ita kad'ai take yinta, don Umma ta bar gurin saukar tun sanda ta fara maganar, saboda ganin za ta d'ora

mata wani bak'in cikin ne kawai, da ta jujjuya ba taga Umman ba itama sai ta nufo gida ta na tafe ta na kuma kasafta dubu d'ari biyun da za'a bata.

Sai kusan k'arfe uku suka baro gurin saukar, saboda an yiyyi hotuna acan, a matuk'ar gajiye d

ukkaninsu suke, don haka ko waccensu sai da tai wanka kafin su kwanta zuwan jiran yamma ta yi, duk da gidan nasu a cike yake da 'yan hidimar saukar.

Da yamma sukai walimarsu anan cikin gidan, kaya iri d'aya suka saka dukansu, Aunty Maryam ce ta d'inka m

usu, itace ma ta d'au nauyin kayan snacks d'in da suka raba a walimar.

Har kusan dare Iya na d'akin Mama tak'i tafiya sai jan Mama take da hira, Mama kwa sai dai tai ta binta da um da umum saboda rashin sabo.

"Aini fa ko, tun tuni dama ina sonki da 'ya'y

anki dama duk makircin shegiyar matar can ne wallahi, kullum ita kenan kawo mini b'atanci akanku, ai gashinan ta haifi yarinya mai k'wak'walwa irin ta jaki, da k'afafuwanta kamar na babyn roba. “

"Uhm“

Mama tace kawai, ta na mik'ewa don jin ana kiran sal

lar isha, in ba sallar ta tayar ba Iya ba za ta k'yaleta da wa'yannan zantuttukan nata mara sa kan gado ba, ganin Maman ta tayar da sallah yasa Iya ta tashi ta fice ta na jifan d'akin Umma da banzan kallo, Umma ta na hangota ta labule a ranta tace.

'Makir

ar mata kawai, insha Allahu k'wandala ba za'a baki cikin kud'in ba inga ta tsiya, ina nan kuma za ki dawo jikina in miki rashin mutumcin da har ki koma ga mahaliccinki baza ki manta shi ba, tsohuwar banza kawai.'

Iya tun ta na jiran shigowar Ba

ba yazo a kasafta kud'in, har bacci yai gaba da ita ba tare da ta sani ba, Baba kuwa sai gurin 11 na dare ya shigo, bayan ya rufe gurinsu ya kirawo Mama da su Shukhura anan ya ke gaya musu.

"Na kai Accaunt number d'ina makarantarku, Alhmdlillh d'azu na j

i kud'inku sun shigo har million d'aya, yanzu me kuke gani za'ai da kud'in?“

Shiru dukkaninsu sukai su na kallon Mama, ganin Maman ba za tai magana ba yasa Nusrat tace.

"Nidai Baba a shawarata kawai ka bar kud'in a Accaunt d'inka, in yaso sai a 'yebi w

asu daga ciki a siyo kayan abinci, duk wata lalaura da za ta taso sai a magance da kud'in ko kuwa? “

Ta fad'a ta na kallon Shukhura.

"Eh Yayarmu, nima hakan nake shirin fad'a kika riga ni. “

Murmushi Mama ta yi, ta na mai yabawa da hankalin yaran nat

a, kuma taji dad'in abinda suka ce da mahaifin nasu tace.

"Na ji dad'i matuk'a da abinda kuka yanke, dama nak'i maganane don na ji ta bakinku, ku tashi maza kuje d'aki, Allah ya yi muku albarka. “

"Amin.“Suka amsa a tare suka tashi suka fita, bayan fitar

tasu Mama ta kalli Baba tace.

"Ta bakin nasu nima zanyi, ka d'ebi wasu kud'in ka siyo mana kayan abinci, kabar ragowar a asu sun naka, in yaso duk abinda aka d'an samu sai ka dinga ajiye su, saboda kwanan nan za ka ji auran yaran nan ya tashi, kuma duk

su ukun nake magana, don Nimha da Shukhura sun fi Yayartasu gab'b'an girma, in suka jero sai ka rantse itace k'aramar su, shiyasa ma ita Yayartasu d'in ba saurayin da ke zuwa gurinta, sab'anin Nimha da Shukhura, bare ma Shukhura babu ranar banza da ba za'

a zo ace ana sallama da ita ba, sai na tursasa ta take fita, sai tace ai wai ita Yayarsu ba ta zance. “

"Da gaskiyarki Maimuna, nima ina tunani idan akace mini auran yaran nan ya taso, duk dai da Allah na dogara shi na mik'awa lamurana, tabbas kuma da ace

Nusrat na da tsayayye a yanzu zan aurar da ita, tunda ta yi candy tai sauka me kuma za'a jira, amnan tunda babu sai muyi rok'on Allah ya kawo mata na gari, su Shukhura kuwa babu zancen ai yayarsu ba ta zance, shi aure ai lokaci ne ba'a jiran sai yaya tayi

sannan k'anwa za tayi, duk wacce ta samu miji zan aurar da ita, fatana dai Allah duk ya had'a su da mazaje na gari, kuma na ji dad'in shawararki hakan kuma za'ai Allah ya shiga lamarinmu ya kuma dafa mana. “

Mama ta amsa masa da.

"Amin. “

3

00 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.

NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK

In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta.

09037093702

In katin wayane 400 zaku biya.



Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta s

ayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana.

Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin.

#Team KTG

#N.W.A

[10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH*

Wattpad@Rashuna

https://my.w.tt/Cjpv9nxoJ9?utm_

*KATANGA*



____________

*EIGHT*



Tun kan ta k'arasa soro k'irjinta ke dukan

uku² shikuwa Mustapha alamun tafiyar da ya jiyo ne yasa shi k'urawa k'ofar da za ta fito ido, sai da ta janyo mayafinta ta rufe fuskarta kafin ta tako a hankali zuwa gurin da akai masa shimfid'a da tabarma zuciyarta na harbawa da gudun gaske, can gefe da s

hi ta samu ta zauna ta sunkui da kanta k'asa kafin tace.

"Ina wuni.?“

"Nima ban ganshi ba, tun da dai ba ajiyarsa kika bani ba, idan kwa kina son na amsa miki to ki tabbata kin yaye rufin da ya Katange mini kyakkyawar fuskar da nake da muradin kallo a ko

da yaushe. “

K'asa ta kuma yi da kanta ta na murmushi.

"Please nidai a taimaka mini, yau kusan sati guda rabon da na ganta, tun a ranar da ta samu babban guri a zuciyata, idanuwana suka aminta da ita, suka tabbatar da itace sanyinsu kuma haskensu.“

"To

aini kunya nake ji."

Ta fad'a kamar a shagwab'e.

"Idan kika sShukhuraki cikin nawa za ki daina jin kunyar. “

'Cif, na ma kasa bud'e mayafina na ganshi, duk da zuciyata da take ta azalzalata na gansa shine har zan saka idona cikin na, hod'ijam aikam d

ai sai dai kar na daina jin kunyar'

Muryarsa ce ta dawo da ita daga d'an k'aramin guntun maganar zucin da ta tafi.

"Zan fa zo da kaina na cire mayafin gaba d'aya wallahi idan har ba ki d'aga sa ba.“

'Cif saboda kai d'an ikka ne haka kawai ka ciren may

afina, hod'ijam aikam dai da kaga tsigalewa.'

K'irjinta ne ya buga, zuciyarta tai wani irin harbawa yayin da ta jisa ya matso dab da ita.

'Laa kaddai ciren mayafin zaiyi kuwa, na shige yau na had'u da mara kunyar mutum.'

Da sauri ta yaye mayafin da ke f

uskarta, wani kyakkyawan murmushi Mustapha ya saki da yayi sanadiyar motsawar zuciyar Shukhura, wani fitinannen kyahu ta gani a tattare da Mustaphan wanda ba za ta iya bayyana muku shi ba saboda tsabar rud'ewa da cikar kyahunsa.

Gira d'aya ya d'age mata h

ad'e da fad'in.

"Na miki ne? “

Lumshe idanuwanta ta yi don jin bak'on yanayin da ke sauka a ilahirin jikinta, ta d'au tsayin lokaci a haka yayin da shi kuma yake morewa kallonta son ranshi.

Hira suka d'an tab'a kad'an, k'ofofin zuciyar Shukhura su

n bud'e gaba d'aya suna d'iban sak'onnin da ke samun babban matsuguni a cikinta, da ya tashi tafiya ya dubeta yace.

"A taimaka mini a tura mini hotunan da zasu dinga d'ebe mini kewa. “

Ya fad'a ya na me mik'o mata kyakkyawar wayarsa kamar shi, ta fuskanc

i yadda yake me kyau haka komai nasa yake me kyau.

"Aini bana da hoto ko d'aya.“

"Ko a wayar Yayarmu ne a d'an samo mini mana. “

Don a d'an hirar nan da sukai ta ambaci Yayarmu ya kai wajen sau nawa, anan ya gane da wacce take zaune kusa da ita yai tuna

nin 'yan biyune itace Yayarmun, kuma ya fuskanci akwai soyayya me matuk'ar girma a tsakaninsu.

"Yayarmu ba ta da waya ai. “

"Kawai dai rowa za ki mini, tom shi kenan a gaishe mini da su Mamarmu da Yayarmu da kuma k'annenmu. “

"Tom shikenan zasu ji insha

Allah, nima a gaisar mini da so Hajiya, da kuma Hajiya Inna.“

Dariya ya yi had'e da fad'in.

"Hajiya Inna za ta ji da kyau. “

Tunowa da ya yi darun da ta saka da Hajiya ta sanar mata su Shukhura ba 'yan biyu bane, Hajiya Inna har da kuka don ita har ga

Allah ta saka ran samun tattab'a kunnenta 'yan biyu da zasu dinga sanyata farin ciki, sai da Hajiya ta lallab'a ta tace ai ba dole sai 'yan biyu ne ke haifar 'yan biyu ba, sai kiga ma 'yan biyun basu haifa, ita kuwa idan da rabo sai kiga ta haifa mana, Haj

iya Inna tace.

"To Allah yasa, amma 'yan biyunne suma suna tafiya da gado, shiyasa na fi samun tabbacin da 'yan biyu ce za ta haifa mana 'yan biyu.“

Zaune suke suna fuskantar juna da wani kyakkyawan bafulatani hannuwanta ya rik'o yace

.

"Yarinyata hak'ik'a ke haske ce a cikin rayuwar TURAKI ke za ki masa Katanga da damuwar da yake ciki a yanzu, za ki zame masa alkhairi, farin ciki, kuma madubin rayuwarsa.

Hak'ik'a Turaki ya na cikin matsananciyar damuwa, kuma ina da tabbacin kece

kad'ai za ki iya fiddashi daga ciki, kece za ki d'ora murmushin da ya dad'e da barin kan fuskarsa, ina mai kuma tabbatar miki ke haske ce cikin rayuwarsa domin kece kad'ai za ki yaye duhun da ke lullub'e da shi. “

"To ta ya'ya kake ganin zan zame masa has

ke bayan ban sanshi ba ban san a ina yake ba, ban kuma san a ina zan same sa ba. “

"Nima ban sani ba, amman kuma ina so ki mini alqawari guda d'aya. “

"Wani alqawari ne ka fad'a ina jinka, zan cika maka shi domin ina maka kallo tamkar mahaifina. “

Shafa

kanta ya yi had'e da fad'in.

"Na yi matuk'ar farin ciki yarinyata, Allah ya yi miki albarka.“

"Aminnn, ina jinka gaya mini alqawarin.“

"Kada ki bud'e k'ofofin zuciyarki ga kowa bare har ki basu muhalli, har sai lokacin da zai bayyana gare ki sai ki b

ashi gurbi a ciki ki kuma rufeta gaba d'aya, idan kwa ba haka ba akwai wani abu da zai muku Katanga a tsakani. “

"To amma. “

"Ba na so kice komai, tun da kin riga kin amsa mini tun a farko. “

Shiru tayi, ta na son ta sanar da shine ta riga ta yiwa wani

wannan alqawarin, gashi kuma ya katseta, yanzu ya za ta yi, meye mafita gareta?

"To meye alak'arka da shi, kuma meye sunansa na gaskiya? “

"Kafin na amsa miki tambayar zan sanar da ke ba za ki sake ganina ba daga yau, kuma ansar wannan tambayar da zan b

aki itace maganarmu ta k'arshe.

D'ana ne shi, amman kuma mutuwa tai mana Katanga a tsakani tun shud'ad'd'an zamani, sunansa na gaskiya ALIYU ana kiransa da Aa............

Girgizata Shukhura ta yi had'e da fad'in.

"Yayarmu.“

Wanda hakan ya yi

sanadiyar farkawarta daga baccin da take wanda tai mafarkin nan a ciki.

"Mtsss kin kama kin tashe ni, gashi ban samu ya fad'a mini sunan da ake kiransa da shi ba yadda in ya bayyana gareni zan ganesa, gashi yace daga yau bazan kuma ganinsa ba. “

Ta fad'

a ta na me jin haushin yadda Shukhura ta katse mata mafarkinta ba tare da an gaya mata sunan da ake kiransa da shi ba, to kuma da yake ce masa Turaki waye ke kiransa da hakan?

Oho ta bawa kanta ansa.

"Kiyi hak'uri, Mama ce tace na taso ki ki k'arasa wa

nke-wanken yankewa na yi a hannuna in omon ya shiga zafi yake mini kuma bakwan ta kusa da kikace a tashe ki, to amman kuma waye kike kiran ba'a gaya miki sunan da ake kiransa da shi ba? “

"Mafarkin da na gaya miki ina yi ne Shukhura, gashi kuma yace daga

yau ba zan sake ganinsa ba, bansan ta inda zamu had'u da Turaki ba Shukhura kuma ban san da wata alama zan ganesa ba. “

"Yayarmu na gaya miki fa ki watsi da lamarin mafarkin nan na ki mafarki fa ba gaskiya ba ne. “

"Wani mafarkin gaskiya ne Shukhura, do

n na ji ance wasu malaman sunce duk mafarkin da za kayi shi da daddare ka sake yinsa bayan sallar asuba gaskiya ne, wannan dalilin ne nake jin nima nawa gaskiya ne, kuma ina jin hakan a jikina.“

"Wai Shukhura Ina Yayar takun take ne.”

"Gani nan Mama. “

Nusrat ta fad'a had'e da ficewa daga d'akin Shukhura ta bita da kallo.

Washe gari Mustapha ya dawo ya kawowa su Shukhura ita da Nusrar wayoyi sababbi fil a kwalinsu sai walwali suke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login