Showing 24001 words to 27000 words out of 45109 words
nuna ba'a son Nimha, hakan yasa suma suka d'auki dukkanin tsana suka d'ora akan Nusrat.
Nusrat Fara ce, amman
farinta mai duhu ne, fuskarta siririya ce mai d'auke da siririn dogon hanci, idanuwanta suna da girma matsakaici masu shape d'in k'wan k'walati, cikin idonta fari ne tas ruwa ya kwanta a cikinsa mai maik'o, k'wayar idonta kuwa bak'a ce me silkin brown a ci
ki, bakinta d'an madai daici ne haka zalika lab'b'anta basu da wani tudu, ko ya ta motsa bakinta wani siririn dimple ne ke bayyana a gefen kumatunta na tsaye wanda yake k'ara fito da zallar kyahunta.
Shukhura kuwa fara ce k'al, suna yanayi da Nusrat, amma
n ta fi Nusrat kyau, kina ganinta kai tsaye za ki kirata kyakkyawa, saboda ita ko ba tai murmushi ba kumatunta a lotse yake, kuma nata irin na kwance ne.
Yusra ma fara ce kamar Shukhura, itama ta na yanayi da su, amman kuma ba ta da dimple.
A yanzu shekarun Nusrat goma sha biyar a duniya, ta na sss1, su Shukhura kuma shekarunsu goma sha hud'u suna jss 3
auta Yusra kuma shakarunta tara a duniya ta na aji hud'u a primary.
Allah ya yiwa Malam rasuwa shekaru hud'u da suka wuce bayan ya yi jiny
a kad'an, kowa ya ji babu dad'i domin anyi babban rashi mai girma, musamman Nusrat, bayan mutuwarsa ne kuma soyayyar da Abdullahi wanda yanzu suke kira da Baba yakewa Nusrat ta fara bayyana, don har ga Allah ya fi k'aunarta ya na b'oyewa ne saboda kada ya
kuma janyo mata bak'in jini.
mutum ne me wadatar zuciya, ba wani k'arfi ne da shi ba sai dai rufin asiri na Ubangiji, don sun wuce cin yau da na gobe a gidansa, haka zalika bai bar iyalansa a wulak'ance ba, a ko da yaushe za ka samesu cikin kyakkyawar k
amala.
Shamsu ya yi aure da matarsa Fiddausi da d'iyarsu Amima sa'ar yusra, sunanta na gaskiya Zainab, shima Iya ya yiwa takwara, a kaduna suke a zaune a saboda anan ne yake aiki, ya ninka yayan nasa sosai a fannin dukiya wanda k'arara Iya k
e nuna banbanci tsakaninsu da Baba.
Aunty Maryam kuma mijinta ya koma kano da aiki don haka ya d'ebe su suka koma kano da zama, 'ya'yansu hud'u yanzu, Hidaya, Abdul, Hibba, Abbas, suma sosai Iya take ji da su saboda suma mahaifinsu na da kud'i, kuma ana
i mata aike akan kari.
*Wannan kenan*
300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.
0567838462
NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK
in kuma katin waya ne ki turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta.
09037093702
In katin waya
ne 400 zaku biya.
Garab'asa gareku masoyana, duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana.
Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana.
#Team KTG
#N.W.A
[10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH*
Wattpad@Rashuna
*KATANGA*
____________
*TWO*
Yau ta kama lahad
i, duk da suna cikin hutun makarantar boko, su Nusrat duk sun tsefe kawunansu zasu kitso, sai da Nusrat ta fara wanka ta yiwa Yusra ma ta wanke mata kanta ta taje ta shafe mata shi da mai sannan suka shirya zasu tafi, kallon Shukhura Mama ta yi da ta saka
hijabi zasu tafi tace.
"Ke yanzu ba za ki wankan ba haka za ki bisu?“
Sai da ta fara turo baki gaba kana tace.
"To Mama nan da nan d'in sai na yi wanka, abinda yanzun nan za'a mana mu dawo. “
"Allah ya shirya. “
Mama kawai tace ta na mik'awa Nusrat
kud'in kitson nasu had'e da fad'in.
"Ta fara yi miki kitson, kuma tai miki manya don kinsan yadda yawan kanki yake, kuma ke zan barwa girkin dare don fita zan yi, saura kuma kice a fara yiwa Yusra don na san hali. “
Murmushi Nusrat ta yi, bayan ta saka
hannu biyu ta anshi kud'in kana tace.
"Mun tafi.“
Maman tace.
"Allah ya tsare, ku dai yi addu'a kafin ku fita. “Tace.
"Amin, tom insha Allah.“ Tare da jan hannun Yusra suka bi bayan Shukhura da ta fita tun d'azu.
Har sun d'an gota gurin Iya
ta hango giftawarsu da sauri ta k'walowa Nusrat kira.
"Ke ke A'i zo nan. “
Da yake haka take kiranta tun ma Malam na raye, juyowa Nusrat ta yi, Yusra ta turo baki gaba tace.
"Wallahi na san aiki za ta sakaki, kawai kizo mui tafiyarmu mu rabu da ita.“
M
urmushi Nusrat ta yi tace.
"Bara dai naje na ji kiran da take mini.“
"Tak'i ta rabu da ni d'in, shegiya ifrituwa me zunb'utun baki. “
Suka jiyo muryar Iya daga ciki, kuma turo baki Yusra ta yi ta na hararar gurin kafin ta fice waje da sauri, Nusrat kuma
ta nufi gurin Iyan ta na murmushi.
Gyaran d'aki tace tai mata da wankin band'aki sai 'yan tsunmokaranta ma da tace ta wanke mata.
Kallon Shukhura Nana me kitso ta yi tace.
"Ina su Yayar taku?“
"Ga sunan suna hanya. “
"To shiga ci
ki, gani nan bari na k'arasa sharar nan. “
Rufe bakinta kenan Yusra ta yi sallama, kallon ta Shukhura ta yi bayan ta amsa sallamar ta ta tace.
"Ina Yayarmun?“
"Ba Iya ce ta kirata ba, har ta na ce mini ifrituwa. “
Wani haushi ne ya kama Shukhura, ta
zura takalminta ta fasa shiga d'akin ta fice a fusace Yusra ta biyo bayanta.
Kamar an jefota ta shigo ta na kallon Nusrat da ke zubar da shara.
"Sannu"
Tace mata, kafin ta shige zuwa gurin Iya, iya na ganinta ta d'aure b'arin goron da ta b'anta
ra a gefen zaninta kana tace.
"To rasa kunya b'eran tanka, kinzo kimin rashin kunyar taki ne? “
Kar katar da kai Shukhura ta yi tace.
"Ashe 'Yar aljanu na da rana tun da har an iya sakata aiki, me yasa ba ki kirawo 'yar lelen taki tai miki ba sai ita za
ki saka, amma in abu zaki bayar babu wanda ke gabanki sai Nimha, amman in aikine sai wacce kika raina, don kin san Nimha ko tsintsiya ba za ta iya d'aga miki ba.
Bayan kuma kitso zamu je kina gani kuma Mamanmu na zaman jiranmu“
"Tunda dai ba ke
na saka ba, ki shige ki bani guri, kiyi can da rashin kunyarki. “
Cewar Iya
"Waa aini kin san abinda bazai tab'a yuyuwa bane, don wallahi bazan bautawa wanda bai san ina yi ba, in cin mutumci ne ya taso azo a tarkace mini, lalalala wallahi, itama ita
taga za ta iya.“
"Ni kikewa cin mutumci Safiya, Allah ya dawo da Audu, wallahi za ki gane Ubanki na haifa. “
"Amin, ya dawo d'in ki gaya masa, wallahi duka d'aya yamin kinsan sai na bi ta inda zan rama, Allah ya baki sa'a. “
"Wai da sa'ar ki kikeyi ne
Shukhura?“
Cewar Nusrat ta na kallonta, ba ta bata amsa ba ta fice ta na zunb'uro baki, Iya kuwa k'ifi² ta yi da ido tunowa da ta yi sanda ta saka Nusrat a gaba ta na zaginta Shukhura ta amshe ta hayayyak'o kamar za ta daketa har sai da Mama ta fito ta ki
kkifawa Shukhura mari, shine Baba ya na dawowa Iya ta kwashe ta gaya masa, aikwa ranar Shukhura ta sha duka gurin Baba, ita kuwa ta d'auki aniyar wallahi sai ta rama akan Iya, sai da ta bari duhu ya yi ta kad'a karkashinsu me yauk'i taje ta zuba a band'aki
n Iya,don ta na da tabbacin yanzu za ta fito ta shiga band'akin ta lab'e a bayan k'ofa, Iya na shiga ta yi sufa ta fad'i Shukhura ta fito ta na ta k'yak'yata mata dariya, tace mata kad'an ta gani muddun ta na sakawa Baba na dukanta, Iya kuwa jiki yai tsa
mi da k'yar ta iya mik'ewa.
"Yanzu Mama kina kallo ga Iya can ta saka Nusrat aiki.“
Shukhura ta fad'a ta na turo baki gaba. “
"To meye, don ta sakata aiki?“
Mama ta fad'a ta na cigaba da tankad'en da take.
"Amma Mama kefa kikace a fara ma
ta kitson saboda za ki bar mata girki.“
"Yanzu kuma na fasa ba, kije ke a fara miki sai ki baro Yusran a can in Yayar taku tazo sa taho tare sai ki karb'i girkin na samu na fita. “
"Amma Mama....“
Dakatar da ita Mama ta yi had'e da fad'in.
"Ban san jin
komai ki shige kije kiyi abinda na saki. “
Fita ta yi ta na tutturo baki Mama ta girgiza kai had'e da fad'in.
"Allah ya shirya. “
Sai da Iya ta kinta tanci dawowar Baba ta fito babban tsakar gida ta k'wama kujera ta na jiran dawowar
sa, aikwa ta na jin sallamarsa ta saki kuka me k'arfi, a gigice ya nufota ya na tambayarta.
"Lafiya Iya, me ya faru kike kuka haka?"
Face hanci Iya ta yi tace.
"Wai ni yau A'i za ta kalli tsabar idona ta zageni ta uwa ta uba. “
" 'Yar baiwa.“
Baba ya
k'wallawa Nusrat kira, Nusrat da ke d'aki tun da ta dawo daga kitso kanta ke ciwo shine ta nemi guri ta kwanta, ta na jiyo abinda Iya ke cewa Baba gabanta ya yanke ya fad'i, da ta ji kwa ya k'wallo mata kira nan da nan idonta ya yi rau-rau zai fidda ruwa,
a hankali ta mik'e ta fito ba tare da ta amsa kiran ba, kallonta Shukhura ta yi da ke kwashe tuwo ta cika k'atuwar kula ta kai d'akinsu, tace.
"Kinga dai da abinda ta saka miki ko? kuma wannan ba shi zai hana gobe idan tace yimin kaza kiyi mata ba. “
Ba
tace mata komai ba sai juya idonta da tayi da ya fara fitar da ruwa ta nufi tsakar gidan, Shuk'hura kuwa taci gaba da kwashe tuwonta ta na mamakin sanyin hali irin na Nusrat, ta yi k'wafa a hankali, a ranta tace.
'Iya kenan, ai gara ki tab'ani akan ki ta
b'a Yayarmu wallahi, don ba ki son son da nake mata bane.'
Baba na ganin ta taho a sanyaye ya saki murmushi had'e da fad'in.
"Taho mana 'yar baiwa. “
Ganin murmushi akan fuskar Baban nata yasa ta samu k'arfin guiwar k'arasawa gareshi, bak'ar le
dar hannunsa ya mik'a mata, me d'auke da d'ata manya-manya kasancewar yasan ta na matuk'ar son d'ata, kana yace.
"Ga masoyin naki.“
Murmushi me sauti ta saki tace.
"Na gode Babana. “
Baki galala Iya ta saki ta na kallonsu daga bisani ta tafa hannuwa
tace.
"Yau naga lalacewa ni Asabe, yanzu ina gaya maka abinda yarinyar nan ta yi mini amma kai d'ata ka d'auka ka bata, gani ni wacce na yi silar zuwanka duniya ka san da cewa ina mutuwar son ka'za amma baka tab'a siyowa ka bani ni kad'ai a gidan nan ba,
sai dai ka siyo gaba d'aya aci, amman ita da yake shafi da mai ce ka ware ta cikin 'yan uwanta uku, ture biyunma tunda su cikinsu d'aya ai ko Nimha ka siyowa don gudun fitina.“
"D'atan da na siyo mata na tabbata ba za ta cishi ita kad'ai ba, rabawa
zasui gaba d'aya da ita da 'yan uwanta, zancen kuma Nusrat ta zage ki wallahi Iya ko jikina duk kunne ne bazan tab'a yadda za ta iya zaginki ba, ko da kuwa dukan mutuwa kikai mata a cikin gidan nan, bare kuma na san halinta ba sawa ba fitarwa, da dai Shuk
hura kika ce to tabbas wannan zan yadda amma 'yar baiwa
lalala, sai dai kice Shukhura ce ta zageki kikace 'yar baiwa ce saboda.... ”Da sauri Iya ta dakatar da shi da fad'in.
'Ni wallahi bance maka Safiya ba, ko sunanta ban ambata a gurin nan ba in ba yanz
u ba, jama'a ko kunji na ambaci Safiya? “
Ta fad'a da k'arfi yadda 'yan ciki zasu jiyo ta, murmushi Baba kawai ya yi ya ja hannun Nusrat sukai ciki.
"Kedai Mero kin haifi jarabar aljanu a gidan nan, yarinya ta bi ta zamar muku masifa duk kunfi k'aunar
ta cikin 'yan uwanta, su kuma hakan ko kad'an hakan ba ya damunsu, wannan wata iriyar musifa ce?
Kai kuwa Audu k'atuwar asara ce ta hau kanka don zan iya dafa qur'ani kafi son wannan 'yar aljanun ko nace 'yar ruwa akan ni da na diroka duniya, bacin haka h
ar maganata za ka k'aryata ka zab'i d'iyarka, babu komai ai gobe Shamsu zai zo garin, Allah sarki d'an albarka na san gobe miyarmu da ka'ji zan cisu har na ture, don ni ina jin idan yazo ma tattara kayana zan na bisa, don wallahi na gaji da cin shinkafa 'y
ar hausa da tuwon garin masara kullum suna cushe maka a ciki, don na ji ana rad'e rad'en tuwon masara gini yake a cikin mutum, haka kawai na zauna naje na kashe kaina tun wa'adina bai cika ba. “
Sai misalin k'arfe takwas Mama ta dawo, kallon
Nusrat da ke kwance ta yi tace.
"Ina Mamana, Yusra taci abinci da kika barta tai bacci?”
"Cikin gida tace mini za ta shiga tun d'azu, Yusra kuma sai da taci abinci tukunna tai bacci. “
"Lafiyanki kuwa naga kina yatsina fuska? “
Ta tambayeta duk da a
ranta mamakin wai Shukhura ce tace ta tafi cikin gida, bayan ba k'aunar zuwa gidan take ba, aike ma da dole take shiga.
"To ki tashi ga fura na taho miki da ita kisha sai ki sha magani.“
Da hanzari ta mik'e don dama yunwa take ji kuma har ga Allah ba ta
k'aunar cin tuwon donma ta d'an ci d'atan da Baba ya kawo mata duk da wasu sunce shima ya na faifaye ciki, ita kuwa Mama sanin halin d'iyar ta ta yasa ta yo mata guzurin furar.
Sauke idanuwanta ta yi akan kular tuwon da Shukhura ta ajiye, a fili
tace.
"Allah ya shirya mini ke mamana. Maza Nusrat ki gama kije ki kira mini ita. “
Ta na rufe bakinta ta jiyo sallamarta suka amsa mata.
"Laa Mamanmu kin dawo ashe? sannunki da dawowa. “
Fuska a had'e tace.
"Yauwa, me kika je yi cikin gida? “
"Nifa
ba cikin gida nace mata zanje ba, gidan su Farha nace mata za ni kallo.“
Takai k'arshen maganar ta na kallon fuskar Nusrat.
"Ban hana ki zuwa kallo ba?to da Babanku kawai zan had'aki na huta, Ke kuma ai ga shinan kin rufa mata asiri ta tonawa kanta. “
Takai k'arshen maganar ta na kallon Nusrat, yayin da ita kuma ta saki murmushi.
"Kiyi hak'uri Mamanmu bazan sake ba. “
"Sau nawa kina fad'in haka? “
"Allah da gaske nake Mamanmu daga wannan bazan sake ba. “
"To wancan uban tuwon da kika ajiye da fatan
abincinki ne na sati guda ko?“
"Haba² Mama, sai kace wacce uwarta ta tsine mata duniya ta juya mata baya zan jera sati guda ina cin tuwo, tuwonma ba sabo za'a dinga yi mini ba. “
Mama ta so yin dariya amma ta kanne tace.
"Koma me zaki ce kice, amma w
ancen tuwon sai kinyi sati kina cinsa a gidan nan tun da ke kunnenki na k'ashi ne ba ya jin magana, bacin sau nawa zance ki daina cika mini kula kina kawo mini d'aki? “
Sai da ta fara turo bakin nan gaba kana tace.
"To kina dai kallo duk ran girkinta sai
ta cika kula fam ta kai d'aki, bacin daga ita sai 'yarta d'aya kamar rai, mu kuwa ta milliro mana, ta cikawa Baba da sirikarta kwano, nima kuwa yau na rama na millira musu na millirawa Iya ma, Baba kuwa na cika masa kwano har ya na zuba. “
Salati Mama t
a yi ta saki baki ta na kallon Shukhura.
"To don ita ta na cika kula ta kai d'aki ita ta shafa, sune mayunwata ba mu ba, ga shinan yanzu kin sakani a bakin duniya, tijarar Iya ma kad'ai ta isheni, don cewa za tai ina sani na baki girkin shiyasa har ga A
llah ban son na bar miki girki na fita. “
"A to don wallahi muddun ni nai girki bazan fasa ciko mana kula na kawo d'aki ba, ko ba za muci ba sai dai mui asararsa. “
"Me kika ce?“
Mama ta tambayeta kasancewar k'asa² tai maganar.
"A'a cewa na yi kiyi hak
'uri bazan kuma ba. “
"To zo ki fice mini da kular, kije ki k'ara musu tuwon.“
Ta na jin haka ta saki k'ara.
"Waishhhhhh Mama kashi² ina zuwa ta fice da gudu zuwa ban d'aki, murmushi Mama ta yi a ranta ta na nemawa Shukhura shiriya ta d'auki kular tuwon
ta fita, murmushi ma Nusrat keyi tun fara dramar Maman da Shukhura, don dama sun riga da sun saba......
300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.
0567838462
NABABA FADILA SHU'AIB
GTBANK
In kuma katin waya ne